← Book details Yan Gidan Haya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 11

Sashe 10

Yan Gidan Haya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dake tsaye bakin kofarta, inda ta rufe Ladi dake aikin kuka ita batasan mai unguwa. Yace" Nazo daukar matata da kai na." "Sai dai idan uwar matar ka zaka dauka."ta bashi amsa. Ya kalli Baban Ladi, ai kuwa da sauri ya matso jiki na kakkarwa yace"Haba Maman Ladi don Allah ki bari a tafi da ita wallahi yanzu bamu da iko da ita." "Algungumi ba inda zata indai nina haifeta, kuma wallahi naga uban da zai dauketa." "Nine kuwa uban da zai dauketa billahillazi."cewar mai unguwa. "To kana iya zuwa ka dauketa ai matsiyaci." "Kece dai matsiyaciya shegiya me bakin hali." Da sauri Kallah yace" Ranka-ya-dade surukar kace fa yanzu a tauna kalamai." Wani kallo ya buga ma Kallah wanda yasa Kallah tsugunnawa yana fadin "Tuba nake Yallabai." "Wallahi yau zaa bani matata ko kuma na yi bala'i billahillazi,kuma wannan mai kama da buhun fulawar ta yi kadan na kira ta da suruka." "Kana iya zuwa ka dauketa ai idan kai ka haifa min yarinyar, mai kama da sauro." Karasawa kofar dak'in ya yi yana kokarin shiga, aikuwa Maman Ladi da mutanen ta suka rufe shi da duka ga makota nata shigowa kallo. Dukan shi suke suna karawa shikuma kokarin ceton kansa ya ke don kuwa baisan tsiyar da suka shirya mai ba kenan. Kallah da Baban Ladi nata rokon su dai na amma sunki don haka Kallah ya ranta ana kare yana fadin"Naji bayanin yanda aka kare idan mun hadu, domin wa'innan matan babu alamun tausayi tare dasu." Makota na leke suna bada hakuri wasu kuma suna kara zuga wa. Jiniyar motan 'yan sanda suka jiyo, aikuwa suka sake mai unguwa da sauri suka shige dakunan su.'Yan sanda suka shigo su biyar uku mata biyu maza cikin gidan. Mai unguwa na ganin su ya sanya ya mike da kyar yana goge jinin bakin shi yace"Kuci uban su sosai ku tafi dasu setation don Allah, billahillazi bazan yafe musu ba kuma a fito min da matata." "Kayi hakuri mai unguwa zamu dauki mataki insha Allah." Nan aka sanya 'yan sanda matan suka shiga dakunan duk aka tarkato su waje. Maman Usman ce kadai bata nan, domin ta yi tafiya bata gari duk wannan bidirin da ake yi. Gaba daya matan gidan aka tasa su gaba zuwa ofishi, mai unguwa yace a taho masa da mata, aka kuwa fito da ita sai kuka take. Aka tasa keyarsu hada 'yan biki sai setation. *Ofishin' yan sanda* Suna zaune Dpo ya shigo, ganin mai unguwa manne da bandeji a Hannunsa da gefen kunne yasa ya karaso da sauri. "Mai unguwa maiya same ka haka ne, ba dai hatsari kayi ba?" "Bari Ddo waccan tsinanniyar matar ce ta jimin ciwo wallahi." Sai lokacin Dpo Muhammad Abubakar ya lura da matan dake tsaye gefe guda. Da mamaki ya kira sajan yana tambayar meyafaru, nan suka fada mishi tun daga kiran da akayi musu da kuma yanda suka tadda mai unguwa ga Maimounath ma sun daketa. "Dankari! Kenan menene matsalar?" "Ranka-ya-dade sai dai a kira mai unguwa ya yi bayani." "Kirashi su." "Yes sir." ya fita ya kira mai unguwa suka shigo tare. Nan ya zaiyane komai da ya sani dangane da fad'an da kuma dukan da suka yi mishi da Maimounath. Nan Dpo ya fito ya tara su wuri daya ya fara tambayar ba'asi. Wasu su fadi gaskiya wasu akasin haka, dukka ya tattara ya hada ya yi tagumi yana kallon su. Duk sukai shiru suna kallon shi yace "Aba mai unguwa matarsa su tafi." Kuka Maman Ladi ta sa tana fadin" Wallahi bazan yarda diyata taje gidan shi ba, domin da farko ai basu fadamin gaskiya duk munafukai ne." Tsawa ya daka mata ta yi shiru tana kallon shi. Ya yi musu dogon sharhi kan boye mata da suka yi sannan ya yi umarnin Maman Ladi da sauran duk zasu bada dari biyar-biyar na dukan mai unguwa da Maimounath kudin magani. Haka suka bayar suna Allah ya isa a zuci. Haka ya dinga musu nasiha yana ankarar dasu illar abun da suke yi, daga bisani ya sallame su suka fito. Maman Ladi na kuka Ladi nayi suka rabo ta hau mashin din mai unguwa suka tafi. Su kuma matan gidan da 'yan biki ko wacce ta yi hanyar gidan ta. Maman Ladi na koma wa ta dinga rabawa 'yan gidan duk kayan bikin data hada tana cewa "Wallahi dana kai gidan mai unguwa gara na zubar dashi." Ta kira almajirai ta dinga rabo. *GIDAN MAI UNGUWA* Yana tsayar da mashin ta sauka ta tirje taki shiga, juyin duniya Ladi taki shiga gidan. Mai unguwa ya fusata ya dinga zaginta. Hayaniyarshi ta sanya matan lekowa jin yana surfa zagi, aikuwa ganin Ladi tsaye kikam kamar gunki yasa Jummai dauko mayafi ta fito,tana zuwa ta riko hannun Ladi, aikuwa bata yi gardama ba ta bita suka shiga gidan. Takaicin hakan yasa mai unguwa gunduma musu ashar yana cewa"Ban aurota don ku zauna da ita ba, billahillazi kar wacce ta koya mata bakin hali." basu kula shi ba suka shige dak'in Jummai dukkansu. Zaunar da Ladi ta yi tana rarrashi Hannatu ta debo mata abinci suka saka ta gaba suna ta bata hakuri. Da kyar ta yi shiru yana ajiyar zuciya taci abincin tasha ruwa ta haye gadon Jummai ta kwanta. Kallon juna suka yi Hannatu tace "To yanzu ya zaki yi taje dak'inta?, kuma fa dak'in ba komai basu kawo kaya ba." "Barni dashi Hannatu zai gane kuranshi ya sake ya shigo da sunan tafiya da yarinyar nan dak'inta." Duk suka zauna suna dakon zuwan mai unguwa, kamar ya sani kuwa yaki zuwa ya shige dak'i ya kwanta yana jinyar jikin shi. *WASHEGARI GIDAN HAYA* Maman Ladi ta tashi zuciya tunkushe da bakin ciki, ta kira Inno tace "Inno ki kwashe kayan gadon nan ki siyar dasu ki ban kudina ko nawane gara nayi asara dana kai ma mai unguwa." "Haba Maman Ladi kiyi domin diyar ki mana, kinsan dai mai unguwa bazai kula da ita yanda ya dace ba, kiyi hakuri ki kai mata." Shiru Maman Ladi ta yi tana tunani, can tace "Shikenan ku shirya kukai kayan to." ta shige dak'i. Gyada kai Inno ta yi domin ta tausaya wa Ladi da auren mai unguwa dama dan basu san waye angon ba yasa suke bakin ciki. Haka kuwa rana na yi aka kwashe kaya sai gidan mai unguwa. *LADI GIDAN MAI UNGUWA* Da safe suka tashi suka fara ayyukansu, Ladi nata baccin gajiya har suka gama hadin karin safe. Hannatu t taso ta, aikuwa t sanya kuka ita gida zata je, da kyar suka samu ta yi shiru t zauna suka kar ya. Mai unguwa na jinsu yana kwance dak'i duk jikin shi ciwo yake domin yaci duka ba kadan ba. Suka zauna suna da janta da hira har ta sake dasu. Mai kura ya yi sallama suka shigo tare dasu Inno da Ladidi, Abule, Maman Dare, Maman Akintola, Inna Talatu, matar Malam da sauran matan gidan d makota. Nan su Jummai suka yi musu tarba ta mutunci, mai kura ya jide musu kayan suka hau shiryawa. Ladi t dinga yi musu kuka tana cewa su tafi da ita. Hakuri suka dinga bata Maman Akintola tace " Ladi kana da iyaye fa a gida na me anguwa kayi hakuri kawai ka zona kaji ko." ta gyada mata kai tana kuka har suka gama jere suka tafi. Mai unguwa na dak'i yaki fitowa yana kunyar ya yi ido biyu dasu saboda dukan da ya sha jiya, sai da suka tafi sannan y fito yana hura hanci. Yace"Jummala ruwan wanka" "Babu." ta fadi a takaice. "Allah ya hana ki muguwa kawai." ya fice yana hararar Ladi. Nan Jummai ta dinga rarrashe tana nuna mata ta yi biyayya zata ji dadin zama tare dasu, ta gyada mata kai tana kuka suka shigar da ita dak'inta. *'YAN GIDAN HAYA* Suka koma suna bata labarin matan mai unguwa sun rike Ladi kamar yarsu, wannan yasa Maman Ladi ta saki ranta domin tasan matan nada mutunci ba kamar shi ba. Hankalinta ya dan kwanta ta rage fargabar diyarta zata cutu gidan mai unguwa. Mijin kuwa tun ranar bai dawo ba sai yau, ko kallon shi bata yi ba. *Ya ya zaman Ladi zai kasance da mai unguwa kenan??* *Badeeyerh Beauty Queen* [3/1, 12:45 PM] Beauty Queen: *'YAN GIDAN HAYA* . *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Badeeyerh Beauty Queen* Dedicated to *AUNTY ZETTY MAMAN HANAN* Zaku iya samun littafan mu a Facebook Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu [email protected] _ALHAMDULILLAH SADAUKARWA GA DAUKACIN AHALIN ALHAJI ABUBAKAR SA'EED ARDO BORO, UBANGIJI YA TSARE MU YA KARE MU GA SHARRIN MAKIYA, ALLAH YA SHIRYA MANA ZURI'A DAYYIBA AMEEN._ *BAMU DACE DA JUNA BA* _UMMU BASHER_ *Allah sarki wasu iyayen basu san cewa kwanciyar hankali yafi kudi ba, shiyasa suke ganin 'ya'yansu sunfi karfin talaka. Amma ga Ummu basher ta fada mana cewa zaman lafiya, kwanciyar hankali, soyayya da sauransu duk ana samu koda babu kudi, zaa dace da juna. ina taya ki murna na kammala wannan littafi k'awas, Allah ya kara basira da zakin hannu hade da kwarin idanu. Ina yinki sosai dinnan. Muna biye a DANA SANI* _Ma cherie ta mai unguwa Tanko ina kika kai mana SAADAT angon BUSHRA, kina kamshi muna miki feshin humra tawan more grease._ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *80~End* Sosai gidan 'yan haya fad'a ya yi sauki, ko wacce na kokarin kare martabar sana'arta tun bayan dawowar Maman Usman taji duk abun da ya faru, nan ta nuna musu cewa muddin suna da sana'ar yi to ba zasu kasance suna ganin bakin juna ba. Hakan yasa suka dage kowa ya kama sana'a suna kuma kokarin ganin an zauna lafiya. Bata taba kai ma diyarta ziyara ba, sai dai tana samun labarinta wurin kawayenta. *GIDAN MAI UNGUWA* Sosai suka rike amanar Ladi, kasancewar yarinyar tana yi musu biyayya ta shammace su basu yi tsammanin zata yi hakuri ba duba da halayya ta gidan data fito. Suna kare ta sosai don ganin mai unguwa baici zarafinta ba, sun yarda duk abun da zai ma ta ya yi musu gudun magana cikin gari. Sun hada kai suna ganinta kamar yaran su mata dake gidan aure.mai unguwa ya yi jarabar ya yi masifar hadin kansu yaga basu da niyar
Chapter 10 · 0% Book details