Sashe 9
Yan Gidan Haya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ladi kuwa sai rawar kai take tana nuna isa da takama diyarta zata aure mai arziki. *MAI UNGUWA* Matan mai unguwa sai murna suke ganin ana gyara dak'in amarya, suna fatan zasu huta da wannan masifar tashi. Sun tambayeshi wacece amaryar yaki fadi musu wai kada suje suyi mai munafuncin da suka saba, shiyasa suka saka mai idanu suna kallon duk abun da yake yi. Mai unguwa zaune a cikin zaure tare da Baban Ladi. "Kai Lawal nawa ne sadakin?, sannan ka tabbata wannan shegiyar matar taka bata san ni zan auri diyarta ba." cewar mai unguwa. "Ka bada jaka goma Ranka-ya-dade, kuma na rantse maka bata sani ba ce mata nayi wani attajiri ne." Haka ya kirga ya mika yana washe baki ya kusa zama ango. Shikuma Malam Lawal gida y nufa ya damka ma Maman Ladi kudin sadakin, ita kuma ta mika ma Inno dillaliya data kawo mata kayan gado da dorowa. Ana ta shirye-shiryen aure sai gyara amarya Maman Ladi take, yayin da matan gidan wasu ke bakin ciki wasu kuma suna taya ta murna. Sosai Maman Ladi ta shirya ma wannan aure ganin kudin sadaki jaka goma wanda a tarihin unguwar ba wanda aka taba ba irin wannan kudin matsayin sadaki. Hidima sosai matan gidan ke ta yata kama daga kan alkaki, dubulan, nakiya, da sauransu. *RANAR AURE* Ranar gidan 'yan haya ya cika sosai, domin gayyata Maman Ladi ta yi na auren tilon diyarta. A nata hidimar girki, amarya ansha atamfar batik cikin kayan auren da mai unguwa ya aiko. Karfe biyu aka daura auren Zainab wato Ladi da ango Nasiru Tanko mai unguwa. Maman Ladi anci kwalliya ana tsakiyar jama'a wannan sakon the isketa, a hargitse take tambayar "wani mai unguwa aka ba auren Ladi?" "Wanne kuwa bayan mai unguwa Tanko."cewar Inna Talatu dake tsaye bakin kofa. Ai a tamanin Maman Ladi ta fito tana kwallo da duk abun da tagani a hanya, tamkar zararra tana kwalla kiran sunan Baban Ladi. Mutane da aka gayyata suka dinga kallonta domin basu san komai ba, matan gidan kuwa sai yamadidi suke da ita suna dariya. Shigowar su kenan daga wurin daurin mazan gidan, Baban Ladi na gaba suna biye dashi a baya. Yana sako kai yaji an shake shi sosai ba da wasa ba, kokari yake ya ya kece daga rikon amma ya kasa. Maman Ladi data yi shakar ta wanke shi da mari tana fadin " munafuki macuci kace min wani attajiri zai auri Ladi, ashe wancan shegen ne to wallahi sai an warware auren nan muddin kana bidar zaman lafiya dani." Juya kai kawai yake yana kokarin kwace wa daga rikonta, mazan nata aikin bada hakuri inda matan dake wurin suka maidata tamkar talabijin suna ganin ikon Allah. Da kyar ta sake shi, aikuwa yana jin yasha ya sa kafa sai hanyar waje yana fadin "Na rantse da Allah aure ya auru naga uban da zai kwance shi mahaukaciya kawai." " Zaka dawo ai wallahi zaka san da Hajara uwar Ladi ka yi a gidan nan". *INA LABARIN ANGO MAI UNGUWA TANKO??* *Badeeyerh Beauty Queen* [3/1, 12:45 PM] Beauty Queen: *'YAN GIDAN HAYA* . *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Badeeyerh Beauty Queen* Dedicated to *AUNTY ZETTY MAMAN HANAN* Zaku iya samun littafan mu a Facebook Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu [email protected] No matter the Distance between Us.. I am as Close To U today As I was Yesterday.. For as Long As U are In my Heart.. We are Never Truely Far Apart.! I love you fan's of 'YAN GIDAN HAYA. One love to you. *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *65~70* *GIDAN MAI UNGUWA* Suna zaune suna hira da yaran su da makota da suka zo biki. Lado ya shigo yana sharce zufa ranshi a hade yace "Mama zo kiji wai diyar gidan haya baba ya aura." Salati Hannatu ta sanya tana dafe kirji" Diyar gidan haya fa kace Lado?" "Wallahi ita ce ya aura wannan yarinya karama da ita, wacce wallahi ko ni ta yimin kankanta da aure wai ita baba ya aura." Zugum suka yi suna jimamin wannan masifa da mai unguwa ya kwaso musu. Sai gashi ya shigo yana saba babbar riga, yasha fararen kaya yana ta bude hakora. Makota sukai mishi fatan alheri suka fita. Ya kalle su yanda duk sukai shiru kamar masu zaman makoki yace "Lafiya kuwa kuke zaune da tagumi kamar ance iyayen ku sun mutu?" Cikin takaici Hannatu tace " cewa akayi mai unguwa Tanko ya mutu shine muke jimami." "Ubankine ya mutu billahillazi bani ba, munafukai kawai duk kishi ne na sani." Jummai ta kalli yanda yaran ke zaune rai a hade tace" Ko wacce ta wuce gidanta, kuma ku tafi wurin sana'ar ku an gama taro." "Allah sarki Jummala ayi hakuri dai aure ne nariga nayi ko da taro ko babu taro sai amarya tazo." ya fice daga gidan. Haka kuwa yaran jiki a sabule suka yi musu sallama duk suka fita. Suka bar iyayen cikin jimamin wacce mai unguwa ya debo musu matsayin kishiya. Yana fita ya hadu da da baban Ladi yana haki kamar dan tsere. "Kai Lawal meye haka kake ta haki, lafiya dai ko?" "Ina lafiya Ranka-ya-dade Maman Ladi ta gane kai ne mijin, tace wallahi ba zata bada amarya ba." Shekeke mai unguwa ya bishi da kallo "Yo ita shegiyar matar taka an gaya mata tana da ikon kan matar dana biya sadaki ne?, to billahillazi ka koma ka fada mata anjima a bani amaryata ko wallahi taga kalar nawa haukan, banzaye bayan na biya kudi na sai ace za'ayi min iko." "Ranka-ya-dade wallahi shakeni ta yi bazan iya komawa ba." "Aikuwa zata san waye Tanko billahillazi a garin nan." ya shige gida a fusace. *CIKIN GIDAN HAYA* Maman Ladi da 'yan korenta zaune kofar dak'inta, suna kara zugata kan kada t yarda akai diyarta gidan mai unguwa. "Nifa da hankali na wallahi bazan ba Tanko Ladi ba, kuma yazo ya gani." "Wallahi Maman Ladi gidan shi babu abinci, babu suturar arziki."cewar Ladidi. "Nifa nasan waye Tanko, domin munyi artabu da shi watarana ana fad'a gidan mu yazo rabo y dinga tsine mana" cewar wata kawar Maman Ladi mai suna Atuwa. "Ayererre a dade anayi, aure dai the auro dole a ba Tanko matarsa." "Ke Talatu wallahi ko Ubankine bazan bayar ba, kuma ki daina shiga sabgata Maman Ladi nake." "Aifa yau ko uwata zaki zaga bazan damu ba ai dama duk wanda y shiga motar kwadayi yasan inda zata kaishi." Cikin fusata Maman Ladi ta nufo Inna Talatu ta hauta da duka, sai dambe. Kaya-kaya ana kokarin rabawa sunki rabuwa domin a zuciye Maman Ladi take sai jibgar Inna Talatu take yi, ganin haka yasa Inno shigarwa Inna Talatu dama tare suke adawa da wannan aure. Aikuwa hadasu Maman Ladi ta yi t dinga jibga tana gwara kawunansu. Ladidi dake tsaye gefe ta kalli Mairon Ado tace"Ke Mairo zo ki tayani dibar abinci idan kina so." Abule dake zaune tana kallon fad'a ta dubi su Mairo "Walle Mairo ta karkije wanga cin amana ta zata yi." "Wani shegen yace miki cin amana zanyi?" "Ke na shegiya." cewar Abule. Mari Ladidi ta kawo ma Abule, Mairon Ado ta tare tana hararar Ladidi"Kika tabata sai na sabautaki wallahi matsiyaciya kawai mai..." bugun bakinta da Ladidi ta yi yasa ta yi shiru ba tare data shirya ba. Abule na ganin haka ta hau Ladidi da duka baji ba gani. Suma suka hau fad'an su uku, gefe kuma gasu Maman Ladi. Gudar masu daukar amarya ne y dakatar da wannan rikice, aka shiga kallon-kallo. "Munzo daukar amaryar mai unguwa."Cewar Maimounath makociyar mai unguwa da ya roka suzo dauko amarya tunda yan'uwan shi sunki zuwa. Ita kuma Maimounath dama da biyu tazo saboda basa ga maciji da 'yan gidan haya. Shewa Inno data gama dokuwa gurin Maman Ladi tasa tana fadin"Gaya musu su fito muku da amarya ku cika umarnin mai unguwa." "Aikuwa dai yar'uwa abamu amarya a mutunce mu kaita dak'in ango a mutum.." wani duka taji ya sauka a kanta wanda yasa ganinta ya dauke na 'yan sakanni. "Bari naji' yar iskar data kara cewa na bada diyata akai gidan mai unguwa." cewar Maman Ladi dake tsaye rike da muciya. Nan fa 'yan koren Maman Ladi ko wacce t dauko abun duka.'Yan daukar amarya na ganin haka ga Maimounath durkushe a kasa, ai sai suka sanya gudu suka barta. Ladidi ta kalle ta ta tuntsire da dariya tana fadin "Su yan daukar amarya ansha wahala, ina bakin fadin amarya yake?" Cikin karfin hali Maimounath ta mike ta shake wuyan Ladidi ta fara jibga, ganin haka Maman Ladi da sauran suka rufeta da duka, sukai mata lilis suka barta kwance. *WURIN MAI UNGUWA* Sauran da suka koma suka fadi ma mai unguwa abun dake faruwa, aikuwa ya mike ya saba riga shida abokin shi Kallah da baban Ladi suka nufi gidan. Yana fadin " Wallahi yau Lawal matar ka zata san Tanko take raina wa." " Ayi hakuri don Allah Ranka-ya-dade." Matan naji Hannatu t dinga dariya "Maman Sani yau zaki ga angon da daukar amarya, Allah yasa Maman Ladi ta mai dukan tsiya." " Uhm Uhm Hannatu mijin kine fa." "Maman Sani ayi sha'ani kawai wallahi." Nan suka dinga tattaunawa suna kara jajantawa kansu aikin da ya dauko musu. *CIKIN GIDAN 'YAN HAYA KUWA* _MEZAI FARU DA ZUWAN MAI UNGUWA_ *Badeeyerh Beauty Queen* [3/1, 12:45 PM] Beauty Queen: *'YAN GIDAN HAYA* . *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Badeeyerh Beauty Queen* Dedicated to *AUNTY ZETTY MAMAN HANAN* Zaku iya samun littafan mu a Facebook Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu [email protected] *WANNAN SHAFIN NA MUSAMMAN NE GAREKU DOMIN KU DIN NA MUSAMMAN NE, KODAYAUSHE INA YI MUKU FATAN ALHERI* _BRO HUSSAIN ATK_ -BRO HASSAN ATK_ _AUNTY HASSANA ATK_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *70~75* Maimounath kwance ko motsi bata yi saboda ta daku, su mai unguwa suka doka sallama suka shigo. Ganin ta kwance yasa sauran matan suka nufeta da sauri suna tambayar lafiya. Inna Talatu dake tsaye kofar dak'inta ta bude baki da karfi tace"Su Maman Ladi ne suka jibgeta wallahi." Mai unguwa ya kalle su fuskannan a daure yace " ku dauketa ko kaita kemis ina zuwa." Suka dauketa su uku suka fice. Ya kalli Maman Ladi