BABI NA ASHIRIN DA BIYAR.
Uwa Uwa Ce Part 2 Complete Hausa Novel · about 34 min read
Zaune yake gaban likita na goma sha uku cikin jerin likitocin da ya ziyarta domin magance matsalarsa. Amsa yake nema don ya san a wane babi zai ajiye lafiyar kwakwalwa da tunaninsa.
Ya gama bayani tsaf akan yadda ya dauki Abbati da zargin da mutane makusantansa suke yi masa kamar yadda ya yiwa sauran likitocin. Ya kare da cewa,
"Bayani nake so a mahanga ta addini. Idan bani da rabon samun rahama ne saboda irin tunanina gara..."
"Subhanallahi" cewar likitan da sauri "Munzali wannan magana taka bata dace da dan musulmi ba. Ni ba malamim addini bane. Amma tabbas har yau ban bar gaban malamai ba. Na kuma godewa Allah da malumanmu na yanzu suka kasance masu ilimin boko wanda yake taimaka musu wurin warware matsalolin da suke tafe da zamani. Idan za ka iya gobe ka zo nan da la'asar. In sha Allah zan kai ka wurin Dr. Abdallah Saraki. Kawu ne kuma siriki a wurin abokina Dr. Huzaifa."
Tun bayan zaman nan da aka yi a gidan Abbati sati biyu da suka wuce, sai yau Munzali ya yi murmushi. Da ya tashi zai tafi likitan nasa ya ce su taho tare da Abbati da iyayensa.
"Hakan ne zai sa kowa ya sami gamsuwa akan amsar da zai baka"
Yana shiga mota ya kira Abbati. A lokacin shi kuma yana cikin ofishin Alh. Sadisu. Kiran na shiga ya dauka da sauri.
"Munzali lafiya dai ko?"
"Lafiya kalau. Kana gida ne?"
"Ina office din Alh. Sadisu ne. Yanzu muka dawo daga duba Abdul"
Munzali yaji kunya ta kama shi. Ba irin lallashi, fada da nasihar da Abbati bai yi masa ba amma kememe ya daina yarda ko zaman minti biyar suyi a wuri daya. Abbati ya yi fushi sosai saboda ya fuskanci akwai abin da yake boye masa. Shi kuma baya son fada saboda a take Abbatin zai soke masa zargin. Gashi zuciyarsa ta riga ta fara rawa akan maganganun iyayensa. Ya zama wajibi ya san me yake ciki.
"Kwatanta min wurin zan zo na same ka"
Minti ashirin ya kaishi. Suka zauna tare da Alh. Sadisu. A yau godiya mai tarin yawa ya sake yi musu sannan ya koma kan batun abubuwan da yaji a police station din.
"Kuna ganin da gaske zaku iya dainawa? Nayi bimcike ance da wahala rabuwa da wannan dabi'ar. Idan Abdul ya tashi a haka ban san yadda zan yi ba"
Munzali bai yi kasa a gwiwa ba ya fada masa shirinsu na zuwa asibiti a Italy. Rashin zuwa a duba lafiyarsu da kuma neman hanyar rabuwa da lalurar har abada ba karamin kalubale bane ga tubansu. Ita wannan dabi'a tana tattare da matsaloli da yawa ga lafiya. Ciki kuwa harda kasa jurewa rashin samun biyan bukata ta inda aka saba. Wannan abu ya kan fi karfin furtawar baki da yakinin zuci. Wani duk dauriyarsa idan abin ya ciwo shi sai ya biya bukatar yake jin dadi.
"Abdul yaro ne. Sake komawarsa ba abu bane mai wahala. Mafi a'ala shi ma ka kai shi asibiti" inji Abbati.
Godiya ya yi musu da zasu tafi da alkawarin tsaya musu a duk lokacin da suke da bukatar taimakonsa.
"Magana nake son muyi Abbati." Munzali ya ce da suka fito waje.
"Dama jikina ya bani tunda ka kira. Ka gaji da yajin ne kazo biko da kanka?"
Da sauri Munzali ya ce "don Allah ka bar amfani da kalmar yaji da biko kamar wasu mata da miji"
Abbati na jin haka ya gano inda matsalar take. Motarsa ya bude suka shiga ya tayar. Gida ya wuce kai tsaye. Yanzu babu kowa daga kuku sai Maigadi. Iya Kande bata dawo ba tun tafiyar Qibdiyya gida.
A waje suka zauna wurin wasu kujeru da 'yar rumfa. Munzali ya fadawa Abbati dukkanin damuwarsa.
"Na san za ka iya cewa ba komai bane. To amma hankalina ba zai taba kwanciya ba. Don Allah gobe ka zo muje wurin malamin."
Kamar uwa da d'a. Tausayin Munzali ya kama Abbati sosai. Don gudun kara masa damuwa sai bai yi masa yadda ya saba ba idan yana cikin yanayi mara dadi. Lokutan da yake yi masa fada ko nasiha da rarrashi har sai ya sauko.
"Allah Ya kaimu goben. Dama nima ina son yi maka magana akan mu nemi fatawa kan dukiyarmu. Goben sai muje masa da komai muji me zai ce."
Munzali ya mike zai shiga ciki. Abbati ya kai hannu zai taba kafadarsa don ya tsaya sai ya fasa.
"Munzali."
Juyowa ya yi fuskarsa duk ta rame kamar ya dade yana ciwo.
"Ina so ka sani cewa ko yaya makomar alakarmu ta kasance gobe ba zan taba barinka ba"
"Ko da ya tabbata wannan kazantar bata barni ba"
"Zama da kazanta fa sai ka so. A matsayin kani kuma amini na daukeka. Banda an riga an dasa maka wani irin tunani a zuciyarka da na fada maka matsayinka a wurina. Yanzu kuwa ina magana za ka iya tsoron kada nace gobe zan kawo sadaki"
Murmushi suka yi a tare sannan kowa ya nufi gidansa.
Washegari basu hadu da safe ba. Munzali ya tafi gida dauko su Asabe. Ya sami gidan a cike makil. Larai da su Fati sun zo dukkaninsu kwai da kwarkwata. Gaban Innayo ta zauna ta roki gafararta na rashin kyautawa da tasa 'ya'yanta yi mata. Ta karbi laifinta kamar yadda 'ya'yanta su ma suka karba. Aka yafi juna tare da alkawarin sabunta zumumci.
Hasiya ce kadai bai samu ba. Hakan ya yi masa dadi domin yana jin kunyarta saboda rashin samun sukunin zuwa duba Abbas. Uwani kuwa tana jin muryarsa ta fito ta tare shi a gefe. Mita ta soma yi masa na rashin kiranta da ya ce zai yi domin ta duba Qibdiyya. Hakuri zai bata sai ta kula da ramar da ya yi. Mantawa tayi da fadan ta koma tambayarsa damuwarsa.
"Na manta gidanmu ba irin da bane, da na sani ban zauna abubuwa suna ta damuna ba a cikin kwanakin nan" yace ba tare da wasa a fuskarsa ba.
"Komai mai wucewa ne Munzali. Tunda muka dinke da Innayo kaima kawai ka jira lokaci. Kafin ka farga zaka ga ya koma tarihi. Ko ka bayar dashi ko rike abinka a zuci"
Karfin gwiwa ya samu daga gareta wadda da ita ya yi amfani wajen jajircewa iyayensa suka bi shi.
Sheikh Dr. Abdallah Saraki ya saurari jawabin Munzali da Abbati da dukkan nutsuwar da ake bukata daga malami. Labarinsu gabadaya izina ce kuma babban darasi ga iyaye da su kansu 'ya'yan.
(Ni din ba Malamar addini bace. Daliba ce mai koyo har yanzu. Bakin gwargwado ina nazari da bincike kafin na kawo wani batu mai girma cikin labaraina. A nan ma na duba matsayar malamai na kuma hada da tawa fahimtar. Saboda haka idan mai karatu yaci karo da abin da ya sabawa nasa ilimin, kada a manta cewa wannan labari ne. Abin da ya shafi fatawa a nemi sahihancinsa a wajen maluma. Rabbi Yasa mu dace da khairi duniya da lahira. Amin)
Da Alh. Rabi'u ya ga zai fara magana, hankalinsa kacokan ya mika masa. Yana so yaji malamin ya wanke shi daga abin da Munzali ya ce, wato yana da hannu a cikin lalacewar rayuwarsa.
Dr. Abdallah ya fara jawabinsa da sallama tare da addu'ar bude taro ko wani zama da za a tattauna abu mai mahimmanci. Sannan ya karkare da yiwa fiyayyen halitta salati SAW.
"Da farko zan fara da yaba muku tare da kara muku karfin gwiwa. Duk wanda ya nufi Allah SWT da kyakkyawar zuciya, to ya sani cewa Allah ba zai tab'ar dashi ba. Saboda haka ku cigaba akan niyyarku. Ko a duniya ko a lahira sai kun yi mamakin falala da girman Mahaliccinmu. Zai baku fiye da rokonku. Ya yafe fiye da tubanku domin Shi din gagara misali ne wajen jink'ai da tausayi."
Ya gyara zama saboda su san cewa zancena gaba yana da mahimmanci.
"Munzali ina so kai da iyayenka ku sani cewa tsaftatacciyar soyayya ce tsakaninka da Abbati. Irin soyayyar da Allah SWT Yayi alkawarin inuwar Al'arshi rana gobe kiyama ga ma'abotanta. Wato mutum biyu masu kaunar juna domin Allah Shi kadai."
Munzali ya hau murmushi yayinda Abbati ya dinga kiran sunan Allah a iya a lebbensa.
"Malam baka ji inda ya ce yana son Abbati fiye da kowa ba? Ma'ana fa harda mu. Babu jin nauyi ko kadan yake nuna min cewa yaron nan ya fini a wurinsa." Cewar Alh. Rabi'u yana huci.
Dr. Abdallah ya ayyana a ransa cewa lallai Alh. Rabi'u akwai gagarumin gyara a lamarinsa.
"Aikin sab'o sakamako ne na raunin dan Adam. Shi kuma rauni ana gane shi ne daga zuciya. Idan aka haneta ga barin abin da take so sai ta ce ta kasa. Idan aka umarceta da abin da bata so nan ma ta nuna gazawarta. To da zarar mamallakinta ya biyewa ra'ayinta ba tare da dora shi a mizanin hankali, dabi'a da addini ba, dole nadama ta saukar masa watarana. Alh Rabi'u, ka yi godiya muddin rai ga Allah da Ya bawa yaran nan damar fin karfin zukatansu a lokaci irin wannan. Gurbacewar zamanin nan ta kai ta kawo. An kawata zina ana tallatawa mutane. Tserewa tarkonta wallahi sai wanda Allah Ya azurta da jarumar zuciya. Wadda tana so din kuma tana tsoron mummunar makoma. Zuciya ta ma'abota tsoron Allah da kwadayin rahamarSa."
Asabe ta dinga gyada kai tana yiwa Munzali da Abbati kallon tausayi. Alh. Rabi'u kuwa cikin kosawa ya ce,
"Nifa so nake naji inda aka halattawa baligin namiji kaunar kato kamarsa har ma kake ganin cewa hakan ba laifi bane. Addinin nan bakin gwargwado nima fa na san shi. Maluman zamanin nan banda son zuciya da kwadayin abin hannun masu neman fatawa basu iya komai ba. Sai ayi ta halatta haram don kada ran mai kudi ya baci"
Kunya sosai ta rufe Abbati da Munzali. Asabe ta dinga bawa Dr. Abdallah hakuri. Shi kuwa ko a jikinsa. Mutane irin wannan da wadanda ma suka fi shi nawa ya gani?
"Soyayya tana samuwa ne daga kyautatawa. Babu ruwanta da jini ko alaka. A inda aka samar da ita a nan take samun wurin zama. Ku duba hikimar Ubangijinmu a wurin zamantakewar rayuwa. Da farko Ya sanya soyayyar da a zukatan iyayensa tun yana ciki. Wannan ita ce ainihin sunnar rayuwa game da iyaye da 'ya'ya. Duk wanda Allah Ya bamu mai kyau ko akasinsa. Nagari ko shakiyi sai kaga muna son kayanmu. Har muna jin ciwon hukuncin da mukan yi musu idan sun yi laifi. Su kuma 'ya'ya ana haifarsu ne ba tare da ilimin komai ba. Tunda anyi zuciya da kaunar mai kyautata mata, fuskar da mutum ya nufeta da ita, itama za ta je da kwatankwacinta. Yaro baya sanin wace uwa a gareshi a farkon rayuwa. Shi dai kawai wannan mai kawar masa da yunwa da kula da damuwarsa ita ce mutum a wurinsa. Wannan dalilin yasa wadanda maraici ke riskarsu tun a zanin goyo suke tashi da kaunar marikansu indai an yi musu rikon amana."
Daga nan Alh. Rabi' u ya soma shan jinin jikinsa. Asabe kuma ta soma hawaye.
"Yaran nan sun hadu a lokacin kuruciya. A shekarun da ko iyaye suna kokarinsu sai sun kara sun dage sannan an hada da addu'a. Dalili kuwa shine wannan shekara shabiyu zuwa sama mataki ne na farkon balaga. Lokaci ne da yara suke fara sanin kawunansu. Munzali yana da zuciyar tausayi da jinkai. Amma ya tashi da kishirwa da yunwar kulawa. Wannan shi ma a tsarin halitta zaka ga wani yafi wani cikin yara son kulawa. Wasu yaran tun kuruciya suna son a dinga basu damar yin komai su kadai. Wani kuwa burinsa na gaba ya sanya shi a hanya kullum. Yana son ayi ta ririta shi. In kun duba Munzali da ya san ya taimakawa wani tun kuruciya tabbas shi mutum ne mai raunin zuciya. Duk wanda zai ja shi a jiki shi ne mutum mafi girman kima a idonsa. Ya zo ya hadu da Abbati. Wanda shi kuma bai kasance daga cikin butulun mutane masu manta alkhairi ba. A zamanin nan duk wanda ya kawar maka da yunwa babu ya shi. Kyautatawa junansu a lokacin da ido da sawun iyaye baya garesu shi ya janyo musu shakuwa. Babu ce ta hadasu ba arziki ba balle ace wani yana kwadayin abin hannun dan uwansa. Kune ku ka kora danku zuwa ga mai kaunarsa da zuciya daya. Misalin haka kan faru tsakanin iyaye mata da masu raino. Idan mace ta sakarwa mai raino ragamar komai na danta, watarana sai ta mika hannu ya noke kafada. In ta dauke shi ta karfi ya yi mata ihun da jama'a zasu iya yi mata kallon mai satar yara."
"Tabbas malam kayi gaskiya" Asabe ta furta tana kuka "sakacinmu ya janyo Munzali ya hada Abbati da miyagun mutane. Dole yake kukan cewa ya yi sanadin bata rayuwar Abbati."
"Don Allah ku daina zancen wani ya bata wani cikinmu. Kaddara ce irin wadda bawa bai isa ya kauce mata ba"
Munzali ya kalli Abbati ya yi murmushi. Dama ya san haka zai ce.
"Ni dai duk da haka ka yafe min"
"Nima ka yafe min"
Asabe ta ce "Allah Ya yafe mana baki daya" ta dubi Alh. Rabi'u "Alhaji ka dai ji abin da Malam ya fada. Duka abin da ya ce babu wanda bamu aikata ba. Mu karbi laifinmu kawai mu tuba shi ne maslaha. Wani borin kunya ba namu bane"
"Ke, bana son rashin kunya. Kin sa danki da bare sun kawo ni nan domin a ci min mutumci ne dama?" Ya tashi tsaye yana karkade riga yadda ya saba idan ransa ya baci "tunda bani da amfani a gareku da 'ya'yanku yau dinnan ba gobe ba zan sauwake muku. Kuma ku zuba ido ku gani idan ban auro yara sa'annin jikokina ba. Wadanda zasu karbi irin kulawar da nake baku hannu bibbiyu suna son barka"
Maza irin Alh. Rabi'u masu kafiya, taurin kai, yiwa addini raguwar fahimta da karan tsaye suna daga cikin babbar matsalar arewacin kasarmu. Suna yin ba daidai ba. Sun sani sarai, kuma in an gyara musu sun san kurakuransu. Amma saboda bahagon tunani basa yarda su karbi gyaran. Kuma a haka wani mai zuciya irin tasu zai basu 'ya su aura. Ukubar da za ta fuskanta da sunan aure ba matsalar mijin da uba bace.
"Ba ayi haka ba Alhaji. In zaman nan bai kawo gyara ba ina ganin bai kamata ya kara lalata lamura ba." Dr. Abdallah ya ce dashi. A ransa yana mai cigaba da nazarin hanyoyin karkato tunanin dattijon.
"Na gama zama. Ki sameni a gida idan kun gama"
Abbati ne ya hana shi fita "Alhaji ka zauna ka yi mana shaida akan kudirinmu na gaba. Malam mece ce makomar dukiyarmu a yanzu da muka tuba?"
"A shari'ance dukiya kala biyu ce. Halattacciya da haramtacciya. Tunda kokontonku yana ga son sanin ko dukiyarku ta haram ce to akan ta biyun zamu yi magana. Ita dukiyar haram an kasata biyu. Akwai ta haramci a dalilin abin mallakar mai cutarwa ne kamar giya, naman alade ko mushe. Da kuma wadda ta haramta a dalilin hanyar samuwarta da izini ko babu izinin mai ita. Misali dukiyar da aka sata ko ta bokanci, kwangilar kisan kai, caca, sayar da kayan maye, karuwanci da ribaa. Kun ga irin taku dukiyar ta fado cikin aji daya da karuwanci. To game da wannan nau'in dukiyar wadda ake samu da izinin mai ita amma sanadin samuwarta haram ne, dukkanin malaman mazhabobinmu wato Imam Hannafi, Imam Hanbali, Imam Malik da Imam Shafi'i sun tafi akan cewa wajibi ne a rabu da ita. Ko dai a mayar da ita ga mai ita ko ayi sadakarta ga mabukata idan babu halin mayarwa. Ibnul Qayyim Aljauzi ma yana cewa a bayar din shi ya fi. Domin a lokacin samunta wanda ya bayar ya amfana da abin da ya biya kudinsa ne duk da cewa abin haram ne. A wani kaulin, Imam Al-Ghazali ma ya ce sadaka, zakka ko Hajji basu wajaba akan wanda duka dukiyarsa ta kasance haramtacciya ba.
Duka maluman nan sun yi duba ne ga ayoyin Alqur'ani da Hadisan Annabi SAW wurin fitar da fatawar. Misali, akwai wani hadisi wanda Imam Bukhari, Muslim, Ibn Majah, Nasa'i, Abu Dawud da Tirmizi duka suka rawaito [an karbo daga Abi Mas'ud Uqbah bin Amr RA cewa Manzon Allah SAW ya haramta kudin cinikin kare, kudin karuwanci da kudin bokanci.] (Ownership of Unlawful Wealth from Islamic Legal Perspective. Badruddin HjIbrahim da Azizah Mohd, 2017)
Hakika ba zan gushe ba wurin yaba muku matuka. Ina kuma yi muku albishir da cewa dukkan wanda ya bar wani abu da yake so domin Allah, to ladan wannan aikin yana ga Allah (Annawawi hadisi na daya). Zaku kwashi rabonku na alkhairi a duniya ko lahira. Ku sani dai cewa wallahi baku yi asara ba."
Kallon juna suka yi suka gyada kai a tare. In sha Allahu ba za su bari son duniya ya rufe musu ido daga barin mummunan alkaba'in da suka jima suna aikatawa ba.
"Akaramakallah akwai wani batu guda daya da ya rage. Ka san wannan abin yana tattare da matsaloli da dama da suka shafi lafiya. Musamman ga wanda ya tasarma barinta. A haka dai bamu da wani ciwo cikin ciwukan da ake dauka ta wannan hanyar. To amma mu dan yi bincike ana samun abin da ya shafi kwakwalwa. Hanyoyin da ya kamata mu bi a likitance domin kauracewa sha'awar da ta kan taso mana saboda sabo. Rashin kulawa zai iya janyo mana rubewa ko fitar tsutsa..." kasa karasawa ya yi saboda takaicin halin da suke ciki.
Abbati ne ya cigaba da bayanin "mun biya miliyoyin kudi ga wani asibiti a Italy wanda suka kware wurin dakilar da sha'awar sake fadawa zunubin. Sannan duk wata lalura da ta shafi lafiya wadda da wuya mu tsallakewa samunta a nan gaba kadan zasu magance ta. Tambayarmu a nan shi ne zamu iya zuwa? Idan bamu je ba Allah kadai Ya san halin da zamu iya tsintar kawunanmu. Sannan bamu da halin sake samun kudin da zamu biya. Duk abin da muka mallaka yanzu hatta waya zamu rabu da ita saboda duka da kudin muka samu"
Iska Dr. Abdallah ya fesar daga bakinsa. Wannan tambaya akwai rudani a cikinta. Ya dubi matasan ya auna duka maganganun da suka yi. Ya tambayi nawa suka biya yaji kudin ba na kusa bane. Bayan nazari ya fada musu abin da yake ganin shi ne mafita.
"Ku je ku nemi lafiyar ku. Domin sai da ita ne kadai zaku iya barin wannan abu har abada. Idan nace ku zauna ban yi muku adalci ba. Bani da halin sama muku irin wannan kudi. Iyakar shawarar da zan baku shi ne ku kiyaye. Kada ku dauki kari akan abin da ku kw san lallai zai isheku iya zamanku a can."
(Wannan ba fatawa bace. Fahimtata ce ba fadin malami ba)
Ragowar bayanin da aka yi shi ne ya dan taba zuciyar Alh. Rabi'u. Ya auna da kwakwalwarsa ba son zuciya ba ya tabbatar duk a kokarin samun lahira Munzali yake wannan abu. Shi kuwa wane irin shaidan ne a kansa da zai sa ya cigaba da riko da mummunar akidar da har mahaifiyarsa ta rasu bata taba goyon bayansa a kai ba?
Bayan Wata Hudu
Sannu sannu bata hana zuwa, sai dai a dade ba a je ba. Abubuwa da yawa sun faru a cikin watannin nan ga jaruman labarinmu.
Mami Khadija ta koma hadadden gidan da Alh. Tahir ya mallaka mata ita da 'ya'yanta. Ta cigaba da aikinta cikin kwanciyar hankali. Iyayenta da Yakumbo sun yi fushi har sun sauko. Mardiyya bata yarda an barta ita kadai ba. Kamar yadda suma yaran basu kwashe duka kayansu daga wancan gidan ba. Musamman Sauda da Mardiyya da basa rabuwa. Kullum in basa wannan gidan suna wancan. Jiddo ta dade da tafiya. Gida ta kama mai kyau ta cigaba da shashancinta bisa zugar kawaye. Gidan ya zama dandalin fitinannun mata. Ba a dade ba kuwa suka cinye fiye da rabin kudin da Alh. Tahir ya bata. Tunda bata iya juyasu ba sai bushasha. A halin yanzu ta gamu da ciwon gonoriya. Kuraje manya manya masu dan karen kaikayi da kazamin ruwa sun firfito mata. Ga kudin asibiti ya soma gagararta.
Alh. Tahir ya auri Yumna domin biyayya ga umarnin Yakumbo. Da kuma rufin asirinsa akan abin da Mami Khadija ta fadawa 'ya'yanta. Ya daina bin mata kamar anyi ruwa an dauke. Rayuwarsa babu wani farinciki a ciki saboda rashin Mami da zubar girmansa a idon manyan 'ya'yansa. Mama Nasima ta rage rashin zaman gida saboda tsoron kada ita ma ayi waje da ita. Yumna kuwa babu wannan fadar da take tsammanin samu. Ga kudi ga komai amma mijin bashi da lokacin biye mwa shirmenta.
Lilu ya mayar da hankali akan karatu. Suhaib kafa ta warke ya koma bakin aikinsa. Ayaah tana nan a ransa. Suna yawan gaisawa a waya wadda bata wuce ya gida, jikin Abbas da jarabawarta (a tsarinsa sai ta gama jarabawa zai nemi soyayyarta wadda ya gama nutsewa a ciki). Farha ce ta koma abar tausayi a wurin Mami. A zahiri ta cigaba da gudanar da rayuwarta kamar da. A badini kuwa kewar Abbati tana neman wargaza tuninta. Kara son shi tayi bayan Mami ta fayyace musu komai kamar yadda Alh. Tahir ya fada mata. Ta dai sakaya yanayin haduwarsu da babansu. Sai ta ce wurin abokinsa yaje yaga Abbatin. Wayar duniya ta buga bata samunsa. Tunda tayi na sati ta hakura ta fawwalawa Allah.
A Kano gidan Innayo sai san barka. Kansu ya hadu 'ya'yan suna ta zumuncinsu. Asabe da Innayo ma kamar 'yan uwa. Maigidan ne dai sai a hankali. Yau fari gobe tsumma. Wata dabi'ar barinta yana da wuya. Tuni Zara ta koma gidanta bayan Hajiyan Fatakwal ta zo da kanta sun sasanta da Innayo. Aka yiwa Ummulkhairi taron sunan da ya shiga bakin 'yan unguwa. Da wuya a hadu ayi hira mai tsayi ba ayi zancensa ba. Uwani ma da kanta ta koma. Salihi dawowa ya yi gida kawai ya sameta a falo da Mubasshir suna hira. Yayi murna kwarai da irin canjin da aka sam
u a tattare da ita. Ya hadasu da Ummule ya musu nasihar zaman lafiyar da kowane magidanci yake yi. Har yanzu dai babu wani abu mara dadi da ya faru gashi har Ummule ta haihu. Uwani ce ta karbi haihuwar tayi komai babu ha'inci a gida. Saura wata daya suspension dinta ya kare. Sannan ba tare da sanin kowa ba sai mijinta ta dauki Zakiyya da Qibdiyya sun je asibiti. Duk wani abu da ya dace ayi Salihi ne ya dauki nauyin biyan kudin. Ita da 'yan uwanta duk sun karbi zancen da yabi bakin kowa na cewa karayar arziki ce ta sami su Munzali. Asabe ta gina zancen akan wanda Mami Khadija tace mata taji a wurin Alh. Tahir lokacin da ta kira tayi musu jaje.
Salima dai aure ya mutu murus. Ale Gambo ya yi rantsuwar idan bata koma ba cikin kayadadden lokacin da ya bata tana da damar sake aure domin babu shi babu ita. Innayo ta lamunce mata tayi abin da zuciyarta take so. Cikin farinciki don har ta murmure ta ce ta gama zama dashi. Kwanaki kadan da suka wuce ta gama iddarta.
Abbas ya warke ya koma gida. Sauki ya samu don ya fara magana kuma yana tafiya da kansa. Tsakanin su Honourable da Abdulkarim sai tarin godiya. Shi da Ummita soyayya suke yi mai ban sha'awa. Biki saura sati biyu. Ayaah ma ta gama NECO sauran WAEC wadda jarabawa biyu suka rage su kammala baki daya. Anti Hasiya ciki ya fito. Laulayi ya yi sauki sosai. Tana samun riritawa daga mijinta, mahaifiya, 'yan uwa da 'ya'ya. Haihuwa kawai ake jira. Karshen abin farinciki shine kulle Danliti da Shazali da Alh. Sadisu yasa aka yi. Duka malamai da masu gadin makarantar da sukw da hannu su ma an rufe su. Shi Shazali ma a kurkukun bai tsira ba domin kusan kullum sai an yi masa duka.
Tunda Baaba Mari take bata taba samun kwanciyar hankali dari bisa dari ba sai yanzu. Alkawarin Allah Ya cika. Bayan kowanne tsanani akwai sauki tafe. Damuwarta ta shekara da shekaru ta kau. Sauran 'ya'yanta dama basu da matsala irin wadda ta jima tana damunta akan Abbati. Yanzu da komai ya daidaita ta sami nutsuwa.
Mal. Sa'idu ya soke karatun Allah. Sauran 'ya'ya da jikoki duk yasa an dawo dasu gaban iyayensu. Ya kuma aurar da 'Yashshafa ga wani tsohon saurayinta. Deluwa kamar ta hadiyi zuciya. Tana ta mitar yaya zasu yi ida Sha'aib ya zo. Hanne ma ta gama idda har manema sun fara kawo caffa. Ta cigaba da rayuwarta sannan ta rike sirrin Abbati.
Wata biyu kenan Abbati da Munzali suna karbar treatment akan hanyoyin tsira daga komawa tsohuwar rayuwarsu. Kafin su taho duk wani abu da suka mallaka sun damka shi a hannun Dr. Abdallah Saraki. Zunzurutun kudi da kadarori. Sutura da takalma kadai ne basu bayar duka ba. Amma hatta zobe da agogo basu bari ba. Motocinsu sun sayar. Gidan ma a satin aka sami mai saya. Sauran abin da basu kammala ba suka bar masa amanar sayarwa. Cikin kankanin lokaci aka dinga gina rijiyoyin burtsatse a kauyukan da suke tsananin bukata. Aka biyawa marasa lafiya da yawa kudin asibiti. Kudi ya zaga inds ya kamata. Dr. Abdallah ya taimaka musu kwarai wurin sauke nauyin da yake wuyansu. Hankulansu kwance a inda suke. Wayoyin hannunsu ma shi ya saya musu kafin su tafi.
Bayan tafiyarsu Alh. Sadisu ya neme su a waya shiru. Sai ya tuntubi Alh. Tahir. Shi ma bai san inda suke ba. A wurin Mami Khadija ya sami numbar Baaba Mari. Takanas ya tafi Kano inda suka hadu shi da Alh. Sadisu suka kirata. Ta hadasu da Mal. Inuwa shi kuma ya faygace musu halin da ake ciki.
"Alhaji da zuciya daya nake kaunar yaran nan. Idan suka dawo kana ganin zasu yarda in saka su cikin siyasa? Ba wai 'yan banga ko makamancin haka ba. Ina so in daga su a idon duniya. Su fara da zama PA dina ko Secretary. Ta yadda duk inda nasa kafa muna tare. A hankali har a sansu wata rana idan muna raye in daga hannuwansu a zaben manyan mukamai" Alh. Sadisu ya ce da Alh. Tahir bayan sun koma gidan Alh. Sadisun.
"Nima nayi tunanin janyo su aikin kwangilata. Amma ina gudun kada su ki amincewa saboda yarana da suka nema a baya. Sannan bani da wani mutumci a tunani a idanunsu. Dama auren zai yiwu da naji dadi. Musamman na Farha." Shi ma Alh. Tahir ya fadi nasa kudirin. Jari zai basu mai tsoka da zai ishesu tsayuwa akan kafafunsu. Amma kuma Alh. Sadisu zai bawa "ina gudun kada su ki karba. Ko kuma su ga kamar nayi ne da wata manufa"
"Hakika haduwarka da yaran nan izina ce garemu baki daya Alh. Tahir. Duba ka gani yadda rayuwarka ta canja. Ina fada ba don izgilanci ba. Yadda ka rabu da harkar mata haka idanuna suka bude na rabu da duk wani abu na haramci a siyasata. Don gani nake kamar hakki ne ya kama Abdul. Kuma naga fa'ida domin na kara samun masoya. Kwarjinin da nake fata na kara yinsa ba tare da na bawa kowa tsoro saboda cin zali ba."
Garin Parioli wanda yake cikin babban birnin Italy wato Rome shi ne inda ake da babban masallacin kasar. Saboda girmansa zai iya daukar masallata dubu goma sha biyu a lokaci guda. A daya daga cikin wuraren alwalar maza Abbati da Munzali ne suke alwala. Sun cika burinsu na ziyartarsa kafin su bar kasar. Abbati sanye yake da shudin wando da shudiyar shet wadda ya dorawa jacket sea green. Munzali kuwa bakin wando ne da polo shet ruwan madara a jikinsa. Su biyun sun yi kumari sosai. Ashe duk yadda jikinsu yake wannan abu yana tsotsesu basu sani ba. Sai yanzu suka kara zama cikakkun maza masu cikar kamala. Kowanne ya ajiye gashi a fuska wanda ya kara musu haiba. Alwala suke Munzali yana ta rawar dari. Abbati da ya gama ya koma gefe yana yi masa dariya.
"Nace maka ka k'ara riga akan ta jikinka amma ka dage wai da alamun rana a waje. Yanzu kuma ka zo ka sani a gaba kana makyarkyata kamar wanda ya kulla abota da DJ"
Munzali ya ciko hannu da ruwa zai watsa masa ya kauce yana kara yi masa dariya. A hasale Munzali ya ce,
"Ka dai ji kunya. Wai a matsayin wa na kake amma ka kasa sadaukar min da rigar sanyi. Sai surutu kake min kamar ..."
Kunnensu Abbati ya kamo yana cewa "ban hanaka rashin kunya ba?"
Munzali ya karkace kai saboda zafi yana magiya "me yasa baka san wasa bane. Don Allah ka saki kada kayi min kunne daya"
Zungure masa kai Abbati ya yi sannan ya cire rigar ya mika masa.
"Minti talatin zata yi a jikinka ka bani"
Da farinciki Munzali ya karba ya saka suka shiga masallacin domin yin sallar azahar.
Da suka idar hotuna suka dinga dauka domin tarihi. Ba su suka tafi ba sai da suka yi sallar la'asar. Lokacin jacket din ta koma jikin Abbati. Kowa minti talatin din yake ya bawa dan uwansa. Suna ta atishawa. Abbati ya yi ta mita. Munzali yana tunzura shi da cewa don kada ya barshi da jinya ne ma fa yake karbar aron rigar sanyin. Da zasu tafi addu'a kowannensu ya yi. Kusan abu daya suke roko. Cigaba da samun rufin asiri akan abin da ya gabata na rayuwarsu. Samun sana'ar yi sai kuma kowa ya yiwa dan uwansa fatan samun abokiyar zama tagari ba tare da sanin dayan ba.
Ranar da zasu tafi a airport dukkaninsu dokin ganin Qibdiyya suke yi. Sabo da rigima kamar yara harda fadan waye zai fara daukarta.
"Bayan ma yau baka kira mana ita ba" Abbati ya harari Munzali.
Zama suka yi akan kujerunsu daga jikin juna a jirgi sannan Munzali ya ce "na fada maka kashe min murya Zakiyya take yi. Sai ta kusa cinye kudin da surutu. Kai kuma ka wani dage ba za ka dinga kiranta ba sai kace surukarka"
"Ka sani ko ayi kome?"
Seatbelt din da yake kokarin sakawa ya saki ba shiri ya kalli Abbati.
"Kome a ina? Ni nace maka ina son aure ne ko kuwa ina son Zakiyya?"
Abbati ya ce "ko daya. Aure dolenmu ne Munzali. Indai ba so kake iyaye su sake fara zargin ko mun koma ruwa ne. Ba don na san mun rabu kenan dasu Diamond girl dinka ba ai da ita zan ce ka aura. To amma kaga babu wadda ya dace ka zauna da ita kamar Zakiyya. Ita ce ta haifi Qibdiyya. Ita ta san me ya faru da ita. Ita ce kuma zata san hanyar hana maimaici."
"Shawara ce kake bani?"
"Eh"
"Kana ganin akwai alkhairi idan aka daina rabawa Qibdiyya hankali?"
"Tana bukatar tsayayyen gida da uwa da uba."
"To kai yaushe za ka yi auren?"
"Wa yake ta tawa? Da Hanne tana nan da yanzu bakina alaikum. Yanzu kuwa dole in nema can nesa da gida."
Zancen Farha ya so yi masa amma ya fasa saboda baya son yi masa fami.
"To Allah Ya kawo tagari. Amma ka daina zancen Hanne baiwar Allah. Ni na san ko kadan baka sonta. Shi yasa kana samun dama ka sallameta" cewar Munzali yana dariya.
Shi ma Abbatin dariya ya yi yace "Cutar juna muke kawai. Tana jin haushina ina jin nata."
Jirgin na shirin tashi suka kira Dr. Abdallah, Alh. Sadisu wanda yanzu yake yawan kiransu sannan kowa ya kira iyayensa. Munzali kadaran kadahan suka gaisa da babansa. A hakan ma sun sami cigaba ne a alakarsu saboda jajircewar Munzalin.
Tafiyar awa biyar da minti hudu ce ta kawosu Nnamdi Azikiwe International Airport Abuja. Suna fitowa daga ciki mota tazo ta daukesu kamar yadda Alh. Sadisu ya ce musu ya bada umarni da suka yi waya.
"Zai kai ku hotel. Gobe zan zo garin ganin party chairman. Sai mu juya jibi tare. Ina fatan hakan ba zai zama takura a gareku ba"
Wannan shi ne abin da ya fada musu a wayar. Cike da girmamawa suka yi masa godiya. Da zasu fita daga motar bayan sun isa hotel din kudi direban ya basu a envelop.
"Yallabai ya ce ku rike kafin ya iso"
Suka sake yin godiya sannan kamar lokacin tasowarsu duk da dare ya yi sai da suka kira iyayensu. Cikin daren suka tattauna yadda zasu yi idan Alhaji Sadisu ya zo musu da wani abu da zai iya bata musu rayuwa. A yanzu sun hankalta suna matukar tsoron shigewa masu kudi. Babu dangin Iya babu na Baba. Watakila wani abin ake nema a garesu.
Washegari sai bayan isha Alh. Sadisu ya iso. Tare suka je suka ci abinci. Dakinsa a hotel din yace su biyo shi. Gabansu ya fadi amma suka daure.
Yana zaune a kan kujera suna kasa a gefensa ya yi musu magana.
"Na san cewa zukatanku suna cike da tambayoyi da fargabar manufar janyoku da nayi a jiki. Dom Allah ku kwantar da hankalinku. Ko babu komai ceton rayuwar Abdul da ku ka yi ya isheni dalilin son saka musu da abin alkhairi. A dalilinku ya sami sauki har ina shirye shiryen tura shi kasa mai tsarki da biyu cikin iyayensa mata. Sai ya yi a kalla shekara guda yana karatun addini zai dawo gabana ya karasa sakandire. "
Murna suka taya shi yaji dadi kuwa
"Magana ta gaskiya labarinku ya tsaya min a zuciya. Ban taba ganin almara irin wannan ba. Giyar kudi bala'i ce. Musamman ga matasa irinku wadanda kuruciya take diba. Yaran yanzu zasu yi komai domin kudi. Sai gaku na hadu daku zahiri ba labari ba. Kun bude min ido da kusanto da tunanin lahira a dukkan lamurana. A takaice rayuwata duka na canjata kuma duka kune sila. Wannan yasa na daukarwa kaina alkawarin ba zan bari ku tagayyara ba. Rashin abin yi da rashin kudi a hannun wanda ya saba rikewa ba karamar jarabawa bace. Tsananin rabo da tsoron Allah ne kadai zai dakushe zukatanku daga tunanin hanyoyin samun kudi ko ta wace siga. Saboda haka idan kuna da ra'ayi ni Alh. Sadisu Nakano nayi muku alkawarin muddin ina raye da rai da lafiya, zan yi iya yina domin ganin kun zama wasu ababen misali da alkhairi a cikin al'ummarmu. Ina burin duniya ta amfana da alkhairin da nake da yakinin Allah Ya wanzar muku sakamakon mika wuya gareShi. Me ku ka ce?"
Basu ce komai ba sai kwalla. Ikon Allah akwai ban tsoro. Duka duka awanni nawa da suka wuce ne suka zauna suna tunanin yadda zasu yi da rayuwarsu yanzu? Sai gashi mafita tazo daga inda basu tsammani.
Alh. Sadisu ya yi murmushi "in dauki shirunku a matsayin amincewa?"
"Alhaji ko za ka bamu zuwa gobe domin mu shawarci iyayenmu"
"Ka cika babba Abbati. Dama gaggawa daga shaidan take. Ku yi shawara da duk wanda ya dace. Fatana Allah Yasa ku bani damar zame muku uwa da ubs a siyasance. Da yardar Allah ni daku babu mai yin nadama."
Dr. Abdallah suka fara kira. Ya ce idan sun shigo Kano gobe su zo su same shi a gida. Da makomar tattaunawarsu da shi zasu yiwa iyayensu bayani. Daga nan su nemi amincewarsu.
Direban da ya daukosu daga airport shi ne ya kuma zuwa daukarsu. Alh. Sadisu ya sanar dasu cewa zasu tsaya a Kaduna zai ga abokinsa kafin su wuce. Haka suka jera suna biye dashi a baya.
Suhaib, Farha, Lilu, Sauda da Mardiyya ne suka fito daga wani babban shopping mall wanda yake makwabtaka da ofishin Alh. Tahir. Mami Khadija ya kuma roka akan burinsa na daidaitawa da yaran. Tayi musu magana harma da fada akan lallai su cire abin da yake ransu su kyautatawa mahaifinsu.
"Shi kadai gareku. Ba zai yiwu don ya auri Yumna kowa ya dauki gaba dashi ba. Duk alkhairinsa gareku bai kyautu ku manta ba saboda wani abu guda daya da bai sabawa shari'a ba"
Fadan a gaban kannensu ne. Su manyan sun san me take nufi. Hakuri suka bata tace to tana so bishi office su nuna masa komai ya wuce. Da yake kullum cikin kokarin janyosu jiki yake suna yakicewa sai kowa yaji babu dadi. Shi ne Suhaib ya ce su fara zuwa kowa ya sayi gift guda daya su bashi.
Sauda da Mardiyya sai tsalle da murna. Ji suke kamar sun dade basu ga Abbansu ba. Kowa ya yi kewarsa. Harda Suhaib kuwa.
Abbati da Munzali a hadadden reception din office din suka zauna suna hira. Alh. Sadisu ya shiga wurin Alh. Tahir ba tare da sun san wurinwa ya zo ba. Yana ciki suna tattauna makomar rayuwar yaran. Niyarsu sai sun gama magana sannan Alh. Sadisu zai kirasu ciki domin su sami fahimta da Alh. Tahir. Yana so su dauke shi a matsayin makusancinsu.
Waya suke yi da Qibdiyya ta cikasu da surutu mai bude kofar ya hangameta. Basu dago sun kalli su waye suka shigo ba koda suka ji ma'aikatan dake wucewa suna ta yi musu maraba.
"Oga yana tare da bako." Wani masinja ya fada musu.
"Bari mu jira shi a nan" Suhaib ya nuna kujerun reception din.
Kafin su karasa duka su biyar din sun ga su waye a zaune. Farha ji tayi kamar zazzabi zai kama ta. Kujerar farko ta gabanta ta dafa yayinda Suhaib da Lilu suka karasa gabansu.
Earpiece ne a kunnen Abbati yana kallon video din Qibdiyya na zuwa sabuwar makaranta wanda tasa mamanta tura musu a lokacin. Munzali ne ya daga kai da yaji alamun ana tahowa gabansu. Mamakin dake fuskarsu Suhaib shi ne a tasa. Da hannu ya zunguri gefen hannun Abbati. Yana daga kai idanunsa a bangaren hagu suka sauka. Duniyar sai ta tsaya cak. Numfashinsa ya dinga fita da sauri da sauri da yayi tozali da Farha.
Jikinsa nauyi ya yi masa saboda bai san me zai ce mata ba. Akwai tarin tambayoyi da ma bayani da zata bukata wanda bashi dasu. Kwanciyar hankalinsa daya shi ne sanin cewa Alh. Tahir ya rufa musu asiri.
Yana can duniyar tunani da kallonta har Munzali suka gama gaisawa dasu Suhaib. Ya rike hannun Lilu yana cewa "ka gafarceni. Kunya ta hanani nemanka."
"Komai ya wuce. Naga message dinka tun lokacin" Lilu ya bashi amsa da fara'a.
Sauda ta turo Mardiyya gaba don su gaisa tana ta nokewa.
"Diamond girl da Hasanarta kuna lafiya? Ya kwana biyu?"
Sama sama suka amsa, hankulansu sun karkata ga Abbati da ya yi mutuwar zaune ga Farha tana takowa wurinsu a hankali. Har ta iso Abbati bai dauke idonsa daga gareta ba. Tana zuwa gefen Munzali taje ta tsaya tayi masa sallama.
"Don Allah ko za ka iya bani wuri in zauna kusa da dan uwanka?" Ta nuna inda yake zaune kusa da Abbati.
Idanu ya dan ware ya ce "na'am?"
Idanun Abbati basu bar kanta ba duk da taki juyowa.
"Hoto nake so a daukemu" ta furta a dake. Hannunta ne ma ya soma rawa wurin kokarin bude jaka domin ta dauko wayarta. Idan ta kama dan karfen budewar sai ta kasa juya shi yadda ya dace. Saboda dauriyarta ta kusa karewa.
"Bashi wannan" Abbati ya mika mata wayarsa ko earpiece din jiki bai cire ba.
Ta mika hannu ta karba kanta a kasa bata yarda sun sake hada ido ba. Lilu ta mikawa don hannunsa tuni ya yo gaba. Ta koma ta zauna a inda Munzali ya tashi.
"Ya Farha"
Ko da wasa bata yi yunkurin amsa kiran da ya yi mata iya jin kunnuwanta ba don ta san muryar ta bace. Daga kai tayi kawai aka yi dace shi ma ita din yake kallo. A haka Lilu ya daukesu hoton suna yiwa juna kallo mai cike da sakonni kala kala.
Ana dauka ta mika hannu ta karbo masa wayarsa. 'Yan uwanta da Munzali suna ta kallon ikon Allah. Numbarta ta soma sakawa sai gani tayi sunanta ya fito baro-baro a jikin screen din.
(Ya Farhata)
Kwalla mai zafi ya sauko mata kowa yana gani tasa hannu ta dauketa. Cikin whtsapp dinsa ta shiga ta bude sunanta ta tura hoton da suka dauka sannan ta mika masa. Yana karba ta haye sama.
Su Mardiyya suka bi bayanta da sauri. Office din Alh. Tahir taje. Ta bude da sallama ta fada kai tsaye. Yana ganinta ya tashi ta iso ta rungume shi sai kuka. Lilu ya rike baki a hankali ya ce "see love"
"Me ya sameta?" Alh Tahir ya tambayi su Suhaib hankalinsa a tashe.
Amsar ya gani da idonsa da isowar su Abbati kofar office din.
Alh. Sadisu ya saki murmushi "Munzali me ku ka yi mata?"
"Babu ruwana fa. Aikin Abbati ne."
Abbati yaji kamar yana kan k'aya a inda yake. Ta daina kukan amma ko fuskarta baya hangowa.
Alh. Tahir dadi kamar ya yi yaya. Farincikin da ya rasa na watanni ya samu da ganin yaransa. Gashi alamu sun nuna Farha da Abbati suna son juna har lokacin. Alfarma ya roki Alh. Sadisu akan su je gidansa kafin su wuce.
"Abba da alama mun kusa shan biki a gida" Sauda ta ce tana tafa hannuwa.
Aka yi dariya sannan kowa cikinsu ya mikawa Alh. Tahir kyautar da ya kawo masa. Bawan Allah sai yaji yana neman yin kuka. Sauda da Mardiyya ya rungume don kada a gane suka fita tare.
Idan Abbati da Munzali sun yi mamakin sabon gidan da suka gani na Alh. Tahir sam basu nuna ba. Mami Khadija tasa mai aikinta ta kawo musu lemo da ruwa sannan ta fito. Ita kanta taji dadin sake ganinsu Abbati.
"Shikenan sai kuka bace Munzali?"
"Dawowarsu kenan kasar tun bayan faruwar wannan abin" Alh. Tahir ya bata amsa.
Bayan tambayoyin yaushe gamo, Sauda da Mardiyya kadai aka sallama daga falon sannan Alh. Tahir ya sake nanata abin da ya fada a gabansu.
"Alh. Sadisu ne ya basu shawarar barin kasar har kura ta lafa. Dukiyar da aka basu kuma sun tattara komai sun mayar ga masu ita. Shi ne suka gujemu a tunaninsu zumunci zai kare tunda yanzu basu da komai."
Wannan abu ya kara tausayinsu ga su Mami Khadija.
"Bawa bai taba yi domin Allah Ya tabe ba. Ba kowa zai iya abin da kuka yi ba Abbati. Mara tsoron Allah ne kadai zai gujeku"
Dama tunda Alh. Tahir ya kirata a waya ya fada mata zai kawo nan shi ne tasa aka kara abinci.
Falon cikin gidan tasa Lilu ya shigo dasu Munzali domin su ci abinci. Alh. Tahir kuma ya ce zai tafi da Alh. Sadisu don gujewa kananun magana kamar yadda Mami ta ce. Harda direbobin zasu tafi. Idan suka gama zasu dawo su daukesu su wuce.
Mai aiki ce tayi jigilar kai kayan abincin falo. A ciki kuma ba babba ba yaro an hadu ana bawa Mami Khadija labarin hoton Farha da Abbati. Ita da tayi hoton ma sai yanzu kunya ta rufeta. Dariyar da Mami Khadija tayi ne yasa "Mami sharri ne fa. In akwai su nuna miki."
"Lallai ma Ya Farha. Bari naje na karbo wayarsa" inji Lilu uban gayya.
Suhaib ya janyo hannunsa "dawo gadanga abinci zasu ci"
Falon Mami Khadija ta tura mazan. Su Mardiyya ta saka su aikin hada fruitsalad sannan ta tsare Farha a daki.
"Na jima rabona da ganinki cikin yanayi irin wannan na zallar farinciki Farha." Kai Farha ta sunkuyar. Mami ta cigaba da cewa "bana so ki zura jiki da yawa. Tun haduwar farko na lura Abbati yana da hankali. Na tabbata faruwar wannan lamari ne ya koresu. Kin ji ance basu da komai yanzu. Sai dai nayi imani tunda Alh. Sadisu yake bibiyarsu he has a plan for them. Abbanku ma ya ce akwai abin da ya shirya. Tambayata a nan Farha za ki iya zama da Abbati sabanin yanda kike zatonsa?"
Idan tayi shiru tabbas za ta kwari kanta. Sannan bata kasance cikin masu zurfafawa da naci ba tare da neman zabin Allah ba.
"Ina addu'a sosai Mami. Sai gashi na ganshi a wurin da ban taba zato ba. Indai kin yarda dashi in sha Allah zan iya zama dashi.
Cikin farinciki Mami Khadija ta ce "Alhamdulillah. Abbanku ne ya ce na tambayeki kafin su dawo don yana so a yau a tsayar da magana guda."
Da gudu Farha ta bar dakin saboda kunya. Dakinta ta shiga tayi sallah ta sake gyara fuska. Tana gaban mudubi taji kira ya shigo. Haka kawai jikinta ya bata Abbati ne. Da ta duba kuwa sai taga bakuwar namba. Sake kira aka yi still taki dauka. Sai ma haushi da taji cewa yana da nambarta amma bai taba kira ba. Fitowa tayi daga dakin suka kusa karo da Lilu. A ranta tace dama ya saba rawar jiki idan ya gansu.
"Yauwa dama ke nake nema. Wai ya ce ki fito ku yi zance"
Bakin Lilu ta rufe da sauri ta waiga hanyar kitchen. Ai kuwa masu aikinsu biyu suna wurin kuma sun ji. Ga Sauda da Mardiyya. Sai suka hau yi mata dariyar shakiyanci.