Sashe 8
Yan Gidan Haya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
idan Allah ya baka mata irin nawa, na tabbata mutuwa zaka yi." "To babbar magana kenan dai mata ne suka tasa ka gaba Ranka-ya-dade?" "Kwarai kuwa matan gidana Jummala da Hannatu duk munafukai ne, don yanzu zakai fad'a da wannan idan kaje wurin dayar to billahillazi ita ma fad'a zaku yi." "toh na gane, kenan sun hade kai?" "Kamar kashin awaki kuwa." "wannan ai abune mai sauki, kawai aure zaka kara." Da sauri mai unguwa ya dubi shi yana zare idanu "Aure fa kace Kallamu?" "Kwarai kuwa aure zaka kara, kuma yarinya zaka auro." Shiru mai unguwa ya yi can kuma yace "To ina zan samu matar auren Kallamu idon gari?" "Don wannan ai mai sauki ne, Ladi kawai zaka samu ka aure ta." "Wacece Ladi kuma?" "Diyar Maman Ladi ta gidan 'yan haya." Zabura mai unguwa ya yi yace "Kallamu baka kaunar farin ciki na billahillazi, ban da haka ta ina zaka hadani da wannan matar mai kirar samudawa kace na aure diyarta?, matar da ko mutuncina bata gani?" Kallah ya dubi mai unguwa yana dariya" Ranka-ya-dade ai uban yarinyar yana iya komai kan kudi" "Kenan zai bada diyarsa don kudi?" "Na rantse maka zai bayar, amma ga wata shawara." ya matsa sosai kusa da mai unguwa sukai kus-kus, dariya suka sanya. Mai unguwa na fadin "Haka za a yi Kallah shawara mai kyau, nagode sosai Kallamu idon gari zan same ka gobe." "To Allah ya kaimu." Sukai sallama ya wuce, shi kuma mai unguwa ya shiga gida cike da farin ciki. *Tabdijam! Wata sabuwa kenan, muje zuwa..* *Badeeyerh Beauty Queen* [3/1, 12:45 PM] Beauty Queen: *'YAN GIDAN HAYA* . *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Badeeyerh Beauty Queen* Dedicated to *AUNTY ZETTY MAMAN HANAN* Zaku iya samun littafan mu a Facebook Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu [email protected] Dedicated to *GSS Dr. Ahmad makarki hayin Banki kawo. Ina mutukar alfahari daku sosai duk inda kuke, Allah ya kara ilmi. One love 2013* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *55~60* Mai unguwa na shiga gida ya nemi wuri kan turmi ya zauna, yana cika yana batsewa shi ga mai gida sai zare ido yake. Ya dubi matan ba wacce ta kalle shi ya yi kwafa yace "Na kusa kawo karshen wulakanci a gidan nan." Babu wacce ta kalle shi sai aikin su suke ta yi. " Jummala zan kara aure kwananan nan billahillazi." Duk suka kalle shi cike da farin ciki kwance kan fuskar su, Hannatu tace "Kai amma naji dadi wallahi, yaushe ne bikin Malam?" Harara ya daka mata" Munafuka mai bakin hali kawai, harda murna ko?, to billahillazi ba da wasa nake ba." "Malam ai murna muke yi zaka kara aure shiyasa muke tambaya." cewar Jummai. "Lallai matan nan iyayen ku sun koya muku mugun hali, inace idan za ayi ma mace kishiya haushi take jin, amma ku don tsabar algungumai ne wai murna kuke ko?" "Malam kenan mai hali bai canzawa." "Ke Jummala alqur'an ki fita idona, bazan canza halin ba inga uban da zai can zani." "Allah ya baka hakuri." ta shige dak'i, ganin haka Hannatu ma ta shige dak'i tana hararar shi. "Duk zaku gane kuranku billahillazi bari na auro yarinya danya sharkaf ku gani." ya kakkabe rigarsa ya fice daga gidan yana sababi. *CIKIN GIDAN 'YAN HAYA* Kwana biyu anyi sauki da fad'a, ana zaman lafiya gidan yasha iska. Ko wacce na sana'arta cikin lumana, mazan su na cikin kwanciyar hankali. Gashi an fara wahalar ruwa kuma babu na fanfo, da kyar ake samu a rijiya. Da asubar fari suke rige-rigen fitowa dibar ruwa a rijiyar, kowa na kokarin ya ri ga wani diba, idan ka ri ga tashi ka diba sai a dinga hararar ka ana yada habaici. Yau duk suna dak'i basu fito ba, sai matar Malam tana zaune tana wanke-wanke hanyar fanfo ita kadai, kawai taga an kawo ruwan fanfo. Da sauri ta karasa ta kashe fanfo tana waige kar wani ya ganta, ta ruga dak'i ta kwaso robobinta masu yawa ta nufi fanfo. Ta dinga tarawa tana cikawa. Jin karar zuban ruwa yasa Maman Dare lekowa, aikuwa tana ganin ruwan fanfo ne ta koma dak'i da sauri ita ma ta debo kayanta harda tukwane ta nufi fanfo, daga ita sai matar Malam ke jidar ruwa suna kai wa dak'i. Abule ta fito zata bandaki ita ma taga wannan al'amari, amma maimakon ta yi yanda sauran suka yi na yin shiru, it kurma guda ta yi tana sanar da mutan gidan an kawo ruwan fanfo. Da sauri suka dinga fitowa da manyan robobi suna rige-rigen bin layi. Haushi ya kama Maman Dare ganin gayyar da Abule ta yi musu tace "Shegiya mai hankali a hannun riga." matar Malam ta fashe da dariya "Banza ce ai bata da nutsuwa." Ba wacce ta kula su, kowa so yake ya samu ruwa. Maman Ladi ta ga alamun za a raina mata hankali ganin harda tukunya ake diban ruwa, gashi bata da ruwan ko kadan dan haka tace "Yakama ta kusan me kuke yi, kubari muma mu diba gaskiya." "Maman Ladi a dai bi layi sannu a hankali zamu samu." cewar Inno. "A'a Inno duba fa ki gani harda tukwane dan bakin ciki ake dibar ruwa." "An saka ayi yanda za ayi damu." cewar matar Malam. Shiru Maman Ladi da Inno suka yi basu kara magana ba, ganin Iya beji na hararar matar Malam. Can dai da suka ga zasu iya rasa ruwan, Iya beji ta kutsa ta warce tukunyar hannun Maman Dare ta yi jifa dashi ta aza nata robar. Maman Dare ta kalle ta ta kalli tukunyarta dake yashe a kasa tace " iya beji nawane fa bana matar Malam ba kika yadda." *Badeeyerh Beauty Queen* [3/1, 12:45 PM] Beauty Queen: *'YAN GIDAN HAYA* . *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Badeeyerh Beauty Queen* Dedicated to *AUNTY ZETTY MAMAN HANAN* Zaku iya samun littafan mu a Facebook Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu [email protected] *Wannan shafin na kune hazikan masana, jagororin adabi, _MARUBUTA GROUP_ gaskiya bani da group a whatsapp dake ilmantar da al'umma da kuma koyar da zallar adabi irin ku, ina alfahari daku a kodayaushe fatan alheri ga ilahirin al'ummar wannan gida, Allah ya kara daukaka ya bar zumunci mun gode.* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *60~65* Harara Iya beji ta zabga nata, "Ai nasan na kine shiyasa na yarda shi." "Lallai ma Iya beji, mun ri ga ki zuwa layi ai." cewar Inno. "Baku damu ku samu ruwa ba, ai wuri kuka samu ku ka tsaya." "Dalla can matsa min." Maman Ladi ta bige robar hannun Iya beji ruwan y zube, ta sanya nata robar. Haushi ya kama Iya beji ita ma ta kifar da ruwan Maman Ladi. Nan fa fad'a ya kaure tsakanin su, Abule ganin yawanci hankalin su na wurin rabon fad'a yasa ta dinga jidar ruwan tana kaiwa dak'i. Maman Dare ta yi dariya ita ma rabi sahun Abule, lura da hakan da Inna Talatu ta yi ne yasa ita ma ta tara robarta bakin fanfo, aikuwa Matar Malam ta kifar da shi tana fadin"Algungumai kun wani zo kuna jidar ruwa kamar.." Mari aka sauke mata wanda ya tilasta mata yin shiru. Inna Talatu ce rike da robarta tsaye tana hararar matar Malam, "Kece dai algunguma bani ba, banza kawai mai halin matsiyata." "Talatu ni kika mara?" "Kina da abun yi ne?" Haba sai fada kuma ya tsarke, suna yi suna jifar juna da robobin ruwa. Maman Ladi ta yarda Iya beji kasa gashi wurin duk ruwa ne, aikuwa ta bugu sosai ta kasa tashi. Maman Dare nasan shiga kuma tana tsoro don haka ta je taimakon daga Iya beji wanda ya yi dai-dai da Matar Malam ta jeho bokitin karfe ya sauka kuwa kan Maman Dare ta zube kasa jikin Iya beji. Kuka Iya beji tasa tana tsine masu Maman Ladi, da kyar Maman Dare to mike tana dafe da kanta ta taimaka ma Iya beji ta mike. Hayaniya da fad'a sosai suke yi a bakin fanfo. Shigowar Malam Lawal mijin Maman Ladi ne ya sanya Maman Ladi barin wurin da sauri ganin shi da manyan ledoji a hannu, ta amsa tana mai sannu da zuwa. Washe baki ya yi yace " ke kam kin iya haihuwa wallahi, wannan arzikin duk dalilin haihuwa ne."ya fadi tare da shigewa dak'i. Gudar da Maman Ladi tasa ce ta dakatar da fad'an da matan gidan ke yi, suka juyo suna kallonta. Yara suka dinga shigowa da kayan abinci suna zubewa kofar Maman Ladi. Ladidi ta karaso tana fadin " Maman Ladi wannan kayan fa?" "Ahayye duniya Ladidi gulma, to bari naje dak'i na tambayi wanda ya kawo sai nazo na baki satonri (story)" ta shiga dak'i ta same shi. "Baban Ladi ina ka samu kaya haka?" "Kedai bari uwargida kayan toshen Ladi ne, wani attajiri ya ganta shine dazu y kirani ya ban wa'innan kayan."ya fadi yana kirgo kudi a aljihun 'yan dari biyu. Maman Ladi t warce kudin tana cewa"Wannan rabo na ne kenan ko?, nasan dai an baka naka." "Kayya Maman Ladi kina da gajen hakuri baki zanyi dama wallahi, yanzu yaushe zamu sanya bikin?" "Sati biyu kawai za a saka saboda mahassada malam."cewar Maman Ladi. Gyada kai ya yi yana gyara aljihun shi wanda ke damke da kudi. Galala matan gidan ke bin kayan da kallo kamar makafi sun warke makanta, nan suka fara kus-kus aka manta da batun fad'an ruwa. Fitowar Maman Ladi daga dak'i tana washe jajayen hakoranta yasa suka marmatso kusa da ita domin jin kanun labarai. "Ladi ce zata auri wani attajiri shine aka kawo wa'innan kayan, ku duba harda su buhun shinkafar waina wallahi na samu karin jari." "Yanzu Ladi nawa take da zaki aurar da ita?" "A'a Talatu kardai kina bakin ciki kan wannan abun arzikin dana samu ne?" "To wani mai arziki kenan zata aura?" matar Malam ta yi tambayar. "Sai ranar auren zaku sani, nan da kwana goma sha hudi zaa yi bikin." Nan aka dinga cafta ana duba kayan arziki, Inno da Inna Talatu muraran suke nuna bakin ciki kan kayan, yayin da Maman Dare wacce har gefen goshinta ya kumbura sanadin wannan bokiti ke nuna ma Maman Ladi illar auran. Iya beji dama data samu ta tashi dak'i ta wuce da alwashin sai ta rama. Maman