← Book details Yan Gidan Haya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 11

Sashe 5

Yan Gidan Haya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*A CIKIN GIDAN' YAN HAYA*
Zage-zage akeyi tsakanin su, ko wacce na zagin wanda sukai fad'a tare. Ganin mazan sun dawo ya sanya sukai shiru aka koma hararar juna.
Baban Dare ya dubi Maman Dare cikin yarensu yace "Na gode da kika zubarmin da mutunci, kullum ina fada miki ki daina shiga abun da babu ruwanki kinki, to wallahi duk abun da ya faru babu ruwana" ya shige dak'i.
Tasan halin mijinta da zuciya, jikanta ya yi sanyi ta rufa masa baya ita ma.
Malam Isah ya kalle su yanda sukai tsaye suna jifan juna da mummunan kallo yace "Talatu kuna da masaniyar kun kar ya mai unguwa ko?"
"Kar ya shi kuma, ta ina?" ta tambaya a rikice.
"A'a wallahi Maman Dare ce ta buga mai icce" cewar Mairon Ado dake tsaye gefe.
"To wata shegiyar ce ma ta kira shi gidan nan?" Maman Ladi ta tambaya tana hararar Mairon Ado.
Takaici ya kama Malam Isah ganin mai makon su jajanta, amma suna kokarin mai da zuwan nashi ma abun fad'a, dan haka yace,
"Ko wacce ta kira mijinta kafin zuwan 'yan sanda gidan nan,kun san halin mai unguwa" ya shige dak'i.
Suna tsoran batun' yan sanda don haka ko wacce ta shige dakin ta, tare da neman mazajen su.
An hallarra a tsakiyar gidan.
*Kome zai faru???*
*Ina labarin mai unguwa???*
*Badeeyerh Beauty Queen*
[3/1, 12:36 PM] Beauty Queen:
*'YAN GIDAN HAYA*
.
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Badeeyerh Beauty Queen*
Dedicated to
*AUNTY ZETTY
MAMAN HANAN*
*WANNAN SHAFIN KYAUTA NE GARE KI ZUWAIRA MADARA. AUNTY ZETTY NAYIN KI IRIN SOSAI DINNAN, TANA YI MIKI FATAN ALKAHAIRI, ALLAH YA RAYA HANEEFAH, KEDIN TA MUSAMMAN CE.*
Zaku iya samun littafan mu a Facebook
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION
Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu
[email protected]
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*30~35*
Mai Unguwa zaune gaban Hussaini mai gyara, yana jiran ayi gyaran hannunshi saboda azabar ciwon da yake ji. Hussaini ya kalle shi bayan ya taba hannun yace "Mai unguwa ka samu tsagewar k'ashi a kafadar ka, garin ya hakan ya faru?"
"kayi aikin ka ba tambaya ba malam "cewar mai unguwa a fusace.
Gyada kai Hussaini ya yi yana murmushi, ya dauko wani mai ya diba sannan ya kama hannun mai unguwa da karfin tsiya. Wani ihu mai unguwa ya saki wanda ya janyo hankalin yaran gidan, suka dinga leke suna dariya.
Cikin azaba mai unguwa yace "Allah ya isa Hussaini, billahillazi ban yafe maka ba duniya da lahira azzalumi kawai".
Kara shafa man Hussaini ya yi ba tare da ya kula mai unguwa ba, ya sake riko hannun ya matsa ya shafe da wannan mai. Mai unguwa ya kwalla kara yana hawaye yana zagin Hussaini, shi kuma Hussaini saiya kama kafadar mai unguwa sai ya fanshe zagin da yake yi mishi. Ganin azabar ta yi yawa ya sanya ya warce hannun shi tare da mikewa ya share kwallar idonsa yace "Zakasan ni mai unguwa Tanko ka yi ma wannan mugunta wallahi, har da kai 'yan sanda zasu hada yau." ya juya zai fita.
"Mai unguwa kudin aiki na fa?" cewar Hussaini.
"Na karfine kazo ka k'wata azzalumi kawai"
"Haba mai unguwa, wannan fa hakkina ne."
"Naci hakkin naka, kayi abun da zaka yi." ya juya ya fice. Yana isa tsakiyar gidan ya ga dandazon yara sai dariya suke ganin ya fito. Tsawa ya daka musu, amma ina sai fadi suke "Mai unguwa ya yi kukan gyara yeeee ra go, matsoraci mai unguwa Tanko" suna shewa.
Da gudu ya bisu ga hannu a rike, aikuwa suka k'wasa da gudu suna dariya. Ganin bazai ka masu ba ya sanya ya wuce yana aikin sababi yana fadin "Yau hatta iyayen ku suma sai sun kwana ofishin 'yan sanda, billahillazi tare da 'yan gidan haya. Yanzu ma can zani na kira su." jin hannun nashi namai ciwo idan yana tafiya, yasa ya k'wance rawaninsa ya daure hannun dashi yana cije baki. Sannan ya mike hanya sai station.
*********
*A TSAKAR GIDAN 'YAN HAYA*
Kowa dake gidan ya hallara wurin wannan taro, bayan an zauna ne malam Isah ya mike da bayani kamar haka.
"Ina fatan zaku mai da hankali ku fahimci ainahin abun da ya taramu anan? Dalilin wannan taro kuwa bazai rasa nasaba da fadace-fadacen dake yawan faruwa ba a gidan nan. Misali na yau wanda ya kai mizanin babu mai hankali a cikin matan mu, ko wacce kokari take na ganin ta yi fad'a badai ta raba fadan ba yau, mai unguwa da ya kasance uban al'umma kuma matsayin mai kula da wannan gida yau shima sun ji masa ciwo a hannu. Kuyi sani cewa mai unguwa bazai taba barin wannan magana ba face ya danganta ta da hukuma, shiyasa nace ko wacce ta kira mijinta domin sanin abun yi"
Cikin takaici Baban Dare yace " sunayi fad'a kaman kaji wada beci abinci ba".Dariya wasu suka yi dajin hausar shi. Mijin Maman Ladi ya mike yace" Tabbas abun da matan mu keyi kwata-kwata basu tsare mana mutunci, sai kace mu kadaine 'yan haya cikin wannan gari, kullum sai sun ja mana jaraba wurin mai unguwa. Ranar cewa ya yi wurin sarki zai kai karar mu a koremu domin ya gaji da masifar matan mu" ya karasa cikin bakin ciki.
Haka aka dinga mai da bayani kan halayyar matan gidan, inda aka hana matan magana. Kowa ya yi ma matarsa kashedi kan wannan halayyar tasu. Ana cikin wannan magana ne suka ji jiniyar motar 'yan sanda, cikin takaici mazan suka mike da niyar fita waje, amma sai ganin 'yan sanda suka yi tare da jagorancin mai unguwa dake sak'ale da hannu a wuya kai babu rawani.
Mazan ne suka yi musu tayin zaman sulhu, amma mai unguwa yace sam babu sulhu sai dai a tafi da Maman Dare ofishi tunda itace taji mai ciwo.
"Kwarankwatsi sai an tafi da ita, matsiyaciya ita ta bugamin icce kawai don nazo rabon fad'a, shi kuma shegen mijinta ya barni a waje harda cewa wai na mutu ai basu suka kirani ba."
"Haba me unguwa kiyi hakuri mana ki fadi gaskiya" cewar Baban Dare jin bayanin mai unguwa.
"Yauwa Usmanu kaji ba? Mace yake kirana shegen kwanon" Mai unguwa ya fadi yana nuna Baban Dare.
Dariya dan sandan da ya kira da sunan Usmanu ya yi yace "afuwan mai unguwa bai iya hausa bane shiyasa"
" Yo dama an fadi mai hausar kayan banza ce? Ai dole ya kasa tunda ba muhallinsa bace" Mai Unguwa kenan.
Sauran mazan ne suka shiga maganar don ganin ba a tafi da Maman Dare ba albarkacin mijinta, sunyi ma mai Unguwa Alkawarin biyan kudin jinyar hannun shi har ya warke. Jin haka dama gashi da masifaffen son kudi, take ya amince da wannan tayin.
Nasiha sosai 'yan sanda sukai musu, tare da basu hakuri ganin an zauna tare, sannan mai unguwa ma yace "Na daina zuwa gidan nan koda zaku kashe kanku." Dariya sosai suka yi, sannan kowa ya kama kansa.
*SHIGAR MAI UNGUWA GIDANSA*
Matan na zaune tare da Lado, Sani da Buba suna hira. suka ganshi kai babu rawani, da sauri yaran suka mike cike da mamaki suna yi mishi sannu da zuwa. Ko kallon su baiyi ba ya zauna cikin zafin ciwo yana fadin "Hanne kawo min ruwa"
"Malam meyasa meka a hannu?"
"Jummala! Jummala! Kar wata banza ta kuma tambayata abun da ya faru muddin nine mai gidan nan"
"To babu mai kara tambaya Malam, kayi hakuri." taja bakinta ta yi shiru tana binshi da ido.
Ruwa yasha sannan yace "wato Jummala mata matsiyata da ban suke". Banza ta yi da shi.
Cikin hassala yace" magana fa nake kuka shareni"
"Baba kayi hakuri"cewar Lado.
"Don uwar ka na saka bakinka ne a wannan maganar?"
"Yi hakuri Malam bazai kara ba" Hannatu ta fadi tana mikewa.
"Zauna ma za anan munahika kawai, za aje dak'in don ga bala'i ya dawo ko?"
"Abince zan kawo maka Malam " ta fadi ta yi hanyar dak'inta.
Abincin ta kawo mai, amma ko kallon kayan bai yi ba sai ma cewa da ya yi ta kwashe bazai ci ba. Ta kuwa kwashe a ranta tana fadin"Mun samu na karyawa da safe".
"Baba ga wannan ka sai magani, ni zan wuce sai da safe." cewar Sani ya mika mai dari biyu.
Amsa ya yi yana dariya yace "Sani dan albarka, yaro mai halin dattijai na gode sosai magaji na"
"Yauwa Baba had'ari kayi ne?" Sani ya tambaya.
"Hmm! Sani in fad'a maka matan 'yan gidan haya ne suka kassarani yau wallahi"
Kunshe dariya suka yi dukkansu, sannan yaran sukai mai sallama suka tafi. Su kuwa matan dak'i suka shige suna dariya jin mai unguwa na fadin,"wallahi ban kara zuwa gidan 'yan hawa billahillazi kuwa".
*ANYA KUWA MAI UNGUWA? MADARA KIN YARDA DA HAKAN KUWA??*
*********
*' YAN GIDAN HAYA*
Kwana biyu an samu kwanciyar hankali babu fad'a, amma ko wacce na nan da cikin yar'uwarta.
"Ke Inno jibi ranar cika ciki fa" cewar Ladidi dake wanke-wanke.
"Ayererere" Inno tasa guda, sannan ta dora da fadin"Za muga k'wanjin mazaje masu zuciyar siyan akuya, da masu cin bashi irin na waccan shekarar.
Mairon Ado ta yi tsalle ta ja gefe tana fadin "Uban mata zanci wallahi muddin ta kasa dani cikin zancenta."
"Uba fa kinka ce Mairo kawata? Ai wanga uban Baban ta shi ad dai-dai walle" suka tafa suna dariya.
Ladidi ta yi murmushi ta kama waka"_ayye nanaye wacce mijinta bai da sulalla, wazai taimaka yaji tausai, ya aiko da gashin kaza ran dadi"
Kau! aka dauketa da mari, da sauri ta dafe kuncinta tana waigen mai marin. Inna Talatu ce tsaye gabanta.
*Hmm yanzu aka soma*
*Badeeyerh Beauty Queen*
[3/1, 12:45 PM] Beauty Queen:
*'YAN GIDAN HAYA*
.
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Badeeyerh Beauty Queen*
Dedicated to
*AUNTY ZETTY MAMAN HANAN*
Zaku iya samun littafan mu a Facebook
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION
Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu
[email protected]
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Chapter 5 · 0% Book details