← Book details Yaudara Da Cin Amana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 8

Sashe 6

Yaudara Da Cin Amana Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

{ *A short and interesting true life story*}
*NA*
*UMMU BASHEER*
*REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart
of reader's
#[email protected]
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
*DEDICATED TO RAHMAT MUHAMMAD RUFA'I NALELE*
*PAGE* *25*~*30*
*Wannan shafin sadaukarwa ne gare ku Yan group din REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
*Ina matuk'ar k'aunar ku a raina Ina alfaharin kasancewa na a cikin ku Allah ya had'a kan mu, Ameen, Na gaishe ku kyauta Mommy'n sultan, indon k'auye, MSB, Rafee'at, Faty Axland, Lubabatu Ismail, wash hannu na wallahi bazan iya lissafo sunayen ku ba Dan za mu k'arar da shafin ne anan ama ina son ku sani ni UMMU BASHEER Ina matuk'ar k'aunar ku a raina*
Washegari da safe
Lokacin da ya shigo gurin JAWAHIR ya tarar da ita sai faman aiki takeyi, dad'i yaji a ranshi yanda ta danne kishin ta har tana aikin gaban ta yasan da HAFSAT ce da sai sunyi fad'a ma, cike da murmushi ya k'arasa gurin ta yace" Princess aiki kike yi ne?"
Fuskar ta cike da fara'a tace"Ya ABRAR Ina kwana har ka tashi?"
Rungume ta yayi a ranshi cewa yake gaskiya ya gode ma Allah da ya bashi mata ta gari ga ladabi da biyayya ga tsafta ga iya kwanciyar aure, ga iya kalamai masu sanyaya zuciya, yace"fine, hope kinyi breakfast kike wannan aiki?"
Tab'e baki tayi tace"Nifa bana wani Jin yunwa"
Cafko bakin yayi tare da sucking yace"ni kike ma haka ko, zanyi maganin wannan d'an k'aramin bakin naki" ya d'an ja bakin da hannun shi.
Gyara hannun rigar shi yayi ya fara taya ta aikin.
A dai yayi kwana biyu d'akin HAFSAT ya dawo d'akin JAWAHIR, ranar sai farin ciki yake zai kasance da JAWAHIR, ita kanta taga yanda ya canza mata gurin kwanciyar aure kamar ba daga d'akin HAFSAT yake ba, har sai da tayi mai kuka sannan ya bar ta.
Satin shi biyu ya koma Germany dan yace yana da aiki dayawa acan, Mama da Abba(Daddy'n shi) sai fad'a sukeyi akan ya kamata ya dawo Nigeria haka Nan ya dawo gurin matan shi da 'Yan uwa'n shi, Nan yace su bashi lokaci, SA'EED ne ya kai shi Airport as usual.
Suna tafe a hanya SA'EED ya kalle shi yace"yanzu sai yaushe Zaka dawo kenan?"
Yace"I really don't know, Ina ma tunanin dawo da duk wani business na Nan kawai"
Cikin sauri da rud'ewa SA'EED yace"meyasa kake son dawowa Nan?"
Yace"kasan Abba yayi min magana akan in dawo Nan d'in hankali na zai fi kwanciya Kuma kaga HAFSAT da JAWAHIR ya kamata ace Ina tare da su bare kuma ayukan Nan nasan sunyi ma yawa, Kai in tak'aice maka akwai reasons dayawa"
Cikin haushi yace" ni ina ganin gara kawai kayi zaman ka acan, kasan k'asashen waje sunfi Nan komai"
Sauka motar ABRAR yayi yace"sai na k'ara tunani dai"
Nan sukayi sallama SA'EED na cike da haushin shi, haka ya tafi gida cikin Jin haushi.
Lokacin da ya Isa gida ba k'aramin mamaki yayi ba da yaga motar AZEEZA wato hak'ura Kenan da abin da ya faru, Yana shiga ya ganta a parlour.
Cikin murmushi tace"oh darling you're back tun d'azu nake jiran ka ai"
Murmushi yayi yace"Mai Kika kawo min ne na dad'i?"
Rungume shi tayi tare da had'a lips d'in su ta suka Fara kissing, daga nan suka shiga bedroom.
Sosai JAWAHIR ta yi missing d'in ABRAR domin wani irin shak'uwa ce mai tsanani a tsakanin su, HAFSAT da SA'EED sun rasa yanda za'ayi su dinga had'uwa course basa son JAWAHIR ta fahimci akwai wani abu a tsakanin su, Nan suka yanke shawaran had'uwa a hotel, haka ko suka shiga ba da had'uwa a hotel suna aikata masha'a, har ya Kai wani lokacin HAFSAT a hotel take kwana, JAWAHIR ko tun bata lura har ta fara ganewa cewa HAFSAT bata cika zaman gida ba Kuma wani lokacin bata kwana a gida duk ta lura tana son ta tambaye ABRAR ko HAFSAT tafiya takeyi Amma sai tayi shiru dan bata yin mai maganar HAFSAT kowa harkar gaban ta takeyi.
Tun bayan tafiyar ABRAR JAWAHIR bata cika lafiya ba, kullum cikin ciwo Nan taje hospital inda doctor yayi mata bincike ya gano cewa tana d'auke da cikin wata biyu, ai ko tayi murna Kuma tak'i sanar da ABRAR tace sai dai ya dawo ya ganta da ciki.
Wannan kenan
Daddy'n AZEEZA ne ke zaune abubuwa sunyi mai yawa yana nadamar k'in yarda da yayi ya aurar da AZEEZA gashi yanzu an sanar da shi cewa tana tare da SA'EED, hakan yasa ya same ta yace ta fito da miji zaiyi Mata aure, habawa ba k'aramin farin ciki tayi ba, da farko yace bazai yarda ta aura SA'EED ba amma yanda ta nuna tana son SA'EED d'in sai ya amince dan shi yanzu gara ta aura wanda take so akan su cigaba da yawo a titi, Nan yace ta sanar da SA'EED d'in akan idan Yana son auren ta ya turo magabatan shi asa ranar aure, cikin farin ciki AZEEZA ta nufa gidan SA'EED.
Yana ganin ta ya rungume ta Yana murmushi yace"duk yanda akayi akwai wani abu da Kika samu na farin ciki, rabon da in ganki kina irin wannan farin cikin haka har na manta"
Cikin farin ciki tace"ai dole inyi farin ciki dan Daddy ya amince inyi aure"
Dum gaban shi ya fad'i cikin tsoro yace"da gaske to wa zaki aura?"
Cikin mamaki tace"Daddy ya amince in aure ka, yanzu haka ma yace in sanar da Kai ka turo magabatan ka"
Ba K'aramin tashin hankali ya shiga ba gaskiya shi dai ba zai iya auren ta ba duk son da yake mata kuwa, Dan shi ba zai tab'a auren macen da sukayi taraya ba, burin shi ya aura yarinyan da ta fito daga gidan mutunci ya aura.
Katse mishi tunanin da yakeyi tayi ta hanyar cewa"lafiya kake tunani Kuma banga kana farin ciki ba?"
K'ara d'aure fuska yayi yace" I'm sorry da abin da zan ce Miki gaskiya ni bazan iya auran ki ba domin lokacin da na buk'aci in aure ki mahaifin ki ya hana to sai yanzu da yaga kin Zama karuwa zaice in aure ki? Kiyi hak'uri kawai mu cigaba da Rayuwar mu"
Cikin rud'ewa da tashin hankali tare da wasu hawaye masu zafin gaske ne ya zubo mata cikin rawar baki tace"what.....do...... you..... mean...ban .....gane ba?"
Murmushin mugunta yayi yace" da wani yare kike sonta in fad'a miki, abin da Kika ji shine nake nufi"
Cikin zuciya ta nufe shi tare da d'aukar wani kwalban Fanta tayi kan shi a gigice...............
*I'm sorry fan's kuyi managing wannan Kai na ke ciwo, Ina buk'atar addu'an ku, thanks*
*TAKU CE UMMU BASHEER*
[06/01 3:48 pm] Sis Ummu Bashir:
*YAUDARA DA CIN AMANA*
Chapter 6 · 0% Book details