Sashe 2
Yan Gidan Haya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
madadin kumin jaje shine ko wacce zata bude baki kamar kofar gari tana dariya, to wallahi na karaji ku gani." Shiru sukayi suna kallon shi, jin ya kuke yana sababi hade da tallafe kanshi dake tsananin bugawa ya shige dak'i. "Maman Sani abinci ya sauka" "to Hannatu zuba mana muci" "Nima a zuba min zanci insha magani." Suka ji mai unguwa na fadi. Zuba mai sukayi aka kai mai, nan suka zauna sunaci, sai da ya cinye yasa ruwa ya kalle su. "Amma kuwa abincin nan da dadi yake, ina kuka samu shinkafa?" "Malam kenan, ai rumbu muka bude muka debo." "Rumbu Jummala?" "Eh Malam ko so kake mu zauna da yunwa bayan ka zubar mana da kumallon safe" ta bashi amsa cikin zafi itama. Da yake yasan halinta idan ranta ya baci bata mai da sauki, dan haka yace, "To shikenan an debo Allah ya isa, kuma anci Allah ya isa." ******** Zaune ko wacce take a bakin kofarta tana gyaran kayan sana'arta. Maman Usman tana ta yi musu nasiha kan abun da suka yi yau basu kyauta ba. " Yanzu ba kuji kunyar kanku ba don Allah, ace matan aure a ofishin yan sanda?" "wallahi Maman Usman duk laifin wa'innan munafukanne" cewar Ladidi tana nuna su Iya beji. Aikuwa Maman David ta mike tana fadin, "Ledidi kace nine munafuki? ehen baban kane munafuki." "Babana fa ki kace, don uwarki na kira sunan ubanki ne?" "Ladidi amma magana nake yi daku ko?"Maman Usman ta fadi cikin tsawa. "Haba Maman Usman kina ji fa wai ubana take cewa munafuki" kawai ta saka kuka tana cigaba da fadin, "Malam mai carbi har ya bar duniya bai taba zagina ba, amma yau ga wata tsinanniya ta zage shi dalilina." "Wallahi ki zagi uban babanta Ladidi karki yarda taci bulus" cewar matar Malam dake zaune tana gyaran kayan miya. "Au Matar Malam ina magana kina kara iza wuta ko?" "A,a ayi hakuri Maman Usman na tuba." Nan dai Maman Usman ta sasanta tare da kara basu hakuri, da nusar dasu illar abun da sukeyi. Da yake suna ganin girmanta yasa suka aminta da abun da tace musu kamar gaske. Da daddare Maman Ladi ta kafa kaskon wainarta ta fara sana'arta a kicin din gidan. Bata kula kowa ba da yake tana ciki dasu kan kudin maganin data kashe, ta fara sana'arta masu siye nata zuwa. Mama akintola ce ta fito da niyyar daura girki, bayan ta dawo daga wurin sana'arta. "Iya Ladi kenan ya kasuwa fa" "lafiya, kuma sunana Maman Ladi ba iya Ladi ba." "oh I'm sorry Maman Ladi" "Allah ka tsine ma duk matar data zageni da yare." Inna Talatu dake zaune bisa rijiya ta kwashe da dariya, "Kai jahilci dai baiyi ba wallahi, su oo a taimaka a je makaranta" "Malam Dauda dai baida kudin zuwa makaranta nasani" Maman Ladi ta bata amsa. "Aifa shiyasa a kace sorry mutum ya zata zagin shi akayi, gara ubana zamanin su babu makaranta" "Wai cin danko harda su kaza"cewar Ladidi. "Ganemim hanya Ladidi wai makaho yaso tsegumi" "a,a ba dani ba gada a hurumi Maman Ladi" A fusace Inna Talatu tai kan Maman Ladi dake zuba waina, aikuwa kaya-kaya aka hau dambe kan tandar waina. "Maman Usman taimaka ki fito kafin ayi aika-aika cikin gidan nan" Baiwar Allah da sauri ta fito jin maganar Ladidi, wanda yasa sauran matan gidan fitowa. Tana shiga kicin din lokacin Inna Talatu ta daga bokitin kullun waina sai a jikin Maman Usman. *Badeeyerh Beauty Queen* [3/1, 12:34 PM] Beauty Queen: *'YAN GIDAN HAYA* . *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Badeeyerh Beauty Queen* Dedicated to *AUNTY ZETTY MAMAN HANAN* Zaku iya samun littafan mu a Facebook Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu [email protected] *Ummyn Yusrah nida sweet mum Rano muna godiya da dedicating Allah ya kara basira, muna Jin dadin Rayuwar Aseeya.* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *15~20* Wani irin zabura Maman Ladi ta yi ganin an shekar da kullin waina kasa. Ita kuwa Maman Usman mamaki ya hana ta motsi ganin wannan almubazzaranci irin na Inna Talatu. Bakin wuta Maman Ladi ta dauka ta yi kan inna Talatu tana duka inda Maman Usman ke kokarin raba su, ganin ta kasa yasanya ta fara kiran sauran matan gidan dasu kawo mata dauki. Dai-dai shigowar malam Isah mijin Inna Talatu, yana hango wannan fada ya afka kicin din da niyar ceto matarsa. Rufe su da duka Maman Ladi ta yi ta ko'ina tana fadin, "Dama haushin ku nake ji, kuma wallahi a biyani kullin wainata ko na daki kudina yau." ganin da gaske ba zata bar dukan su ba, yasa Maman Usman shiga tsakani. Maman Ladi ta sauke bakin wutan tana haki gata dama jibgegiya. "Zo ki fita daga kicin dinnan inna Talatu" cewar Maman Usman tana nuna mata hanyar waje. "Ba inda zani wallahi sai na rama dukana da ta yi harda hadawa da mijina." "A,a Talatu mu fita kawai ina ganin aljanu gareta." Cikin takaici ta kalle shi "kaidai wallahi anyi matsaoracin namiji, to yau kodai ka rama min dukana wallahi ko kuma ayi tashin hankali a gidan nan". Shiru ya yi yana kallon Maman Usman wacce ke tsaye cikin takaicin fadan su ga shi anyi mata wanka da kullin waina. "baki daku bane wallahi shiyasa kike tunanin ramawa, saura kudin wainata wallahi kodai a bani ko kuma mutum yaji a jikinsa." Fadin Maman Ladi kenan dake tsaye rike da robar wainarta. "Maman Ladi nawane kudin wainar?" malam Isah ya tambaya domin bai kyaunar a sake wani tashin hankali tunda yasha jibga. "hadin dubu uku da dari tara nayi, na saida ta dari tara" ta bashi amsa. Lalibo aljihu ya fara yi yaji an riko shi da karfi. Gaban shi ya fadi ya zata wani fadan ne dan haka a tamanin ya waiga, Inna Talatu ya gani, ya saki ajiyar zuciya. "lafiya kuwa Talatu?" "Na rantse da Allah ba zaka biya kudin nan ba, bata isa ba ubanta ya yi kadan bayan dukan da tai mana, sai kuma a kara da kudi to wallahi bazaka biya ba." kau! Taji an dauketa da mari. Maman Ladi kuwa kallon matan dake leke ta yi tace "Angama ai sai ko wacce shegiya ta bar lekena" "A, a Maman Ladi karki sake ki zage mu wallahi" cewar matar Malam dake tsaye gefen rijiya. "Na zaga nace ko wacce shegiya naji duka, yan iska maglmata" "Ko wacce ta tafi dak'in ta don Allah na roke ku" Maman Usman ta fadi lokacin da take fitowa daga wanka. Sumi-sumi suka wuce ba wacce ta kara magana. Washegari Lahadi Kasancewar yau lahadi, yasa da yawansu wanki su keyi da kwalemar dakunansu. "Matan gida zanje sunan kanwata sai na dawo, don Allah mu zauna lafiya" cewar Maman Usman sanda ta fito daga dak'inta. Sukai mata a dawo lafiya ta fice. Mairon Ado zaune kofar Abule suna wanki tare, ta dubi Abule tace. "Ban baki labari ba kawata." "Menana ankayi hwadi mun". "Wata mata ce a tsohuwar unguwar da muka taso, kullum saita tsine ma mijinta, gata da masifa amma bata da karfi." "Kai Mairo taya kinka sani?" Abule ta tambaye ta tana cigaba da wankinta. Mtsw... Mairon Ado ta yi tsaki "kefa dadina dake wulakanci, to ai a kusa da gidanta nake". Girgiza kai Abule ta yi tana dariya domin ta gane dawa Mairon Ado ta keyi, tace "Alkur'ani Mairo wanga batu nake haka yiki, kin hwadi gaskiya" ta mika mata hannu suka tafa hardasa shewa. Ba tare da sun lura ba, saijin saukar ruwa sukayi a jikinsu. Cikin masifa suka mike tsaye suna kallonta, Maman Dare ce mai icce ta wanke su da ruwa. "Me mukai miki ke kuma?"Mairon Ado ta tambaye ta cikin bacin rai. Kasancewar tana jin hausa sosai yasa ta fahimci abun da suke nufi tace. "Mairo muna zaune lafiya shine zaki janyo mana masifa ko, ina ruwanki da ita?" "Tabdijam! Shine zaki watsa mana ruwa, to kanwar tsohuwar kice kenan?" "Mairo kenan, kinsan dai bani da lokacin batawa don haka ki shiga hankalinki dani." Tass! Abule ta dauketa da mari tana huci take fadin,"Kekam anyi bagidaja walla, yo mi naki da zaki wanke muna jikki da wanga ruwan wanki?to walla ki yi abun da yadda meki ba ruwana ta dake". "Yauwa Abule tawa haka nake so kicimin kaniyar duk wacce ta yi damu a gidan nan." "Barsu ta dani ina ma mace dukan tsiya walla ni bani daukar reni". "Ni kika mara Abule?" Maman Dare ta tambaya tana dafe da kuncinta. "Yo me zaki yi?" "Ina zuwa zakiga abun da zanyi yanzu kuwa" ta wuce dak'inta da sauri. Ita dama Mairo bata da karfin yin fada, dan haka tana ganin Maman Dare rike da wuka tai daki da gudu tare da danna sakata a kofarta. Abule ta ruga kicin ta dauko bakin wuta gashi sai ci yake wanda matar Malam ta hada ta dora girki. *Badeeyerh Beauty Queen* [3/1, 12:35 PM] Beauty Queen: *'YAN GIDAN HAYA* . *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Badeeyerh Beauty Queen* Dedicated to *AUNTY ZETTY MAMAN HANAN* Zaku iya samun littafan mu a Facebook Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu [email protected] When I Am Glad, You Are In My Smile, When I Am Sad, You Are In My Tears, When I Am Walking you Are In My Steps, When I Am Sleeping, you Are In My Dreams. I Love You! Abu Uthaemin. *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *20~25* InnaTalatu dake wanke injin nikarta ta kalle su ta yi dariya, domin duk zancen da suke yi tasan da ita suke, gashi yanzu ta kwabe musu. Maman Akintola ce ta fito daga dak'inta dauke da buhun kankara a kanta zata kasuwa, taga wannan aika-aika dake shirin faruwa, ta ajiye buhun tare da riko Maman Dare. "A'a Mama Dare menene yana faruwa aka, da wanini zakiyi fad'a da wuka?" Tana haki ta kalli Maman Akintola tace "waccan shegiyar zan koya ma hankali naga alama bata da shi". "kece shegiya wallahi ba Abule ba"cewar Mairon Ado dake makale jikin tagar dakin ta. Abule dake tsaye rike da bakin wuta ta yi dariya tana kallon Mairon Ado tace "walla ke kau kin rako mata matsoraciya na kawai" "A'a Mama Dare idan kayi fad'a da wuka kasen dai mai anguwa zata kai karan ka station ko? So please be patient". Hararar