BABI NA SHA BIYAR.
Uwa Uwa Ce Part 2 Complete Hausa Novel · about 36 min read
Abbati ya zagaye gidansa yafi a kirga. Babu wani lungu da sako da bai leka ba bayan fitowarsa daga wurin Baaba Mari. Akwai wuraren da rabonsa da taka kafarsa tun ana ginin. Wasu irin tunane tunane suka dinga zarya a cikin kansa. Son muhallin nasa ya darsu a zuciyarsa irin wanda bai taba ji ba. Sai idanu sun zaga sosai a cikin garin nasu ma za a sami gida makamancin nasa. Lallai shi yasa ake cewa idan an ga matashi da kudi bayan bashi da kwakkwarar sana'a ya kamata a bincike shi.
To wai ma ya aka yi bai taba jin korafi ko da wasa game da tarin arzikinsa da wadak'ar da yake da kudi ba a garin? Ko ana tsegungumi a bayan idonsa ne bai sani ba? Yau daya da ya yiwa gidan kallon tsanaki sai ya fahimci yawan titsiyen da Baaba Mari take yi masa akan wurin aiki. Wajibi ne uwa ta matsu da son jin silar rayuwa irin tasa.
Ga gida ga motoci ga kudi kamar bai san ciwonsu ba. Samarin garin da dama idan sun kawo kawunansu ko iyayensu sun musu jagora akan ya saka su a hanyar sana'arsa sai da ya cikasu da kudi. Ana karbe kudin zaka ga mutum ya ja gefe an koma kasuwanci ko a cinyesu a banza. Ya gode Allah da ya kasance ba shi da alhakin sanya d'an kowa a layinsu. Da yanzu bai san yadda zai yi da lodin zunubai ba. Ga nasa da yake fatan samun gafara ga na wasu da babu lallai su so tuba.
Kan kasaitacciyar kujerar kushin din dakin da aka yi domin kwanciya ya tafi ya kwanta rigingine. Tunani bai barshi ba har ya luluka yana tuna masa yadda aka yi suka kawo zuwa yanzu. Yayinda Munzali ya zama mukullin bude masa wannan duniyar, shi Abbati, shi ne ya fara mayar musu da ita sana'a a lokacin da Munzali ya kwanta ciwo. Shi ne ya nemi Shazali wanda ya kaishi wurin wani babban mutum.
Tunanin komai da kowa ya yakice ya sanya kansa a faifan zuciyarsa yana tuhuma. Shin yana wannan dabiar ne a matsayin sana'a ko matsayin namijin da yake jindadi mu'amala da jinsinsa? Amsarsa ita ce zabi na biyu.
Hakika ya yi mugun sabo da wannan dabi'a wadda ta sanya har yanzu sha'awar mu'amalar ta kan taso masa. A kalla kusan bayan kwana bibbiyu ko uku ya kan sami kansa a mugun yanayin son wannan abu. Yana jin wahala har ma ya kai ga siyan magani don wani zubin ko bacci kasawa yake. Haka kuma take a wurin Munzali shi ne ma dalilinsa na biya musu makudan kudade domin samun lafiya. M
Matsalar irin wannan zinar ya wuce mutum ya tashi watarana kawai yace ya tuba. Ita jiki take bi tana yi masa illah. Idan bukatarta ta taso mutum dole ya nemi hanyar biyanta ko ya wahala. Allah ne shaidarsu amma rabonsu da neman juna tun gabanin ciwon Munzalin. Shamaki ne Allah Ya saka musu sannan Ya maye musu zukata da tsaftatacciyar kaunar juna domin lokaci irin wannan.
Duk wannan abu zuciyarsa bata fasa fada masa cewa shi din har yanzu namiji bane. Soyayya dai ta zuciya da zuciya Farha yake yiwa. Tunaninta kadai sai da yasa tsigar jikinsa ta tashi. Yana sonta da dukkan abin da zuciya za ta iya bawa wanda take kauna. Burinsa na duniya akan mace ahi ne ya mallaketa a matsayin matar aure. A wayi gari wasu yara suna kiransa Baba suna kiranta Mama.
Duk mazan da yake mu'amala dasu kallon maza yake yi musu. Mata kuma suna nan a mata. Bai taba sanya kansa a ajin 'yan daudu ko wadanda suke karyar cewa da son jinsinsu aka haifesu ba. Shi lafiyayyen namiji ne wanda ya mayar da kusantar maza 'yan uwansa sana'a. Idan babu namiji zai rayu sarai da mace sai dai kawai illar wancan abu zai dinga damunsa kafin Allah Ya yaye masa jarabar.
Infact yana daga cikin dalilansa na cigaba da zama da Hanne duk irin rashin dadin zamansu kuwa. Tuntuni auren ya wuce na umarnin Mal. Sa'idu, domin kuwa a irin kudinsa da ya saketa idan har da mai ce masa don me ba zai wuce Baaba Mari da Gwaggo Jummai mahaifiyarta ba. Sauran kowa so yake ya zo ya auri tasa 'yar. Abin da ya hada auren nasu ma tuni an manta dashi. Shi da ita suna zaune ne kawai saboda auren rai gareshi. Babu soyayya, babu shakuwa sannan babu damuwa. Gara ma shi yana bata kulawa domin sauke nauyin hakki. Ita kuwa tsakaninta dashi bai wuce kudi idan har ta neme shi. Ga misali yanzu rabonsa da gida tun asabar daga zuwa daurin aure. Amma har yau ko flashing bata yi masa ba.
A kasalance ya tashi ya shiga hada kayansa na sakawa a wasu manyan akwatuna. Ya zabi aikin ne domin rage radadin rashin Munzali da Qibdiyya. Sai dai ko kusa bai sami abin da yake so ba. Komai ya taba indai nasa ne to Munzali ma yana da irinsa sak. Haka ya gama loda kaya masu muguwar tsada a jakunkuna da akwatuna ya jeresu a gefe. Sai da ya gama da nasa ya soma tunanin ta ina zai fara sabuwar rayuwa? Duk abin da ya mallaka da kudin zina mafi muni ne don haka dole su rabu.
To yanzu me zai ce da duniya? Yaya mutane zasu kalle shi? Da ya dauki aniyar sauya rayuwarsa sai ya ga ashe abu ne mai matukar wahala. Ashe rayuwar da ya bari lokacin yana dan shekara goma sha biyu sai bayan shekaru ashirin da hudu zai cigaba da ita. Abbati almajiri ne zai taso ya dora rayuwarsa daga inda Abbatin Munzali ya yi masa katsalandan. Abin da wuya....da matukar wuya.
Shaidan ya shiga kai kawo wurin nuna masa tarin kalubalen da zai fuskanta da zarar ya sanya kafarsa a waje. Ya shawarta zuwa ya baiwa Baaba Mari hakuri akan ta barshi da iya abin da ya tara yafi a kirga amma ya fasa. Dukiyar ta haram ce. Indai ba yana so daga shi har mata da 'ya'yan da yake fatan haifa a gaba su zama cikin wadanda Allah ba zai ji kukansu ba dole ya hakura. Shaidan din yana nan amma so da addu'ar uwa sun yi matukar tasiri a zuciyarda da gaske Allah take fuskanta. Faduwa ya yi cikin sujjada domin neman karfin zuciya daga Sarkin dake jujjuya zukatan bayi.
"Ya Rabbi kada Ka barmu. Idan Ka barmu munyi asara. Allah Ka haska min hanyar da zata bulle dani kamar yadda nake fatan Ka haskawa Munzali. Duk wani abin da zai lullube mana zuciya daga barin yi maka da'a Ya Allah Ka nesantamu dashi. Ya Allah Ka jagoranci sabuwar rayuwarmu kada Ka kunyata tubanmu a duniya da lahira. Ya Allah Ka rufe sirrinmu kada Ka bari mu tozarta a idon duniya."
Adduarsa kenan. Kuma ya yita cikin kuka da kankantar da kai hade da yakinin ganin kudurar Ubangiji akan lamarinsu. Abin da Allah Ya hukunta ba zai wuce bawanSa ba. Abin bukata bai wuce tsayuwa akan imani da kyautatawa Allah zato ba.
Yana tashi sai ga wayar Baaba Mari. Sarkin da baya bacci Ya juya zuciyarta. Hakika tun bayan fitarsa da abin da Munzali ya ce ya sami takwararta sai ta rasa sukuni. Hukuncinta na rabasu tun farko domin su jidadin tuba yana nan. A matsayinta na uwa dole ne tayi duk wani abu da ta san cewa zai taimakawa danta ya tuba. Tabbas d'a na kowa ne to amma fa game da naka Allah zai fara tambayarka ranar lahira kafin na wani. Sannan yana daga cikin sharudan tuba da aka koyar da ita a Islamiyya, bawa ya nesanci wurin da yake aikata wani sab'o, ko ya canja abokai ko abin da zai kusanta shi da hakan a yayin tuba. Shin ta so kanta kenan don tana nemawarwa danta tsira daga azabar wuta? Kwalla mai zafi ta silalo mata ta share. Zuciyarta a kuntace take. Lallai ita Mari tafi uwar da 'yarta take yawon karuwanci shiga tashin hankali. Luwadi? Luwadin da Allah Yasa aka kife al'ummar Annabi guda a sanadinta amma ace dan da tayi rainon cikinsa ta haifa kuma ta shayar ita ce sana'arsa?
Kaico! 'ya'yan mutane da suke cikin wannan mummunar rayuwa ba zasu kirgu ba. Wadanda suka shigeta a matsayin sana'a ko hanyar jindadi a sanadiyar almajiranci sun ninka masu shiga a gaban iyayensu. Babu dalili komai dadin bakin mutum da za a fada mata wanda zai sa ta taba goyon bayan a cigaba da tura yara almajiranci. (Wannan gaba zaman fayyace halin da almajirai suke ciki zai iya cinye ragowar labarin namu. Na dai yi imanin cewa mun sani ko mun saba jin labarai marasa dadi akan yaran da suka tsinci kansu a nesa da iyaye da sunan neman karatu. Fatanmu Allah Yasa masu ruwa da tsaki su kawo gyaran da ya dace game da rayuwar al'ummar nan a kowane fanni.)
Munzali! Matsayin Munzali ta tuno a wurin Abbati ba rawar da ya taka a rayuwarsa ba. Lokuta babu adadi Abbati zai turo mata katin waya ko da tana dashi ya ce don Allah ta kira Munzali.
"Ki yi hira dashi Baaba irin ta uwa da danta. Ki dinga yi masa fada kina bashi shawara. Yana bukatar hakan."
Tun tana kiran bayan Abbati ya saka ta har ta koma yi a karan kanta. A duk lokacin da ta kira sai ta kara jin kaunarsa a zuciyarta. Yaro ne mai saukin kai ga wanda ya fahimce shi. Mutum ne shi wanda yake fama da k'ishin (thirst) uwa a rayuwarsa. A hirarrakinsu yana bude mata sirrinsa da damuwa akan gidansu. A dalilin haka ta yi yunkurin hada zumunci da Asabe amma abin bai yi nisa ba.
Lokacin 'ya'yan nasu basu yi kudi kamar yanzu ba. Asabe ta dinga yi mata lakabi da Uwar Almajiri. Ko a waya suke gaisawa da wannan sunan take kiranta. Da aka yi masa haihuwa ya sanyawa diyarsa Mariyatul Qibdiyya kuwa kiranta tayi ta ci mata mutumci. Bata fadawa kowa ba har Abbati amma ta janye jikinta. Sai dai abin da ya sami takwararta ya mata karan tsaye. Fyade ta furta kazamar kalmar a raunane. Tufka da warwara basu barta ba sai dai tunaninta ya tsaya wuri guda. A takaice raba Abbati da Munzali ba zai zama mafita ba. Hadasu da nuna musu hanya a tare shi ne jigo.
(Wato 'yan uwa na fa sha korafi akan dalilin sanya Baaba Mari ta umarci Abbati da rabuwa da Munzali. Da yawa basu san manufar yin haka ba. Na so nuna muku hukuncin farko da iyaye kan zartarwa yaransu ne a duk lokacin da aka sami bullowar mummunan hali. Za ka sami uwar abokin barawo da son raba danta da barawon harma tana ikirarin zai bata mata d'a. Sau tari bata ma san cewa nata shi ne ya bata na wani ba. Illar rabawar musamman ga masu wayo shi ne su dinga haduwa a bayan idon uwa.
Idan da zata zurfafa tunani sai ta gano matakin farko shi ne ta kokarta wurin taimakawa duka yaran da suka yi tarayya a barna. Ita da iyayensu su hada kai su gyara. A inda aka kasa samun haka sai guda daya ta gwada. Sai taga hakan ya kasa zama maslaha sannan ta canja tsari. Idan zamansu tare da fadan da nasihu yaki aiki sai a shigo da shawarar rabuwarsu. Wannan shi ne abin da naso nunawa da hukuncin farkon. Wallahu Ta'ala A'alam)
"Zo ina son ganinka"
Da sauri ya mike domin ya zata jikin ne. Ya sameta a zaune a dakinta ita kadai. Ta nuna masa wurin zama da hannu.
"Abbati na baka amanar kanka da ta Munzali. Na yarje muku zamewa juna jagora a kokarinku na inganta tuba. Na amince ku hada kai ku nemi taimakon Allah akan umarnin da na baku na rabuwa da duk wata dukiyar haram. Wallahi Abbati albarka ba za ta bi ku ba alhali kuna ci kuna sha da kudin zina. Rayuwarku za ta tafi akan tsarin da zai haskaka zukatanku ne a lokacin da ku ke cikin halalinku komai kankantarsa. Ita haram banda tarin zunubi harda kuncin zuciya take sakawa."
Ko kusa bai zata abin da zata fada masa ba kenan. A bazata mafi girma kalamanta suka dirar masa. Hawaye ya cika idanunsa har ya zubo a lokacin da ya matsa ya kama hannunta ya rike cikin nasa.
"Allahu Akbar. Allahu Akbar. Baaba kin sani cewa ban taba kokwonta akan Sarautar Allah ba amma yau na kara imani. Na roki Allah kuma hakika Ya taba zuciyarki. Na gode. Mun gode"
Hancinta ta ja ta hanyar shaka alamun kukanta bai kare ba ta murmusa.
"Allah Ya karawa Annabinmu SAW daraja."
"Amin"
"Ka bar duk abin da kake yi ka tafi Kano domin Munzali yana bukatarka. Ni shaida ce ba don matsalar da ta taso ba da tuni ya biyoka."
Abbati yaji gabansa ya fadi "akan Qibdiyya da ya ambata ne?"
Baaba Mari ta gyada kai.
"Fyade aka yi mata"
"La haula wala quwwata..." Abbati ya ce a yayinda ya yi wata irin mikewa cikin mummunan tashin hankali.
"Ka nutsu domin a yanzu kai ne kwakwalwar tunaninsa. Idan kaima ka makance babu lallai ku iya daukar matakin da ya dace. Ka tafi Allah Ya tsare."
Cikin minti goma sha biyar har ya isa tasha. Wurin mutum uku ya biya domin motar tayi saurin tashi.
****
Ana amsa sallamar Suhaib Ayaah ma sai tayi cikin muryarta da ta dusashe saboda kukan da tayi. Ba a amsa ba. Sai dai cikin abin da bai fi sakan biyar ba ilahirin jama'ar dake cikin gidan
Honourable a wannan lokaci suka tsaya a bakin kofa. Sunan Ayaah kawai ake kira ana kukan murna da hamdala. Jikin Hasiya ta fada tana kuka sosai. Kukanta ya tayar musu da hankali. Farincikin da suke yi na ganinta ya koma alhinin jin daga ina take da kuma abin da ya sami suturar jikinta.
Honourable kurawa Suhaib ido ya yi yana neman fassara yanayin da ya gansu a ciki. Matashi mai jini a jika sanye da 'yar singiletin da ta bi jiki da damatsansa. Ga 'yarsa ta suturta jikinta da rigar da ya yi imanin ta matashin ce. Me yake faruwa? Gabansa ya shiga faduwa yana fatan ba abin da yake tunani bane.
"Ya kamata mu zauna aji me yake tafe da yaron nan ko?"
Larai ce tayi magana tana janyo Ayaah daga jikin Hasiya ta rungume. Gani take ta fi kowa damuwa da son jikokin nata na wurin marigayiya A'i.
Ita dai Ayaah hawaye kawai take yi tare da yayyenta Ummita da Murja har suka shiga cikin dan falon da ba zai dauki mutanen gidan ba. Basu san me ya sami kanwar tasu ba amma hankalinsu a tashe kamar na kowa. Mazan duka suna waje. Honourable wayar Abdulkarim ya kira ya fada masa dawowar Ayaah tare da tsawaita godiya akan taimakonsu da ya yi.
Zamansu Ayaah ke da wuya sai ga Anti Hasiya da kwanukan abinci. Murja ce ta karbi tray din ta ajiye a kasa ita kuma ta koma kusa da Ayaah ta zauna. Tana zaman Ayaah ta dora kanta a cinyarta ta cigaba da kuka. Kasa daurewa tayi ta biye mata suna yi tare har sai da Innayo tayi magana.
"Kun bar mutum a waje kin zo kin sakata a gaba da kuka maimakon ki rarrasheta."
Larai ta harareta saboda so take ace ita ce mai rarrashin. Bata son duk wani abu da zai nuna Innayo ko Hasiya sun fi ta sanin me ya kamata akan jikokin. Sai cewa tayi,
"Wani irin rarrashi a wannan yanayin da ake ciki? Ai ki barta tayi kuka ko zata sami sa'ida."
A tsakar gidan kuma Honourable ne ya ce da Suhaib idan babu damuwa ya zauna zasu yi magana. Bai yi mamakin jin hakan ba shi yasa ya zauna akan tabarmar dake shimfide a wurin. Honourable ya shiga falon ya ce don Allah su fito waje amma yana son a dan jira zuwan Abdulkarim. A ganinsa yadda ya kokarta masa yau dinnan ya kashe duk lalurar gabansa ya dace shi ma ya san me ya faru. Ita dai Ayaah ji tayi kamar wata igiya ta kwance daga wuyanta zuwa kafafu. Yawun bakinta duk ya kafe ta rasa na jika lebenta ma. Rawar jiki kawai take yi saboda firgici. Da Salima ta kula da yanayinta sai ta yiwa Honourable magana cikin hikima. Mutumin da yake a tsorace bai dace idanu su yi masa yawa ba a irin wannan lokacin. Tana gudun tayi musu karya saboda rashin sakewa. Shi yasa taga gara ace mahaifinta ne kawai da Hasiya.
"Inaga duk abin da za a tattauna gara ayi a nan. A kira saurayin da ya kawota ya shigo ciki sai mu baku wuri."
Larai da 'ya'yanta sun so kin tashi sai dai Salima bata barsu ba. Musamman ma dai 'yan uwan nasu. Ai kuwa ta hau fada akan cewa a madadin uwa tafi kowa cancanta da zaman jin bayanin Ayaah da bakonta.
"Don Allah mu koma dakin yaran nan tunda ya dan fi yin ciki. Sai kuyi shawarar a can ko don bakon da bamu san ko waye ba."
Honourable ne da kansa ya yi magana saboda ya san halin Larai. Jan zance zata yi, gashi shi kuma a matse yake yaji bayani.
Da suka fito Hasiya ta nunawa Suhaib kofar falon ta ce ya shiga suna zuwa. Suna zuwa Honourable ya ce da Hasiya, Innayo da Larai zasu zauna da yaran. Sai Abdulkarim idan ya iso. Daga jin haka Larai tayi gaba tana mitar ai 'ya'yan cikinta ya kamata ya kira ba Innayo ba. Babu wanda ya ce mata komai a cikinsu. Suna zuwa bakin kofar Abdulkarim ya yi sallama ya shigo gidan suka rankaya ciki tare.
Suhaib ya shiga ya sami Ayaah tana faman goge hawaye da rigar jikinta-rigarsa! Haka nan yaji hakan ya zo masa a matsayin kusanci da ita. Kasa yi mata magana ya yi bayan sallamar da ya yi sai kallon yadda ta take kuka.
A nata bangaren kuma ganinsa yasa taji wani kwarin gwiwa fiye da farkon shigowarta. Wasu hawayen ta goge ta dago kai ta dube shi.
"Don Allah ka rufa min asiri kada ka fadawa su Baba abin da ya faru. Ban san me zasu yi min ba."
Kwayar idanunta wadanda suka yi jazur gami da kankancewa Suhaib ya kalla ya dan yi murmushi.
"Kada ki firgitani yadda kika firgita kanki mana. Nace ki kwantar da hankalinki komai zai daidaita in sha Allahu"
Amsarsa bata bata nutsuwar da take nema ba domin ba abin da take muradi ya fada ba. Jikinta duk ya yi sanyi ta marairaice fuska.
"Kenan fada musu gaskiya zaka yi?"
"Banda gaskiya babu wani abu da zai fitar dake. Me zamu ce a matsayin dalilin da ya hadamu har na kawoki gida? Banga wani abu da zamu fada wanda zai gamsar damu kanmu ba balle su."
Bata hakura ba ta ce "Iyayena zasu ji kamar naci amanarsu. Don Allah..."
A tausashe ya ce "I will be here Ayaah. Zan yi musu bayani yadda zasu gamsu in sha Allahu."
Abubuwa taji suna shiga zuciyarta daga sautin kalaman har zuwa sakon da suke tafe dashi. Hankalinta ya dan kwanta amma tsoron bai barta ba. Turo baki tayi ganin magiyarta taki tasiri cikin kunkuni ta ce,
"Ni wallahi na zata ma sona kake shi yasa ka taimaka min."
Tun bayan zuwansa Kano a yau sai yanzu Suhaib ya yi dariya. Dariya mara karfin amo amma mai nuni da har cikin zuciya mai yinta yana cikin nishadi.
"Wato kin zata sonki nake?"
Ayaah ta murguda baki da kumburarrun idanunta ta ce
"Dariya ma na baka?"
"Ai dole nayi dariya."
Ance wai mai hali baya fasawa. To Ayaah ma bata manta tsiwarta ba tunda Danliti bai sami damar koya mata hankali ba. Juya idanu taso yi amma nauyinsu ya hanasu bata hadin kai. Sai ma zafi da suka yi wanda yasa ta runtsesu da sauri. Duk da haka bata hakura ba sai da ta ce,
"Ko a nan gaba kaji kana sona kada ma ka fada don ba zan baka hadin kai ba."
"Zamu gani" ya ce yana cigaba da murmushi.
Kofar da aka taba ta danyi kara ce ta kawo karshen maganar tasu. Honourable ne a gaba sai Minista, matan suna biye dasu.
An zazzauna kowa ya fuskanci Ayaah wadda ta rakube a jikin Anti Hasiya. Honourable ne ya soma magana cikin nutsuwar da ya arawa kansa ta dole.
"Kun san zaman me muke yi a nan? Ku dubi girman Allah ku fada mana gaskiyar abin da ya faru."
Ayaah baki sai ya soma rawa. Dauriyar da taso yi ta kasa sai kuka. Wannan yasa Suhaib ya karbi ragamar jawabin daga inda ya sani.
"Suna na Suhaib Tahir kuma a Kaduna nake da zama. Kanwata Mardiyya ita ce Alh. Munzali yake nema..."
Innayo ta gyada kai saboda tun dazu take yi masa kallon sani. Ya cigaba da fada musu ranar da ya fara ganin Danliti a wurin dinner. Sai ya sakaya ya ce matar dan uwansa ce ba matar babansa ba. Irin abubuwan da ya gani da maganganun da Danlitin ya yiwa Jiddo da Ayaah duk ya fada. Akan haka ne hankalinsa bai kwanta ba har ya karbi nambarsa a wurin Jiddo da zuwansa Kano. Dama duka abubuwan da suka biyo baya har ya sami damar kubutar da ita da taimakon Allah.
La haula wala quwwata illa billah. Suhaib yana bayani Anti Hasiya da Larai suna kuka. Innayo ma ba a barta a baya ba domin tabbas ba don tsarewar Ubangiji ba da yanzu suna kukan bakinciki. Honourable kuwa sunkuyar da kansa ya yi kasa. Shi kadai ya san halin da zuciyarsa take ciki. Sam ya kasa magana sai Abdulkarim ne ya dauki matsayin uban. Godiya ya fara yiwa Suhaib sannan ya koma kan Ayaah.
"Saura ke"
"Don Allah ku yi hakuri" ta fara cewa Larai ta daka mata tsawa.
"Za kiyi bayani ko sai na saba miki? Mutuniyar banza mutuniyar hofi."
Idanunta a kasa ta fadi abin da ya kamata ta fada. Tana magana hannunta yana cikin na Hasiya wadda ta rike domin bata kwarin gwiwa. Labarin bai yi mata dadi ba amma kuma bata so tsoro ya hanasu gane bakin zaren.
Kunyar duniya yau Ayaah ta gama sha. Da bakinta take maimaita yadda abubuwa suka kasance a gaban iyayenta da Suhaib. Ko ba a fada ba ita da kanta ta dinga ganin wautarta na yarda da zantukansa baro baro.
Honourable ya dago kai a fusace bayan ta gama magana.
"Taso ki zo nan?"
Suhaib ya kula da bacin ransa sosai. Shi ma zuciyarsa a cunkushe take da takaici amma bai bar tausayinta ba. Yana jin kiran da mahaifinta ya yi mata sai ya mike tsam. Hukunci ya zama wajibi sannan shi din bashi da hurumin hanawa.
"Bari na baku wuri"
Bai jira yaji abin da zasu ce ba ya fita daga falon. Haka Ayaah ta rarrafa gaban babanta ta kama kafafunsa tana kuka. Hakan bai hana shi tureta ba ya daga hannu zai mareta Abdulkarim ya hana.
"Bata kyauta ba amma don Allah kayi hakuri. Mace kamar wannan ta wuce ladabtarwa da duka"
"Inji wa?" Cewar Larai tana face majina "yau ba don yaron can dan albarka ba da yanzu muna cizon yatsa"
"Duk da haka dukan bashi da amfani. Kamata ya yi mu godewa Allah da Ya tsare mutumcinta"
"Sai kuma ayi mata me bayan addu'ar? In kyaleta gobe ma ta bi wani katon banzan?" Honourable ya tambaya cikin fushi.
Kafafunsa Ayaah ta sake dafawa ta ce "Don Allah kayi hakuri Baba ka yafe min. Wallahi ba zan kara ba."
Girgiza kai ya yi da disappointment karara a fuskarsa "kin bani mamaki Ayaah. Kamarki ace kin iya hada baki da namiji ya zo makaranta ya daukeki. To ma wa ya san tun yaushe hakan take faruwa?"
A gigice ta dora hannu a baki tana rantsuwa "wallahi yau ne kadai."
"Kina tunanin zan yarda ne?"
Bata fuska Larai tayi "ban gane ba Habu, me kake son cewa? Tun dazu nake ta bata laifi tunda na san bata kyauta ba. Amma ba zan zuba ido ka jefeta da kazafi ba." Ta juya bangaren Anti Hasiya "dama na fada da sa hannunki akan abin da Ayaah tayi. Banda haka wace uwa ce zata kasa gane irin wadannan abubuwan? Da ace kina kula da marayun nan ai da kin fahimci abin da take yi tun kafin ya yi nisa. Ki bari ki haihu din kafin ki wargaza rayuwar 'ya'yan gidan."
"Maganganu irin wadannan basu dace da gab'ar da muke kai ba Larai." Innayo ta furta cikin lumana. Na farko Honourable Habu suruki ne sannan ga bakonsa. Bai dace magana irin wannan ma ta raso a yanayin da ake ciki ba. Sannan ta gaji da daure zuciyarta kan kalaman Larai akan Hasiya. Tana tsoron kada a kai ta bango ta rama duk su taru su bawa kansu kunya.
Mayar da kallonta tayi ga Ayaah ta ce "ina ji a jikina abin da ya faru yau ya isheki darasi da ishara akan rayuwar da kika so jefa kanki a baya. Ki kiyayi maimaituwar yau din a rayuwarki domin duk ranar da namiji a sami galaba a kanki walau da son ranki ko babu indai babu aure a tsakaninku ya cuceki har abada. Wani tsautsayin kirawo shi ake yi da sakaci. Allah Ya kiyaye gaba."
Amin suka amsa su duka har Larai din. Abdulkarim ya yi murmushi a ransa yana kara yabawa da tsatson da Hasiya ta fito wanda ya yi tasiri akan 'ya'yan Honourable. Dolensa ma ya zage damtse akan Ummita don bai ga wadda ta dace ya nema da gaske ba kamar ita.
Innayo sallama ta yi musu ta ce zata tafi. Honourable sai ya ce yana son su zama shaida akan hukuncin da zai yankewa Ayaah. Jin batunsa Anti Hasiya da Ayaan suka dinga bashi hakuri. Suna cike da tsoron abin da zai ce. Sun san shi mutum ne mai hakuri da kawaici amma bashi da dadi idan ya kai bango. Ummita da Murja yasa Ayaah ta fita ta kirawo masa. Babu bata lokaci sai gasu duka a tare kowacce ciki ya duri ruwa. Fadan baban nasu bashi da dadi ko kadan.
"Ku zama shaida" ya ce dasu Innayo, "ban yarda Ayaah ta sake fita in ba tare da wani daga cikin gidan nan ba. Makaranta ma in sha Allahu ta bar zuwa sai ranakun jarabawa. Shi ma da kaina zan dinga rakata na daukota. Sannan in sha Allahu sati daya da gama jarabawar Ayaah zan aurar dasu. Duk wadda bata da manemi zan samar mata kafin lokacin. Ke kuma..." Ya nuna Murja "ki fadawa Mahiru tunda dama ni suke jira. Ku tashi ku tafi."
Murja ta mike. Ayaah da Ummita suka kasa kwakkwaran motsi. Maganar abin da bai fi wata uku ake ba. Kuma basu da maneman a hannu. Anti Hasiya ma maganar dirar mikiya tayi mata. Ayaah kam tayi laifi mai girma sai dai ko kusa ba za ta yarda ya yiwa yaran nan auren dole ba. Ita da nata mahaifin ya yi mata, Allah ne kawai Ya dubi zukatansu ita da mahaifiyarta Ya daidaita zaman. Sai ya kasance Honourable din ya zarce duka tunaninsu a fagen kyautatawa sabanin sanin da suke tunanin sun yi masa lokacin yana auren A'i.
"Ku tashi mu tafi" ta ce da 'ya'yan nata ganin hatta Ummita ita ma kukan take. Suka bi bayanta kuwa suna tafe kamar kwai ya fashe musu a ciki.
Da fitarsu Honourable ya bawa kowa mamaki da ya yi 'yar dariya. Innayo ma da Abdulkarim sai da suka murmusa. Ita nata ya dace da na Honourable. Fushi ne suke gani muraran Hasiya tana yi na sanya mata yara a tsaka mai wuya. Shi kuwa Abdulkarim na farincikin fahimtar cewa Ummita bata da kowa a hannu yake. Lallai zai ci karensa babu babbaka. Tunda babu wani yaro a hannu da zai masa shigar sauri ya hure mata kunne.
Dakin da suka baro su Maimuna suka shiga, Ummita da Ayaah suna kuka babar tasu ma tana yi. Maimuna ta gaji da rarrashinsu ta koma fada.
"Tunda baku san hakuri ba sai kuyi ta yi. Amma ki sa Ayaah ta cire rigar d'an mutane ta mika masa"
Sai a lokacin ta tuna da rigar. Da sauri ta shiga balle maballan ta cire ta mikawa Murja.
"Don Allah ki kai masa"
Anti Hasiya ta kai mata duka ta kauce
"Amma baki da kirki Ayaah. Mutum ya yi miki irin wannan taimakon amma godiya ta kasa shiga tsakaninku. Tashi maza ki kai masa da kanki."
Hijab ta dora ta fita tana jiyo muryar Larai tana bada labarin abin da ya faru. Duk inda take tunanin ganinsa kama daga tsakar gidan, soro da kofar gida. Bata manta da gargadin babanta ba saboda haka bata yarda ta fita ba. Ciki ta dawo da niyar daukar wayarta ta kira shi sai ta kula da takalminsa a kofar falon. Kenan Baba ne ya sake kiransa ta ambata a zuciyarta. Kamar wadda tayi magana da karfi sai ji tayi Babanta ya kwala mata kira.
Da hanzari ta shiga don yanzu bata kaunar abin da zai bata masa rai.
"Dama rigarsa zan ce ki kawo ashe ma kin dauko."
Abdulkarim sai cewa yayi "muje waje in ganka kafin na wuce Honourable."
Hon. Habu ya dan yi turus sai da ya sake maimaitawa ya mike. Suna fita Abdulkarim din ya ce da Suhaib idan ya fito zasu yi sallah don har biyu da rabi.
Rigar ta mika masa bayan sun fita ta furta kalmar godiya a hankali.
"Ya naga duk kin yi laushi ne? Ko hukuncin da Baba ya ce min ya yanke ne bai yi miki ba?"
Dago rinannun idanunta tayj da sauri ta ce "yanzu sai da ya fada maka zai min auren dole?"
"A'a" ya ce yana mai girgiza kansa "cewa ya yi kawai za ki daina fita har zuwa school sai kina da paper" ya kare da dan murmushi.
"Auren dolen ka ke yiwa dariya ko hanani fita?"
"Kina da rigima" Suhaib ya furta da wani irin yanayi sannan ya tashi tsaye "ni zan wuce. Sai in ce sai mun zo biki ko?"
Shiru tayi bata kula shi ba don ta kula yana jindadin zolayarta.
"Au ba za ki amsa ba?"
"Kana farinciki da auren dolen da za ayi min ya za ayi na amsa?"
Sai da ya je bakin kofa sannan ya juyo ya kalleta cikin ido ya ce "dazun nan ki ka yi warning dina da cewa ko ina sonki kada na fada domin ba za ki yarda ba. Ba don haka ba da na sake introducing kaina a wurinsa a matsayin...." Ya lumshe ido ya budesu a gajiye "idan kin bani matsayin da ya dace na sake gabatar da kaina a wurinsa ki kirani kafin lokaci ya kure mana. Take care."
Har ya fita su Ummita suka shigo bata sani ba don ba karamin kashe mata jiki da zuciya kalamansa suka yi ba.
Sallah ya tsaya suka yi sannan ya ce zai tafi. Ba yadda Honourable bai yi dashi ba akan ya zauna yaci abinci yace ya koshi. Da fitarsa bai zame ko ina ba sai garejin su Danliti. Ogansu ne ya kira shi yana shiga mota zai bar unguwarsu Ayaah.
"Mal. Suhaib muna kara godiya akan taimakon da kayi mana. Dalilin kiran naka kuwa yanzu ba wani abu bane illa wayarsa da nake son baka kafin 'yan sanda su nema."
"Waya kuma?" Suhaib ya furta yana yamutsa fuska saboda son sanin dalili.
Mutumin ya ce "Kwarai kuwa. 'Yan sandan da suka zo basu kula da ita ba sai wani cikin yarana ne ya dauko. Yanzu suka budeta har sun cire lock din ma. A garin bibiyar hirarrakinsa na chatting muka ci karo da hirarsa da wata mata suna kuma yawan ambaton sunanka. Matar har tana cewa idan ka zo Kano ya sake maka kamanni da duka. Shi ne nace gara dai ka zo ka gani kada ya cuci wata"
'Alhamdulillah' Suhaib ya ce yana mai fadada murmushin fuskarsa domin wannan batu ba karamin taimako zai yi masa ba. Shaida ce guda da zai samu ya nunawa Abbansu akan Jiddo. In anyi sa'a yaga cewa matarsa ma tana yin yadda yake ko kusa da kila ya canja hali. Da wannan tunanin ya wuce garejin.
Kafin ya karasa kafarsa ta dama ta soma wani irin tsukku kamar ana cakarta da allura. Da kyar ya iya karasawa sai dai yana fitowa ya kasa takata da kyau. Ogansu Danliti yana ganin yanayin tafiyarsa ya ce,
"Dama na san a rina. Wannan duka da ka yiwa kofar dakin nan da wuya idan baka bugu ba ko targade. Don da karaya ce da wuri zaka fara jin ciwon."
Wasa-wasa Suhaib kasa jan motar ya yi. Shi da ya yi niyar komawa Kaduna a lokacin sai gashi wani aka samu ya mayar dashi gidan kawunsu inda aka yi zaman biki. Abinci ma kasa ci yayi dole suka tafi wani asibitin kashi na kudi. Har x-ray aka yi masa saboda kafar ta fara kumbura ta wurin idon sawu. Dunduniyar kuma tana ciwo. Babu karaya yadda suke tsammani sai tsabar buguwa. Irin leg brace dinnan aka daura masa bayan an yi mata gashi sannan suka koma gida. Matan gidan suna can suna kiran Mami Khadija su sanar da ita shi kuwa ya kira Lilu ya ce ya taho washegari su koma tare.
Zara taga ikon Allah zamansu da Uwani bayan fitar su Innayo. Surutai take yi ita kadai kamar wadda ta sami tabin hankali. Kalma ko daya ba za ta iya cewa ta gane ba amma ga bakinta nan yana ta motsi da sauri-sauri. Abin tsoro ya soma bata ta tashi daga dakin ta koma falo. Kafin ta zauna Uwani ta fito tana mai cigaba da maganganunta. Babu zato taji ta ce mata,
"Kiyayyar da kuke min har ta kai
a rasa mai tambayata damuwata Zara?"
"Idan na tambaya za ki fada min ne?"
Uwani na jin haka ta dawo kusa da ita ta zauna. Da gaske neman wanda zata saukewa damuwarta take. Innayo din da ta zata har abada ba za ta taba juya mata baya ba yau gashi tana magana taki sauraronta da kyau. Kanta ta dinga dunguri da yatsanta manuni.
"Zara ina ji wadansu notina suna kwancewa a kwakwalwata wallahi. Daf nake da zarewa idan Habibu bai dauki wayata ba"
"Habibu kuma ko Salihi?"
Uwani ta maimaita sunan da karfi "Habibu nace. Ai ce miki nayi kaina zai kwance ba wai ya kwance din ba"
Mikewa Zara tayi "me yayi zafi za ki sauke min fadanki. A kira Habibu lafiya"
Da sauri Uwani ta riko hannunta ta dawo ta zauna. Bata boye mata komai ba cikin matsalolin da suka fuskantota a dan kankanin lokaci.
"Idan na rasa komai wallahi zuciyata za ta iya bugawa. Zara gabadaya rayuwata fa akan yadda zan gujewa rayuwa irin ta Innayo na yita. Sai yanzu bayan na gama shan wahalar har ina hango soma cin arzikin sai komai ya rushe? Meye marabata da Innayo yanzu? Karatun da aikin duka babu riba."
Kwalla ce ta taru a idon Zara saboda ita kanta ta hango tsagwaron rashin hankali a zantukan Uwani.
"Ko kadan baki yi kuskure ba don kin yi fatan gujewa irin rayuwar Innayo. Babu wani mai hankali da zai so bayan ya tashi a wahale ya cigaba da rayuwa a haka. To amma kuskurenmu daya ne ni da ke. Mun so gujewa rayuwar ne mu kadai ba tare da tunanin wadda tayi sanadiyar rabamu da ita ba. Da gumin wa muka rayu? Wa ya ciyar dake? Waye ya kai ki makaranta? Wa ya aurar dake? Addu'ar waye ya zame miki garkuwa tsahon rayuwarki? Sai ace kuma da kika sami dadi ita ce mutum ta farko da kike gudu tamkar ita ta zabawa kanta kuncin da take ciki. Ke din wayonki ne yasa ki ka sami duka nasarorin da kike tinkaho dasu? Idan wayonki ne to ki sake tsallake wannan ramin dake gabanki. Ni dai na dawo daga rakiyar shaidanin da ya taba min zuciya. Uwata ita ce madubin rayuwata. Ranar da kika gane haka kuma ki ka roketa gafara shi ne lokacin da zaki fara ganin haske."
Tun zuwanta gidan ta kula da yadda Zara take neman shiri da Innayo. A zatonta abin na ganin ido ne kadai. Sai gashi taji daga bakinta. Wannan yasa tayi wata irin dariya. So take ta san waye mara hankali tsakanin ita da kanwar ta ta.
"Da bambanci sosai tsakanin matsalata da taki. Baki san juya kudi ba sai dai a dauka a baki. Shi yasa da miji ya juya miki baya ki ka yi saurin laushi a hannun Innayo tunda arzikinta kike ci. Ni kuwa gumina ne. Nafi karfin tozarcin da namiji wallahi."
"Hakka!" Cewar Zara da gatsali.
"Don kin ganni a gida ki ke min magana haka? Hala baki ji na fada miki ina da gidan kaina ba?"
"Kan ki kuma ake ji"
Zara dama ba kyalle bace. Da ta fuskanci Uwani bata da niyyar bin hanyar da take nuna mata sai taji gara a bar maganar kafin su fara fada. Tashi tayi ta fito falo. Uwani sai ta biyota rai a bace.
"Ni kike cewa kaina ake ji saboda ga 'yar macukule ko? Har kina da bakin fadawa wani magana ma ke da kike goyon 'ya mara suna?"
"Wai in tambayeki Uwani. Anya kin taba zama kin karewa Innayo kallo kuwa? Kin ma santa kuwa? Sani na wace ce ita a matsayin 'yar Adam ba na matsayinta na uwa a gareki ba." Shiru Uwani tayi tana sauraron zancen da Zara ta dauko.
"Innayo bata sami gatan uwa da uba ba a dalilin maraici amma mu ta zame mana uwa da uba harda kari. Mu tara ta aurar Uwani. Mata tara wata na bin wata. Ta sadaukar da lafiyarta da jindadinta domin rayuwarmu ta inganta. Amma cikinmu banda Hasiya waye take jindadi a jikinsa? Salima da Maimuna suna kyautata mata amma ai har yau guminta suke ci. Su Hasina dama tun zamanin marigayiya Allah Ya jikanta suka juya mata baya. Me tayi mana da zafi Uwani? Saboda ta auri ubanmu ta haifemu shi ne laifi? Ko don ta jure wahalar gidansa domin ta zauna damu don kada rayuwarmu ta tagayyara? Kiyi tunani idan har kina da rabon jindadin duniya da lahira. Innayo jininta ne kadai bata zubar domin mu ci, mu sha kuma mu sami ilimi ba. Tun karfe hudu take tashi amma babu ita babu sake kwanciya sai wuraren shadaya ko shabiyun dare. Hannunta kullum a ruwa, ido a gaban murhu. Haba Uwani? Kamar baki rike ciki kin yi nakuda ba? UWA, UWACE komai lalacewarta. Balle kyautar Allah irin Innayo."
Bata kara tofa komai ba bayan haka ta shige daki saboda kukan da yaci karfinta. Uwani kuwa zama tayi dabas akan kujera duka jikinta babu kwari. Ta kwashi kusan minti ashirin tana juyayin maganganun Zara kafin wani irin bacci ya dauketa. Tabbas sau tari mutum yana ganin abin dake zuciyarsa ne a cikin bacci. A yadda take a zaunen ko gyara zama bata yi ba baccin nata ya dauketa zuwa duniyar mafarki mai ban tsoro. A cikin baccin take fatan Allah Ya kawo mai tashinta saboda firgicin da ba za ta ce ga abin da ya kawo mata shi ba.
"Shazali ya maganarmu ne? Ranar laraba muka yi da Alh. Tahir gashi har yau litinin baka ce min komai ba"
Gefen titi Shazali ya gangara da motarsa domin maganar da zai yi da Comared tana bukatar nutsuwarsa sosai.
"Ranka ya dade akwai shirin da nake yi ne. Hatsaniya ta shiga tsakanina da mutumin da nake son kawo masa ne, saboda haka sai na lallaba shi a hankali."
Tsaki Comared ya ja ya kuma kama yi nasa fada harda zagi.
"Ka tabbata yaron ya zo domin idan aka sami akasi raina da naka duk sai sun baci"
Hakuri Shazali ya bashi a ransa yana ta tufka da warwarar yadda zai yi ya sami kan Abbati cikin lumana. Aikin Comared din da ya yi masa bayani ya wuce biyawa Alhajin da zai zo bukata kadai. Aiki ne na sihiri wanda Alh. Tahir ya zata za ayi ne domin toshiyar baki (Yumna). Bai san cewa Comared tasa tukunyar yake son gyarawa ba. Sharri yake son kulla masa ya watsa hotunansa ta yadda zai rasa duk wata kwangilar dake hannunsa. Sai a bawa Comared don dama irin sana'arsu daya. Lokaci guda Alh. Tahir din ya yi musu zarra, sunansa kadai ake ji. Abotar sai ta koma murmushin gaban ido da gulmar bayan ido, batare da saninsa ba.
To shi ma Shazali burinsa ya yi amfani da wannan damar ya tozarta Abbati. Duk da cewa a gaskiyar lamari yafi jin haushin Munzali saboda yafi baki. To amma wulakantar Abbati sai tafi ta Munzali ciwo kamar yadda ya yi hasashen tonon asirinsu. Abbati dan dangi ne. Munzali kuwa da danginsa da babu duk daya a tunaninsa. Sannan son da Munzali yake yiwa Abbati zai sa yaji ciwon abin sosai. Dama ce ya samu da zai nuna musu shi din ba kanwar lasa bane. A matsayinsa na silar arzikinsu bai kamata su juya masa baya ba. Sai da suke ganiyar samun kudi kamar hauka sannan zasu ce wai sun tuba. Ko waye ya fada musu cewa shi baya son samun rahama bai sani ba. Lokacin tubansu idan ya zo ba sai kowa ya fada musu ba. Tsufansu ya ishesu sanin cewa ya kamata a koma ga Allah. Su gina masallatai su dinga bayar da sadaka. A haka zasu koma lahira kamar jarirai. (Babu bawan da Allah Ya yiwa alkawarin jinkirta masa rayuwa zuwa wani wa'adi. Lokaci yana zuwa ne ko da tsufa ko babu. Ko an tuba ko ba a tuba ba sai an tafi. Ya Rabbi Ka yafe mana zunubanmu na zahiri da badini. Amin)
Da waccan magana ya katse kiran Comared ya shiga laluben layin Abbati. Cikin sa'a kuwa ta shiga sai fatan a dauka. Abbati na ganin sunansa a jikin wayarsa ya ja tsaki ya mayar da ita aljihu. Sun kusa Jogana motar tasu ta soma hayaki suka tsaya. Abin duniya ya taru ya yi masa yawa domin ya kasa samun mota mai tsayuwa ta dauke shi. Ga yamma ta kawo kai. A gefe guda kuma ya kasa samun Munzali. Hanne da yake tunanin zata hadasu ita ma wayarta a kashe. Daga baya ne ya yi tunanin kiran Kukunsu. Cikin sa'a kuwa ya sameta. Shazali da bai hakura da nemansa ba ya dinga jin wayar tana shiga number busy.
Kalmar lafiya kalau kadai Abbati ya iya cewa ga dukkan tarin kalaman gaisuwa da kukun yake jefa masa. Jin zai fara tambayarsa mutanen gida ya yi saurin katse shi.
"Don Allah hadani da Munzali"
Kuku ya dubi hanyar bene ya ce "yau ko sau daya bai fito ba. Sannan yaki barin Qibdiyya ma ta sauko. Abincinsu ma ni ban sani ba ko sun ci don ya kulle kofarsa"
Dunkule hannu Abbati ya yi ya daddaki goshinsa cikin rashin sanin abin yi. Can dai ya ce masa yana zuwa ya kashe wayarsa. Hannunsa yana rawa ga gumin tashin hankali ya shiga scrolling din sunaye a wayarsa. So yake ya gani ko zai yi dacen samun nambar 'yan uwan Munzali amma babu ko daya. Tsoronsa kada ya dauki mummunan mataki musamman da Kukun yace yana tare da Qibdiyya. Kiran kukun ya sake yi da wata shawara ta zo ransa.
"Ka san gidan iyayen Munzali ko?"
"Na sani ranka ya dade"
"Ka je gidan ka nemi mahaifiyarsa Asabe ka fada mata. Ita zata san me ya kamata ayi kafin na iso. Ka tabbatar ita ka samu"
A kofar gidan Alh. Rabi'u kukun ya tsayar da mashin dinsa ya sauka ya dinga kwada sallama.
A cikin gidan Asabe tana kuryar dakinta abin duniya ya yi mata yawa. Zantukan Munzali basu da ma'anar da zata iya cewa ga dalilin da yasa yake rokon Qibdiyya gafara don an mata fyade. Ta so tahowa ma da ita a jiya a hana. Yau kuma yaki daukar wayarta. Daga baya ita ma bata samunsa. Ga sunan yaron da Qibdiyya ta ambata ma ya kwanta mata don bata taba jinsa ba. Shawara tayi tafi dari akan ta kira su Ummakati ta fada musu ko tayi shiru. She was never a Mom to all of them. Ta dai san wahalar daukar ciki da nakuda. Ta kuma dan san wahalar raino musamman kafin yaro ya fara zama. Daga nan kuma sai abin da hali ya yi. Allah Mai rayawa Shi ya raya mata zuri'arta cikin mugun sakaci da rashin sanin ciwon kai.
Da Innayo ce tabbas ta san da tuni ta lalubo abin da ya dace har ma ta aiwatar. Yinin ranar bata tsinana komai ba sai kullawa da kwancewa. Ga ranar da duk girman d'a yake bukatar mahaifiyarsa. Gata da rai da lafiya amma bata san me ya kamata ta yiwa Munzali ba.
Tashin da Uwani tayi daga firgitaccen baccinta yana da alaka da karfin sallamar Kuku. A razane ta tashi tayi hanyar kofa da sauri. Zara ta kalleta ta girgiza kai. Ita ma sallamar ce ta fito da ita.
Kallon ina-na-sanka Uwani ta dinga yiwa masa. Shi bai ma ganeta ba sai Asabe da ya tambayeta.
Juyawa tayi kamar ta koma daki sai dai ta karasa ta fadawa Asaben. Tare suka dawo bakin kofar. A gabanta ya fada mata halin da Munzali yake ciki. Cikin tsantsar rudani kuwa Asabe ta soma kuka. Ita kuma Uwani wani case ta tuna a asibitinsu inda uba ya kusa kashe 'yarsa saboda bakincikin an mata fyade a kauye. Ya ce gara ta mutu akan duniya taji wannan labari. Ba tare da tunanin komai ba sama da ran kaninta da 'yarsa ta koma daki da gudu. Mayafin dake jikin Zara wanda ta lulluba zata fito tun zuwan Kuku ta warware ta yafa. Ta ruga daki ta dauko jakarta mai dauke da kayan aikin gaggawa ta fito.
"Ki fadawa Innayo na tafi gidan Munzali"
Zara ta bita da sauri "gidan Munzali kuma? Me ya faru?"
Uwani bata ce komai ba ta fita. Asabe har lokacin tana tsaye tana koke koke bata iya cewa komai ba ga kuku. Isowar Uwani ce ma ta ankarar da its cewa ya kamata tayi wani abu.
"Malam muje don ba gane gidan zanyi ba"
Kuku ya dan ja baya "ke ce Asaben?"
Rai a bace da ganin yana bata mata lokaci ta ce "ni yayar Munzali ce. Ka wuce mu tafi"
Asabe sai ta gyada masa kai ta koma ciki da zummar dauko mayafi. Kafin ta fito sun bar wurin. Duk da tsoro irin na Uwani haka ta hau mashin din tana salati har suka isa.