← Book details Uwa Uwa Ce Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 4 OF 19

BABI NA GOMA SHA UKU.

Uwa Uwa Ce Part 2 Complete Hausa Novel · about 28 min read

Naji korafe korafe kai tsaye da ma na aike kala kala game da dorawa Lilu laifin da ba nasa ba. Na so kamewa daga bayar da amsa sai dai ku gani a rubuce. To amma wasu har ikirarin barin karatun suke. Jama'a idan kun barwa Batul labaranta ina ta kama? Sakon da nake fatan Allah Ya bani ikon isarwa bai je ko ina ba kenan. Ya zama dole na magantu.
Kafin na fara wanke kaina, ina so inyi amfani da wannan damar wurin yi muku godiya. Akwai gajiya matuka idan marubuci yana daukan dogon zango kafin ya yi post. Sai dai kamar kullum hakuri dai zan cigaba da baku. Ba da gangan bane. Yau da gobe ce wadda take nukurkusar daukacin al'ummar kasar duniya ba ma kasar nan ba. Allah Mabuwayi Ya kawo mana saukin lamura. Amin
To mu koma ga labarinmu. Kwanakin baya korafin akan yawan wahalhalun Innayo da rashin cin moriyar guminta ne suka yi yawa. Wasu har suna ganin kamar zan sagar musu da gwiwa wajen kulawa da amanar da Allah Ya bamu ta zuri'a. Ko daya ba nufina ba kenan. Labarin nan kacokan ban yi shi domin tsantsar nishadi ba. Wasu lamura nayi ta nazari a rayuwarmu shi yasa nake son yinsa ta yadda zaiyi kamanceceniya da zahirin rayuwa. Akwai Innayo bila'adadin a cikin al'ummarmu. Mace ta wahaltawa miji ta kuma wahaltawa 'ya'ya. Amma a karshe haka zata koma ga Allah da bakincikin dukkansu. Ta rayu a talauce ta mutu cikin talauci. To amma fa shafin rayuwarta ba zai kare a wurin Maqaginta ba muddin ta koma gareshi tana mai gaskata kadaitar mulkinSa. Daga lokacin ne ma zata fara shan romon ladan ayyuka da hakurinta har zuwa tashin qiyama. Sai dai taji ance ta wuce Aljanna gidan dauwamamen farincki.
Game da Lilu kada mu manta su waye iyayensa. Uba mazinaci wanda har yanzu babu wata kwakkwarar nadama a tattare dashi. Shin idan zina bata dawo masa a inda zai yi masa ciwo ba kuna ganin zai san Annabi ya faku? Zai ji ciwon da iyayen 'ya'yan da ya mu'amalanta suka ji? Zai yi nadamar ayyukansa har ma ya tuba? Sanin tsohuwar sana'ar maneman 'ya'yansa ba ta da babban tasiri indai ba an riga an daura aure ba. A yanzu kam ba zai wuce ya soke auren ba ya cigaba da yawonsa. Wanda kuma duk ya yi zina da ahalin wani shi ma sai anyi da nasa.
A gefe guda kuma mahaifiya ga Lilu mace ce tagari. Uwa ce da ta amsa sunanta wurin tarbiyya da yawan yiwa 'ya'yanta addua. Ga Ubangijin da take mikawa lamuranta Mai ji ne ga kukan bayinSa. Al Hayyu, Al Qayyumu ba zai bata kunya ba.
Gamu ga Sarkin da baya saba alkawari. Mahaliccin da Adalci ya kasance cikin suffofinSa. Duk da cewa labari ne amma ina son tunatar damu uwaye karfin addua. Tabbas alkawarin Allah na dawowa mazinata da sharrinsu ta hanyar da zasu koka ba zai tashi ba. Sannan kuma adduar Uwa ta gari ga 'ya'yanta wannan kaifiyan ce.
Indai haka ne kuwa to lallai Alh. Tahir sai ya yi kuka akan sharrin da aka yiwa Lilu. Sannan Mami Khadija sai ta kara mika wuya ga Allah a yayinda Ya kubutar mata da danta daga dabaibayin da bai isa ya kwance ba.
Ya Rabbi ka karawa Annabinka daraja, Ka azurta shi da kololuwar daukaka. Amin.
Mami Khadija kiran Lilu tayi bayan ta rufe kofarta. A zatonta Alh. Tahir ya bar wurin ashe yana tsaye. Kafafunsa sun yi masa nauyi ya kasa dagasu. Lalacewarsa bata yi kamarin da zai iya cigaba da jure juya baya daga tsatsonsa ba. Bazuwar zancen nan zuwa kunnuwan ragowar 'ya'yansa ba karamar barazana bane ga mutumcinsa a idanunsu. Shi kuwa zai iya komai domin kare wannan martabar. A tsarinsa miji ko mata kada ya fishi girman masauki a zuciyarsu. Yana son ya zama babban amininsu kamar yadda suka faro tun kuruciya. Wannan dalilin ne ma yasa Farha da Lilu suka ji ciwon laifin nasa fiye da yadda zasu misalta. Muryar Mami yaji cikin dakiyar da ya saba gani a tare da ita tana magana da Lilu.
"Ina ka tafi?"
Bai ji amsar ba sai abin da ta mayar masa. Yadda tayi magana babu alamun wasa ko wargi. Umarni ne take bayarwa domin ta kare dan nata.
"Yana daga cikin rahamomin Ubangiji garemu da Ya halatta mana yin abota. Lokuta da dama suna maye gurbi ko ma su fi family dinmu tsaya mana akan matsaloli. Sai dai kuma ba kowacce irin matsala ya kamata a fadawa aboki ba. Wani abin sirrinka ne har lahira. Idan yau kaje wurin abokai da damuwar nan har ka fada musu komai ka cuci kanka. Ba kai kadai ba hatta 'yan uwanka ka tozartasu a idon duniya. Saboda haka duk mummunan sirrinka da Allah bai tona ba kada ka zama mai fitar dashi. Zai zama tamkar ka cakawa kanka wuka ne da kanka. Shi mahaifi sutura ne ga zuri'arsa. Abu kadan idan ya faru wanda ya dauke uba daga muhallinsa a wurin 'ya'ya sai kaji ana kiransu 'ya'yan mace. Kuskure guda daya tak zasu aikata sai a kusa shekara ana goranta musu duk don babu uba kuma babu madadin uban. To ina ga kai da kanka ka tona halin naka? Abokanka karshenta suyi maka tayin kayan maye. A halin da kake ciki na san karba zaka yi"
Shiru suka yi na 'yan dakiku kafin Mami Khadija ta ambaci alkunyarsa wadda mutane suka bar kiransa da ita.
"Khalil?"
"Na'am" ya amsa da muryar da ta makale a makoshi saboda damuwa.
"Ina fata sunanka zai jagoranci hukuncin da za ka yanke domin ni kam bani da sauran abin cewa gareka. Banda iyayena dominku nake komai. Don Allah kada ku sa bayan kukan miji na dora da na 'ya'ya."
Lilu sai ya fashe da kuka. Mami Khadija ta dinga rarrashinsa da kalmomi masu dadi. Ba don gargadin da tayi masa ba tabbas idan yaje wurin abokan nasa sai ya farkewa mahaifinsa laya. A ganinsa hakan ba zai zama komai ga mutumin da bai iya daraja kansa ba. Ya manta bayan shi akwai 'yan uwansa. 'Yan uwan ma mata masu rauni. Gashi babu wadda tayi aure. Wane dan mutumcin ne zai so auren 'yar mutumin da aminiyar 'yarsa take ikirarin yayi mata ciki?
Da wannan tunanin ya sauyawa shawararsa akala. Alwala ya dauro ya sanya dogon wando da tsaftatacciyar jallabiya ya dauki littafi mai tsarki ya soma karantawa.
(Babu wani abu mai canja kaddarar bawa ko ya sassauta ta kamar addua. Duk takun da bawa zai yi domin kusanta kansa da Mahalicci, Sarkin da bashi da wa'adin zamani zai zo gareshi da fiye da wannan.)
Shi kuwa Alh. Tahir kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki haka ya bar kofar dakin. Kamar da wasa haka ya shigo tariyo wasu kazaman mu'amala da ya yi da mata daban daban. Tunanin kuwa yayi sanadiyar radadi mai azaba a cikin zuciyarsa. Yana cike da tsoro matuka a wayi gari duka 'ya'yansa suna yi masa kallon fasiki. Wannan rana ya tabbata zata fi kowacce muni a gareshi. Ba zai jure kallon kyama irin wanda Suhaib da Farha suka bishi dashi ba daga dukkansu. Shi bai ma san soyayyarsu tayi masa irin wannan kamun ba sai yau. Har musu ya yi da zuciyarsa akan cewa yanzu son da fargabar kiyayyarsu ya ninku sau adadin da bai sani ba a ransa. Zazzabi ya soma ji tun kafin ya isa nasa bangaren. Tunani ya sha masa kai bai ga isowar Suhaib gabansa ba sai muryarsa wadda ta dawo dashi hayyacinsa yaji.
"Ina son zuwa Kano gobe in sha Allahu."
Alh. Tahir ya ware idanunsa sosai da son dawo da nutsuwarsa jikinsa. Bashi da lokacin zurfafa tambaya ko binciken me dan nasa zai je yi a Kano daga dawowarsu yau. Ya dai aminta dashi ya san ba shashanci ne zai kai shi ba. 'To ma idan shashancin ne ai a wurinka ya gada' wani sashe na zuciyarsa ya tuna masa.
Shi dai Suhaib yanayin sanyin da ya gani a wurin mahaifin nasa ya bashi mamaki. Domin Alh. Tahir mutum ne mai yin komai da kuzari. Sai ya sami kansa da kasa sharewa.
"Abba lafiya dai?"
Alh. Tahir yayi murmushin jindadi har hakoransa suka fito. Yau shi ne Suhaib yake nuna damuwa akan damuwarsa.
"Lafiya kalau. Kaina ke ciwo shi yasa ma na dawo da wuri. Anjima kazo in kara maka guzuri"
"Na gode. Kuma Allah Ya kara sauki" cewar Suhaib yana yin gaba.
Wurin Mami Khadija ya wuce don baya son sai dare yaje yace zai yi tafiya da safe.
Tunda taji sallamarsa bata yarda ya karaso dakin ya sameta a yanayin da take ciki ba. Fuska ta saki har ya shigo ya fada mata zancen tafiyar. Ba karamin dadi taji ba kuwa saboda ko kadan bata so ya fuskanci abin da ya faru. Tafiyar tasa tamkar rage karfin rikicin da take gudu ne. Dagula komai zai yi da fushinsa da zuciya.
"Allah Ya kiyaye hanya. Kwana nawa zaka yi?"
Suhaib wani irin kallo ya yi mata na rashin gamsuwa. Maminsa mai bin kwakkwafin yara normally cewa zata yi me zai je yi.
"Mami lafiya kuwa? Ko baki da lafiya?"
Fahimtar inda ya dagota da tayi yasa ta nemo murmushi ta dora akan fuskarta.
"Wai don kaga ban tambayeka komai game da tafiyar ba?"
Kai ya gyada kawai yana yi mata kallo na son gano inda baraka take idan akwai ta.
Murmushi ta sake yi sosai ta ce "jikina ne ya bani kamar surukata daga Kanon zata zo. Ko dai wurinta zaka je ko kuma idan ka tafi yau zaku hadu."
Suhaib dai bai san kujerar da Ayaah ta samu a zuciyarsa ba amma kalaman Mami sun saka shi jin kunya. Shi din ba ma'abocin harkar mata bane saboda tsoronsa na zama tamkar babansa. Faffadan murmushin kama kai ya shiga yi gami da susar keya.
Mami Khadija ta mike cike da farinciki tana dariyar da ta bayyana hakora.
"Hasashena ya zama gaskiya akwaita kenan. Alhamdulillahi. Na santa?"
"Nifa Mami ki ma daina wannan batu don ban girma ba."
Kallon ka-ma-rainani tayi masa tana cewa "to bari nayi addu'a ga wadda zaka je wurinta din. Allah Ya kawo mata santalelen miji wanda zai aureta nan ba da jim...."
Abin da yayi a lokacin har ya koma dakinsa yana mamakin kansa. Katse addu'ar Mami ya yi da saurinsa yana mai bata fuska.
"Ba amin ba."
Ta dage gira tana leken fuskarsa da yayi kicin kicin da ita.
"Koda kaine mijin?"
Shi ma sai sannan ya gano tasa katobarar. Gaggawar fita daga dakin nata ya yi cike da jin kunya yana cewa ba abin da take zato bane.
Sai da ta tabbatar ya fita ta iya sauke ajiyar zuciya. Farha ce kuma a ranta yanzu. Yarinyar tana da dauriya fiye da zato da tsammani. Da ta matsa mata da tambaya tabbas ta sanar da ita cewa har yanzu bata ji daga Abbati ba. Bai daga wayarta ba sannan kuma bai nemeta ba. Hankalinta taji ya tashi da tsoron kada zuwansa rayuwar Farha ya zama tamkar lasawa yaro zuma a baki. Da ace abin da ya saka shi komawa gida ya girmama bata jin mahaifiyarsa zata boye mata lokacin da suka yi waya. Tunanin ba zai fissheta komai ba shi yasa ta fita zuwa dakin 'yan matan.
(Allah Ya zama gatanka akan duk abin da baka da iko akansa)
Sakon sms da Farha ta turawa Abbati kenan taji an murda kofar dakinta. Mami Khadija ce ta shigo da sallama. Farha tayi saurin gyara zama daga kashingiden da tayi.
"Ya naga kowa ido biyu ne? Na zata zan sameku duk kun kwanta saboda sammakon da akayi."
Dan murmushi Farha tayi tana cewa kwanciyar zata yi yanzu. Mami sai ta sami wuri a bakin ta zauna.
"Farha" ta kirata a tausashe. Ba da baki Farhan ta amsa ba, sai dai ta tattaro hankalinta da nutsuwa ta mikawa mahaifiyarta. Mami Khadija ta cigaba da magana "kafin faruwar abin nan, ina nufin tafiyarsu gida babu shiri ranar da suke ganawa dasu Abbanku kun samu sabani ne?"
"A'a Mami" cewar Farha tana danne kwallarta. Kewa da damuwa akan rashin sanin halin da Abbati yake ciki sun yi mata yawa. Karfin hali da dauriyar tata sun kai makurarsu.
"Ki kwantar da hankalinki ki kuma yawaita addu'a. Ba komai da muke so bane alkhairi a garemu. Miji kuma babu matar da zata auri wanda ba nata ba" da dan sauri Farha ta dago ta dubeta tana son ta ce ita dai Abbatin kadai take so amma ta kasa. Mamin ma dai murmushi tayi "ke dai ki kasance mai mika wuya wurin karbar kaddara. Mijinki da yardar Allah wanda zaku kama hannun juna ne har aljanna. Bana miki fatan haduwa da abokin rayuwa wanda zaki so tatayyarku ta kare a duniya kadai."
Farha ta san da wa Mami take shi yasa ta dinga zubar da hawaye. Duniyar gabadaya sauki ne da ita amma mazauna cikinta suyi ta jajibowa kansu matsaloli ta hanyar sabon Allah.
A daren ranar Jiddo ta kira Danliti ta fada masa Suhaib ya karbi nambarsa a wurinta. Ta kara da cewa bata san manufarsa ba saboda haka tana mai gargadinsa da ya yi taka tsantsan. Ya kuwa yi mata alkawarin kiyayewa.
Sai dai kuma ta riga ta makaro. Tun bayan komawar Suhaib dakinsa ya kira shi. Sauya murya ya yi yadda ba zai saurin gano shi ba ya ce kwatancen garejinsu yake nema.
"Kwanaki mun zo tare da wani abokina daga Abuja har ka bashi nambarka. Na shigo gari ne mota take ta bani matsala. Idan zan sami gyaran da wuri ina son kawo maka ita gobe."
Kalmar Abuja kadai da Danliti yaji tasa shi bayar da cikakken kwatance harda wata nambar idan bai same shi a wannan ba. A gefe guda kuma maganar Jiddo ta sanya shi yiwa Ayaah mugun tanadi. Indai akwai wata alaka tsakaninta da Suhaib da wannan shirin nasa zai bakanta masa rai. Ita kuma ya zama ladan bata masa lokaci kamar bata san me ya kawo shi ba tun farko.
Duk wani taimako da Uwani zata iya bawa Qibdiyya tayi a lokacin wanda bashi da wani yawa. Mafi a'ala a kaita asibiti wurin kwakrarren likita domin a dubata yadda ya dace. Shawarar da ta bawa Munzali kenan bayan sun fito daga dakin.
Kai ya gyada mata ba tare da ya iya magana ba. Zazzabi yake ji yana bin lungu da sako na jikinsa kamar ana gasawa akan gar
washi. Numfashi da iskar da yake fesarwa ta baki ta hanci duk zafine dasu. Daki ya nuna musu a kasa ya ce idan zasu kwana ne ga wuri nan idan sun idar da sallar magariba. In kuma zasu tafi ne shi ma ga kudin mota don ba zai iya tuki ba. Ficewa ya yi daga gidan bayan ya yi tasa sallar a daddafe yana taku kamar a iska saboda rashin nauyin jiki yaje kofar gidan Abbati. Shi kadai kawai yake son fadawa abin da yake faruwa domin ya dauki mataki. Don sai yanzu ya kara yarda cewa Abbatin ya fishi tunani. Duk inda ya laluba sai yaga kamar idan ya taba Lilu sai ya kashe shi. Ya san zafin fyade tunda Shazali ya yi masa a shekarun da suka fi na Qibdiyya ma. Ya san ciwon da rai ke rikewa a yayinda ya san cewa shi ne sanadiyar dulmiyar wani a aikin sabo. Wannan ya tilasta masa yin sanyin da yake ganin yanzu ba muhallinsa bane. Salamar da ya san Abbati zai cusawa ransa ko yaki ko yaso ya tattaro ya sanyawa zuciyarsa. Saboda idan bai nutsu ba yana da yakinin cewa sai ya yi abin da zai yi nadama a gaba. Gara ya nemi uban Qibdiyya ya nemi shawararsa kafin ya zartar da nasa hukuncin. Ya debi kusan mintuna goma yana sallama da kwankwansa kofa kafin Hanne ta bude masa. Yadda ta bude kofar da dankwali a hannu zai sanar da duk wanda ya ganta cewa daga bacci ta tashi. Yatsina fuska tayi da ta ganshi taja guntun tsaki. Murmushi mai ciwo ya yi mata. A ransa yake jin kinsa da take yi tuntuni ba zai rasa nasaba da kasancewarsa sanadiyar bata rayuwar mijinta ba.
"Don Allah kin yi waya da Abbati? Na neme shi na kasa samunsa."
"Rabona dashi tun ranar asabar da kuka fita tare" ta bashi amsa tana cika tana batsewa. Ganin bai ce mata uffan ba ya juya zai tafi sai ta ce "kayi ka gama munafurcinka na son saka shi ya min kishiya. Ta Allah ba taka ba."
Bai ko waiga ba balle ya kalleta. Yana ji ta buga kofa da karfinta kamar za ta balleta. Gida ya koma ya shige daki bayan sallama da su Uwani sun ce ba zasu kwana ba. Asabe ta so ya bata Qibdiyya su koma ya ki. Bayan tafiyarsu ya karbi abinci a wajen Kande ya bawa Qibdiyya. Yarinyar jikinta duk yayi sanyi ta kasa sakin jiki tayi wasa saboda yanayin da taga babanta. A jikinsa kawai ta sami wuri ta kwanta tayi lakwas.
Munzali ya dinga kallonta yana kara tsinewa Shazali. Ya kuma kara tsanar Alh. Rabi'u wanda sakacinsa ya zama masomin lalacewar tarbiyar gidansu. Duk abin da ya samesu da shi 'yan uwansa babansu ne sila. Sakarwa iyalansa mata ragamar gidansa da hadasu da nauyi da hakkokin da ba nasu ba shi ne matakin farko na tabarbarewar lamuransu. Tsatson Innayo sun dace da uwa ta gari amma halin uba ya zama jirwaye ga tarbiyar irinsu Uwani. Shi kuwa da 'yan uwansa da basu yi sa'ar uwa ba sai dukan ya zame musu biyu.
Waya ya dauka ya sake kiran Abbati duk da bai sa ran cewa za a amsa ba. Jikinsa yana bashi cewa Abbati yana cikin koshin lafiyar jiki. Sai dai bashi da tabbacin ta ruhi. Washegari litinin dama ya yi niyyar binsa idan shirun ya yi yawa. Ya tabbata sirrin boye ya riga ya fito fili. Wannan lokacin ne Abbati yafi bukatarsa. Su Baaba Mari zasu yafewa Abbati idan suka ji cewa shi ne ya fara saka shi a wannan hanyar zasu dauki laifin su dawo masa dashi.
A cikin halin ciwo Baaba Mari take sosai don sun sake komawa asibiti. 'Yan uwa da basu san me yake faruwa ba suna ta al'ajabin wannan abu. Ace mutum kamar Abbati ya kasa kai mahaifiyarsa babban asibiti a halin da take ciki. Tun ana kananun maganganu da safe har aka fara tararsa gaba da gaba ana fada masa zuwa yamma. Kannensa ma sai da suka nuna bacin ransu sosai. Ya rasa inda zai saka ransa yaji dadi. Ciwo yana cinta amma ta ce indai ba halal ya nemo ba ya barta ta mutu ta huta.
Wuraren Isha sai ga Mal. Inuwa ya shigo dakin kamar an koro shi. Kullin leda ya dauko daga aljihun 'yar sharar jikinsa ya mikawa Abbati.
"Ga wannan dubu talatin da hudu ne mu mayar da ita babban asibiti."
Da kyar Baaba Mari ta iya bude idanunta ta dube su. Mal. Inuwa yana ganin fasalin kallon mai kama da na tuhuma ya hau rantse rantse. Yanzu tsoron bacin ranta yake yi da gaske.
"Gonarmu da wajen gari na sayar. Da shike ba girma gareta ba shi yasa bata yi kudi sosai ba. Nan an warewa duka 'ya'yan Malam (yan uwansa da suka hada uba) kasonsu. Wannan ne nawa." Ya sake nuna ledar.
Da Abbati ya karba sai da yaji kamar bai taba rike rabi rabinsu ba a rayuwarsa. Kudi dai ya baya miliyan biyar baya a asusunsa na bankin da atm din yake jikinsa a yanzu haka. Da za a tara abin da ya tara da kadarorinsa shi ma ba zai ce ga adadin abin da za a samu ba. Sai dai duk wannan arziki tubalin toka ne. Kwakkwarar iska guda ta hure komai saboda haram dama bata da nauyi. Da zarar mutum ya dauki damarar rabuwa da ita indai da zuciya daya ne to tafi komai saukin saukewa.
Suna shirin tafiya don har an samu musu mota kwatsam sai ga Mal. Sa'idu a kofar dakin yana sallama. Kallon kallo aka soma tsakanin Abbati da kannensa. Dame kuma yazo?
Mal. Inuwa ne ya leka sai dai bai jima ba ya dawo yace Abbati yaje.
"Gani"
Leda sak irin ta hannun Mal. Inuwa ya mika masa. Da ace hankalin Abbati a kwance yake da yaga yadda tsufan kawun nasa ya sake bayyana. Ya zabge sosai a tashin hankalin kwana daya. Allah Ya ragewa aya zakinta akwai hannunsa dumu dumu a cikin rayuwar duka 'ya'yan gidan. Ba don haka ba da tuni ya lakabawa Baaba Mari laifin bata danta. Kila ma zuwa yanzu duka gidan da garin sun gama ji har an karar da tofin Allah tsinen da za ayi masa. Da yake shi ne uban gayya mai daukar credit din cigaban duka 'ya'yan gidan dole ya karbi lalacewarsu ma. Ta Abbati dai ta fito fili, zuciyarsa kuma tana nan tana raya masa cewa ba shi kadai bane ya fada tarkon shaidan daga zuwa karatu.
"Gashi nan ka kara a kudin asibitin"
Karba kawai Abbati ya yi ya koma ciki ko daga kai ya kalle shi bai yi ba.
Haka suka fita ana ta juyayin wannan lamari na ciwon Baaba Mari da Mal. Sa'idu a cikin gidan. Deluwa tayi nacin har ta saduda aka son jin kwaf.
Habi da Abbati ne kadai masu tafiya tare da mahaifansu. Babban asibitin gwamnatin Dutse suka tafi. Cikin dare sosai suka isa garin. An kuma karbi Baaba Mari an fara bata taimakon da ya dace. Zuwa safiya jikinta ya soma daidaita sosai sai hamdala. Bayan azahar ne da Abbati ya tabbatar an sami kanta yadda yake bukata ya iya dauko wayarsa. Ashe ta shiga silent ba tare da saninsa ba. Missed calls ya gani rututu. Na Munzali sun fi na kowa yawa. Sai na wanda suka nada yake kular musu da ginin plaza. Plazar da sai dai idan gwamnati ta gaji da ganinta ta san yadda zata yi da ita tunda komai na samuwarta haram ne. Na Farha basu fi biyar ba. Ya san lallai ita din ba mai takurawa bace. Tunda ya tafi a irin wannan yanayin kuma bai nemeta ba ta tabbata abin ya girmama. Babu na Hanne ko daya. Dama ita bukata ke sanyata nemansa ko zai yi sati bata ganshi ba.
Wani irin yanayi na shaukin soyayyar da mai yinta ya san bata tafe da cikar buri ne ya shige shi. Abubuwan da ya yi ta gudu a baya game da rasata sun bayyana. Ko yana hauka baya jin zai iya sake komawa gareta. Arzikin da ya zame masa garkuwar neman aurenta ya kau. Yanzu bashi da maraba da almajirin kan hanya mai jiran sadaka. Messages din ta turo masa har sunfi kiran yawa. A kalla a rana ta turo uku. Nasihohi ne da maganganun kwantar da hankali. Zuciyarsa ta sake karaya. Ba don karfin addu'ar mahaifiya ba da jajircewarsa wurin son ya kyautata tuba da ya koma gareta. Zai kirata ya jaddada mata girman soyayyarta da alkawarin aure.
"Allah Ya baki wanda ya fini a wurinsa. Allah Ya cire min kaunarkiba don na daina sonki ba Ya Farha."
Adduar da ya yi kenan iya jin kunnuwansa sai dai Baaba Mari tana ganin motsin bakinsa.
Adadin kiran da Munzali ya yi masa ne ya dakatar dashi daga rufe wayar. Munzali ya san me ya kawo shi gida. Ya san abubuwa marasa dadi dole zasu faru. Ya kuma san cewa zai neme shi da zarar abubuwa sunyi sauki. Babu lafiya jikinsa ya bashi. Bai yi tunanin komai ba ya kira shi tare da fatan ya amsa da gaggawa.
Ringing din farko ma bai gama shiga ba Munzali ya dauki wayar da sauri. Hannunsa yana rawa ya kara wayar a kunnensa. Zazzabi yake mai zafi da matsanancin ciwon kai ya kasa tashi zaune ma balle ya nemi agajin kukunsu a kai shi asibiti ko a bashi magani.
Yadda numfashinsa yake fita da sauti da kuma canjin muryarsa kadai suka ganar da Abbati cewa bashi da lafiya.
"Munzali me ya sameka? Kana ina?"
"Qibdiyya aka yiwa .. "
Sallah Baaba Mari zata tayar daga zaune ba shiri ta katse kabbarar haramarta ta kira Abbati a fusace.
"Abbati. Bani wayar nan!" Ta kalli Habi wadda ta tsorata "bamu wuri". Da saurinta kuwa ta fice duk da tana son jin me ake boye musu.
Tashi Abbati ya yi yaje gabanta ya durkusa sannan ya bata wayar. A wurin ya cigaba da durkuso ita kuma ta kara wayar a kunnenta. Kafin tayi magana Munzali dama yaji kiran da ta yiwa Abbati saboda haka bai yi mamakin jin muryarta ba.
"Munzali..." Da fada taso kiransa domin ya san duk abin da zata fada ba wasa bane. Sai dai kuma yana amsawa taji tausayinsa ya tsirga mata.
Gaisheta ya yi da faduwar gaba "Baaba ina wuni?"
Bata amsa ba. Sai ma kai tsaye fada masa abin da yake gabanta.
"Don sonka da Allah da ManzonSa (SAW) babu kai babu Abbati indai da gaske tuban kuka saka a gaba."
Tunda Abbati yake bai taba yiwa Baaba Mari musu ba amma yanzu bai san lokacin da ya kira sunanta da karfi ba. Jikinsa ya kama rawa ya sanya hannuwa ya dafa cinyarta.
"Baaba don Allah kada kice haka. Nayi miki rantsuwa da sunayen Allah tsarkaka wallahi bama neman juna. Abotarmu ita kadai ce halattaciyar dangantakar dake tsakaninmu. Domin Allah muke yinta ba don..."
Fuskarta babu annuri ko miskala zarratin amma ga hawaye suna gudu akan nagartacciyar fuskarta. A lokacin da Abbati yake nasa maganganun tana jinsa da kunne daya shi ma Munzali nasa yake yi mata.
Magana yake cikin dakewar murya domin kuwa iya abin da ya rage masa kenan. Mutuwa yake yiwa kansa fata domin yana ganim idan har Allah Ya karbi tubansa to lallai can din zai fiye masa akan rayuwa ba tare da aminin kwarai ba. Ashe alkhairi na karshe da zai gifta a tsakaninsa da Abbati shi ne assasa masa tuban da bai hangowa nan kusa ba. Kamar wanda ake cakawa mashi a kahon zuci haka ya dinga ji a lokacin da yake yi mata magana.
"In sha Allahu zaki sameni mai biyayya a gareki Baaba. Babu ni banu Abbati. Zan tashi daga gidan da nake kafin ya dawo Kano."
"Shi ma ba zai dawo ba. Ku nesanta da juna sannan ku nesanta da dukiyar haram. Sannan ne zaku yi tuba da kyakkyawar zuciya. Wala Allah zaku samu rabauta a nan duniya da lahira."
Kuka ya fashe dashi ba tare da sanin cewa Abbati ma kukan yake mata ba.
"Ki yafeni Baaba. Don Allah kada ki kai karata wurin Allah akan Abbati. Ko naki hakkin na rage ina sa ran samun sauki ko yaya yake a wurin Mahaliccina."
Rufe ido tayi wasu hawayen suka sauko a guje masu zafi.
"Na yafe maka. Allah Ya yi muku albarka."
Abbati na jin haka sai ya ce "Baaba don Allah ki tambaye shi me ya sami Qibdiyyan"
Munazali yaji tambayar da yayi. Wani daci ne ya taso masa daga makogaro har wuya a sanda ya ce
"Fyade aka yi mata Baaba amma don Allah kada ki fada masa. Bata ji ba bata gani ba ta soma girbar shukata tun kafin ta fahimci duniyar kanta."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Baaba Mari ta fada tana jin kamar ciwonta zai dawo. Masifun zamanin nan sun yi matukar yawa.
A gigice Abbati ya ce "mutuwa tayi?"
Da ta girgiza masa kai sai ya ce "Baaba ki bani don Allah ko sallama ne muyi dashi."
Tausayi ya bata ta mika masa wayar sai dai yana karawa a kunne yaji kit Munzali ya katse kiran. Kiransa ya yi amma taki shiga domin kuwa yana katsewar ya kasheta. Ya kuma lallaba ya kashe sauran ukun ma wadanda duka Abbati yana da lambobin.
Da Abbati ya gaji da gwada kiransa ya dubi Baaba Mari tamkar karamin yaro ya ce "kinga ya kashe wayoyinsa."
"Saboda yana son ka shiga sahun masu bin maganar iyayensu."
Bai iya cewa komai ba sai kifa kai da yayi akan cinyarta yana sheshekar kuka. Ita ma nata hawayen take yi saboda nauyin raba wannan abota. A bangaren Munzali kuwa shi ma kwanciya ya yi yana jin yadda hawaye suke gangarawa cikin kunnuwansa.
Gari ya waye yau ta kama litinin. A garin Kaduna Mardiyya da Sauda sun shirya sun tafi makaranta. A Kano ma Ayaah tana shirin tafiya tasu makarantar. Dukkaninsu suna aji shida ne a makarantar sakandire. Kwanaki kalilan suka rage su fara jarabawar NECO. Ayaah bata sami damar yin JAMB ba sabods rashin kudi amma su sunyi.
Kunun tsamiya Ayaah ta damawa Anti Hasiya kafin ta fita. Tana sanye da farin dogon wando da shudiyar rigar da ta kawo mata har gwiwa sun sha karin guga. Fitina irin ta dalibai rigar ta kamata tsam sai ka rasa yadda ma take iya numfashi.
A gaban Anti Hasiya ta durkusa da flask din kunu tana tambayarta ko ta zuba mata kafin ta tafi makaranta.
Yamutsa fuska Anti Hasiya tayi saboda rashin dadin baki. Jikinta gabadaya babu dadi ta rasa gane a wace duniyar take. Tunda aka sallamota ta kasa tabuka komai a cikin gidan. Daga amai sai kwanciya. Ita ce zazzabi ita ce ciwon kai. Honourable kansa ya zama kamar mai jinyar. Hasiya ita ce zuciyar gidansa. Matar rufin asiri ce wadda baya fatan ya shiga cikin sahun mazaje masu butulcewa a lokacin samu. Shi da yaransa duka rige rigen kyautata mata suke yi. Ga Abbas an sanya ranar aikinsa nan da sati hudu. An hado shi da magunguna kuma ana ganin amfaninsu. Sai da ta gama yi mata fadan dinkin rigarta wanda bata san lokacin da aka tsuke shi ba da kashedin tana dawowa yau ta bayar a budeta sannan ta bata amsa.
"Kadan zaki zuba amma ki matsa min lemon tsami a ciki"
Ayaah ta fiddo ido waje ba shiri da taji abin da ta ce.
"Tsamiyar ta fito fa yadda kike so. Don Allah ki hakura ki sha a haka."
"In kin tafi ma Murja zata bani, gara ma ki saka min kawai."
Rabin wani dan karami Ayaah ta matse mata sannan ta dauke ledar lemon tsamin ta tura a jaka akan idon Anti Hasiya.
Ita kuwa ta marairaice mata saboda tsamin kadai ke taimaka mata ta sanya wani abu a cikinta.
Murja da ta zama raguwar karfi da yaji saboda tsabar tausayin halin da antinsu take ciki ta taso za ta duba jakar Ayaah ta dauki lemon tsamin. Ayaah ta galla mata harara tana kankame jakarta. Cikin fushi ta ce no
"Tunda ba ke za a haifawa kanin ko kanwar ba ai gara ki bata tasha ta haifo mai yamushasshiyar fata irin na Altine. Kin manta yadda muka dinga tsoron daukar dan saboda kamaninsa da tsofaffi?"
Murja ta ja tsaki "sai aka ce miki lemon tsami ne ya busar masa da fata?"
"Idan ma dai ba shi kadai bane wallahi kika bata bayan na tafi makaranta ban yaf..."
Anti Hasiya bata san lokacin da tayi murmushi ba.
"Ya isa Ayaah ba ma zan sha ba kada Allah Ya isan ta bini nima."
Duk sai suka yi dariya har Ummi da ke wankin wake. Bayan fitar Ayaah shiru Anti Hasiya tayi tana mai al'ajabin kudurar Ubangiji. Watanni biyu da suka wuce idan ance Ayaah zata sauko daga dokin da ta hau su zauna lafiya zata karyata. Sai gashi cikin lokaci kankani da ta dage da addua da kuma bin shawarwarin Salima komai ya sauya. Ko yanzu sai dai tayi ta hamdala ga Allah. Rayuwa kam tayi juyin alkhairi dasu. Zuwan Minister Abdulkarim ya kawo musu canji a rayuwa. Abbas ana sa masa rai da samun lafiya. Kan 'ya'yanta kuma a hade yanzu sannan uwa uba wannan gagarumar kyauta ta samun ciki.
Ayaah na adaidaita sahu wayarta ta dauki ruri. Lokuta da dama tafiyar kafa take yi kusan mintuna talatin a hanya zuwa da dawowa. Yanzu kuwa kudin mota na sati aka bata wannan satin. Mamakin mai kiranta da sanyin safiyar nan me ya kama ta. Cikin aljihun wandonta inda ta boye wayar ta zura hannu ta lalubota. Dama ta tafi da ita ne domin kawarta ta saka mata fim. Sunan Dani ta gani baro baro a jiki. Gabanta ya yi mummunar faduwa da ta tuna haduwarsu ta karshe. Amma abin da yafi tsaya mata a rai kuma ya sanyata tsorata bai wuce fuskar wannan saurayin da taji kannensa sun kira shi da Ya Suhaib ba. Ta shaida irin bacin ransa lokacin da Dani yake neman tabata. Tayi ta kokarin hana kanta tunanin abubuwan da suka faru ranar sai gashi wannan wayar ta dagula mata lissafi.
Wani kiran ne ya sake shigowa wancan na tsinkewa. Numfashi ta sauke da karfi sannan ta amsa. Cikin kwantacciyar muryar da ya saba hillatarta da ita ya yi magana. Sai dai wannan karon fushi ya nuna mata.
"Baby ni zaki kai gidan kakanninki ki wulakanta?"
Daburcewa tayi ta ce "wulakanci kuma Dani? Me nayi maka?"
"Au tambayata ma kike yi? Don na bude miki cikina kin san sirrin gidana shi ne kika kira yayanki yazo ya wulakantani. Me ya hanaki tsayuwa kiyi masa bayanin alakarmu banda kina min kallon dan iska?"
Gabadaya hankalin Ayaah sai ya tashi ta soma bashi hakuri. Ya dinga ja mata rai har sai da direban adaidaita sahun ya dan waiga ya kalleta saboda jin yadda take magiya.
A gadarance Danliti ya ce "Abu daya ne zai sa na hakura Baby. Zan zo makarantarku na daukeki anjima ki zo ki gaishe da Mummy"
Da murnar ganin rikicinsu yazo karshe Ayaah ta ce "ta dawo ne?"
"Ta dawo kuma na fada mata komai game dake. Tana son ganinki ne domin gobe ta yiwa kawunnai na magana. Wikent (weekend) dinnan sai su zo su ga Baba asa mana rana."
Dan jim Ayaah tayi kafin ta ce "yanzu makaranta zanje kuma gaskiya Anti Hasiya ba za ta yarda na bika ko ina ba."
"Matar da kika ce bata sonki."
Ita ta fada masa da bakinta amma da ya maimaita sai da taji mugun haushi. Yanzu kam uwa ta dauki Anti Hasiya kuma ba za ta yarda wani ya fadi maganar batanci akanta ba. Kwalla taji a idanunta ta daukesu da yatsanta. Danliti tuni ya gane zuciyarta a karye take. Hakuri kawai ya bata ya cigaba da dorata a keken bera.
"Ban san me nayi miki wanda ya dauke duk wata daraja da girmana da kike gani ba a baya. Ni dai alfarma nake nema ko daga makarantar ne ki zo muje taga zabina. In Allah Ya yarda nan da sati biyu ko ba ayi biki ba na tabbata an daura mana aure"
Sunan makarantar ta bashi tare da fada masa yadda zasu hadu idan an fito break karfe goma da minti arba'in da biyar.
Goma daidai Suhaib yana cikin wani gareji a unguwar Na'ibawa wanda ya dace da kwatancen da Danliti ya yi masa. Wani Dan bumburutu ya samu ya kai shi wurin tun daga gadar da zata sada bako da farkon garin Kano daga titin Zaria. Garejin nasu sananne ne saboda kusancinsa da babban titin fita gari. Matafiya da yawa suna tsayawa ko a dauko musu makanike daga nan. Bayan ya sallami yaron da ya kawo shi ya karasa wurin ma'aikatan da suka yi da'ira ana ta mayar da zance da wani Alhaji.
Sallama ya yi musu sannan ya ce "Don Allah Danliti nake nema."
Kusan mutum hudu a tare suka ce masa ya fita. Wani ne ya kara da cewa,
"Kaima wani abu ya hadaka dashi ne?"
"Eh" Suhaib ya ce kai tsaye ganin kowa ya zuba masa ido da alamun bacin rai.
Taron sai ya karkato ya hada dashi inda a take yaji rigimar da ake yi. Motar da ya gama gyarawa ya dauka ya sanar da abokinsa na garejin wai budurwarsa ce bata da lafiya a makaranta shi ne zai je ya kaita gida.
Gaban Suhaib ya yi muguwar faduwar da bai san ainihin dalilinta ba.
"Don Allah waye ya san inda zan same shi?" Ya kara da cewa "me yace sunan budurwar?"
Abokin masa da aka tsare yana bada amsa kamar shi ne Danlitin ya dan jinjina kai kafin ya ce "baby dai naji yana ta cewa. Amma kafin ya tafi ya kira wani abokinsa da suke yawan zuwa nan tare Rabilu ya ce masa wai yau zai rufe shafin Ayaah. Sai dai gaskiya ni ban san abin da yake nufi ba."
Kwatanta irin rudanin da Suhaib ya shiga ba zai misaltu ba. Su kansu mutanen wurin sun tsorata da yanayinsa. Musamman da ya ce,
"Ku san yadda zaku yi ku hadani dashi kafin ya cuci yarinyar mutane domin wallahi idan ya taba mutumcinta gabadayanku sai na daureku."
Hargaginsa bai basu damar binciken ko shi waye ba. Suturarsa da motar da yazo da ita sun ishesu amsa. Dan garejin nasu da bai taka kara ya karya ba basu ga mai kwarjinin ja da Suhaib din ba. Shi ma kuma mai motar da Danlitin ya dauka yabi bayan Suhaib ya ce kararsa zai yi. Saboda haka nan da nan wurin ya kacame ana tattauna yadda za a same shi tunda yaki daukar waya kafin ya ida nufi.
Chapter 4 · 0% Book details