Sashe 3
Yan Gidan Haya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abule ta yi kafin ta juya da nufin komawa daki, rabon ayi saiji ta yi Abule na fadin "Banza da kin hwadi mun wanda bai da hankali yau walla". Aikuwa jefar da wukar ta yi ta nufe Abule tare da cakumar rigarta ta yaga tun daga sama har kasa kasancewar doguwar riga ta sanya, sannan ta hau jibgarta kamar an aikota. Kokari take ta rama amma ba hali domin ba karamin riko Maman Dare ta yi mata ba. Ganin ana dukan Abule yasa matar malam fitowa tana fadin "Bari na rama wa kura aniyarta" ita ma ta hau jibgar Maman Dare. Maman Akintola ta dubesu sannan ta dubi yanda buhun kankararta ya fara ruwa, kawai ta karasa ta dauka tana cewa "Bana da kudi berinje kasuwa nawa kawai" ta fice. Maman David ce ta shigo daga wurin saida akamunta a waje, ganin wannan fad'a na wanda ka sani, ita ma kawai ta shigar ma Maman Dare. "wallahi ba za'ayi babu ni ba gara nima na rama abun da ya faru jiya" cewar Inna Talatu. Itama ta shiga cikin fad'an, sai dai nata kowa duka ta keyi sabanin matar Malam dake ramawa Abule, aikuwa da karfin tsiya itama Abule ta yaga t-shirt din dake jikin Maman Dare, hade da kai mata wawan duka a hanci da ya yi sanadiyar fitar jini. Ganin wannan jini ya harzuka Maman Dare ta gabza ma Abule duka a baki, sai ga hakori ya fado daga bakin Abule. Ihu ta sanya tare da rarumo iccen data yarda ta cire rigar da aka yaga tai kan Maman Dare. Matar Malam kuwa Maman David ta samu ta kwantar kasa tana duka kamar kayan wanki. Hargowa da hayaniyar su ta fito da sauran matan gidan, ganin irin fad'an da a keyi na wanda na sani ya sanya itama Maman Ladi shiga ta hau jibgar Maman David dake kwance kasa suka rufan mata ita da matar Malam. Iya beji na ganin haka tace "Abun nayi ne dole na shiga" ta rufan ma Abule da duka. Gida ya rikice, ba wanda ke kokarin bada hakuri sai dai ya shiga ya rama ma wanda ya sani koya fanshe haushin shi kan wanda yake tsumayi. Ganin ba mai rabo ya sanya Mairon Ado bude sakata, ta fice da gudu sai gidan mai unguwa. *GIDAN MAI UNGUWA KUWA* Zaune yake a zauren gidan sa tare da yaran shi Sani da Lado. Ya dubi Lado yace, "Ya kamata kayi aure badi Lado, ka girma da yawa ga kannen ka nasan kai suke jira" Sosai kai ya yi yace "Insha Allah Baba a tayani da addu'a" "To Ubangiji ya yi maka zabi na gari" "Ameen Baban mu" Sani ya amsa. Mai unguwa ya kalle shi "to mara kunya dama nasan saikai ai, tashi ka bani wuri" tashi ya yi yana dariya ya shiga cikin gidan. Mahaifiyarsa ce zaune bakin madafi tana gyaran shinkafa. "sannu da aiki Mama kawo na tayaki" ya fadi yana niyar amsar tiren shinkafar. "A'a Sani barshi na gode, jeka ga Hanne can a wurin dabbobi tana shara ka amsa ita sai tazo muyi girki" "to Mama" ya wuce. Kasancewar suna zaman lafiya kamar ba kishiyoyi ba, yasa komai nasu tare suke yi. Ta taho tana fadin "Maman Sani shine zaki sanya shi aikin wahala maimakon ki bashi shinkafa ya tsince?" "A'a Hanne gara ya amsa ai, kizo nan muyi aikin abinci" "To shikenan na gode" ta zauna suna hira suna aiki. Mai unguwa ya shigo yana hade fuska ya kalli Hanne "Sai a kaimin ruwan wanka bandaki" "Malam tun dazu fa na sirka ruwan, da naga baka shigo ba shine na juye nai wanka" "Hanne! Hanne! Hanne! Sau nawa na kira ki?" "Uku malam" ta bashi amsa. "To wallahi tun da girma da arziki ki nemo min ruwan wanka na, in ba haka ba billahillazi karar ki zan kai gurin ubanki." Cikin takaici Jummala ta kalle shi tace "Malam wulakancin ka ya fara isar mu cikin gidan nan,meye na saka uba cikin wannan maganar? To wallahi na gaji da wannan halin naka" "Yo ba sai a dakeni ba idan za'a iya, ko kuma a rama zagin" "Ba wanda zai deke ka balle ya rama zagi, saboda munsan darajar aure, amma wallahi halin ka ya isheni" "Aikin banza ruwan wanka nake bukata yanzu ba sai anjima ba" Ta kalle Hannatu wacce ko dago kai ba ta yi ba dan takaici tace "Hanne juye mai ruwan sanwar can, gara ya fita ko zamu sha iska mai dadi" "Ba inda zani ina cikin gidan nan naga mai fitar dani." ya fadi lokacin da yake shiga dak'i. Ba wacce ta kula shi cikin su, Hannatu ta juye mai ruwan ta aje bakin kofar bandak'in. "Malam ga ruwan nan na ajiye" "gani nan zuwa ai 'yar magoriya, zaki fadawa makawafta zanyi wanka ko?" Bata amsa mai ba, taci gaba da gyaran shinkafarta. Yana fitowa ya dauki bokitin da niyar shiga bayi, sai ga Mairon Ado ko mayafi babu ta shigo a guje tana kiran "Taimako! Taimako mai unguwa uban al'umma, gidan 'yan haya zasu janyo a daure ka shekara dari a kurkuku idan sukai kisa a unguwar ka." Sakin bokitin ruwan ya yi ya tuntsire kasa ya bita da gudu, Hannatu na fadin" Malam baka warke ba zaka koma?" Ina tuni ya fice daga gidan. *Badeeyerh Beauty Queen* [3/1, 12:36 PM] Beauty Queen: *'YAN GIDAN HAYA* . *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Badeeyerh Beauty Queen* Dedicated to *AUNTY ZETTY MAMAN HANAN* Zaku iya samun littafan mu a Facebook Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu [email protected] *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *25~30* Tallafe kumatu ta yi tare da duban Jummala tace "Maman Sani kina kallo ko?" "Kema ce da neman magana wallahi, yaje shiyasa ni." Nan suka cigaba da girkinsu suna hirar halin mai gidan nasu. *A GIDAN 'YAN HAYA* Shigowar mai unguwa ya yi dai-dai da bugawa Maman Dare icce akai wanda Abule ta yi wannan aiki. "Kai! Kai! Kubari nace don iyayen ku" cewar mai unguwa. Ina! kamar basu ji ba domin Iya beji ce ta rafka ma Abule icce itama ganin Maman Dare zube a kasa tana kuka. Shake wuyan Iya beji Abule ta yi tana jijjigata, wanda ya sa juwa dibar Iya beji ta zube a kasa, Abule ta hau kanta tana duka. Ganin haka Maman Dare dake dafe da kai ta dau iccen da Iya beji ta yarda da nufin dukan Abule dashi, ganin haka mai unguwa ya yi tunanin shiga tsakani aikuwa sai a gefen kafadarshi yaji saukar iccen wanda ya haddasa mishi yin taga-taga kamar zai fadi, kafin ya samu ya tsaya a gefe dafe da kafadarsa da yake ji kamar zai cire don tsananin zafin da yake ji. Mairon Ado dake labe tana leke, ganin an rafka ma mai unguwa icce yasa ta kurma ihu sanin cewa yanzu ba mai rabon wannan fada. Ganin ihun nata bazai yi maganin komai ba, yasa ta shiga dak'i ta dauko bokitin ruwanta tare da sheka masu Maman Ladi dake dambe a kasa. Saukar ruwan yasa suka mike a firgice suna kallon mai wannan aiki, yayin da mai unguwa ke duk'e a kasa ya dafe kafadarsa kamar ya yi kuka. Maman Dare ta samu gefen kumatun Abule ta gantsara mata cizo wanda ya sanya ta saki Iya beji ba shiri ta kurma ihu domin taji zafin cizon. Sanadin da ko wacce ta mike tsaye kenan ana kallon-kallo. Shigowar Malam Isah da Baban Dare kenan gidan domin makwafta suna jin wannan fad'a amma suna tsoran shiga gidan. Shigar mai unguwa ma duk akan idanunsu, jin ihun ya cigaba suka san mai unguwa baiyi nasarar rabawa ba, shine suka kira mazajen a waya. Kasancewa suna kusa domin kanikawane su biyun a bakin titin kan layin. Baban Dare nufi mai unguwa dake tsugunne ko numfashin arziki ya kasa yi, yace "Mai unguwa kina lafiya, menene ya same ki?" Cikin zafin mai dashi jinsin mace ga kuma azabar ciwon hannu yace "Dalla daukeni ka kaini gidan Usaini mai dori kafin hanuna ya lalace, kuma wallahi sai nayi shari'a da matar ka". Duk da Baban Dare bai fahimci abun da mai unguwa ke nufi ba, amma yasan wurin Usaini mai dori, don haka ya mike yana kiran "Esa kizo ki rike mai unguwa akaita wurin Huseni ya yi gyara annu nata". Da sauri malam Isah ya karaso don dama yana tsaye ne wurin su Inna Talatu dake zage-zage. Suka rike mai unguwa zasu fita da shi, ya juyo yace "ke matsiyaciya! Wallahi ki jira na dawo billahillazi sai nayi karar ki wurin hukuma". Ba wanda ya tanka shi har suka fita, malam isa cike da zullumin mai zai faru idan suka bar gidan? Sanin cewa zasu iya yin wani abun ya sanya ya kalli baban Dare sanda suka isa waje yace "Ka rike mai unguwa ku tafi nasan matan nan zasu iya yin wani aika-aikar, bari na koma gidan" ya fadi cikin harshe turanci yanda baban Dare zai fahimta. Ya gyada mishi kai kawai tare da kara riko mai unguwa domin su tafi, fir mai unguwa ya dage lallai sai malam Isah yazo an tafe tare dashi duk da bayanin da ya yi mai, amma mai unguwa ya dage. Haushi ya kama Baban Dare yace "ke mai unguwa kina so mata namu ya yi kisa ne? Kina gani fa mun bershi shi kadai ya na fada ba meza a gida fa." "Yo ina ruwana dasu? su kashe kansu mana, amma billahillazi sai kun kaini gidan Usaini dukkan ku." "Haba mai unguwa taya kake tunanin dukkanmu mubar gidan? Kiran mu aka yi domin tsawatar musu, amma ganin halin da kake ciki muka zabi taimaka maka, shine kuma kake cewa su kashe kansu?" cewar Malam Isah. "Esa berta ki shiga gida, nine kadai ze kaita gidana huseni tefi kawai" Baban Dare ya fadi. Malam Isah ya wuce ba tare da sauraron abun da mai unguwa ke fadi ba. Baban Dare ya kalli mai unguwa dake ta aikin sababi, ya nade hannun riga tare da daukar mai unguwa da nufin goyawa a bayan shi. Ganin wannan aiki yasa mai unguwa daga hannun mai ciwo ya kaimai duka a baya, wanda yasa hannun kara amsawa sai kuma ya dafe tare da matsar kwalla don ciwo .Baban Dare ya kalli mai unguwa yace