BABI NA ASHIRIN DA HU
Uwa Uwa Ce Part 2 Complete Hausa Novel · about 26 min read
Shiru ne ya ratsa office din na wani lokaci bayan su Abbati sun gama bayaninsu. Baka jin komai sai jan hancin Asabe da saukar numfashin mazan da karfi. Hakika wannan zama ya zama tamkar daukar darasi ne ga dukkanin wadanda Allah Yasa aka yi a gabansu. Kowa ya kalli labarin ta fuskar da ya shafe shi.
Baaba Mari fin karfi ne.
Mal. Inuwa makauniyar biyayya.
Mal. Sa'idu kasa bambance neman ilimi (almajiranci) da bara (rokon abinci, da kudin gabatar da bukatun rayuwa). (Jama'a da yawa sun jahilci kiyayyar da ake nunawa wannan na'u'in karatun domin sun hada shi wuri guda da littafi mai tsarki. Abin da basu gane ba shi ne da makaho, da gurgu, da kuturu da dan malam wato almajiri dukkaninsu mabarata ne. Gyaran da muke nema shi ne a gatancewa yaran da ake turowa karatu ta yadda karatun kadai zasu yi cikin aminci da kulawa. Ita kanta bara tana kashe zuciyar ma'abocinta ne. Kenan tana rage darajar ilimin da suke nema. Duk inda almajiri mai roko yake ba shi da wata kima a idon mutane saboda kullum shi ne hannun karba.)
Asabe sakarar uwa wadda ta biyewa sawun miji wurin banzatar da 'ya'ya.
Alh. Rabi'u irin uban da ake yiwa yawancin hausawa kudin goro da halayyarsa. A haifa a kasa rikewa saboda son zuciya da zalunci. Irinsu da yawa 'ya'yansu lalacewa suke yi kuma su zama silar lalacewar 'ya'yan wasu.
Alh. Tahir magidancin da ya dauka zai ci bulus a tattare da alfashar da ya rayu cikin biyewa zuciya wurin kosar da ita. A yau duk wani tunaninsa ya ruguje. Ashe ita zina ba a cin bulus. Ko ayi a inda zai maka radadi ko aje lahira a girbe shuka. Ko a hadawa bawa duka biyun. Sanin zahirin su Abbati ya firgita shi fiye da zato. Gashi kuma suma bashi da sauran kima a idons.
Alh. Sadisu masu madafan iko wadanda nasu kadai suka sani. Duka matsalolin yau zasu iya zama tarihi idan gwamnati ta saka hannu tayi abin da ya dace. Maimakon haka sai suka zabi amfani da gurbatattun cikin al'umma wurin cimma burikansu na siyasa. Sai gashi daya daga cikin baragurbin ya harbi tilon dansa har ma yana shirin rasa shi baki daya.
Da aka rasa mai fara tashi ko kara cewa komai bayan sun yi shiru sai Munzali ya tambaya ko zasu iya tafiya domin yana son ya kai Abbati asibiti.
DPO ya cike takardun da suka dace wadanda suka wanke Abbati daga zargi ya ce zasu iya tafiya.
Gabadayansu tare suka firfito waje. Jikkunan su Asabe a sanyaye. Yayinda wadanda basu san abin da aka tattauna a ciki ba suke ta farinciki.
Kasancewar Hanne tana wurin, Farha bata yi gigin matsowa inda ake ta yiwa Abbati murnar kubuta ba. Amma rashin samun yin hakan ya bayyana tsantsar damuwar da Mami Khadija tayi saurin fahimta a tattare da ita. Tausayi taji ta bata. Tunda bata amsa sunan matarsa ba tabbas bai dace tayi abin da zai sosa ran matar tasa a yanayin da ake ciki ba. A wani bangaren na zuciyarta kuma sai ta shiga wasiwasi akan al'amuran da suka faru a yau. Tabbas idan ta ce babu zargin lauje cikin nadi a game da su waye Abbati da Munzali ta yiwa kanta karya. Babbar damuwarta bata wuce alakarsu da wanda ya sace Qibdiyya da kuma dalilinsa na sace ta ba. Alhalin da kunnuwansu duka sun ji daga bakin Comared cewa kawali ne na kusoshin kasar nan. Abbati ya ce shi almajiri ne amma ji gidansa da irin motocinsu. Shin ko dai su ma kawalan ne???
"Mami?"
Firgigit ta dawo daga duniyar tunanin da take sakamakon tabata da kiran sunanta da Lilu yayi.
"Na bude motar ke muke jira"
Kallon motar tasu tayi taga ashe duk sun shiga bayan sun yi sallama dasu Abbati. Ta shiga baya kusa da Suhaib ta zauna. Sun iso kusa da gate din station din Abbati da ya rufewa Baaba Mari kofar motar Munzali ya tari motar tasu kafin su fita. Saitin tagar gaba inda Farha take zaune ya tsaya amma idanunsa baya suke fuskanta wurin Mami Khadija.
"Mami ku yi hakuri da abin da ya faru dazu da ma damuwar da muka janyo muku yanzu."
Murmushi tayi tana mai kara yabawa da sanyin halinsa.
"Ka bar wannan magana Abbati ta riga ta wuce. Allah Ya tsare gaba. Gara ku samu ku tafi don ka ga likita da wuri."
"In sha Allahu. Nagode..." Ya kallo Suhaib da Lilu ya sake cewa "Nagode"
Farha ce kadai bai yiwa magana ba. Sai murmushi kadai saboda idon Mami. Waje suka yi da motar suka bi bayan Comared wanda yake tare da Alh. Tahir. Kuma shi zai yi musu jagora su koma gida.
A ranar Asabe gidan Lami ta wuce. Bata iya komawa gida ba sannan ba za ta iya fuskantar Munzali ba. Duniyar ce kaf ta daina yi mata dadi. Ta rasa tudun dafawa. Yau ko mashi aka caka mata a zuci iyakar ciwon da za ta ji kenan. Dole bahaushe yake cewa gaskiya tana da daci. Maganganun da taji daga bakin danta basu yi mata dadi ba ko kusa. Amma cikinsu babu karya. Idan Alh. Rabi'u halinsa ne tsallake iyalinsa ya barsu suyi ta kansu da zarar sun fito duniya, ita mene ne nata uzurin? Bata taka rawarta ta uwa a wurin 'ya'yanta ba. Duk wata alamar mace ko uwa ta gari babu a tattare da ita. Kaiconta! Ta ina za ta fara?
Alh. Rabi'u da ya koma gida shi kuma ko runtsawa bai iya yi ba. Dakinsa ya shige ya rufe kofa tun dawowarsa. Gabanin magariba Innayo da su Uwani suka shirya tafiya asibiti dubo Abbas. Aikin nasa karfe bakwai ne da an idar da sallah. Ta cikin dakin ya iya cewa su gaishe su.
Yanayinsa da rashin dawowar Asabe ya sanyata shiga damuwa. Damuwa ba akansu ba. Tunaninta ya tafi kan Munzali da take da yakinin akwai abin da yake faruwa dashi. Da kuma Qibdiyya. Aikin da aka shiga da Abbas ne yasa kowa tsammanin shi ne damuwarta. Shi yasa babu wanda ya dameta da tambaya. Tare dasu Hasiya suka zauna har aka fito dashi suka tabbatar lafiyarsa kalau sannan kowa ya kama hanyar gida.
Allah Ya yi dare, gari ya waye. Kowane mahaluki safiyarsa tana zuwa da fuskar da Allah Ya kaddara masa. Wani da dariya wani da kuka. Wani da damuwa wani kuma zuciyarsa fes. Shi bawa har kullum idan yana kwadayin dacewa sai ya zama mai karban rayuwa a duk halin ta zo masa.
A wannan rana wadda ta biyo rana mai tarihi a rayuwarsu Abbati, sun wayi gari da ciwon da jiya ta bar musu. Daga asibitin da Munzali ya kai Abbati, gida suka dawo dukkaninsu. Munzali ya fita ya nemi gidan abinci mai kyau ya sayo musu. Aka taru aka ci kamar ana tura magani. Hanne da Habu kadai ne suka zata shirun nasu yana da nasaba da dukan da aka yiwa Abbati. Ko da suka shishshiga daki domin bawa jiki hakkinsa, babu wanda ya runtsa sai mutum biyun can dai. Juye juye kowa ya dinga yi har aka kira assalatu. Kowa ya tashi kamar jira suke yi. Kafin takwas duk sun hallara a falo.
Zamansu ke da wuya maigadi ya shigo ya fadawa Munzali mahaifinsa yana nemansa. Dan murmushi ya sami kansa da yi domin ya tabbata yau dai neman da yake yi masa na damuwa da lamarinsa ne ba na neman kudi ba. Bai so ace karon farko da mahaifinsa zai damu haka dashi ya kasance akan abu makamancin wannan bane.
Bangaren Abbati ya ce a kawo shi. Ya zo ya zauna suka fara gaisawa da su Mal. Inuwa sai ga Asabe. Kayan jiya ne a jikinta da alamun rashin wanka ma. Tayi wuri wuri da ita gwanin ban tausayi.
"Hanne da Habu ku dan bamu wuri don Allah" cewar Mal. Sa'idu yana mai dubansu da mutuntawa.
Bambarakwai suka ga abin tunda bai saba lallaba dan kowa ba. Habu ya fita waje. Hanne kuma ta haye sama.
Munzali da Abbati suka zazzauna a kasa domin girmamawa ga iyayensu sannan Mal. Sa'idu ya soma magana cike da rauni.
"Ba don wannan al'amari mai muni bane wanda nake fatan daga yau kada a sake tayar da maganar ba, da sai in ce ina son sauran kannena su kasance a wannan zama."
Caraf maganar ta shiga kunnuwan Hanne. Kafafuwanta kuwa suka ci burki a bakin kofar shiga saman daga ciki. Sannu a hankali ta sakaya kofar ta sami wuri ta labe abinta.
Mal. Sa'idu ya cigaba da cewa "Allah shi ne shaida cewa ni Sa'idu ina kaunar 'yan uwana da 'ya'yansu da zuciya daya. A tawa wautar soyayya ce tasa nake juya kowa a gidan a matsayina na babba. Girman kai yasa nake ganin tunda gaba nake da kowa yi min biyayya wajibi ne. Sannan kowa bai san daidai ba sai ni kadai."
Ya dubi Baaba Mari, duba na mai jin nauyin wanda ya sabawa.
"Ki yi min aikin gafara duk da cewa na roka a makare. Tun ranar da ki ka dawo da gawar Sani a bayanki ya dace ace na zauna nayi tunanin halin da na jefamu a ciki. Son zuciya da girman kan da na ambata a baya suka sanya nake jin baki isa na janye kudurina ba. Yin haka tamkar kin yi galaba ne a kaina. Wannan dalilin yasa na kara tamke dammarar juya duk wani abu da kike tunanin kina da iko dashi. Musamman rayuwar Abbati. Sannan magana ta gaskiya, a duk lokacin da ki ka tayar da maganar son sannin sana'ar Abbati, nima ina kwadaituwa da haka. Na kan riski kaina cikin halin tunani da rashin bacci a wadannan lokuta domin nima a tsorace nake. Gudun kada abin da nake gudu ya tabbata yasa bana kaunar jin kina tayar da wannan zancen."
Bayan ya yi shiru Mal. Inuwa ya yi gyaran murya ya ce "laifi ba naka bane kai kadai Yaya. Harda mu da duka wadanda suke da alhakin sanyawa ko hana irin wannan na'u'in karatun. Hakika bana jin akwai wani mai sanya gaba gabas da zai kalubalanci tura 'ya'yan musulmi neman ilimin islama. To amma wannan hanya da aka biyo ba mai bullewa bace. A da can zan yarda idan aka ce mu iyaye maza muna tura yaranmu ne domin karatun Muhammadiya. Yawancin 'yan kasuwa da masu kudin da ake ji dasu a arewacin kasar nan akwai almajiranci a cikin tarihinsu. Su nemi ilimi su hada da koyon sana'a'o'in hannu komai kankantarsu. Yanzu kuwa babu tantama abin ya koma hanyar gujewa daukar nauyin da Allah Ya dora mana na 'ya'yanmu ne. Muna fakewa a bayan addini muna wulakanta rayuwar yaranmu. Ko babu komai duk mai roko baya daraja da kima a idon mutane. Zuciyarsa mutuwa take wurin jiran a bashi. Sannan ta kangare idan bai samu ba, ya dinga ganin laifin duka duniyar baki daya wurin kin nuna masa tausayi."
Baaba Mari dai bata ce komai ba sai sauraron Mal. Inuwa da Mal. Sa'idu suna bankado rawar da suka taka wurin bata rayuwar Abbati.
Munzali kuma ya tsurawa iyayensa ido. Da ya gaji da shirunsu ya kasa hakuri dole sai da ya yi magana.
"Baku ce komai ba Baba"
Asabe ta dukar da kai cikin jin nauyin kowa. Kunya da bakinciki sun mamaye zuciyarta. Tana mamakin yadda akayi ta makance da son duniya a baya har ta iya aikata wannan danyen aikin na sakaci da rayuwar 'ya'yanta.
"Me zan ce Munzali? Ina cike da kunya da nadama amma hakan ba zai canja komai ba. Laifinmu ni da mahaifinka yafi na kowa yawa a wurin nan. Bamu bar muku komai na tinkaho ba sai yawanku wanda ba don kun yi yunkuri da kanku ba da bai amfaneku da komai ba. Kalmar hakuri kadai bana jin za ta yi wani tasiri wurin rage maka radadin wannan al'amari"
Kalaminta ya zaburar da Alh. Rabi'u ga yin magana tana rufe bakinta.
"Mene ne aibun 'ya'yana? A iya sani na arziki ne yawan haihuwar domin kuwa rana gobe kiyama da irina Annabin Rahama zai yi alfahari"
Sallallahu alaihi wa sallam ya ji falon ya karade da ambata kafin muryar Munzali ta doki kunnuwansa cikin fushi.
"Ina abin alfaharin Baba? Waye cikinmu za ka iya fitarwa ka nuna hankali kwance har ma ka yi zaton za ayi alfahari da shi"
"Munzali meye haka ne?" Abbati ya ce dashi da alamun rashin jindadi.
" Gaskiyar da 'yan uwa, makota, surukai, abokai da mu kanmu 'ya'yansa muka kasa fada masa da wuri zan sanar da shi."
Ya mayar da hankalinsa ga Alh. Rabi'u wanda shi ma kallonsa yake da mamaki. Duk jahilcin da yake tunanin Munzali yana fama dashi bai yi tsammanin zai kasance cikin masu kokonto akan hadisan Ma'aiki ba. Hadisi ma irin wannan da ya dade da karade al'ummar da ya taso a cikinta.
"Baba idan anje lahirar za ka tsame wasu cikinmu ne ka nuna a matsayin 'ya'yanka?"
"Munzali kada ka yi sa6o mana" Asabe ta gargade shi ganin kamar zai saki layi.
"Allah Ya tsareni. Laifukana na baya ma sun isheni. Da yardar Allah ba zan sake afkawa zunubi da gangan ba. Ina dai so in ji shin da wa Baba zai yi alfahirin." Ya soma lissafi da yatsun hannunsa "Da 'yan dakin su Marigayiya A'i wadanda suka butulcewa hannun da ya ciccibi rayuwarsu a lokacin da basu da gata zai yi (Innayo)? Su suka fi morar lafiya da kuruciyarta amma saboda rashin uba tsayayye suka manta alkhairi. Ko Uwani da Zara da suka zabi kyama da tozarci ga mahaifiya kamar Innayo saboda gudun talauci? Ko ni da nafi kowa kazanta? Ko Bature da baka san a gidan wa yake kwana ba? Ko Lawisa dake canja samari kamar hula ta kuma gagara zaman gidanka? Ko Ummakati dake jin kunyar a hadata da ku a matsayin iyaye?"
Alh. Rabi'u shiru ba amsa sai muguwar kunyar da ta mamaye shi. Su Mal. Inuwa kuwa nauyi yasa suka ji ina ma kafin a fara maganar suka fita.
Idanu cike da kwalla Munzali ya dubi Baaba Mari ya ce "ki fada musu babu abin alfahiri a haihuwar da 'ya'ya basu sami kulawa, soyayya da kwab'a ba. Wadannan abubuwan masu saukin samuwa ne tunda babu ruwansu da da kudi ko talauci balle mutum ya dorawa halin rayuwa laifi. Annabi SAW ba haihuwar yuyuyu yace ayi ba. Me zai yi da taron al'ummar da fiye da rabinta suka zabi hanyar shaidan a matsayin tafarkin da zasu bi saboda rashin kulawar iyaye? Da kun sauke hakkina da na 'yan uwana da yake kanku da a yau iyayen Abbati ba suyi kukan fadawarsa harkar neman maza ba."
"Neman maza?" Hanne ta yiwa kanta tambayar a hankali tamkar tana jira wani ya sake fassara mata abin da ta riga ta sani. Ta sake maimaita kalmar tana cije lebe kafin kuma a hankali ta dora hannuwa a ka ta dinga nanata "na shiga uku" tana mai buga kafafunta a kasa a hankali don kada a ji. Matsanancin tsoro da fargabar da suka kama ta basu kawar mata da tunani ta yadda za ta so ta bayyana kanta a garesu kafin ta gama jin komai ba.
"Munzali yawan tada maganar nan ba shi da amfani tunda mai afkuwa ta afku. Ku yafi juna kai da iyayenka a cigaba da addu'a" cewar Mal. Sa'idu wanda hasashen halin da Alh. Rabi'u yake ciki na kunya yasa shi magana.
Shi kuwa Mal. Inuwa sai cewa ya yi "tada zancen akwai amfani Yaya Sa'idu. Ai zaman zubeben kwarya ake. A fitar da komai don kowa ya gane ta inda ya kuskure saboda a ji dadin gyarawa" idanun Munzali ya kalla dake cike da zallar bacin rai da tarin damuwa ya kuma kalli Asabe da Alh. Rabi'u "har yanzu da mu daku bamu makara ba. Dama ce muka samu domin shafe abin da ya faru da yaranmu. Don ko mun ki ko mun so, mu ma muna da namu kason a cikin zunubinsu tunda sakenmu ne sila. Musamman mu iyaye maza."
Asabe ta share hawaye ta ce "haka ne."
Shi kuwa Alh. Rabi'u daure fuska ya yi. Yadda bahaushe yakan ce gaskiya tana da daci to shi ma wannan ba karamin dacinta ya ji ba. Ba kuma ya jin zai bari a cigaba da fadarta balle tayi tasiri a zuciyarsa.
"Dakata Malam wa kake da suna?...wace irin magana ce wannan za ka ce muna da rabo a zunubinsu? Na san lokacin da ya fara ne? Ko ni na aike shi?
"Alhaji mene ne haka kuma?" Asabe ta furta ranta ya soma baci. Ko ba komai mahaifin Abbati bai cancanci irin wannan maganar ta rashin girmamawa ba.
Harararta ya yi kafin ya ce "dama tunda kika fara sauraron Innayo na soma kasa gane kanki. Idan ke kina maraba da a qaqaba miki zunubin irin mutanen Annabi Ludu ni bana so" ya mike tsaye yana baza babbar riga "ban san me ya dawo dani gidan nan ba. Na dai tabbata ba wannan maganar bace don wallahi da ba zan zo ba."
Mal. Inuwa ba shiri ya ce "kayi hakuri ban fada da wata manufa ba"
Munzali cije lebensa ya yi bayan ka karewa yanayin da Abbati ya shiga tunda Alh. Rabi'u ya soma magana. Takaicinsa ya karu da ya fahimci har yanzu akwai sauran gyara a lamarin mahaifinsa.
"Har a yanzu da nake kan siratsi irin wannan na rayuwa ba zan ji ni kamar kowane d'a mai iyaye ba?"
Asabe ta yi saurin cewa "Kada ka dauki maganganun Alhaji cikin fushi ya fada. Ka yafe mana don Allah"
"Kada Allah Yasa ya yafe. Aikin banza. Kaje ka gama iskancinka sannan ka dawo kana neman wanda za ka dorawa alhakin aikin da gabbanka suka aikata."
Su Mal. Sa'idu jiki duka ya yi sanyi. Ana neman gyara ga alamun sake tabarbarewar lamari ya taso.
Idan ya cigaba da sauraron mahaifinsa yana jin tabbas zuciyarsa sai tayi bugawar da take ta shirin yi tunda abubuwan nan suka soma faruwa. Shi yasa ya murje idanunsa ya fadi abin da yake ganin daidai ne.
"Idan ka so Baba ka cireni daga cikin 'ya'yanka. Wannan shi ne kadai nake jin abin da zai rabaka da amsa tambaya akan halin rayuwata..."
"Munzali mahaifinka ne fa..." Cewar Asabe tana jan hannunsa don ya kalleta"
"A suna ba. Na cinye kuruciyata sanda nake matukar bukatarsa ma na rayuwa balle yanzu"
"Munzali" Mal. Sa'idu da Baaba Mari suka kira shi kusan lokaci guda.
"Ku barshi ya nuna min iyakata. Dama can kawunanku yafi gani da gashi ba nawa ba"
"Ka taba yi min wani abu da zan gan ka da kimar da Allah Ya baka ta ubana..."
Da karfi Abbati ya ce "Munzali? Hauka kake ko me? Alhaji ne fa! Zo ka tafi gida gani nan zuwa."
Maganar da Munzali bai karasa ba kenan domin baya jin akwai ranar da Abbati zai saka shi ko ya hana shi ya kuma musantawa. Tuntuben bakin da ya yi akan Qibdiyya yake gudu kada Allah Yasa ya kuma maimaitawa.
Alh. Rabi'u da su Baaba Mari kowa ya ji kuma ya gani cewa Munzali bai bar fadi in fada da babansa ba sai da Abbati ya tsawatar. Hakan ya zama sanadin da Alh. Rabi'u ya sake samun abin aibata dan nasa.
Kujerar da ya tashi ya koma ya zauna a dofane yana kare musu kallo shi da Abbati.
"Ikon Mai Sama. Yanzu Munzali duk fadin wurin nan da jama'ar ciki babu wanda ya isa ya hanaka ka hanu sai wannan almajirin? Ka dubi tsabar idanuna ka dinga cab'a min magana son rai."
"Wallahi Abbati ya isa dani"
"Tabdijan!" Ya dubi su Mal. Inuwa "to
Billahillazi da sake. Yaran nan basu tuba ba. Sannan ina tsammanin mu'amalarsu bata sauya ba tun kuruciya. Iya shegenku kuke yi har kwanan gobe." Ya kalli Asabe tana sharbar hawaye "ki adana kukanki don basu cancance shi ba. Alhaki kwikuyo gashi nan ya bi kan 'yarku ai. Shi ne don borin kunya ku ka tara mu a nan kuna karanta mana karya da gaskiya."
"A'uzubillahi" cewar Mal. Sa'idu yana mai duban mutuwar tsayen da Abbati da Munzali suka yi "Alhaji wace irin magana ce wannan? Ana kokarin kawo gyara ya za ka sake jifansu da abin da su da kansu suke neman tsari daga gareshi?"
"Baka ji me yake cewa ba? Wai fa ni yake fadawa cewa Abbati ya isa da shi. Koda yake ba damuwa zaku yi ba tunda wanda ya zaba akan mu iyayensa danku ne."
Asabe kuka kawai take yi. Yayinda Hanne ta sulale a kasa bakin kofar da take labe ta zauna. Wani sashe na zuciyarta yana kokarin karbar zancen Alh. Rabi'u. Domin alal hakika ta dade da rashin son alakarsu duba da yadda komai zasu yi sai sun tuntubi juna. Sutura wannan daidaikun ranaku ne suke bambantawa. Bata ganin kowa sai muryar Munzali da ta karade falon cikin rauni, karaya da bakinciki ya mayar da martani ga zargin da mahaifinsa yake yi musu.
"Ba zan janye kalamaina ba. Abbati ya isa dani. Haihuwata ce kadai bai yi ba amma duk wani abu da ya kamata uwa da uba su yiwa d'a ya yi min. A kuma matsayinsa na ALMAJIRI" Alh Rabi'u ya fuskanta da tambaya "ka taba sanin cewa da ina karami ina yawan fama da ciwon namoniya (pneumonia)? Duk lokacin da ya tashi Abbati ke jinyata. Ita Asabe ai ta sani. Ya nemo kudi ta kazamar hanya ya kaini asibiti. Bata taba son sanin a ina yake nema ba tunda ba ita yake tambaya ba."
"Ke, yaushe aka yi haka ban sani ba?"
Ya tambayi Asabe a zafafe.
"Ban sani ba" ita ce amsar da ta bashi.
"Kun gani ko?" Ya nuna iyayen nasa yana girgiza kai "Abbati ne ya kaini makarantar boko ta yaki da jahilci. Yasa muka koma zuwa makarantar dare duk da mun san cewa mu din masu aikata laifi ne. Sannan tuban da muke hanyar yi shi ne dai sila kuma jagora. Ya yi min komai wallahi. Ya cancanci girmamawa da mutuntawa. Tunda ya ce na tafi gida kuma zan tafi domin wannan almajirin yana da iko da ni" yana kaiwa nan yasa kai ya fita ko waige babu.
"Malam ina neman izinin yin magana"
Abbati ya kai idanunsa ga Baaba Mari ita kuma tana fuskantar Mal. Inuwa. Kai ya gyada mata da sauri sauri don ya san zancenta a kullum abin duba ne.
Asabe da Alh. Rabi'u ta yiwa magana da cewa "Da farko ina son baku hakuri akan duk wani abu da Munzali da Abbati suka yi wanda ya bata muku rai. Abu na biyu kuma ina son tunatar da mu duka cewa zama iyaye ba a ciki da haihuwa bane kadai kamar yadda Munzali ya yi ta nanatawa. Shiriya da 'bata ba a hannun iyaye yake ba. Amma akwai kokari da dagewa. So, kulawa, sawa da hanawa duk namu ne. Su din basu isa su gyara mana 'ya'ya ba. Amma kuma aikatasu yana kosar da zuciya. Yana sanya nutsuwa da kwanciyar hankali domin mutum ya san idan ya koma ga Allah yana da hujjar da za ta cece shi daga azabar tozarta amana."
"Ni wallahi na karbi laifina Maman Abbati. Zanyi duk abin da ya dace domin gyara kuskure na"
"Ki je wurinsa" Abbati ya ce da ita da farinciki.
Tana fita Alh. Rabi'u ya fita kamar zai tashi sama yana faman hardewa da babbar riga.
An fi ganin nisan daren da washegarinsa bawa yake da burin aiwatar da wani aikin da dole sai an jira gushewar daren. Haka mutum zai kwana zuciyarsa tana azalzalarsa da son ganin lokaci duk bayan gilmawar hannun agogo. Wani zai iya kwana yana buga tsaki da k'wafa. Yayinda mai wayo yake dauro alwala ya gana da Mahalicci. Idan hakan bai samu ba ayi ta tasbihi da tahmidi ana neman agajin Maiduka wurin ganin safiyar ta zo daidai da burin mai jiranta.
Mami Khadija a wannan dare bayan sun dawo daga ofishin 'yan sanda ko tunanin kwanciya bata iya yi ba. Duhun dare shi ya bawa Alh. Tahir mafaka ya sami damar sabulewa tuhume tuhumen da suke dankare a kokon zuciyarta.
"Ina da magana da kai" ta ce a lokacin da ta ga yana shirin ficewa daga gidan bayan sun kawosu shi da Comared.
"Ba a nan ba Khadija. Ki yi min alfarmar mu jira gari ya waye mu koma Kaduna"
Rokonta yake. Taji hakan a muryarsa ta kuma gani a yanayinsa. Ba don ta so ba ta amince saboda rufin asirinsu tunda akan ce bango ma yana da kunne. Kwana tayi sallah da jan ambaton Allah har aka kira Assalatu. Nan ma bayan tayi sallah tayi wanka gani tayi rana taki fitowa da wuri. Ba ita ta sami salama ba sai da motarsa ta shigo gidan ya nemi da ta fito su tafi.
"Ba zan bar su Farha su taho su kadai ba saboda tukin Lilu"
"Magana zamu yi kawai na dawo dake"
Ta kula gudun rigima yake. Jikinsa ma duk ya yi sanyi. Sannan ga dukkan alamu yadda bata runtsa ba shi ma haka ya kwana. Ba musu ta bishi. Matan gidan wadanda tuni suka karbi uzurin da Suhaib ya basu na jiya cewar Lilu ya bi saurayin Farha ne ba tare da yiwa Mamin tasu bayanin dalili ba. Shi yasa hankulansu suka tashi. Sai da suka je suka samu 'yarsa aka sace kuma basu dawo ba sai da aka ganta. Shi yasa yau tsokanar Mamin kawai suka dinga yi akan za ta bi mijinta cikin raha ba tare da tayar da zancen jiyan ba. Da zasu tafi har dakin samarin taje ta dauko wayar Danliti dama Suhaib ya cire lock din.
Gidan Comared ya tafi da ita kai tsaye. Suka shiga har falon da Abbati da Shazali suka duku akan boye Qibdiyya.
"Ina ne nan? Me yasa ka kawoni?" Ta tambaya rai a hade tana karewa hargitsin wurin kallo.
Wuri ya nuna mata ta zauna sannan ya bude baki ya fadi abin da yake jin shi ne rufin asirinsa da na su Abbati. Karfin kalaman da ya zube mata sun tafi akan boye laifin matasan ne wadanda zuwa yanzu ya amince da cewa komai na Allah akwai manufa. Wala Allah rufa musu asiri akan yakinin da ya samu na tubansu zai iya rage masa nasa nauyin.
Ya fara da tuna mata shi waye ta fannin mu'amala da mata. Ya cigaba da cewa ya zo gidan ne jiya domin haduwa da 'yan matan sai ya gamu da Abbati.
Katse shi tayi a firgice ta ce "Innalillahi. Kaddai su ma din..."
"Ko kusa" Alh. Tahir ya sami kansa da wani irin karfin gwiwa "kinsan Abbatin ma almajiri ne. Irinsu yawanci babu gata da kulawar babba a kusa. A nan suka hadu da shi wannan Shazalin dake unguwarsu Munzali. Abinka da kuruciya da rayuwar da abinci ma sai ka roka. Bai wahala ba wurin jan ra'ayinsu ya hadasu da manya aka dinga sakar musu kudi suna kasuwanci. Sai da aka bari kudin ya zauna musu sannan aka bijiro musu da irin aikin Shazali na kawalcin maza da mata. Da suka ki amincewa ne fa Shazalin ya dauke musu yarinya. Shi ne abin da ki ka gani jiya"
Mami ta dinga salati da hailala
"To amma kana da tabbas akan basu taba yi ba"
Tunawa yayi da irin rantsuwar da Abbati ya yi da kuma fushin da ya yi akan gara mutuwarsu da su komawa tsohuwar sana'arsu. Sai ya sake zabo kalmomin da zasu kwantar mata da hankali sannan a lokaci guda basu kaucewa abin da ya ji ba.
"Khadija wallahi Abbati bai san ina cikin gidan nan ba da farko. Amma ya yi ta rantsuwa akan gara ya rasa komai akan ya sabawa Mahaliccinsa."
Ajiyar zuciya tayi. Wani abu da ya kwana a wuyanta ya sauka ba tare da ta farga ba. Ta mika godiyarta ga Allah a fili da zahiri da Ya sanya basu cikin masu sabon Allah.
Alh. Tahir shi ma hakan ce ta kasance dashi. Zuciyarsa ta amince da tafiya da sirrinsu Abbati kushewa. Ba komai ya janyo hakan ba kuwa sai ganin cewa izina ce abin da ya faru jiya a gare shi. Kazamin mazinaci irinsa bai isa ya tserewa abin da ya shuka ba. To Amma Allah Buwayi Ya dubi zuciyar uwar 'ya'yan da su kansu Ya kangesu daga zinar. Shin wannan bai ishe shi godiya ba? Da kunnuwansa yaji kalaman tuba da nadamar Abbati. Idan ya hana shi 'yarsa ya san wane irin fasikin za ta hadu dashi? Rayuwarsu curarren zare ne mai wahalar warwara. To amma idan mutum ya nutsu zai gane cewa Allah Shi ne Gwani mai jujjuya lamura domin su dace da rubutun kaddarar allon kowane bawa.
"Ya ganka a nan din?"
Muryar Mami ta sauka a gare shi cike da alhinin amsarsa.
"Ya ganni. Ya kuma alkawarta min ba zasu taba tayar da maganar ba." Wata kwalla yaji ta cika idanunsa ya ce "kinga irin abin da ki ka jima kina fada min duk ya faru ko? 'Ya'yana sun san ko ni waye sannan maneman 'ya'yana ma sun sani"
An dawo inda ya dade yana mata kaikayi. Wayar Danliti ta damka masa bayan ta bude sakonnin da suke musaya shi da Jiddo. Jijiyoyin wuyansa suka tashi suka firfito saboda bakinciki.
Ta fara magana da fada masa zargin da ama yiwa Lilu na bata Qibdiyya. Da tsoron da take kada watarana gangan ta zama gaske. Sai ta koma batun Jiddo
"Tonon asirin wani ba abin kirki bane. Ban taba tunanin yin haka ga kowa ba. To amma ina gudun yadda kaddara ta fada mata nima wata rana za ta zo ta riskeni. Duk wata kamewata da yawan nasihar da nake yi maka ai ba iyawata bace. Ko kadan ban fi karfin Allah Ya jarabceni da aikata wani na'u'i na alfasha ba. Musamman na zina ko danginta wanda kubuce musu yake da wuya. Shi yasa na zabi ka sahale min wannan auren d..."
Mikewa ya yi ba shiri ya ce "Haba Khadija? In kina yiwa Allah ki bar maganar nan zan tuba"
Mami Khadija ta tashi ita ma "Allah Ya haramta zama da fasiki. Aurenmu tuntuni ya dace a raba shi domin in tsira da mutumcina. Zaman nawa me ya haifar banda kwaye maka baya a idon 'ya'yan cikinka?"
"Na tuba"
"Bukata daya ce yanzu ta rage a tsakaninmu. Ina rokonka arziki ka barni in yi maka idda mu rabu a mutumce. Zan yi bakinciki mafi girma da muni ace na mutu ka sanya hannu wurin sakani a makwancina a matsayinka na mijina. Haka kuma zan yi shi ace ina zaman yi maka takaba alhalin baka kasance cikin masu kunyar mummunan aikinsu ba"
Shiru ya yi na dan lokaci maganar ta sami kowace kusurwa a jikinsa ta shiga. Sannu a hankali ya daga kai ya dubeta ya ce,
"Tsanar da ki ka yi min har ta kai haka?"
"Ko kusa. Me zai sa na tsani mijina uban 'ya'yana? Mutumin da ya kyautata rayuwata da ta 'ya'yana da dukiyarsa da soyayya. Kyamar halinka nake yi domin duk dadin mu'amalar mu ta gidan duniya akwai ta lahira. Wadda zata nuna ina mutum ya nufa bayan an kare wannan gajeruwar rayuwar da bata da tabbas. Ina tsoron kada jindadin more rayuwa yasa in daina ganin aibun laifinka harma zuciyata ta daina yi masa kallon haram."
Kuka take yi. Kuka sosai. Ta durkushe akan gwiwoyinta ta daga hannuwa gareshi. A dimauce Alh. Tahir ya tayar da ita tsaye ya yi nufin rungumeta don lallashi amma ta kame jikinta wuri daya.
Jikinsa ya kara yin sanyi. Yaushe rabonta da amince masa a matsayin miji? Shi kansa ya manta.
"Ki yi shiru"
"Ka taimakeni ka sauwake min."
Kamar wani mahaukaci ya dubeta ya ce "Khadija wallahi zan tuba. Ke na ma tuba. Astagfirullah"
"Don Allah. Ka dubi darajar mai cikakkiyar daraja SAW. Ka raba ko igiya daya ce a tsakaninmu don Allah"
"Nace miki na tuba" ya furta hawaye na sauko masa. Bai taba sanin zafin soyayyarta ba sai a wannan gabar "ta yaya zan rayu babu ke? Ta yaya zan zuba ido ki zama mallakin wani?"
Mami Khadija ta daure ta kamo hannunsa ta rike tamkar suna musabiha.
"Ban san gobe ba. Bani da masaniya akan gaibu. Sai dai ina rokon Allah Sarkin Sarakuna. Idan akwai sauran zama a tsakaninmu, kada Ya bani ikon sake aure har na koma gareshi. Ya baka ikon tuba wanda ya cika dukkan sharudda. Ya tsayar da digadiganka akan siradil mustaqim. Ya tasheka cikin bayin da Ya aminta dasu. Ya kuma sake hada aurenmu a aljannah. Amma a duniya kam na gama auren nan in sha Allahu."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" a gabanta ya durkushe yana nanata wannan kalma sannan da kyar bayan ta soma fitar da rai ya ce "na sake ki saki daya. Don Allahn da kika sa na sake ki kada ki auri wani. Ki jirani. Ko a duniya ko a lahira zan tuba. Wallahi na tuba. Kai...me ya kaini? Wannan wane irin zalunci na yiwa kaina?"
Jikinta ya dauki rawa da jin kalmar sakin. Ta jima tana nema. Ashe duk dauriyar da take tunanin tana da ita bata kai ta kawo ba?
"Ina da gida a Kabala zan baki. Ki jira a gyara takardun in sanya sunanki kafin ki tashi."
"Nagode"
"Batun yara fa? Na san ke zasu bi. Da wuya su zauna a inda nake. Ina nufin ya zanyi in dawo da koda rabin ko kwatan mutumcina a idonsu?"
"Ka tuba. Allah zai yi maka sauran indai dominSa kayi."
Bai san shi dan gata bane kuma asararrarre sai yau. Yau ne ya nutsu ya saurari Khadija. Yau ne kuma igiyar aurensu ta sami targade.
Ya Allah Ka shafe mana kurakuran da suka gabata. Ka hanemu aikata wasu. Amin