← Book details Yaudara Da Cin Amana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 8

Sashe 4

Yaudara Da Cin Amana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

{ *A short and interesting true life story*}
*NA*
*UMMU BASHEER*
*REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart
of reader's
#[email protected]
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
*DEDICATED TO RAHMAT MUHAMMAD RUFA'I NALELE*
*PAGE* *15*~*20*
*HAFSAT ta rasa meke damun ta gaba d'aya wani iri take ji, ita ga babban matsalan ta da ABRAR amma Kuma wai dan rashin imani yace aure zaiyi, to dole ta d'auki mataki dan baza ta tab'a yarda ba.
********************
A guje ta shigo da motar ta cikin gidan cikin tashin hankali ta fito ko parking bata tsaya yi ba, Yana zaune a parlour sai ganin ta yayi ta shigo da sauri ya mik'e yana cewa"AZEEZA meke damun ki?"
Ya rik'o hannun ta ya zaunar da ita, ya sake cewa"come-on baby tell me meke damun ki na ganki a hargitse ne?"
Kuka ta fashe mai da shi, da k'yar ya lalashe ta tayi shiru, sannan cikin damuwa tace"SA'EED daga hospital nake yanzu, doctor ya duba ni yace Ina d'auke da ciki"
A razane ya kalle ta yace"What you mean you're pregnant?"
Tace"Yeah"
Dafe kai yayi, gaba d'aya hankalin shi a tashe yake, he's speechless, duk a rud'e yake, dan duk holewar da yakeyi da mata baya yarda su samu ciki da shi, wata Bata tab'a samun ciki da shi ba sai yanzu da AZEEZA tazo mai da maganar, Kuma gaskiya shi bai shirya tarb'an baby ba bare kuma ba aure sukayi ba to mai zai ce ma iyayen shi ba kai ya ma zama dole a zubar da cikin dan baya buk'ata.
Kallon ta yayi yace"ya akayi Kika bari har kikayi ciki, bayan Kuma kinsan ba aure muka yi ba? Ina ganin kawai a zubar da cikin shine solution kawai"
Cikin zafi tace"Au haka zaka ce? To wallahi bazan yarda a zubar da cikin ba Ina son abuna" taja tsaki ta bar gidan cikin b'acin rai.
Tsakin shima yaja yace"kina k'aryan hauka ne, duk iskanci na bazan so in haifa 'dan zina ba" ya cigaba da danna wayan shi.
A cikin kwana biyun nan SA'EED da AZEEZA basa shiri dan tace ita Sam bata yarda a cire cikin nan ba tana son abun ta, shi Kuma ya dage sai yaga bayan cikin,
Duk suna zaune a dining suna breakfast, AZEEZA da iyayen ta kenan, gaba d'aya cusa abincin takeyi dan wani iri take ji kamar zatayi amai, can dai ta kasa daurewa kawai ta nufa wani sink dake cikin gurin ta fara kwarara amai, hankalin Mommy'n ta a tashe ta nufe ta tana tambayar ta ko lafiya.
Bayan ta gama aman ne Mommy take k'ara tambayar ta, cewa kawai tayi ba komai, hankalin Mommy'n duk ya tashi dan tana zargin ta ko ciki take da shi, Daddy'n ta ko kamar gunki ya tsaya yana fad'in suyi mai bayanin abin da ke faruwa.
Mommy tace"AZEEZA kiyi min bayanin abin da ke damun ki, tukuna ma yaushe rabon ki da yin menstruation?"
D'aure fuska tayi tace" two months kenan"
Ba K'aramin razana tayi ba ai Nan ta rufe ta da duka tana cewa"Kina cikin hankalin ki kuwa? 'Yar banza ki gaya min waye ne yayi miki cikin?"
Daddy ya razana shima yace"Wai me kike nufi ne kina son cemin Daughter na da ciki ne?"
Tace" ciki ne da ita dan alamu ya nuna, Kuma tun ba yau ba nake ganin alaman ciki a tare da ita"
Cikin zafi yace"ke gaya Mana wani 'dan iskan ne yayi miki cikin?"
Idon ta ba alamar tsoro tace"Daddy ai ko mene ne kaine sanadi, shekaru had'u da suka wuce ta fad'a maka ina son aure amma kace sai nayi karatu, to ai ga sakamakon karatun Nan, Kuma SA'EED Wanda ka tsana cikin shine"
Kau ya gaura mata wani irin azababben mari yace"to dan uwar ki idan kinyi ciki ne Dan in yarda kiyi aure to wallahi bazan yarda ba kuma sai an zubar da cikin, karatu Kuma yanzu Kika fara idiot kawai mtssss" yaja tsaki yana huci.
Mommy da sauri tace" Ai ta fad'a gaskiya domin Kai ne silar shigan ta Wannan hali, yarinyan nan ta cire kunya irin na mata tace maka aure take so kace kai Sam baka amince ba, ai ga sakamakon karatun da tayi nan Kuma maganar zubar da ciki bai zai yuwu ba dole ta haihu ka raine yaron tunda Kai ne sanadi"
Tsaki yaja yace" Ciki dai bazan karb'a ba dole a zubar Kuma yana Nan sai kinyi" ya bar gurin.
Cikin takaici tace" Amma dai kin cuce mu kin kuma cuce kanki, shin meye zaki fad'a ma abin da zaki haifa?"
Gaba d'aya bata damu da abin da suke cewa ba, ita tana ma jin wani irin son cikin a zuciyar ta kamar Mai, dan haka ko a jikin ta, haka dai Mommy tayi ta mata fad'a da nasiha.
**************************
HAFSAT gaba d'aya ta daina yin ma ABRAR duk wani abu da ya shafa Mata tayi ma miji, ga massifa da kullum cikin yin shi takeyi Sam bata yarda yayi mata kishiya ba shi ko yace umarnin Mahaifiyar shi zai bi, duk da shima ba wai Yana son JAWAHIR bane amma haka nan zai aure ta.
Tunda ya lura da irin abubuwan da take yin mai sai shima ya fita harkar ta, yanzu haka yayi tafiya sai ana biki saura sati d'aya zai dawo, ba k'aramin tashin hankali HAFSAT ta shiga ba, ko da ya tafi da yake ita da SA'EED basu da tsoron Allah, sai suka cigaba da mu'amala, Allah yayi mana tsari da shaid'an Ameen.
B'angaren AZEEZA ko sai harkar gaban ta takeyi, SA'EED ne ya Kira ta a waya Yana bata hak'uri cewa komai ya wuce, ya yarda zasu raine cikin har yace tazo su had'u a gidan shi. Haka ko akayi AZEEZA taje har gidan shi.
Cikin farin ciki ya rungume ta yace"I really miss you baby"
Kiss tayi Mai a kumatu tace"miss you too Sweety"
Nan ya kawo mata abinci da juice tasha sannan suka yi masha'ar su (Wa'izzubila).
Bayan ta shirya ne sukayi sallama ta tafi gida, da isar ta gida ko 2 hour ba ayi ba sai cikin ta ya fara murd'awa tun tana daurewa har ta fara juyi, Dan ba k'aramin azaba take ji ba, can dai da taga alamar abin gaba yakeyi da rarafe ta Isa bedroom d'in Mommy tana nishi.
Lokacin da Mommy ta ganta hankali a tashe ta nufe ta tare da rik'e ta tana tambayar meke damun ta, da k'yar ta nuna mata cikin ta, can sai jini ya fara zuba sosai, cikin tashin hankali driver ya jasu zuwa hospital, suna zuwa aka karb'e ta, sai bayan kamar d'an wani lokaci doctor ya fito ya shaida ma Mommy cewa AZEEZA tayi b'arin ciki sakamakon wani magani da tasha cikin ya zube, sallati Mommy tayi cikin mamaki.
Bayan sun dawo gida ne Mom tasa ta a gaba da fad'a tana cewa"
ke sai yaushe Zakiyi hankali? Kin sab'a ma Allah ta hanyar yin Zina sannan kin samu ciki kin zubar da shi Kinga kin aikata wani abun shin hakan ya dace kenan? Da ace kin mutu fa mai zaki fad'a ma Allah ranar tashin k'iyama hakan kin yi dai-dai kenan? To wallahi ki tuba ki nema gafarar Allah, ki yawaita addu'a da istighifar, a matsayina na mahaifiyar ki babu abin da zance miki da ya wuce hakan" nan ta tashi ta bar gurin.
AZEEZA ko bata d'auki d'aya daga cikin maganar Mommy ba domin haushin Mommy ma taji, a tunanin ta tana takura mata ne, tunani tayi-tayi ko ya akayi cikin ya zube gaskiya ita bata Sha wani Abu ba, Nan zuciyar ta tace tabbas SA'EED ne yayi mata hakan tunda ada baya son cikin lokaci d'aya ya Kira ta gidan shi ya bata abinci yace Yana son cikin, bashi da alamun gaskiya dole ta same shi.
Washegari taje har gidan shi, aiko tayi mai zuwan bazata domin unexpected ya ganta gashi ranar tare da wasu 'yan matan shi biyu ya kwana,
Abubuwa sunyi mata yawa ga bak'in cikin ya zubar Mata da ciki gashi Kuma ta tarar da wasu karuwai a gidan, ai rufe idon ta tayi, ta zage su ta Kore su sannan ta dawo kan shi da massifa na ya zubar Mata da ciki, haka Koh sukayi fad'a sosai suka rabu.
ABRAR ya dawo Nigeria, lokacin biki saura sati d'aya, ranar bai samu tarba daga gurin HAFSAT ba dan a cike take dashi, ko kallon shi ba tayi ba, shima bai bi ta harkar ta ba, Dan aikin gaban shi ya ishe shi,
B'angaren JAWAHIR ko sai shiri suke yi cikin kwanciyar hankali da farin ciki dan gaskiya tayi k'arya idan tace bata k'aunar ABRAR, basuyi wani bidi'a ba, Dan walima kawai akayi, inda akayi nasiha sosai.
Ranar Saturday da missalin k'arfe 2:00pm mutane suka shaida d'aurin auren *ABRAR ABDULHAMEED* da *JAWAHIR NASIR* akan sadaki mafi daraja, Duk da ba Wai yana son auren bane haka yayi ta fara'a yana gaisawa da mutane, SA'EED sai tsokanan shi yake wai har yayi mata biyu shi ko d'aya ma baiyi ba, shi dai murmushi yayi kawai dan shi fa bai son yin magana.
B'angaren JAWAHIR tayi taro da k'awayen ta tayi kyau sosai cikin shigar wani Swiss lace ga heavy make-up da akayi mata gaskiya tayi kyau ba k'adan ba, lokacin da aka d'aura auren, su ABRAR suka shigo gidan dan za'ayi pictures na biki, bai tab'a tsayawa yayi ma JAWAHIR kallo sosai ba sai yanzu da ta zama matar shi gaskiya JAWAHIR kyakyawa ce sosai, Nan dai sukayi pictures sai sunkuyar da Kai take dan ita kunya take tunda akayi maganar auren su bata tsaya guri d'aya da shi ba, duk sai tana jin wani iri.
Da daddare aka Kai amarya d'akin ta, gaba d'aya HAFSAT ta cika da kishi da bak'in ciki ta rasa abin da zatayi,Ashe haka kishi yake, to ita da take Jin kishin ABRAR yayi aure Ina ga shi Kuma idan yasan abin da takeyi ya zaiji? Haka tayi ta tunani.
*TAKU CE UMMU BASHEER*
[04/01 2:18 pm] Sis Ummu Bashir:
*YAUDARA DA CIN AMANA*
Chapter 4 · 0% Book details