BABI NA ASHIRIN DA HU
Uwa Uwa Ce Part 2 Complete Hausa Novel · about 29 min read
Iyalin Innayo sun tashi da alhinin aikin da aka yiwa Abbas. Kowa yana farinciki da jin cewa anyi aikin cikin nasara. To amma duk wanda ya ganshi bayan ya farfado a daren jiya cikin magagin ciwo sai ya tausaya masa. Hasiya tayi kuka tamkar ranta zai fita. Kiran sunayensu yake yana rokonsu da su cire masa ciwon da yake ji. Duka sai gwiwoyinsu suka yi sanyi.
Da wuri 'yan dakin Innayo suka gama shiri zasu tafi dubiya washegari. Hasiya ma man ta taho da sassafe saboda bata yarda ta bar asibitin ba. Da tursasawar Honourable ta taho gida yin wanka tunda nan din yafi kusa da asibitin akan gidansu. Uwani ta riga kowa gamawa. Ta sami wuri ta zauna ta kira Munzali. Muryarsa ta dakushe ba ma a jinsa sosai.
"Kira nayi inji jikin Qibdiyya da naka. Jiya ban wuni cikin kwanciyar hankali ba. Kuma Innayo ta ce akwai sirrin da bai dace mu ji ba ko don mutunta juna shi yasa bamu zo ba".
" 'Baram'barama" cewar Zara dake zaune a dakin tana shayar da diyarta "Hasiya taho ga Metron Uwani tana sakin baki"
"Da yake Hasiyan uwata ce ko? Wai me yasa ku ka raina ni ne?" Uwani ta hau ta da masifa ita kuwa sai dariya.
Tun bayan faruwar lamarin nan sai yau Munzali ya yi dariya. Dariya harda kyakyatawa. Da furucin Uwanin da abin da Zara ta ce duka ya ji. Ya kuma kara kaunar Innayo domin hakika ta karramasu da ta basu damar adana sirrinsu ga mahaifansu kadai. Sai da ya gama dariyar ya ce
"Jiki da sauki. In sha Allahu zan kawota wurinku yau ki dubata sai ki fada min abin da ya dace mu yi."
"Kai ni fa anyi suspending dina. Ranar da muka kai ka ma sai da na barar da girmana wurin roko.Ka kaita na kudi kawai a dubata a sirrance. Irin asibitinmu ai da baki ma za a dinga nuna ni idan na koma aiki. Dama kuma can ba kaunata suke yi ba balle an sami abin gorantawa."
Wata dariyar ya yi sannan ya tambayeta Innayo. A bakinta yaji batun aikin da aka yiwa Abbas. Shi ne ma ta bashi shawarar ko asibitin zai kai Qibdiyya tunda na kudi ne kuma ta yaba da likitocin. Da alkawarin zuwan nasu suka rabu. Ko tashi bata yi ba daga wurin Zara tana ta yi mata tsiya suka ji sallamar 'ya'yan Zaran.
Wayyo dadi! Zara ta kusa sakin jinjirarta saboda tsananin farinciki da taji Salima tana cewa "marhabin da su Maryam, maza ku shiga ciki ki ga kanwarku"
'Yan matan Zara su hudu suka shigo falon Innayo suna ta rab'e-rab'e a jikin bango. Yanayinsu ya nuna sam basu so shigowa ba. Duk da haka Salima ta cije ta dinga cewa
"Ku shiga mana"
Taku daya biyu a daddafe suka sake jan burki. Zara ta taso ta tsaya a gabansu da farincikinta. A zatonta wallahi suna ganinta zasu rufeta don murna. Sai taga sun sake jan tunga an rasa mai fara zuwa jikinta. Wani irin kallo ma suke yi mata mai kama da kyama. Kwala taji ta taho mata ta kuma kasa tareta. Innayo ta kawar da kanta gefe kawai don 'yarta ba karamin tausayi ta bata ba. Sai ta tuna mata da lokutan da ita Zaran take yi mata haka.
Cikin bacin rai Uwani ta daka musu tsawa bayan ta gama karantarsu da kanwarta. A ranta ta kissima irin bakincikin da zata ji idan nata 'ya'yan suka gwada yi mata haka. Ta sake jinjinawa hakurin Innayo.
"Kun wuce jikin uwarku taji duminku kun ji nata ko sai na taso muku?"
Jiki na rawa kuwa suka tafi wurinta amma a bayanta suka labe saboda tsawar Uwani ba don farincikin d'a ya ga mahaifiyarsa ba.
Karamar da yake babu hankali sai cewa tayi "hummm, Mummy ba kya wanka ko?"
Mai bi mata kuma ta ce "ba Aunty ta fada mana a gidansu Mummy ba..."
Mas'uda ce babbar, ta sa hannu ta buge bakin kanwarta tana mai cewa "ba ta ce kada mu fada ba?"
Ta dubi mamanta ta tabe baki "tare da Daddy muke. Ya ce ki zo." Ta kuma ce da kannenta "ku zo mu koma mota"
Salima ta hadiye nata fushin ta ce "ku zo ga kanwarku ku ganta. Sai mu ga da wa take kama"
Maryam har ta fara murna ta soma takawa wurinta sai ta fasa.
"Karaso mana"
"Aunty ta ce kada mu taba komai a gid..."
Mas'uda ta janyo hannunta tana gargadinta "ba ta hanaki surutu ba? Ni ku zo mu tafi kafin mu fara warin talauci"
"Ke???" Uwani ta yi musu tsawa a karo na biyu.
Zara sai kuka. Jikinta har rawa yake. Ta ruga gaban Innayo ta durkusa akan gwiwoyinta.
"Wane mutum Innayo? Waye zai buga kirji ya ce ya zama sanadin hawayen iyayensa kuma ya gama da duniya lafiya? Ki yafe min. Ki yafe daga kasan zuciyarki don girma da isa da tsarkin Mulkin Allah. Nayi miki rantsuwa idan yaran nan suka gwada min abin da nayi miki na sati guda zuciyata za ta buga. Kaicona. Ba zan iya addu'ar cewa Allah Yasa yarana su ji kaina kamar yadda nayi miki ba"
Hawaye Innayo take ita ma. Ta rike hannuwan Zara ta ce "na yafe muku ke da 'yan uwanki tun kafin ku roka. Babu komai a zuciyata game daku sai fatan alkhairi da albarkar rayuwar duniya da ta lahira."
Da hannu ta yafito 'ya'yan tasa suka zauna a gefen mahaifiyarsu. Da har sun fara matsawa don kada jikinsu ya gogi nata Uwani ta watsa musu kallon ku shiga hankalinku. Ana haka Hasiya ta fito daga bandaki daga ita sai daurin kirji. Fiye da rabin jikinta duk kumfa. Bala'i ya ciwota a bandakin na maganganun da suke tashi ta kasa tsayawa tayi wankan a nutse.
"Wace ce Anti?" Ta tambayesu rai a hade.
"Anti Laurat matar Daddynmu" Mas'uda ta bada amsa da sauri saboda tsoron tsawar Uwani. Fuuu....Hasiya tayi waje a fusace.
Innayo kuma ta dubi yaran ta nuna musu Zara "wace ce wannan a wurinku?"
Da yake rabonta da haihuwa bayan tayi ta ruguntsumin kwanika shekara biyar ne, babu wadda bata fahimci tambayar ba a cikinsu.
"Mummy ce" "Mummy" " suka amsa tare.
"Na san kuna zuwa Islamiyya. Mene ne hukuncin masu sabawa iyaye har su sanyasu kuka? Ina Allah zai saka shi?" Tayi tambayar ga manyan.
Maryam da Mas'uda sai da suka zaro idanu a tsorace sannan suka ce "wuta"
Uwani na jin haka hantar cikinta ta tsirga.
"Mu dai mun roki gafara kuma ance an yafe mana ko Zara?"
Zara ta murmusa don idanun Uwani sosai suka bayyana tsoratar da tayi. Innayo ma sai da tayi murmushi sannan ta ce da yaran idan ba wutar suke so ba kada su kara yin abin da zai bata mata rai.
A hankali suka shiga matsawa jikinta. A karo na biyu Salima ta sake nuna musu kanwarsu. Ba bata lokaci suka tafi. Tun suna dan ja baya har suka ware. Ganin haka Innayo ta ce da Zara sai ta tashi tsaye wurin dawo dasu turbar da ta dace. In ba haka ba nan gaba ba za ta iya tankawarasu ba. Kanta ta sake tunawa da yadda tayi ta ta rayuwar. Cikin rashin gajiyawa ta sake bawa Innayo hakuri.
A waje kuma Hasiya ce tsaye akan dakalin gidansu tana fuskantar Alh. Unaisu.
"Saboda ka kara aure sai ku koyawa yara tsanar mahaifiyarsu? Kaga irin kukan da Zara take yi kuwa? Hakkinta ba zai barku ba." ta kare da goge kwallar tausayin yayarta.
Alh. Unaisu ba shi da zabin da ya wuce yin murmushi bayan ta gama magana. Dalili kuwa shi ne tunawa da labaranta da ya kan ji daga Zara tun ma kafin su yi aure. Tana yawan fadin masifar Hasiya musamman idan aka taba nata. Bai taba zaton za ta damu da damuwar Zara ba duba da rashin jituwarsu. A nan dole ya godewa Hajiyan Fatakwal da ta zama sanadiyar komawar Zara gida.
"Dariya ma na baka?" Hasiya ta tambaye shi a hasale da taga yaki magana.
" Yi hakuri Hasiya kuma ina so ki saurareni game da Laurat da kin zuwana"
"Don kana auren yayata bani da hurumin son sanin dalilin karin aurenka. Rashin zuwa kuwa ni ban san me ya hadoku ba. Matsalata shi ne komai lalacewar uwa ko uba babu ruwan dayan wurin dasawa yaran kiyayyar dan uwansa."
Jajirtacciyar mace ce kuma kaifi daya babu karya ya ayyana a ransa. Sannan ya zauna ya yi mata bayannin duk abin da ya faru har zuwa yanzu. Domin kara horar da Zara da karya lagonta Hajiyan Fatakwal ta sanya shi mikawa Laurat uwargidansa yaran. Zaman Zara ne tuntuni yake karya matsayinta tunda ita bata haihu ba. Shi yasa da wannan damar da ta samu ta fito da makirci kala kala tana juya kan jama'ar gidan. 'Ya'yansa da masu aiki kamar su kwanta mata saboda yadda take kyautata musu. Suka daina ganin girman kowa sai yadda ta ce. Hajiyan Fatakwal na ganin haka ta ce zama bai ganta ba. Da alama da abubuwan da take yi ba wai da kisisina ta dogara ba kadai ba. Shi ne ta ce ya dawo da matarsa tunda yaran ko su yanzu basa gaisarwa sai ta amince.
Tare suka koma ciki. Zara na jin muryarsa gabanta ya fadi. Ta tashi da sauri za ta shige daki. Alh. Unaisu da nasa saurin ya tareta zai karbi jinjirar ta karkace gefe guda tare da rankwafawa da nufin hana shi.
"Bana son sakarci Zara."
Cewar Innayo tana kallon kafafunsa da ya shigo mata har nan da takalma.
Kafar ya bi da kallo shi ma ya koma da baya ya cire takalman. Da ya dawo ya zauna Zara taki mika masa 'yar ta kuma ki kallonsa. Sai ma yaran da ta cewa su shige dakin su jirata.
Shi ma din sai bai bi ta kanta ba. Innayo ya fara gaisarwa sannan ya dora da ban hakuri akan rashin waiwayo iyalinsa.
"Matsayin aurenku nake son sani kafin komai." Shi ne abin da ta ce da shi.
Sai da ta fada ya auna ya ga lallai fa dole ayi tunanin ya daina auren.
"Aure yana nan Innayo. Ku gafarceni akan abin da ya faru" nan ya fada mata abin da ya sanar da Hasiya a waje "zancen da nake muku Hajiya ta ce kada na koma gida ba tare da Zara ba. Ta karbi kuskurenta na hukunta ta ta wannan hanyar akan abubuwan da take ganin halayya ce da bata son jikokinta su koya. Gyara ba zai yiwu da banzatar da matata a cikin halin danyen jego ba."
"Mu kam tsakaninmu da Hajiyarka sai godiya domin kuwa dawowar Zara gida ta haifi d'a mai ido." Inji Uwani.
Innayo sai ta yi musu inkiya da su basu wuri tana mai cewa "gata nan ku sasanta amma babu inda zata tafi yanzu kamar wadda bata da gata" ta kalli fuskar Zara don ta gani shin amsarta ta sami karbuwa ko kuwa son bin miji zai sa ta nuna bacin rai.
Suna hada ido murmushi da alamun godiya ta yiwa mahaifiyarta. Innayo ta cigaba da cewa "yadda ka bamu hakurin wulakanta min rayuwar 'ya da wasa da lafiyarta, zan so Hajiyar taka ita ma ta zo. Zara ta jima tana bata min rai tabbas, amma duk inda bacin raina ya kai akan halayyarta ba zan taba zuba ido ina kallo ana cin zarafinta ba. 'Yar talakawa ce ka aura amma darajarta tafi karfin in baka ita haka sikau kamar kwanakin da suka gabata basu faru ba."
Kai ya gyada tare da cewa "to" da saurinsa. Zai tashi Innayo ta ce a bashi jaririyar.
Zara ta dora masa ita a cinya tana aika masa da mugun kallo. Innayo dauke kai tayi don ko yaya dama ya dace Zaran ta nuna bacin ranta ko don gujewa maimaici idan yaga kamar bata damu ba.
Kurawa yarinyar idanu ya yi har sai da yaji kwalla ta taru.
"Allah Ya baki hakurin jinkirin ganin wannan rana Ummulkhairi. Allah Ya rayaki Yasa ki yi koyi da halin mai sunanki"
Innayo, Uwani, Salima, Hasiya da maijego Zara duk sai da suka yi mamakin wannan irin karamci da ya yiwa Innayo. Wasu cikinsu ma irin Hasiya da Uwani basu zata ya san ainihin sunanta ba. Ita kuwa Zara murmushin da tayi mai hade da dariyar farinciki su kadai suka yi nuni da cewa ta gama yafewa mijinta.
Su Innayo fita suka yi aka basu wuri. Ya kara bata hakuri da nuna mata cewa shi da ita da Hajiyarsa duk sun yi kuskure a baya. Sannan ba a gyara barna da wata barnar.
"Ba jimawa zan yi ba. Ga wannan ki rike. Anjima zan dawo da duk wani abu da ya dace ace nayi tun farkon haihuwar. Na baki dama ki zabi ranar da kike so ayi taron sunanta a gidan nan. Sai anyi za ki koma."
"Na cancanci haka kuwa Daddyn Mas'uda? Laifukana ga mahaifiyata suna da tarin yawa." Ta furta cikin kuka.
"Ki dauki duk abin da zamu yi yanzu a matsayin lallashi da ban hakuri ga Innayo."
"Kai kuma me kayi banda guje min da kayi..?"
"A bar tada zancen gudun nan mana maman Khairi."
Ai kuwa alkunyar da ya kira sunan 'yar tasu dashi ya matukar burgeta har sai da ta sake yin murmushi.
"Nima da laifina sosai. Ban cika masoyi ba tunda ban damu da daidaita tunaninki akan mahaifiyarki ba."
Bayan tafiyarsa Hasiya ta kebe da Zara kafin su tafi asibiti. Maganganun da ta saba yi mata a baya ta kara maimaitawa. Sai dai wannan karon sun sami gurbi mai kyau sun zauna a zuciyar Zara.
"Miji abokin rayuwa ne kuma mahadin rayuwa. Duk wanda Allah Ya zaba miki a matsayin miji, ki sani cewa alakar ta zarce ke da shi da 'ya'yan da zaku haifa. Aure haduwar dangi shida ce. Naki na uwa da uba, nasa na uba da uba, sai kuma abokan arzikinki da nasa. Idan aka sami matsala tsakaninki da guda cikin nasa ko shi da naki, wajibi ne sai ya taba jindadin rayuwar auren mutum. Musamman abin da ya shafi dangi domin su kawaye ko abokan arziki ana iya canjasu. To amma fa duk wanda kika kawo a matsayin makusanci na jini ko na abota, dole ke ce za ki nunawa miji ko shi ya nuna miki mahimmancin dayan a gare shi. Wanda ka mutunta, abokin zamanka ya tayaka mutuntawa. Wanda ka tozarta ko ka wulakanta, wani sai ya fiki ci musu zarafi. Cikin mutanen da na ambata, UWA ita ce tubalin komai. Innayo uwa ce a gareki. Ina fata kin gane me nake nufi."
"Mun gane, kuma mungode."
Tare suka juya suka ga Uwani. Ta karaso ciki ta dubi Hasiya,
"Meye za ki bata shawara ita kadai banda ni?"
"Allah Ya huci zuciyar metiron" cewar Hasiya tana dariya.
"Kin raina ni. Amma muje zuwa. Ba ciki gareki ba? Allah Ya kaimu ranar fafe gora in..."
"Kada ma ki karasa..." Innayo ta shigo cikin dakin ita ma "idan ki ka ci zalin auta rama mata zanyi la'ada waje"
Dakin kaurewa ya yi da dariya kafin kuma su tashi cikin hanzari su cigaba da shirin zuwa asibiti.
Tunda Abbati ya san Asabe ta tafi wurin Munzali, Alh. Rabi'u na tafiya ya haye sama. Wanka yake son yi ya dan gasa jikinsa. Dukan da ya sha a police station da fadansu da Shazali sun sa jikinsa yin tsami. Su Baaba Mari ma dakunan da aka saukesu suka shiga. Fito da komai fili da aka yi yasa zukatansu sun sami sukuni. Abin da ya rage yanzu shi ne kawai a tabbatar da cewa sun nesanta daga wannan rayuwa har abada.
Takun Abbati bai sa Hanne yunkurin tashi ba har ya hawo. Gabansa sai da ya yi mummunar bugawa da ya ganta zaune da jajayen idanun da kuka ya rina. Cikin mutuwar jiki ya karasa hawa ya zo gabanta ya zauna shima jingine da bango. Muskutawa tayi ba tare da tunanin komai ba sai kyankyamin abin da taji game da shi.
Sanin cewa za ta iya tona masa asiri bai hana shi yin murmushi mai ciwo ba. Da kansa ya ja jiki ya sake bada tazara a tsakaninsu.
"Zamanki a nan ya nuna min cewa kin ji komai"
"Naji" ta bashi amsa a dakile.
"Ki saki ranki Hanne. Babu sauran bacin rai ko fargabar da ta rage min a dalilin wannan abu. Duk abin da za ki yi ba komai bane illa tishi akan wanda iyayena suka yi. Allah na sabawa, fargabar ko Ya karbi tubana ya danne duk wani abu mara dadi da ya sameni a sakamakon abin nan"
Gashi dai a hankali yake maganar, amma kalamansa ba karamin haushi suka bata ba. Ta tashi tsaye tana masifa.
"Kana nufin bacin raina ba shi da mahimmanci a wurinka? Kodayake dama ba tun yau na san cewa ba ka sona ba."
Tsareta ya yi da ido ya ce "tsakaninki da Allah ke kina so na?"
Bata zata zai yi mata irin wannan tambayar ba. Sai ta sami kanta da bude baki tana rufewa. Shi kuwa bai yi mamaki ba.
"Kada ki tuhumi zuciyata don nima ba zan tuhumi taki ba."
Kuka kawai ta fashe da shi. Ranta a jagule da bakinciki. Abubuwa da dama ne dankare a zuciyarta wadanda suka haddasa mata bacin rai.
Abbati sai ya mika mata hannu. A zatonsa za ta sake nuna kyama. Sai yaga ta miko nata. Ya rike hannunta suka sauka kasa. Baya son sake kwana da komai a ransa. Idan ta kama duk wani nauyi da hakki ya daidaita shi a yau to zai yi domin gobe ta zama goben dake tattare da budewar sabon shafi. Dakin da su Mal. Sa'idu suke ciki ya kwankwasa tare da yin sallama. Mal. Inuwa ne ya amsa don shi Mal. Sa'idu har ya soma gyangyadi. Suna ganinsu tare suka tashi zumbur kowa ya zauna.
"Abbati fada mata kayi?" Mal. Sa'idu ya tambaye shi yana hankalinsa a tashe "me ya kai ka? Wannan sirrin ai tsakaninka da Allah ne"
"Baba ku yi hakuri." Ya rufa mata asiri bai ce tsayuwa tayi ba bayan ance su tashi ita da Habu.
Zama suka yi akan kafet suna fuskantar gadon da su Mal. Inuwa suke kai a zaune. Abbati ya dubi Hanne ya nuna mata iyayensu,
"Tsayin shekarun da muka dauka a matsayin ma'aurata bisa biyayyar iyayenmu bana jin akwai wanda ya taba damuwa da son sanin ainihin bukata da burinki. Yau gashi kin san abu mafi muni a kaina. Ina so ki yiwa kanki adalci a gaban wanda ya hadamu auren nan ki fadi abin da yake ranki"
"Kamar yaya?" Ta tambaye shi saboda kanta ya kulle ta kasa fahimtarsa.
"A wane matsayi ki ka dauki aurena a da da yanzu?"
Sunkuyar da kai tayi. Mal. Inuwa ya ce kada ta cuci kanta suna sauraronta. Kasa magana tayi har lokacin. Sai da Mal. Sa'idu ya hada da jan idonsa mai sa ayi ko ba a so sannan ta magantu a tsorace.
"Na so auren nan duk da cewa hadamu aka yi. Nayi ta kokarin ganin cewa mun zauna kamar wadanda suka yi auren soyayya amma ban samu ba. Babu abin da na nema na rasa a gidan nan. Sai dai kai da nake zamanka duk kokarinka na sauke hakkina bai hanani jin kamar nesa muke da juna ba. Ra'ayi da tsarin rayuwarmu duka ba iri daya bane. Ko hira muke akan abu daya fuskar da muke kallonsa ta bambanta. Shi yasa tun ina kokarin ganin na shawo kan matsalar har na hakura."
"Ba laifinki bane. Laifin rayuwar da nake yi ce wadda ta hanani ganin aibun nawa tsarin. A ganina ci, sha da sutura da sauran 'yan abubuwan da nake yi sun isa su gamsar dake" cewar Abbati.
"To wai ni yanzu mene ne matsalar? Banda tashin hankalin jin mummunan sirrin mijinki kina son rabuwa da shi ne?"
Sunkuyar da kai tayi da sauri. Abbati ya roki Mal. Sa'idu da ya sassauta mata domin tana da damar nuna bacin ranta. Mal. Inuwa kuma ya ce ta fadi abin da take so shi kuma ya yi alkawarin tsaya mata.
"Babu farinciki a cikin gidan nan. Zaman hakuri kawai muke yi cikin wadata amma kowa rayuwarsa daban. Kudin shi ya rikeni har na kai yanzu. Amma tunda na san silar samuwarsa, wallahi gara min rayuwar kauye da nan. Don Allah Baba ina rokon arzikin komawa gaban iyayena. Zamanmu a lokacin da ban san sirrinsa ba ma bai yi min dadi ba balle yanzu?" Ta daga kai a hankali ta kalli Mal. Sa'idu "Baba ku gafarceni. Abin da naji ba zai taba fita daga zuciyata ba. Ba zan iya zama gida daya da Yaya Abbati da Munzali ba. Zuciyata cikin zargi za ta dawwama matsawar zan gansu a inuwa daya. Nayi imani kuma ba zai taba barin Munzali a kan kowacce mace ba."
Kimamin mintuna biyar ne suka wuce kafin Mal. Sa'idu ya ce "Abbati rubuta mata takardarta. Gobe in sha Allahu zamu tafi tare da ita."
Jikinsu duka su biyun ya yi matukar sanyi. Zaman sama da shekara goma duk rashin dadinsa dole mutum yaji wani iri lokacin rabuwa. Rayuwa suka yi babu duka babu zagi. Babu rashin kunya babu fitsara. Sai gidadancin Hanne da wauta da kuma rashin soyayyar Abbati. Amma su biyun babu wanda yake nufin dan uwansa da sharri. Matsalarsu guda ita ce rashin wannan karsashin da zai sa mutum ya shiga ranka ko babu soyayya. A takure suke da juna, kowa yana gwada sauke hakkin dan uwansa a iya damar da Allah Ya bashi. Irin wannan zaman musamman tunda babu yara sai mutum yaji kamar yana kurkuku. Arziki da wadata basa cike gurbin bukatar zuciya na son samun abokin rayuwar da ya dace da ita.
Abbati ya jima da sanin wannan shi ne kuma dalilinsa na amfani da wannan damar wurin sauwakewa Hanne maimakon neman ta zauna. Idan ya zauna da ita yanzu cutar sai tafi ta da. Domin yanzu aure baya gabansa. Akwai abu mai matukar mahimmanci da ya kamata su fara yi kafin suyi tunanin zama da mata.
"Baka ganin dazu kayi amfani da kausasan lafuza akan mahaifinka? A haka kake so ka ja ra'ayinsa wurin sauke akidar da yafi shekara arba'in da biyar a kai?"
Asabe ce tayi maganar tana zaune akan kujera yayinda Munzali ya takure a kasa. A haka tazo ta same shi dama.
"Ki gafarce ni amma ko kalmomi na basu dace ba ina ganin bai kamata ki ga laifina ba."
"Haka ne. Bamu koya muku ba sannan bamu kaiku inda za ku koya ba." Da bai ce komai ba sama da kada kansa gefe ta fahimci amsarta tayi daidai. Tambaya take so tayi masa amma tana tsoron kada su karke kamar yadda ya yi da mahaifinsa. Sai da taga yana shirin tashi ta ce,
"Munzali ka fada min tsakani da Allah wane irin so kake yiwa Abbati. Na san ya kyautata maka sosai. Amma anya saboda wannan dalilin kadai ya dace ka fadawa Alhaji maganganun da ka fada dazu?"
Taune lebensa ya yi gami da rufe jajayen idanunsa. Yana ganin idan bai yi da gaske ba da wuya ya wayi gari saboda zafin zuciya. Me yasa kowa yake yi masa wannan tambayar ne? Ko dai abin da suke zargi game dashi gaskiya ne? Shin mene ne ainihin abin da yake zuciyarsa?
"Zan bak
i amsa idan na nemota in sha Allahu."
"Munzali?"
"Kiyi hakuri Asabe."
Daga haka ya janyo filon guda daga kan kujera ya ajiye akan kafet ya kwanta a kai. Ko minti goma bai yi vmba bacci ya dauke shi.
Da gudu Sauda da Mardiyya suka fito tarbarsu Mami Khadija. Mardiyya harda kukan ganin kafar Suhaib.
"Yaya accident kayi ne?" Ta tsare shi da tambaya tana tattaba kafar.
"Buguwa ce Mardiyya"
Sauda ta ce "Da me?"
"Ku muje ciki" Farha ta katse su tana bin bayan Mami.
Tun tasowarsu daga Kano Mamin ta canja. Su duka sun san wani abu ya faru kuma yana da nasaba da babansu tunda suna tashi aka sanar dasu sun fita tare.
Alh. Tahir bai shigo gidan ba sai bayan la'asar. Yanayinsa ya nuna yana cikin tsananin tashin hankali. Bangarensa ya wuce yau bai tsaya jiran kowa fitowa ayi masa sannu da zuwa ba. Sauda da Mardiyya ne kadai ya san ko ya tsaya zasu iya fitowa.
Sam bai kula da Mama Nasima dake tsaye a bangaren dinning table da tray a hannu ba sai da tayi magana.
"Diya duk gajiyar ce ka shigo haka babu sallama?"
"Uhm" ya amsa kamar baya so yana mai cigaba da tafiya hanyar dakinsa.
"Ina ka wuce ne? Nayi zaton tare ku ka taso dasu."
Maimakon amsa sai ya tsura mata idanu yana kallonta daga sama har kasa. Ya tuna cin mutumcin da suka yiwa Mami shi da ita a dakinsu. Ya kuma tuna cewa ita ta bayar da shawarar a cirewa Mamin mahaifa kuma ya karba. Tirr da Allah wadai ya yiwa kansa. Tabbas yana daga cikin bambancin halittar namiji da mace son tarayya da mutum sama da daya. Hakan iko ne da ayar Ubangiji SWT. To amma shi wane irin mutum ne da bai san kawaici ba? Me zai sa ya yi masha'arsa a cikin gida da matarsa da 'ya'ya? Be tsaya nan ba duk gatan da Allah Ya yi musu na damar karin aure amma yake yawon bin mata kamar bunsuru.
"Lafiya kuwa Diya?"
Muryar Mama Nasima ce ta katse masa tunani. Ya yi firgigit ya dubeta sannan ya ce ta fita ta kirawo Mami Khadija da Jiddo.
"Kayi musu waya mana" ta ce tana dan murguda baki.
"Ki fita ki yi abin da na saka ki kafin na fito daga wanka"
Da wane bakin zai yiwa Mami magana shi da ita a waya?!
Cikin minti ashirin ya gama kimtsawa sannan matansa duk sun hallara a falon. Ya dauko takardu biyu wadanda ya rubuta ya mikawa Jiddo daya, Mami Khadija ma daya. Mama Nasima ta cika fam da ta tabbatar biyu ne.
"Ina tawa? Alhaji me yasa sam baka son yin adalci ne?"
Za ta kara magana Jiddo ta kwarma wani irin ihu wanda ya fita har wurin masu gadi. Ta tashi tana rawar jiki ta kawo masa takardar gabansa ta saketa a kasa.
"Wallahi, na rantse, wallahi babu inda zani." Ta nuna kanta "ni za ka saka? Ni din? Ko don kaga bana haihuwa?"
Da sauri Mama Nasima ta koma ta zauna nata jikin ita ma yana rawa. Ta kalli Mami Khadija a fakaice amma ta kawar da kai don bata ma son sanin me takardarta ta kunsa.
Sai da Jiddo ta gama hargaginta sannan Alh. Tahir ya zaro wayar Danliti daga aljihunsa.
"Ki godewa Allah baki haihu ba don da yau babu abin da zai hanani bawa danki wannan wayar" ya fada yana mika mata.
Hannu ta noke ta ce "wayar waye?"
"Na zata za ki fini sani. Amma tunda da alama kin manta bari na bawa yayarki Nasima ta karanta"
Kafin ya rufe bakinsa ta karbe wayar.
"Whatsapp za ki bude. Ki nemo sunan da aka sa Kaduna account"
Jikinta ya fara sanyi ta nemo sunan. Tana bude chat din gabanta ya yi mummunan faduwa. Ba hirar ta karanta ba. Hoton farko da idonta ya kai gareshi kirjinta ne tsirara da ta turawa Danliti.
"Na shiga uku na" ta furta a dimauce tana kallonsa "wallahi. Kaga ni. Ban san..."
"Adana zancenki don ba zai min amfani ba. Ina fata dai kin tuna waye"
Nan fa ake yinta. Samari nawa ne suka yi irin wannan hirar dasu? Ai ba za su kirgu ba. Don sun fi wadanda tayi mu'amalar zahiri dasu.
Mama Nasima dai jiki sai bari yake. Ta gama firgicewa don ko ba a fada ba ta fara harbo inda jirgin ya dosa. Dama ta jima tana zargin Jiddo tana yawo sai dai bata da shaida ko guda.
Jiddo tasowa tayi tazo gaban Alh. Tahir tana kuka ta fara cewa sharri ne ake son yi mata. Jikinta ne ta yarda amma bata san waye ya dauka har ya tura ba. Rainin wayon nata ya sosa masa zuciya kuwa. Yana son nuna mata bacin ransa sai ya tuna ba shi da wannan hurumin. A takaice ma ya san cewa sakamako ne ya soma girba tun yanzu. Ya ma godewa Allah da ba 'yar cikinsa bace da bai san inda zai tsoma ransa ba. Janye kafarsa ya yi daga rikon da tayi masa ya ce
"Idan kin gama ganin sakarcin naki bani wayar domin ana bukatar amfani da ita wurin gurfanar da Danliti makanike a kotu"
Kiris ya rage ta kwarma ihu lokacin da ta maimaita sunan da karfi.
"Danliti? Kotu? Wallahi ni dai babu ruwana ko me ya yi"
Tsaki kawai ya yi. Bai kara tanka mata ba ya dubi Mami Khadija da Mama Nasima.
"Khadija ga sakin da kika bukata kamar yadda na alkawarta miki zan yi. Alfarmar da na roka ta ki zauna kafin komai ya kammala na gidan kawai nake nema"
"In sha Allah" ta bashi amsa gami da mikewa.
"Me za ki ce da yaran?" Ya tambaya a raunane.
"Idan ka gama ka same mu a falona"
Ficewa tayi abinta don bata bukatar sanin ragowar me zai tattauna da sauran matansa.
Tana fita Mama Nasima ta cigaba da tsuma. Ita dai ta san indai ba mazan da ta sani kafin aurenta ba, babu wani da namiji da za a danganta ta dashi. Daga ranar da ta haifi Mardiyya ta san cewa gantali ba nata bane. Shi ne ta fada neman kudi ka'in da na'in. Laifinta guda a yanzu wanda shi ma tana ganin namiji zai iya saki dominsa. Shi yasa ba bata lokaci ta zamo daga kan kujera ta hau bashi hakuri.
"Me kika yi ke kuma?" Ya ce da dan murmushi. Ya dade da sanin tana yi. Yana dai kawar da kai ne saboda ganin damarsa.
"Kudi" ta ce tana zufa " idan kayi ajiya ina dauka Diya. Ina maka lalube a jaka da walet.
"Tashi ki tafi."
"Ni dai babu sakin ko? Idan ka sakeni ina zani?"
"Babu. Jeki Nasima. Ina bukatar hutu."
Ai ko bai ce ba dole ta fita. Bata son jimawa kada a fito da dalilin sallamarta. Ita da shi duka sun manta da Jiddo dake sharbar kuka. Sai da ta tafi ya ce da ita,
"Duk abin da na saka a bangarenki da wanda na baki ki tattara ki tafi dasu. Wannan shi ne abu na karshe da zan iya yi miki"
Su Farha ne zaune a kasa iyayensu akan kujera sun yi jigum. Alh. Tahir ya rasa me zai ce. Mami Khadija sai da ta tabbatar ba zai iya magana ba saboda tsoron halin za zasu shiga sannan tayi magana.
"A matsayinku na musulmai masu hankali na san kun san kaddara. Wannan kaddarar ita ce ta kawo mu wannan rana da aurena da mahaifinku ya kare."
Sauda da Mardiyya suka fashe da kuka. Su Suhaib da suka san dalili su ma babu wanda zuciyarsa bata kadu ba.
"Mami me yasa? Don Allah ku yi hakuri ku koma" cewar Mardiyya.
"Ya Suhaib ba za ka ce komai ba kana jin abin da take cewa" inji Sauda.
Alh. Tahir sai ya hau gumi. Tunaninsa abin da zai ce shi ne dalilin da ya san yaran zasu yi ta tambaya. Mami Khadija ce tayi belinsa da dabaibayin da ya zargowa kansa tun farko.
"Aure zai yi. Kun kuma san cewa ba haramun bane. Wacce zai aura din ce dai nayi rantsuwar ba zan taba zama da ita ba. Yakumbo kuma ta ce tunda har ya yi magana da iyayen yarinyar ita ma bata yarda a janye ba. Rabuwarmu ita kadai ce maslaha a yanzu."
"Wace ce?" Sauda da Mardiyya suka tambaya a tare.
Farha wadda amsar Mami ta farantawa rai domin bata son kannenta su san halin babansu ce ta bada amsa.
"Yumna ce. Kawata Yumna"
Sauda da Mardiyya ko kallon uban basu sake ba suka fice daga falon suna kuka. Mami Khadija ta dubi su Lilu da ko tari basu yi ba ta ce,
"Ina rokon arzikin ku rufawa mahaifinku asiri a wurin kannenku. Fushinsu yanzu na dan lokaci ne zai wuce sabanin idan suka san abubuwan da ku ka sani"
Daga nan ta fada musu zancen tashi da zasu yi bisa umarmin baban nasu. Basu ce masa komai ba suka tashi suka fice su ma.
"Na gode Khadija. Na gode kwarai da gaske. Ina fatan Allah Ya yi miki sakayya da mafificin alkhairi"
Dakinsa ya koma yana tunanin yadda zasu kwashe da iyayensu idan suka ji sakin. Ran kowa zai baci to amma wuyarta a kwana a tashi, komai me wucewa ne.
Gwaggo Jummai mahaifiyar Hanne kuma kanwa ga su Mal. Sa'idu ta shiga ta fito don a mayar da aurenta da Abbati abu yaci tura. Sati guda kenan da komawarta gida. Da ta kasa shawo kan 'yarta ta amince a gyara auren sai ta koma wurin yayyenta. Goyon bayan da taga sun bawa Hanne ranar da tazo gidan ya dagula mata lissafi. Abin har ya kaita ga fitowa tsakar gida tana yada magana.
"Anje an gama kullo munafunci an kaso auren 'yata."
Nan da nan tsakar gida da cika ta jama'ar gidan. Dama tun dawowarsu Baaba Mari da fitowar zancen mutuwar auren ake ta kus-kus a kowacce kusurwa. Don ma ita Gwaggo Jummai ba a gidan take ba. Da bakinciki sai ya kusa buga mata zuciya. Da Hanne ta koma gida tayi ta kokarin samun Abbati a waya sai dai bisa umarnin Mal. Sa'idu baya dauka. Yace masa ya bari su zasu yi mata bayani ba tare da tonon asirinsa ba. Suna gudun kada ya fadi wani abin da zai iya darsa mata zargi. Ko kuma ta tilasta masa mayar da auren saboda ganin girmanta. Sai taki zuwa gidan amsa kiran yayanta. Kullum tana faman kiran Abbati. Ga Hanne taki cewa komai. A takaice ma dai tafi walwala. Ga uban kayan abinci da kudi da ya bata. Zuciyarta fes tunda ta san aurensu kam ko a lahira bata muradinsa. Zaman wa da kanwar yafi mata dadi.
Cikin rumfarsa Mal. Sa'idu ya ce ta dawo su yi magana ta ki.
"Ba zan shigo a ninke ni baibai ba. Ni gabadaya zantukan da kuke yi kai da Yaya Inuwa basu da ma'ana. Ai na jima da sanin Deluwa tana son saka 'yarta a gidan Abbati. Kuna fakewa da rashin haihuwarta bayan ni na san kwadayi ne da hassada."
Deluwa tafa hannuwa tayi don dama itama a matse take da son sanin dalilin sakin. Da canjin da ta gani farat daya a wurin murdadden maigidanta.
"Bana fada da kanwar miji Jummai. Ba don haka ba da kin ji ta wuraren da 'yarki ta gaza har Abbati ya kasa zama da ita."
"Zan saba miki Deluwa" ya fada yana yi mata kallon da yasa ta rufe baki ba shiri. Kanwarsa ya kalla da 'yan ganin kwaf ya ce "rabuwar auren bata da alaka da kowa a gidan nan. Hasali ma 'Yashshafa da kike magana a kanta na riga nayi mata miji"
Deluwa ta san bashi da labarin Sha'aib (Suhaib) na Kaduna. Shi yasa cikinta ya wani murde da taji me yace. 'Ya'yan 'yan uwansa maza da suka rage babu wani mai dan romon da za a sha a cikinsu. Magana ta so yi ya ce tana kara bude baki a bakin aurenta. Haka ta cije lebe ta bar wurin cikin bacin rai.
Tafiyarta ke da wuya Hanne ta shigo. Bata san fitar Gwaggo Jummai ba sai da kaninta ya fada mata. Shi ne ta biyo sawu. Ta iske sun koma rumfar Mal. Sa'idu. Hakuri dai suke ta bata taki yarda saboda har yanzu bata ji kwakkwaran dalili ba.
A yau yawan kallon Hanne ya yi mata rana. Zama tayi ta dubi iyayenta. Mal. Inuwa duk ya fita hayyacinsa saboda tsoron kada karshe Mal. Sa'idu ya rasa zabin da ya wuce fada mata gaskiya. Baaba Mari kuwa dama ko uffan bata ce ba.
"Gwaggo ki yi hakuri. Sakin nan ni na nema. Munje asibiti likita ya ce akwai wani abu a jininmu wanda ya sa da matukar wuya mu haihu tare. Masu irin jininmu basa zama da juna. Shi yasa nake yawan bari. Ya so.mu cigaba da zama. Ni kuma gaskiya ina gudun cinye kuruciyata babu d'a ko daya"
Tunda ta bude baki sai yanzu wani abu da ya tokare wuyan Mal. Sa'idu ya sauka.
A take fuskar Gwaggo Jummai ta koma kalar tausayi. Ta girgiza kai tana cewa "ban san abin haka yake ba. Yaya ku gafarce ni. Tabbas lalura idan ta shafi haihuwa maslaha ake nema. Amma me yasa baki fada min ba?" Ta kare da tambayar Hanne.
Hanne bata yarda ta kwashe laifin karyarta ba. Idan bata gyara zancen ba zasu dade Gwaggonta tana mita. Nuna mata tayi basu dade da yin gwajin ba. Abbati yaki yarda ya saketa da ta nema. Shi ne ya kira iyaye don ayi sulhu. Su kuma suka goyi bayanta.
Gwaggo Jummai ta dinga bada hakuri. Da Baaba Mari ta tashi har daki ta bita tana ta rokon tayi hakuri akan kalaman da ta dinga yi. Ita kuwa da ta san cewa ita ce ta karu da abin da ya faru, da wuri ta nuna komai ya wuce. Bayan tafiyarta ta kira Abbati ta sanar dashi. Ta kuma jaddada masa ya yiwa Hanne godiya sannan ya cigaba da tuba.