← Book details Yaudara Da Cin Amana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 8

Sashe 3

Yaudara Da Cin Amana Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

{ *A short and interesting true life story*}
*NA*
*UMMU BASHEER*
*REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart
of reader's
#[email protected]
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
*DEDICATED TO RAHMAT MUHAMMAD RUFA'I NALELE*
*PAGE* *10*~*15*
*Yana* Isa gidan ya tarar da Mama a parlour, cikin ladabi da biyayya ya gaishe ta cikin farin ciki take amsawa, tana tambayar shi ya hanya, can ta Kira JAWAHIR.
Tafiya take cikin natsuwa ta shigo tace"Ya ABRAR Ina yini"
A ciki ya amsa da" lafiya"
Mama tace" Ki kawo mai abinci"
Kitchen ta nufa, yayin da ABRAR ya b'ata fuska yace"Mama bana Jin yunwa fa course sai da naci abinci na fito"
JAWAHIR ce ta fito d'auke da tray, Mama tace"ai tuwo ne nasan kana so"
Cikin murna yace"okay na kwana biyu banci ba, nayi missing tuwon ki Mama"
Duk sukayi murmushi, bayan JAWAHIR ta shiga bedroom ne, Mama ta gyara zama tace"Wai son ya batun maganar mu ne?"
Yace"wani maganar kenan Mama?"
Tace"maganar mu da Kai akan k'arin aure, kana nufin ka manta ne?"
Dafe kai yayi yace"Mama har yanzu dai baki bar maganar ba?"
Tace"Au yanzu Kai ka manta kenan? Haba Son nifa gaskiya Ina son ganin yaran ka shekaru biyu har yanzu shiru ko b'ari, gaskiya Ina son ka k'ara aure" ta k'are cikin damuwa.
Shiru yayi bai ce komai ba can yace"Mama Ina gaya miki ki share wannan maganar ni yanzu aiki ke gabana ba aure ba wanda nayi ma da ana yin Rabin aure to Rabin zanyi"
Hannu ta nuna mai tace"gidan ku, wato rabi ma zakayi ko? To sai Allah yasa ba'a rabin, nifa na gaji da wannan tafiye-tafiyen naka sai ka d'auki tsawon wata biyu baka dawo ba, ya kamata ka dawo da business d'in ka nan"
Gaba d'aya ya rasa mai zaice mata.
Can tace"Kayi min shiru ko sai na had'a ka da baban ka ne tukun za kayi?"
Yace"Dan Allah Mama kiyi hak'uri, Kinga ayuka sunyi min yawa, Kuma ni ba wata wacce nake so, bayan HAFSAT, da kinyi hak'uri da ita"
Cikin fad'a tace"ba wani hak'uri da zanyi, jikoki nake so na gaya maka, idan baka da wacce kake so ni Zan baka mata ka aura"
Har ga Allah Yana son yara, Yana sha'awan su sai dai gaba d'aya shi bai san ya akayi ba duk da baya zargin HAFSAT da yin planning, Allah ne bai kawo ba, yace" shikenan ki zab'a min mata duk yanda kikayi hakan yayi min"
Cikin murna Mama ta mik'e tsaye tace" Kai amma naji dad'i da kace in zab'a maka mata, dama na riga na zab'a maka JAWAHIR a matsayin mata"
Shak'ewa yayi da ruwan da yake Sha Nan ya fara tari, Sannu ta dingayin mai har ya daina sannan da sauri yace" Mama Kika ce kin zab'a min JAWAHIR a matsayin Mata?"
Tace"eh ai kasan mace ta gari zan zab'a maka JAWAHIR yarinyan ce mai hankali da natsuwa nasan zaka ji dad'in auren ta"
Kamar zaiyi kuka yace"Mama yarinyan nan na d'auke ta a matsayin k'anwa ta ce please ki nemo min wata amma ba yarinya nan ba"
Ranta a b'ace tace"me kake nufi ne iye to ba zai yuwu ba ita ce wacce na zab'a maka, ka daina d'aukar ta a matsayin k'anwar ka yanzu Dan ita zaka aura"
Zaiyi magana tayi sauri tace"kayi shiru kawai na riga na gama magana"
Ran shi a b'ace yayi mata sallama ya tafi.
Lokacin da ya isa gida wanka yayi kawai yayi Shirin kwanciya, laptop ya d'auko Yana duba wasu abubuwa.
Cikin wasu nighties masu shegen kyau ta shigo bedroom d'in tare da kwantar da kanta a kafad'ar shi, bai ko kalle ta ba ya cigaba da aiki, can da ta gaji sai ta fara mai wasani, dole ya ajiye aikin ya fara kissing d'in ta dan yayi missing d'in ta kusan two months rabon shi da Nigeria, kissing d'in ta yake you sosai, har ya cire mata kaya, Nan suka Lula duniyar ma'aurata.
The following day
SA'EED na kwance shi da wata budurwan shi, sai Jin Kira yayi a waya da k'yar ya iya d'auka cikin barci, muryan AZEEZA yaji ai da sauri ya zauna yace"Hello baby, lafiya kike Kira na da safen nan?"
Cikin haushi tace"what do you mean? Baka son Kiran nawa ne?"
Da sauri yace"no baby I'm just asking you"
Tace"okay gani Nan zuwa gidan ka yanzu"
A firgice ya mik'e tsaye Yana dukan budurwan wacce ke ta faman barci yace" ke dalla tashi ki tafi yanzun nan"
Bata so haka ba amma ya sata a gaba ta tafi dan idan AZEEZA tazo ta tarar da shi da wata ai ya shiga uku kishin bala'i ne da ita, sai suyi sati suna fad'a shi ko Yana son ta baya son wani Abu na shiga tsakanin su,
Budurwan na tafiya sai ga AZEEZA ta shigo da motar ta gidan, sanye take cikin wani irin Riga da skirt na English wears duk k'irjin ta a waje ga shape d'in duk ya bayyana, tasa wani sunglass da ya rufe rabin fuskar ta,
Rungume juna sukayi suna murmushi, bayan sun zauna ne AZEEZA ta yamutsa fuska tace"Dear I'm hungry, me zan samu?"
Mik'ewa tsaye yayi yace"tell me me kike son ci?"
Kwanciya tayi kan kujera tace" ko Ina son cin wani abu ma bana iya wa I really don't know why?"
Zama yayi kusa da ita Yana shafa fuskar ta yace"you look peal baby meke damun ki kamar baki da lafiya?"
Tace" lafiya na qalau kawai sometimes bana Jin dad'in jiki na"
Yace"oh my sweet love ya kamata kije hospital"
Ta yamutsa fuska tace" I will try and go, amma nifa bana son testing d'in su ne"
Dariya yayi tare da kissing lips d'in ta yace"why are you scared baby? Ya kamata ki daina I'm with you"
Rungume shi tayi suka fara kissing d'in juna, (Wa'izzubila)
Mama ce ta samu JAWAHIR ta fad'a mata cewan tayi mata miji ABRAR, sai da gaban ta ya fad'i course bata tab'a tunanin hakan ba ko a mafarki, Amma kuma ya zatayi dole tayi ma Mama biyayya ko da bata son ABRAR bare kuma tayi k'arya tace bata son shi dan shi namiji ne da duk mace zatayi fatan samu, ya had'u over fans.
Da kanta Mama ta fad'a ma Baba shima yaji dad'i sai dai yace ta bari sai ABRAR ya amince da kan shi, ai ko Nan Mama tasa shi a gaba tace Sam bata yarda ya k'ara wani tafiyar ba sai an d'aura auren shi da JAWAHIR.
Babu yanda zaiyi dole ya amince inda aka sa ranar d'aurin aure nan da wata d'aya, JAWAHIR taji dad'i sai dai ta fuskanci ABRAR ba son ta yake ba, kenan dole tayi hak'uri tayi mai biyayya,gashi kuma dai tana tsoron HAFSAT dan ba shiri suke ba.
B'angaren ABRAR ko ya rasa farin ciki zaiyi ko bak'in ciki, gashi bai san yanda zaiyi ya sanar da HAFSAT ba, Amma ya sanar da SA'EED, shi kanshi yayi mamaki sosai, dan baiyi tunani ba, amma ABRAR ya rok'e shi kar ya fad'a ma HAFSAT.
Tana kitchen ne ya shigo ya same ta yace idan ta gama Yana son magana da ita, tana gamawa ta fito sai wani rangwad'a takeyi, zama tayi kusa da shi, cikin sanyin murya da kwantar da hankali ya fad'a mata abin da ke faruwa na auren shi.
Tunda ya fara maganar ta rasa a wani duniyar take wannan maganar nashi ya mugun razana ta, cikin zafi da bak'in ciki ta tashi tsaye tace" Lalai ka d'ebo ruwan dafa kan ka, aure fa kace? To wallahi Sam ban yarda ba, wannan ai auran munafurci ne aka had'a"
Ran shi ya b'aci sosai yace" su waye suka had'a auren munafurcin? Ashe baki da hankali Koh?"
Cikin zafi tace"ai dole kace haka to wallahi in dai nine mu zuba mu gani, Sam bazan yarda ba, tukuna ma wai JAWAHIR wannan shegiyar yarinyan, mtwwwssss" taja tsaki.
Baya son biye mata kawai sai ya bar gidan.............
*TAKU CE UMMU BASHEER*
[02/01 11:58 am] Sis Ummu Bashir:
*YAUDARA DA CIN AMANA*
Chapter 3 · 0% Book details