← Book details Uwa Uwa Ce Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 10 OF 19

BABI NA SHA TARA.

Uwa Uwa Ce Part 2 Complete Hausa Novel · about 28 min read

Suhaib ya kamata ya kira amma gangar jiki da ruhi suka ki bawa Abbati hadin kai. Haka yatsansa ya dinga jujjuyawa akan sunan Farha yana tuhumar zuciyarsa da rashin jin magana har ya kai ga kira bai ankara ba. Cikin sauri ya kai hannu zai katse kiran sai dannawar tasa tayi daidai da sallamar muradin rayuwarsa. Zuciyarsa wani irin dokawa tayi sai da ya dafe kirjinsa. Ba yadda ya iya dole yayi saurin bin kiran da wani.
Sake dauka Farha tayi cikin macewar jiki da faduwar gaba. Sallamar da ta kuma yi ta riski kunnen Abbati da sautin karaya da tsoro. A take yaji tausayi da soyayyarta sun taso masa. Baya bukatar tuni yana sane da cewa shi mai laifi ne. Cikin kankanin lokaci ya sanya mata rai da soyayya harma da tunanin rayuwa a karkashin inuwa guda. Sai kuma ya soke mafarkin da ta fara ba tare da ya bata gamsashen bayani ba. Barinta cikin rashin sanin tudun dafawa ba karamin cutarwa bane. Bai tashi sanin hakan ba sai yanzu.
Ajiyar zuciya suka sauke a tare wanda sautin ya shiga kunnuwan junansu. Hakan ya sanyasu yin murmushi a lokaci guda.
Farha ce ta fara yin magana da cewa "nayi sallama baka amsa ba"
Tunanin Qibdiyya ne kadai ya hana shi nuna mata zahirin halin da zuciyarsa ta shiga sakamakon jin muryarta kadai.
"Kiyi hakuri. Wa alaikum salam. Kina lafiya?"
"Alhamdulillah. Kai fa?"
"Nima Alhamdulillah"
Shiru suka dan sake yi sannan ya yi ta maza ya ce "Ya Farha muna cikin wani yanayi ne yanzu dake tsananin bukatar addu'a. Don Allah ina neman alfarma ko sau daya ne ki roka mana sauki a wurin Allah."
Tausayi taji ya bata. Ta matsu taji mene ne ya yiwa kyakkyawar alakar da suka fara ginawa shamaki har tazara irin wannan ta wanzu a tsakaninsu.
"In sha Allahu zan yi"
"Baki tambayeni ko meye ba?" Ya ce da dan murmushin karfin hali.
"Na san idan ya kamata naji ba za ka boye ba"
Allah Sarki zuciya. Kalaman Farha kara nutsar da ita suka yi cikin zuciyar Abbati. A kullum yana kara yabawa da irin tarbiya da tsaftar tsatson da ta fito. Kafin ya manta ainihin dalilin kiran nasa ya ce ta yiwa Mami godiya akan taimakon da Suhaib ya yiwa Ayaah kafin su zo Kaduna suyi da kansu. Tunanin sake ganinsa nan kusa yasa ta fada masa cewa suna Kano ga kuma halin da Suhaib din yake ciki.
"Kuna gidan da muka zo biki?"
"Eh"
"Zan zo koda ni kadai ne saboda Munzali ma yau ya fito daga asibiti idan baku koma ba zuwa gobe ko jibi. Don Allah kada ki manta da adduar."
Zai katse wayar kenan yaji ta ce "baka bani abin sadaka ba. Naji ance ku Kanawa ko me zaku yi sai an biyaku"
Dariya ce ta kama shi ya ce "dadin abin kauyenmu a Jigawa yake nima bakon Kano ne"
Da murmushi Farha ta ce "Ai shikenan tunda ka fara rowa"
Da kyar ya iya sallama da ita suka ajiye wayar kowannensu yana jin matsananciyar kewar dan uwansa.
Daga nan zagaye ya dinga yi a titi domin zaman wuri daya ninka masa damuwa yake yi. Wani masallaci ya tsaya a gefen titi da aka kira azahar ya yi sallarsa tare da fatan samun nasara daga wurin Maikowa da komai. Akwai mutane da dama da zai iya kira su wulakanta masa rayuwar Shazali ba tare da ya daga hannu ba. Ya san manyan da zasu yi komai domin farincikinsa. Amma ko kusa ba zai nemi kowa ba. Domin kofar da yake son rufewa ce zata sake budewa. Shi yasa ya zabi kai kukansa inda ba a barin mutum ya dawo empty handed. Kamar jiransa Shazali yake yi kuwa sai ga waya. Sanar dashi adireshin inda zai je yayi da dariyar mugunta. Wannan yasa ya figi motar a guje da fargabar me ya sami 'yarsu.
Minti arba'in kafin Shazali ya kira Abbati ya amsa wayar wani kusan gwamnati wanda yake yiwa kawalcin 'yan mata. Da yake zancen nasu ya hada da yadda zasu koma biyan malaman makarantun kwana kamar yadda suke yi a ta maza ana basu dalibai sai ya fita daga gidan. Hirar sirri ce baya so ko Abdul ya san me yake ciki. Mukullan mota ya dauka ya ce masa zai je siyo wani abu ya dawo. Minti goma da fitarsa kuwa Abdul ya kamo hannun Qibdiyya yace ta zo ya kaita wurin mamanta.
Bata yi musun binsa ba don ta soma galabaita. Sam taki cin abinci sannan ga rashin iyaye ko wani idon sani. Abdul gani ya yi tana jan kafafu ya sunkuceta ya goya. Durowar da ya taba gani Shazali ya ajiye mukulli ya duba yaci sa'ar ganin mukullai daban daban a ciki. Lokutan baya bai taba tunanin dauka ba duk da idan Shazali zai fita yana rufe shi a ciki.
Wurin kala shida ya soka a jikin kofar saboda kusan duka girmansu daya kafin ya yi sa'ar jin ta bude. Ajiyar zuciya ya saki gami da sake ruko kafafun Qibdiyya a cikin hannuwansa. Yana sako kafa a waje yaji kamar an dauke masa kansa sakamakon hada kan da bango da Shazali ya yi. A kofar gida ya zauna yana wayarsa. Duk gwajin mukullan da Abdul yake yana ji. Haka ya shigo gidan a harzuke ya banka kofar ta rufe da karfi kafin ya hankada shi. Da kyar Abdul ya iya tsayuwa akan kafarsa don gudun kada ya kifa da baya ya danne Qibdiyya. Bayan ya sauketa kafafunsa ta rike ta buya a bayansa tana kuka. Shi kuwa kunnen bangaren da ya hadu da bangon yaji ya dauke dif sai wata kararrawa ce take bugawa kamar an kada tara a firamare.
"Har kayi tsaurin idon shiga lamarina Abdul? Waye ubanka a garin nan da kake jin ko kasheka nayi za a tada magana ma?"
Abdul babu amsa sai kunnensa da yake ta bubbugawa ko jinsa zai dawo daidai.
Kafadunsa Shazali ya rirrike ya shiga jijjiga shi yana masifa. Abu biyu ke damunsa. Na farko ya san duk kaunar da yake yiwa Abdul ya rasa shi kenan domin ba zai kuma kawo shi gidan nan ba. Na biyu kuwa wani mutum ya wuce ta kofar gidan a daidai lokacin da Abdul din ya tura kofar gidan. Babu tantama ya san cewa an ganshi. Bayan kuma ba a taba jin duriyar kowa a gidan ba.
Da kansa da ya gaji ya sake shi ya nuna shi da yatsa. Har lokacin dai bai dawo daidai ba. Kana ganin kwayar idanunsa zaka gane a cikin dimuwa yake.
"Ka jawowa kanka bala'i don na fuskanci akwai ganganci idan na mayar da kai makarantarku. Ka jirani in kai yarinyar nan wurin ubanta na dawo."
Cikin gidan ya wuce ya tafi dakinsa ya barsu a dan sararin tsakar gidan. Kukan Qibdiyya tuni ya dauke sai ajiyar zuciya saboda tsorata da tayi. A gabanta Abdul ya durkushe ya fiddo wata 'yar karamar waya kirar samsung mai torchlight. A makaranta ma ba a san yana da ita ba. Bai taba kiran kowa ba sai Shazali da suke musayar text messsage. Shi ma kuma bai san yazo gidan da ita ba. Gefen siket din Qibdiyya ya samu ya saka ta ya yi mata nadi biyu. Siket din sai ya dage sama amma ba za a gane da wayar ba saboda dan fadin rigarta.
"Ki boye wayar nan in kin hadu da babanki ki ce ya kira babana."
Da ka ta amsa tana rike dashi har Shazali ya dawo. Hannunta ya fincika ya fita da ita a ransa yana tunanin ko wa zai hadu dashi cikin makota ba zai damu ba domin yana dawowa zai fita da Abdul ya bar gidan gabadaya.
Fitarsu ke da wuya Abdul ya fadi a tsakar gidan. Jini kuma ya dinga silalowa daga cikin kunnen da ya bugi bango ta bangarensa.
Duk wata addua da Abbati ya sani ya karanta ta a hanyarsa ta zuwa gidan shakatawar Comared. Manyan motoci ya gani har biyar a harabar gidan. Da yake gidan gona ne mai dan karen girma. A kusa da ta Shazali ya ajiye tasa ya fito ya kira shi a waya. Maimakon ya dauka sai ya fito ya yi masa jagora zuwa ciki. Karfin zuciya ne ya hana shi far masa da duka tun a lokacin saboda bai san me zai sami Qibdiyya ba idan haka ta faru.
A cikin gidan kuwa Alh. Tahir ne zaune a wani daki wanda kofarsa take cikin falon suna magana da Comared.
"Har yanzu babu wani canji dole sai da namijin?" Ya sake maimaita tambayar da bai san sau nawa ya yiwa Comared ba.
Fuska ya kyabe kamar mai jin tausayinsa har zuci ya ce "ko dazu sai da na sake kiransa har nace ko ni zan iya yi maka aikin yace a'a"
"Allah Sarki mutumina. A hakan ma nagode sosai. Na san kai mai taimaka min ne har inda karfinka ya kare."
Comared ya tashi daga bakin gado ya ce "so nake ka kwantar da hankalinka. Yaron kwararre ne ya san me yake yi. Kafin ka farga anyi an gama"
Suna ciki suka jiyo sallamar Abbati domin dai shi Shazali bata gabansa. Hasali ma hankalinsa yana wurin Abdul. So yake ya koma gida ya yiwa yaron rashin mutumci kafin ya watsar dashi a titi.
Falon wayam babu kowa sai kayan ciye ciye da karar tv data AC. Qibdiyya Abbati ya nema da ido babu ita babu dalilinta. Cikin zafin nama da gajiya da danne bacin ransa ya riko Shazali ya tsayar dashi a gabansa. Da kakkausar muryar da shi kansa bai san bacin rai zai taba bashi irinta ba ya ce,
"Shazali ina Qibdiyya?"
To shi ma Shazalin bai san dakin da Comared da Alh. Tahir suke yana kusa dasu ba, shi yasa ya bashi amsa babu kwana-kwana. Dariyar mugunta ya fara da ita kafin ya ce,
"Tana nan kalau ko farcenta ban taba ba. Nan da awa guda idan kaso zaka tafi da 'yarka gida. Bukatarmu kawai kabi umarnin da aka baka"
Murya kasa-kasa Alh. Tahir ya tambayi Comared me yake faruwa. Ganin babu wata mafita sannan ya san a cikin matsi abokin nasa yake shi ne ya yi masa takaitaccen bayani. Bai kai ga yin magana ba suka ji Abbati ya daka wata irin tsawa. Su biyun duka jikinsu ya amsa duk da ba dasu yake ba. Barin ma Comared wanda tun isowarsu gidan yasa aka bata maganin bacci. Tana dakinsa na sama yana jiran Abbati da Alh. Tahir su shiga daki shi ma yaje ya afka mata.
"Shazali! Ka fito min da Qibdiyya idan ba haka...."
Cike da dakiyar 'yan barikin da suka yi nisa Shazali ya katse shi da cewa "in ba haka ba sai me Abbati? Kana da abin da zaka iya ne? Duk wani k'usan gwamnati ko maikudin da kake takama dashi ta dalilin wa ka sanshi?"
"Ana takama da Allah waye yake ta mutane? Wawa irinka ne zai dogara da halitta mai kayyadajjen wa'adi bayan akwai Maihalittar da bashi da karshe. Da nace maka ni da Munzali mun tuba ba da wasa nake ba."
"Aikin banza. Wane d'an son zuciyar ne ya ce muku Allah zai karbi irin wannan tuban naku? Shekararku nawa a wannan rayuwar? Kudi da duk wani connection dinku a kasar nan ba jikinku bane sanadinsa? Sai yanzu kuna tunanin kun gama tara abin da kuke so zaku wani ce kun tuba? Malam in zaka sha giya kasha ta duba. Allah Gafurur Rahim ne kowa ya san wannan. Kawai ku cigaba da gashi suya sai ranar sallah. Idan mutuwa tazo ka gaggauta istinginfari me yiwuwa a dace."
Karkada kai Abbati ya yi da murmushin takaici. A matsayinsa na bawa mai tarin zunubi kuma mai neman rahama ya yi imanin cewa shi din ba kowa bane. Amma duk da haka bakinciki mara misaltuwa ya danne zuciyarsa saboda maganar Shazali. Tsanarsa ta kara ruruwa a zuciyarsa saboda kalaman izgilancin da yaji daga bakinsa. Nasa imanin da tawakkalin kuma suka karu domin ya yarda cewa lallai shiriya ta Allah ce. Su da suka tuba ba wayo ko dabararsu bane. Cike da kosawa ya ce,
"Don Allah Shazali ka fito min da ita mu tafi. Bana son wannan case din ya kaimu gaban police."
Sama Shazali ya nuna masa yana yi masa kallon wulakanci
"To ni waye yace maka ina tsoron police? Kaga Abbati ka amince kayi abin nan ka zo ka tafi don nima uzuri ne a gabana. Mutumin nan ya riga ya saba sakarwa mata kudi kamar hauka. Wannan harkar ma don bako ne shi a cikinta shi yasa na nemo ka. "
"Babu ruwana da sanin ko shi waye. Da Allah fa nake hadaka akan ka bani 'yata mu tafi. Mece ce ribarka idan na koma wannan kazamar rayuwar?"
"Riba? Eh to ina da riba gaskiya. Zan jidadi na rabaku da tuban da kuke ikirari wanda yasa kuke yi min kallon dan wuta. Munafunci ne tuban naku tunda sai da aljihunku ya yi nauyi da haram zaku ce wai kun komawa Allah. Indai ina numfashi sai kun koma ruwa."
Murmushi Abbati ya yi mai ciwo. Bin Shazali ta laluma ba zai kara masa komai ba sai bacin rai. Idanuwansa ya daga yana kallon fanka wanda a zahiri zuciyarsa ce take fuskantar Mak'aginta.
"Ya Allah idan tubana dominKa ne, kuma niyyata ta barin dukkan abin da na mallaka ta haramtacciyar hanya dominKa ce ina rokonKa da ka tsare Qibdiyya. Kasa su fito da ita da kansu. Ya Allah kada Ka bawa Makiyanka dama a kaina da abokina. Kada Ka basu ikon sake mayar damu kazamar rayuwar da ka haramtawa bayinKa."
Kafada Shazali ya kada irin na ka yiwa kanka ya ce "Tunda baka da rabon arzikin nan to ka zauna ka jira Qibdiyya. Tana can ubangidana yana morar jikinta. Na san zamu sami fiye da abin da ya kamata a biyaka"
A guje Abbati ya tashi ya yi hanyar benen jikinsa yana rawa ga gumin da ya wanke shi a take. Ko rabin benen bai kai ba Shazali ya finciko shi ya fado. Akan hannunsa daya ya fada kuma yaji karar da ya yi amma hakan bai hana shi mikewa da zafin nama ba ya bangaje Shazali ya sake nufar benen.
"Qibdiyya! Qibdiyya!!"
Da Shazali ya sake riko shi rufe masa baki ya so yi saboda gudun kada Comared yaji hayaniyar. Idan ya rasa kudin wahalarsa ta kawo Abbati gidan nan ba karamin abu zai yi masa ba domin huce haushi.
Hannun da ya kai da nufin toshe masa baki Abbati ya damko ya sami sa'ar janyo shi ya kifar dashi a kasa. Bai dakata ba saboda tsananin bacin rai da kunar zuciya ya haye kansa ya shiga kai masa duka ko ta ina a fuska da lafiyayyen hannunsa. Cikin kankanin lokaci baki da hanci suka soma fitar da jini.
Duk kokarin Shazali da son ture shi ya kasa. Ihun neman ceton da yake yi da kyar yake fita saboda wahala.
Tun farkon maganganunsu Alh. Tahir yaji jikinsa yayi sanyi da Comared ya fada masa wanda aka kawo yayi ikirarin tuba. Kuma hakan ne ma ya zama dalilinsu na dauke 'yar amininsa wadda bata da maraba da matsayin 'yar cikinsa. Zai iya yin komai dominta. Sai kuma kwatsam yaji ya ce Munzali. Sannan ya kara da ambaton tuba da zantuka masu taba zuciya. Irin zantukan da ya saba jinsu da kalamai masu tasiri fiye da na Abbati daga matarsa. Amma a yau ne kadai ya fara shiga hankalinsa. Harbawar zuciya da gudun jininsa a cikin jijiyoyi ya dadu. Ya san suna Munzali da Abbati da kuma kasancewar Munzali uba ga wata yarinya da bai rike sunanta ba. Matasan samarin dake shirin zama surukansa. Idan ya fita Abbatin da ya kasance saurayin Farha na farko zai gani?
Bai san yadda aka yi ba ya iso kofar dakin zai murda Comared ya kama hannunsa.
"Alhaji kada ka fita don na fuskanci dan iskan yaron nan zai iya bamu matsala. Idan yaga fuskarka bai mana aiki ba tabbas zai iya tona mana asiri. Kuma yadda zuciyarsa take a kusan nan mu kanmu bamu san me zai mana ba. Ka jira in kira security."
Fizge hannunsa ya
yi ko amsa bai iya bawa Comared ba ya fita. A halin da ya sami Shazali da Abbati bai san lokacin da ya kwalawa Abbati kira ba bayan ya gama razana da ganin da gaske shi din ne.
"Abbati sake shi kada kayi kisa"
Bai san waye ya yi magana ba amma wuyan Shazali da yake neman shakewa yana maganganu a zauce don duk tunaninsa da gaske ana can ana cin zarafin Qibdiyya ya saki farat daya. Idanunsa hawaye suke fitarwa ya tashi a firgice da tsanar aika-aikan da yaso yi ba don an dakatar dashi ba. Da kakkausar murya ya nuna Shazalin dake kwance sannan ya juya ga mutane biyun da suke tsaye a hagunsa.
"Kai ne mutum na farko da ya fara sakamu cikin wannan masifa Shazali. Kuma har yanzu ka kasa hakura ka barmu mu koma ga Allah. Idan wani abu ya sami Qibdiyya wallahi zaku ga rashin ...."
Bai sami damar karasa maganar ba a sakamakon ido hudu da suka yi da Alh. Tahir. Idanuwansa ne kadai suka kara girma a yayinda wani kololon abu mai daci ya taso daga cikinsa ya tsaya masa a wuya. Cikinsa ya kulle tamau har sai da shiga da fitar iska cikin hancinsa suka soma wahalar dashi. Kafafunsa da yake umarta da su zaga dakunan gidan su nemo Qibdiyya sannan ya fita kuwa suka ki motsawa.
'Zina 'yar aike ce. Duk inda ka turata zata dawo ta isar maka da sako. Bana yi mana fata domin dawowarta gidan nan ba zai taba zama alkhairi ba. Sai dai ina so ka sani koda tayi batan kai da sannu wata rana za a sami mai nuna mata hanya. A lokacin ko bata tuna cikakken sakon ba saboda shudewar lokaci, sallamarta kadai zata hargitsa tunaninmu. Na barka lafiya!'
Ga Alh. Tahir kuwa, wannan sakon na Mami Khadija wanda ta tura masa tun washegarin ranar da Yumna ta fallasa komai ga Farha ne ya dawo masa tar. Ko batan wasali bai yi ba wurin tunano kalmomin daki-daki tamkar yanzu yake karanta su. Hantar cikinsa ta buga a tsorace da ya yiwa sakon fahimtar da ta dace dashi. Tun kafin ya bincika yaji ko akwai wanzuwar haramtacciyar alaka tsakanin su Abbati da 'ya'yansa ya gama shiga tashin hankali. Sanin cewa sun taba yin luwadi duk da a yanzu kunnuwansa sun jiye masa nadama da tubansu kadai ba karamin bala'i ya jefa zuciyarsa ba. Ko shi da zina ta gama bin jinin jikinsa ba karamin kyama yake yiwa wannan nau'in nata ba. Haka ya dinga jin kamar ana sassara adda a sassan jikinsa. Bai san wanne daga cikin masifun da suke gabansa ya kamata ya fara yiwa kukan bakinciki ba. Ganin Abbati a wannan gida da sanin waye shi ko kuwa ganin da Abbati ya yi masa da sanin nasa sirrin?
Kallon kallo da suka tsaya yiwa juna ne ya bawa Comared damar tayar da Shazali ya zaunar dashi akan kujera. Da yaga kallon yaki karewa ne ya dubesu da mamaki sosai.
"Alh. Tahir ko kun san juna ne?"
Yawu yaso hadiya domin bayar da amsa amma ya laluba yaji babu danshi a bakin nasa. Kansa yaso kadawa shi ma yaji ya yi masa nauyi. Comared kawai sai ya ce,
"Shi ne yaron da aka dauko 'yarsu ai domin ya amince da aikinka." Yana gama magana ya juya ga Abbati "wannan haukan da kayi a gidan nan baka ci bulus ba wallahi. Idan kana takama da zafin kai ka tarar da ubangidansa. Sai na daureka igiya tayi rara."
A sanyaye Alh. Tahir ya daga kai ya kalli dakunan dake sama ya ce "Comared a wane daki yarinyar take?"
Wani irin duba Comared din ya yi masa sai dai bai iya yin musu ba ya nuna masa kofar da hannu.
Abbati ya kalla fuskokinsu duka babu digon nutsuwa.
"Daukota ka zo ku tafi"
"A'a Alh. Tahir, bangane ba. Ya zaka sallamesu batare da shawarta ta ba?"
"Nawa ne zai fanshi uba da 'yar Comared? Nawa zan baku ku kyalesu har abada?"
Sakin Shazali Comared ya yi ya taso har gaban Alh. Tahir cike da dumbin mamaki.
"Alhaji ka san shi din da gaske?"
"Da ne a wurina. Iyaka abin da zan iya fada maka kenan"
Kai Comared ya kada alamun ya amince Abbati ya hau saman. A gurguje kuwa ya haye ya bude dakin da aka rufe ta waje amma key na jikin kofar. A tsakiyar gadon ya sameta ta dukunkune jiki tana bacci. Kwalla mai zafi ta zubo masa a lokacin da ya rankwafa ya daukota. Jikinta zafi rau da zazzabi. Yana dorata a kafadarsa yaji dumin zafin yana nasar nasa jikin. Ba shiri ya dagota ya dorata akan kafar damansa da ya dora a bakin gadon.
"Qibdiyya. Bude idonki Papa ne"
Da kyar ta bude idon saboda gajiya, yunwa da kuma aikin maganin baccin da Comared ya dura mata. Yadda kanta yake kifewa da kansa kamar 'yar maye ya sake daga masa hankali. Jikinta yabi da hannu daya ya mammatsa domin son ya farkar da ita. A nan ne kuma yaji ya tabo wani abu mai dan tauri a kugunta A razane ya dan daga rigarta ya ciro shi daga cikin siket dinta. Bakinsa da kyar ya iya hada tambayar wayar waye gareta. Cikin yanayin rashin kuzarin da take ta ce masa,
"Cewa ya yi na baka"
Aljihunsa ya tura wayar ya mayar da ita kafadarsa ya sauka. Idan ta dawo daidai zai tambayeta waye ya bata. Da ya sauko babu wanda ya kalla haka ya fita daga falon. Sai da ya isa bakin motar har ya kwantar da Qibdiyya a baya sannan yaji an ambaci sunansa da murya mai rauni sosai. Gabansa ya yanke ya fadi domin bai san da wane ido zasu kalli juna ba balle har su yi bayanin fidda kai.
Minti goma sha biyar da isar Alh. Sadisu Nakano makarantarsu Abdul ta hargitse kamar ana cin kasuwa. Tun daga Principal har Masinja babu wanda bai shiga sahun zagaye makarantar ba ana neman Abdul. Principal din yafi kowa rikicewa don sai yau ya san akwai dan Alh. Sadisun a makarantar.
Tun lokacin da yasa aka kawo shi makarantar dama ya bukaci a boye ko dan waye. Kudin da yake turowa domin kulawa dashi kuwa bai bambanta da wanda wasu iyayen kan yi ba sai ta adadi. Malamin ajinsu wanda kudin ke biyowa ta hannunsa yana isar da sako tare da yin tasa bushashar son rai.
Daya daga cikin masu gadi ne ya ruga ya sanar da Principal bakon da suka yi tun kafin su shigo ciki. Principal din ya tashi da sauri ya shiga kankanta ofishinsa domin yana da labarin zuwan bazata da Alh. Sadisu ya kan yi makarantu. A zatonsa yau sallarsa ce ta kama don yasa rai da samun wani abu mai nauyi daga babban bako. Bai tashi shiga tashin hankali ba sai bayan sun gaisa Alh. Sadisu ya bukaci a kira masa dansa. Dan aike wato Masinjansa ya dawo da mummunan labari cewa wai washegarin dawowarsu makaranta ya koma gida bashi da lafiya. Daga nan aka soma diramar!
Tashi Alh. Sadisu yayi tsaye cikin fushi da kaduwa ya hankada teburin Principal din dake gabansa. Ji kake kiyyyy, ya tafi ya daki bango. Abubuwan da suke kai wadanda suka yi zaman dakin kishiyar da ba a shiri da ita suka rufto kasa.
"Bana son zancen banza da hofi. Yaron wajena nake nema Abdul. SS2 B yake. Sunan form master dinsu Sir Balarabe. Hostel dinsu kuma Sardauna House. Ya ce min a kwanar da gadonsa yake akwai Victor da Faisal"
Jinjina kai Masinjan da Principal suka yi na mamakin yadda ya rike komai da ya shafi dansa. Direbansa da PA da suka zo tare basu dauki hakan komai ba. Saurin rike abubuwa suna daga cikin manyan jarinsa da suka kawo shi inda yake yanzu.
"Ranka ya dade zauna bari naje ajinsu da kaina na kirawo shi. Ina jin sakon ne bai fahinta da kyau ba."
Principal dai bai sami damar dawowa ba sakamakon matsalar da ya tarar. Lokacin ba a tashi daga aji ba. Yana zuwa Monita da sauran 'yan aji suka tabbatar masa da cewa kamar yadda aka bukaci su dawo asabar saboda damina ana bukatar gyara makaranta, Abdul ya dawo amma ba a wayi garin lahadi dashi ba.
"Me yasa ban san labarin nan ba sai yau?" Cewar Principal yana gumi tare da tsare malamar dake ajin tana koyarwa a lokacin.
"Ranka ya dade Mal. Balarabe ya kamata ka tambaya. Nima ban san komai ba"
Tare da Monitan ajin da Assistant dinsa ya tafi staffroom din malamai maza. Yana shiga ya kira sunan Mal. Balarabe sai dai nan take aka sanar dashi baya nan shi da wasu malamai biyu abokansa.
"Bangane ba? Ina ya tafi ana cikin wannan yanayin?"
Wani malami ne ya bashi amsa da cewa "babu yadda za ayi ya zauna alhalin duka makaranta ta dauka cewa dan Alh. Sadisu ya bata."
"To shi ya batar dashi da zai gudu?" Ya tambaya a fusace.
Malaman dai basu ce komai ba tunda basu san me yake faruwa ba. Haka ya koma ofishinsa da yaran nan biyu cike da fargabar yadda zai fara yiwa Alh. Sadisu bayani. A inda ya barshi tsaye ya dawo ya same shi yana kai gauro da mari. Yana ganinsa kuwa ya ce ina Abdul.
"Yallabai ka zauna kaji daga bakin yaran nan. Daga nan sai mu san abin yi."
Rainin wayo Alh. Sadisu ya dauki zancen Principal din. Sai dai kuma ance idan rakuminka ya bata ka duba har cikin hudar allura. Bisa wannan dalilin ya saurari Monitan wanda ya maimaita sak abin da ya fadawa Principal.
"Yanzu kai baka ji kunyar cewa na tsaya jin wannan wasan yaran ba? Cewa zaka yi makarantarka babu tsaro har ana shigowa a sace 'ya'yan mutane. To wallahi banda dana. Kai, ina tsammanin baka gane ni ba ko? Suna na Alh. Sadisu Nakano kuma ko uban mutum ne yake mulkin kasar nan bai isa ya hanani koya masa hankali ba." Ya nuna kofa da hannu "kaje ka nemo maigadin da ya kwana ranar asabar din. Da malamin ajinsu duk inda yake..ku hadu ku nemo min dana"
Da Principal da mataimakansa biyu tare da malaman da suka yi cirko-cirko a kofar ofishin kowa hankalinsa ya tashi. Alh. Sadisu ma dauriya kawai yake domin zuciyarsa tuni ta fara karanto masa sunayen abokan hamayyarsa wadanda zasu iya dauke masa da a matsayin fansa ko garkuwa.
"Sir?"
Kowa juyowa yayi don jin wa dalibin dake matsayin mataimakin monita yake kira. Kai tsaye Principal din nasu yake duba ya ce,
"Ina jin fa ba bata ya yi ba. Tun kafin hutu yawanci da daddare ranar juma'a Sir Balarabe yana zuwa kiran wasu a hostel. Yawancinsu da safe suke dawowa. Wasu kuma sai lahadi..." Ya kalli monitan "ba shi ne muke cewa ko lesson ake musu banda mu ba?"
Da ace kunnuwa suna jin gaibu yau da ofishin Principal dinnan ya cika da bugun zukata. Duk wani mai hankali a cikin wurin tunaninsa ya karkata daidai da na uban yaron da ake nema. Wannan kuwa ba bakon abu bane tunda akan ji labarai makamantan haka a makarantun kwana.
Cijewa Alh. Sadisu ya yi ya daure ya tambayi yaron ko mutum nawa ne suka bar makaranta rana daya da Abdul. Babu musu kuwa ya lissafo masa su biyar.
"Amma sauran hudun duka ranar lahadi suka dawo da daddare. Shi kadai ne Sir Balarabe ya ce gida ya koma"
Cikin karaji da gigita Alh. Sadisu ya ce "A nemo min Balaraben da masu gadi"
"Sir Balarabe ya fita"
"Mal. Bawa maigadi baya nan"
"Malaman dake abota da Sir Balarabe ma basa nan"
Wadannan ne amsoshin da suka biyo bayan umarnin da Alh. Sadisu ya bayar. Da aka gama fada dariya ya kwashe da ita. Wata irin dariya mai dauke da bakinciki da bacin rai gami da tsoro. Kamar yadda ya fara ta kuma a bazata haka yayi dif ya daina lokaci guda. Kallo mai ban tsoro yabi mutanen da suke gabansa sannan ya daga waya ya kara a kunne.
"Ku fara aikinku"
Cikin kankanin lokaci gabadaya makarantar ta kasance a zagaye da 'yan sanda. Wasu suka shigo aka fara yiwa duk mai ruwa da tsaki tambayoyi. Ya kira su ne tun kafin Principal din ya dawo daga binciko masa me ya faru.
Ma'aikatan jarida kama daga na gidajen rediyo zuwa tv suma suka soma dafifi. Alh. Sadisu ya tsaya a kofar ofishin Principal da na'u'rorin daukar magana kala kala a saitin bakinsa ya ce,
"Ba roko nake ba shawara ce. Na bada awa biyu kacal a dawo min da dana inda aka dauke shi."
Ayaah, Murja da Ummita ne suka tashi daga gaban mahaifinsu da Abdulkarim bayan sun gaishe shi. Kafin su fita ya sake jajantawa Ayaah abin da ya faru jiya tare da shawara gareta da 'yan uwanta akan tsare mutumci saboda gurbacewar zamani. Bayan sun koma wurin Anti Hasiya aikin gabansu suka cigaba. Ayaah kuwa kusa da antinta ta koma ta kwanta ta rufe ido.
"Dalla can tashi, ai kin san yau kece da wanke-wanken safe"
Baki Ayaah ta turo ta tashi rai a bace za ta soma gunaguni Anti Hasiya ta ce ta koma ta kwanta.
"Haba Murja! Yanzu har kin manta abin da ya sameta jiya kike kira mata wanke-wanke? Duka duka yaushe garin ma ya waye?"
Murja da Ummita suka dubi juna suka bushe da dariya. Karfe goma shadaya harda minti bakwai. Shi ne Antinsu take cewa yaushe gari ya waye. Sannan bata tashi ba Ayaah da Murja suka yi fada kamar zasu ari baki a kofar bandaki. Ita kuma tana tasowa ta cigaba da lallabata.
Labarin fadan suka bata ta koma yiwa Ayaah kallon tuhuma. Amma da yake ba a cinyeta da baki sai da ta magantu.
"Dauriya ce fa kawai nake Anti amma har yanzu ban dawo daidai ba. Kuma bana son ki shiga damuwa shi yasa nayi kokarin dawowa daidai."
"Yanzu tsiwa ce daidai dinki Ayaah? Allah nagode Maka" cewar Anti Hasiya tana dariya.
Raharsu suka cigaba da yi cike da so da kaunar juna. Anti Hasiya ta dubesu daya bayan daya ta sake mika godiyarta ga Allah. Irin wannan zaman na ahali daya kuma da zuciya daya tayi ta buri. Sai gashi lokaci guda Allah Ya amsa addu'o'i'nta. Kan yaranta ya hadu sannan ita ma ta sami rabon da zata kira nata. Uwa uba an Abbas yana shirin samun lafiya da yardar Allah.
"Ina ta sa ran jin ka tambayeni me yasa na nacewa gidanka naji shiru"
Abdulkarim ne ya yiwa Honourable tambayar bayan sun gama gaisawa sannan ya fada masa daren yau ake bukatar kwantar da Abbas a asibiti. Washegari ake sa ran yi masa aikin da safe. Likitan da zai jagoranci aikin ya iso Kano.
Da yake Honourable ya fishi kwarewa a sakin magana sai cewa ya yi "Wata kake so cikin 'yan matan gidana ko?"
Yadda ya yi maganar kai tsaye ya bawa Abdulkarim mamaki domin bai yi maganar da kowa ba sai zuciyarsa. Zaro idanun da ya yi ba tare da ya ce komai ba yasa Honourable bude baki.
"Don Allah wai da gaske kake?"
Kwarjini Honourable ya yi masa fiye da kullum amma ya san ranar wanka ba a boyon cibi. Tunda dai Ummita ba za ta aurar da kanta ba dole ne ya fadawa mahaifinta.
"Da gaske nake"
Honourable ya gyara zama yana dariyar kunya da takurar da yake gani a tattare da Abdulkarim.
"Murja dai an kawo kudinta. Ya rage Ayaah da Ummita"
Abdulkarim ya dan tura hularsa baya kadan ya ce "Umminmu din nake so. Allah Yasa wani bai rigani ba. Kuma don Allah kada ka sako zancen shekaru wallahi da sauran tafiya kafin nayi hamsin ma."
Dariya sosai ta kama Honourable. Farincikinsa ba zai misaltu ba. Wato da gaske bayan kowane tsanani akwai sauki. Sai dai wani hanzari ba gudu ba...
" Abdulkarim anya baka yiwa Ummita nisa ba. Ba batun shekara nake maka ba. Ina nufin a zamantakewa ta wayewar rayuwa da arziki. Ina jin tsoron kada ku sami rashin daidaito a dalilin ..."
Dakatar dashi Abdulkarim ya yi ya nuna masa rashin jindadin furucinsa.
"Ka sanni kafin na zama wannan Abdulkarim din. Duk abin da na samu a sakamakon kusanci da kai ne a lokacin da nima ban dace da kusantar mutum irinka ba. Amincewarka nazo nema domin na nemi soyayyarta. Ba zan so ayi mata fin karfi ba saboda wani abu da na samu na takaitaccen lokaci"
Fuskar Honourable dai babu komai cikinta sai annuri. Tashi ya yi ya ce masa idan sun gama shiri anjima zasu tafi asibitin zai kira shi.
Abdulkarim sai ya shiga rudani ya ce "maganar Umminmu din fa?"
Wata dariyar Honourable ya sake yi
"Naga dai yanzu ba lokacin tadi bane da rana tsaka amma dai bari na turota kwashe kwanuka."
Kunya ce ta kama Abdulkarim amma abinka da manya sai ya fuske. Ba jimawa kuwa yaji sallamarta a kofar falon. Da ya amsa ya yi zaton zata shigo amma shiru har kusan minti biyu. Ga alamun tsayuwarta a bayan labule yana gani amma taki motsi. Babu mamaki babanta ya fada mata yadda suka yi. Banda haka me zai hanata shigowa don yana ciki?
"Nifa dan gata ne a gidan nan. Idan baki shigo da kafafunki ba ko Ayaah na kira zasu hadu da Murja su daukoki a ka"
Ja da baya tayi cike da tararrabin me ya kamata tayi. Bayan kusan sakan talatin ta matso jikin labulen ta damke shi da hannu ba tare da ta bude ba ta ce,
"Ni wallahi kunya nake ji"
Murmushi ya sami kansa da yi ya taso ya dawo bakin kofar ya tsaya ta yadda suke iya ganin shatin juna. Ummita bata ma san ya iso wurin ba sai da taji amsarsa a kurkusa.
"Banda abinki idan baki ji kunyata ba ai sai ki sa na fara kokwonton zabina"
A wautarta ji tayi amsar tasa bata cika ba.
"Ni kadai ce mai jin kunyar?"
"A iya sanina dai mata sun fi son namiji mai karancin kunya akansu."
"Wai naga kamar 'ya nake a wajenka"
"Wai idan kin dauka kallon 'ya nake yi miki ki ajiye."
Hannu kawai Ummita ta kai ta rufe bakinta saboda murmushin da ta kasa daina yi. Gabadaya nauyinsa take ji sannan tana mamakin yadda ya sake abinsa ya ma manta ita wace ce. Duk da cewa ba yau ta fara sanin soyayya ba, wannan tazo mata da salo mai girman da yafi karfin shekaru da tunaninta.
Zurfafa da tayi a tunani ya bashi damar kallon irin tsayuwar da tayi. A jikin kofar ta dan jinkina sai gefen labulen da ta rike amma taki budewa. Kusa da inda hannunta yake ya kama bata lura ba sai ganin fuskarsa tayi ta bayyana a gabanta. Ja tayi da baya zata gudu ya girgiza kai wanda yanayin fuskarsa da tayi mata kwarjini ta hanata kin bin umarninsa.
"Gajiya nayi da hirar bayan labulen kamar wani mara gaskiya"
"To ka koma zan shigo na zauna"
"Na yafe. Zan dawo anjima idan za a kai Abbas asibiti."
"To Allah Ya kaimu." Ta furta da azama tana son tafiya.
"Dawo Aminatu ban sallameki ba tukunna."
Dagowa tayi a hankali da niyar kallonsa ta kasa. Ya san mamakin sunanta da ya fada take yi. Shima ya yi mamakin rashin mantawa. Kodayake bai taba manta duk abin da ya shafi Honourable ba.
"Nace ba, wai nayi miki kuwa?"
"Innalillahi ..." Furta tare da rufe fuska tana dariya kasa-kasa.
"Ya kike ja min Innalillahi? Nayi?"
Dariyar dai ta cigaba da yi cike da kunya ya ce "in dauki wannan kunyar a matsayin amincewarki kenan?"
Da ka ta amsa masa.
"Nagode Ummi-ta. In sha Allahu ba zan baki kunya ba daga ranar da zama ya hadamu a inuwar aure."
Kafin ta daga kafa har ya fito. Kunya bata barta tayi masa sallama ba.
Chapter 10 · 0% Book details