← Book details Yan Gidan Haya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 11

Sashe 11

Yan Gidan Haya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

canzawa, gashi duk abun da suka ce shi Ladi keyi don haka yasa musu ido kawai yana kallon su. Lokaci yaja kwanaki sun shude haka satittika haka watanni yau Ladi watan ta biyar gidan mai unguwa ba tare da taje gida ba. don haka yau take ta zumudin zuwa gidan su. Ta gama shiryawa ta fito da mayafinta a hannu tace"Maman Sani zan tafi." "Lallai Ladi da safiyar nan zaki tafi?" Rau-rau ta yi da ido kamar zata yi kuka tace"Maman Sani ina son ganin Mamana fa." Dariya suka yi suna tsokanar ta ganin zata yi kuka. Da sauri mai unguwa ya fito yana gyara mashin dinshi yace " ke zo mu tafi ki bar wa'innan matan." "To a dawo lafiya Ladi a gaida gida." "Insha Allah za suji." ta fita suka tafi. *GIDAN 'YAN HAYA* Maman Usman na zaune cikin su suna hira, sai nishadi suke kamar basu ba. Maman Akintola tace " wallahi gida namu ya yi dadi fa kowa ya yi shiru ya yi hakuri kome ya wuce." Suka sa dariya dukkan su, sai jin sallamar Ladi suka yi. Da gudu ta shigo ta rungume uwar sai kuma tasa kuka. Maman Ladi murna Sosai ta yi na ganin Ladi tace" To rigimatu kukan na menene?" "Mama baki taba zuwa gidana ba." Duk matan gidan sukai dariya, Maman Usman tace " Ladi sai kuma aga Maman ki gidan ki ba kunya ko?, kamar ba diyar fari ba." "Kai mama kema sau daya kika je ai." "To zan dinga zuwa kullum." ta fadi tana dariya. Ladi ta rufe ido da hannayenta tace "Yana waje fa tare muke dashi." Rankwashi matar Malam ta sakar mata akai" Ja'ira shine tun dazu baki fadi ba kika zauna shagwaba?" Da sauri Maman Usman ta dauko tabarma ta shimfida tace "Maza jeki shigo dashi." Tare suka dawo sai sunkuyar da kai yake yi alamun kunya, domin ya tuna abubuwa da yawa da ya faru cikin wannan gida, gashi kuma yau ya shigo matsayin sirikin su. Ya nemi wuri ya zauna, Ladidi ta kawo mai ruwa, matar Malam ta kawo mai fura. Suka zauna suna gaisawa a kunya ce. Bayan sun gama gaisawa suka zauna. Maman Usman tace "Alhamdulillah nayi farin ciki ganin wannan rana, domin ada can ba muyi tsammanin abu makamancin wannan ba, mai unguwa matsayin suriki cikin gidan haya. Lallai abun mamaki ne sosai da hakan ya faru amma sai gashi sanadin haka zaman lafiya da fahimtar juna ya dore tsakanin mu, ina fatan zamu kasance masu hakuri mu jure neman na kanmu mu guje ma rigima da tashin-tashina." "Kwarai hakane Maman Usman domin kin dade kina nusar damu illar fad'a cikin gidan nan, amma bamu dai na ba sai gashi tun bayan auren Ladi da mai unguwa zaman lafiya yazo ya daure sosai, Allah yasa mu kasance koyaushe haka." cewar Inna Talatu. Maman Ladi ta yi ajiyar zuciya tace "Gaskiya munyi zaman rashin hakuri da junan mu, mun kasance masu biye ma zuciya da rashin sanin meke mana ciwo muna fad'a da junan mu alhali Allah ya ri ga ya kaddara zaman mu tare, musamman ni na kasance mai daukar duk abun da diyata ta fadamin game da mutanen gidan nan koda bana nan, sai dai abun farin ciki shine bata dauki wannan hali taje gidan miji dashi ba, ina kira ga iyaye dasu dinga kwabar ya'yansu kan maganganu, su daina yarda da maganar yara koda suna tunanin gaskiya ce. ina fatan zamu yi hakuri mu kasance masu yafiya mu zauna lafiya." "Gaskiya ne Maman Ladi mun kasance masu kyashi da hassada, mun dauki mugun hali na fad'a da juna mun yafa, mun tsane junan mu kan bambamcin ra'ayi, ina fatan zamu cire kyashi a ranmu mu rungume zaman lafiya." cewar Ladidi. Maman Dare ta yi dariya tace "To a madadin yan'uwana da basa jin hausa sosai, muna mika namu hakurin gare ku da fatan zamu cigaba da kasance wa cikin farin ciki da zama lafiya gaba dayan mu duk kuwa da bambanci yare da addini da muke dashi." " Tabbas auratayya na daya daga cikin abun da ke haddasa zaman lafiya, domin sanadin auratayya ne zaman lafiya da farin ciki suka wanzu cikin gidan nan, ina fatan kowa zai maida hankali wurin bada aure tsakanin al'umma domin hakan na bada gudunmawar zaman lafiya." cewar Inna Talatu. Mai unguwa ya kalle su yace " Lallai haka ne maganar ku gaskiya ce, domin dukkan mu masu laifi ne, mun kasance mutane marasa hakuri a rayuwa, komai muna sanya ido kanshi, mun kasance mutane masu addini da ban da kuma harshe wanda mu kammu muka kasa hade kai mu zauna lafiya, amma ina fatan yanzu zamu yi hakuri mu duba akasin da muka fuskanta a baya mu hadu mu gyara da kanmu. Mu gudu tare mu tsira tare domin zaman lafiya yafi zama dan sarki." Kowa ya yi na'am da zancen su aka hadu aka nemi yafiyar juna aka yi addua aka tashi. Mai unguwa ya yi musu sallama ya dau matarsa suka wuce gida cikin farin ciki da annashuwa. *GIDAN MAI UNGUWA* Bayan sun dawo aka zauna hira bayan magriba. Mai unguwa yace " Ina fatan zaku yi hakuri da halina muci gaba da zaman lafiya daku, kuyi hakuri ku yafe min duk abun da nayi muku." Cikin farin ciki suka dinga murna suna jin dadin canjin da aka samu daga mai gidan nasu. Rayuwa kenan yau mai unguwa ne ya bada ijiyar mabudin rumbu a hannun matanshi saboda tsananin zaman lafiya. Yau gashi duk sun fahimci juna sun yanke duk wani abu da zai haddasa masu rashin fahimta, sai fatan daurewar zaman lafiya. Ina fatan madaukakin sarki Allah ya cigaba da zaunar damu lafiya, da kasar mu lafiya. Allah ya bamu ikon fahimtar amfanin zaman lafiya, mu rungume zaman lafiya fiye da tashin hankali mu hade kanmu cikin aminci da salama ameen. Alhamdulillah tammat bihamdi, nan na kawo karshen wannan littafi na 'YAN GIDAN HAYA, ina fatan Kuskuren dake ciki ubangiji ya yafe mun, wanda nayi dai-dai Allah ya karbi niyyata na fadakar d al'umma muhimmancin zaman lafiya ya sanya muyi tarayya cikin ladan da dukkan masoya. *Ina yi muku fatan alheri masoya duk inda kuke, Allah ya sada mu da alheri, na gode ma kowa da kowa duk masu jumurin bibiyar littafi na tunda ga kan BADDEEYERH, GIDAN MARAYU, SANADIN K'AWATA, SAI KUMA 'YAN GIDAN HAYA.* *Ku kasance dani cikin TUSHE MAFARI domin yanzu wasan ya fara, tare da daukacin members dake rubutu kan _TUSHE MAFARI_ . Ga Fauziyya Lawal Ammany muna tafe muku da wani sabon littafi mai suna _BAHAGON TUNANI_ nan ba da dadewa ba insha Allah fans fatan alheri.* _Allah ya daukaka zamani writers ya kara mana zumunci tsakanin mu ameen_ SummaryInformation DocumentSummaryInformation WpsCustomData TECNO LD7 WPS Office Normal Times New Roman Times New Roman Calibri Calibri !%),.:;>?]} $([{ 50d554a6bc864332a7ebfcd21a03d2f9
Chapter 11 · 0% Book details