← Book details Uwa Uwa Ce Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 19

Gabatarwa

Uwa Uwa Ce Part 2 Complete Hausa Novel · about 210 min read

Root Entry
WordDocument
0Table
Data
Normal
Default Paragraph Font
Table Normal
No List
UWA UWA CE
LITTAFI NA BIYU.
BATOOL MAMMAN.
UWA UWACE...21
GODIYA GA MASU KARATU.
Assalam alaikum wa rahmatullah wa barakatuhu.
Da farko ina godiya gareku masu kira da turo sako ta sms da whatsapp, wattpad da facebook. Nagode da shiruna bai sa kun manta dani ba. Allah Ya sakawa kowa da alkhairi. Na so sai na kammala labarin nan gaba daya zan sake post amma yawan tambaya da kuma rashin sanin me ya boyeni yasa ni fito da iya abin da ya samu.
Duk da haka ina mai baku hakuri domin daga wadannan shafukan zamu sake wani zangon kafin cigaba. Addu'arku nake roko don Allah. Akwai abu da ya tunkaroni, ina rokon Allah sa'a da salama a cikinsa. Allah Yasa a dace. Allah Ya biyawa kowa bukatunsu na alkhairi. Ina muku SonSo.
***
AYA MAFARIN IRGA.
A zuciye Uwani ta isa gabansu tana muzurai. Kafadar Ummule ta riko ta yadda dole sai da tasa ta juyo suka fuskanci juna. Bata cire hannun ba ta nunata da dayan.
"Ke bariki ma fa iyawa ce. Naga kuma kamar baki iya ba tunda kin yi shuka a idon makwarwa. Idan sadaka ko taimako ki ke nema me ya hanaki tambayata ina mace 'yar uwarki? Ai mu biyu ne a wurin. Don tsabar is.. sai ki bi namiji?"
Dama Ummule tana fita daga adaidaita sahun ta gane Uwani. Akwai hotunanta a wayar Salihi. Kafadarta ta gotar hannun Uwani ya koma lilo.
"Akan me zan nemi taimakonki bayan ga mijina..."
Uwani ta kan ji ana cewa kunne ya toshe na 'yan dakiku sakamakon jin zance mara dadi. Ashe gaske ne. Daina ji ko gane komai tayi na wani lokaci sai kalmar miji dake neman mazauni a cikin kwanyarta.
Karfin hali Salihi ya yi ya ce "Uwani. Ummule. Ku shiga ciki muyi magana bai dace ana jin muryoyinku a waje ba."
A haukace Uwani ta isa bakin karamin gate din nasu wanda mota bata shiga, shi yasa suke ajiye motocinsu a waje. Tare shi tayi da hannuwanta biyu ta soma masifa ido rufe.
"In ta shiga Allah Ya ..."
"Kar ki karasa tsinuwar nan. Gida dai nawa ne kuma ku duka matana ne" cewar Salihi yayinda ya matso zai cire hannuwan da tasa ta tare hanya. Duhu ya mamaye unguwar sai hasken kwayayen fitilu. Su ukun duka babu wanda ya yi sallar magariba saboda ta riskesu a titi. Ga isha an soma kira. Baya son makotansu masu zuwa masallaci wani ya ga abin da yake faruwa a kofar gidansa.
Kallon baka da hankali Uwani tayi masa kafin ta iya hada labbanta ta ce,
"Su waye matan naka? Aure kayi da gaske ban sani ba?"
"Na ce miki mu shiga ciki ko" ya ce yana dan daga murya.
Mubasshir na cikin tura kudi a aljihunsa yaji muryoyin iyayensa kamar suna fada. Da sauri sauri ya tattara komai ya mayar inda yake. Aljihunsa kam bandiran dubu dai-dai guda uku ya tura. Ga sarkar da ya dauka daya. Ya kuma rufe mata daki kamar ba a shiga ba ya fito.
"Wallahi kayi kadan Salihi. Amanata ka ci? To ka je ka tambayi malamai wannan auren bai dauro ba tunda ban sani ba balle na amince."
"Ki ce kawai idan ki ka tsine masa za ta kama shi." Cewar Ummule, haushin lallabawar da Salihi yake mata a wannan yanayin da suke cik na kara kamata.
"Kar ki yi min rashin kunya! Bani da kyau wallahi" Uwani ta ce a harzuke kamar za ta kai mata duka.
Akan ce idan babba ya yada girmansa sai yaro ya taka ya hau. Ummule ba mai takalar rigima bace amma bata ga dalilin ragawa haukan da Uwani take musu ba.
"Daidai nake dake. Gidan mijina ne saboda haka a matsa min na shiga."
"Wanda ya auroki ma bai isa ya shiga ba."
Shi dai hankalinsa ya gama tashi saboda bai iya hayaniya ba. Da kyar ya cire hannunta ya janyeta suka shigo tare da Ummule. Ita haushi da tausayi ya bata. Yadda yake bin Uwanin a hankali har ta soma tara musu mutane ya kular da ita. Banda tana gudun bacin ransa da tuni ta hankadeta kowa ya huta.
Suna shiga suka ci karo da Mubasshir wanda rashin gaskiya ya fito a fuskarsa baro baro. Amma da yake suna tare da damuwa su duka babu wanda ya kula. Muryar Uwani a sama tana ta zazzaga masifa ba ji ba gani.
"Kaga Salihi ka sallami yarinyar nan kafin na illata ta."
"Mu illata juna dai" cewar Ummule tana jijjiga kafa.
"Kaji ko? A gabanka take yi min rashin kunya."
Ihu ne kawai bai yi ba amma kansa ya dauki chaji sosai.
"Uwani ki saurareni kiji."
"Anki a saurareka din..."
Mubasahir sai yaji wani iri. Mahaifinsa take yiwa magana haka a gabansa.
"Mama don Allah kiyi shiru..."
Dama a wuya take sai kawai ta janyo shi ta kai masa duka a gefen fuska ko ta huce. Ransa kuwa ya baci . Ta kara yiwa kanta bakin fenti a idonsa.
"Munafukai daga kai har uban naka. Saboda baka damu dani ba ko a jikinka an kawo 'yar shila da sunan kishiyata."
Bata tsaya kallon fuskar dan nata da miji ba bayan ta kira su munafukai ta harari Ummule.
"Idan ma dadiro kuke yi ya miki ciki a waje ake son kawo min cikin gida ne to kunyi karya."
Dama kallo daya ta fahimci Ummule tana da ciki. Sai da ta gaji da masifar don kanta ta
nufi dakinta ta soma dauko akwatuna tana budewa. Saboda gudun bacin rana da cin amana irin ta da namiji take ta tanadi. Gininta a Zawaciki filasta kadai ya rage da fenti. An kawata gidan sosai ya dace da zamani ta kowace fuska. Gida ne dan madaidaici wanda ta kudurta niyar komawa idan bai yi musu gyara a nasu na yanzu ba. To ashe mai gabadaya ya tasarma yi. Ajiyayyun kudadenta za ta dauko ta bayar a gama komai cikin watan da ake ciki. Tana ganin idan ta tashi daga shi har kurar da ta kwaso matarsa za tafi karfinsu.
Akwatin da kudaden suke ta durkusa ta bude kudi suka ce daukarmu inda kika ajiye mu!
Bayan tafiyar Uwani da aka idar da sallar Magariba wasu makotansu Innayo suka shigo. Zama na mutumci ne tsakaninsu shi yasa suka shigo tambayar ayyukan da take so su tayata na sunan gobe. Kafin ma ta fada musu babu taro suka fahimci halin da Zara take ciki. Sun tausaya mata sosai kuwa. Da yake Innayo ba mai yawan magana bace bata taba zaman sukar 'ya'yan nata ba. Sai dai wanda ya gani da idonsa ya fahimci irin zaman da suke yi. 'Yar hira suka taba yayinda su Hasiya suka gama kimtsa komai suna shirin tafiya.
Innayo ta fito raka bakinta kenan adaidaita sahun da ya dauko 'yan sakon gidan Salima ya tsaya a kofar gidan. Ihsan da kuka ta fito ta fada jikinta. Gabanta ya yi mummunan faduwa. Dago Ihsan din tayi daga jikinta hankali a tashe.
"Ina Salima? Me ya kawo ki da magaribar nan? Kukan me kike yi?"
Ihsan ta kasa magana sai shesshekar kuka. A tsorace take ko mutuwar gaske mahaifiyarta tayi.
Daya daga cikin 'yan rakiyar ne ya yi mata bayani. Kuka ne ya kwace mata, nan da nan idanunta suka dinga zubar da kwalla. Bata ga ranar hutu akan lamuran 'ya'yanta ba. Kuma tana tsammanin wannan ranar ba za ta taba zuwa ba. Daga ranar da mace ta fara amsa sunan uwa to har abada sunanta kenan. Da damuwar Zara ta wuni, bakincikin Uwani ga kuma tararrabin halin da Salima take ciki ya risketa a farkon dare. A yadda ta fito rakiyar nan haka ta kutsa kai cikin adaidaita sahun da ya kawosu ko cikin gidan bata koma ba. Silifas ne a kafafunta sai hijabin da tayi sallah wanda da shi makotan suka risketa. Hannun Ihsan kawai ta rike tana karanto addu'a a zuci suka koma cikin adaidaitan.
Su Hasiya sai ganin wadanda Innayo ta fita rakawa sun dawo su kadai suka yi. Kusan a tare suke rige rigen fada musu abin da suka ji da gani. Maimuna har ta soma kuka Hasiya ta tabata. Sai da matan suka fita ta sanar da ita yadda suka yi dazu.
"Duk da haka Hasiya idan kuma na gaske ne fa. Ni dai ki zo muje."
"Ban gane wannan sabon shishigi da ku ka soma yiwa matar nan ba ke da Munzali."
Ummakati shiru tayi ta dafe kanta da hannu daya kamar mai ciwon kai tana sauraren Asabe. Tun shigowarta dakin take ta yi mata fadan zuwan da tayi da magariba kamar dole. Sannan ana karo karon kudi ita ma ta dauka ta bayar ko shawara da ita bata yi ba.
"Tunda kin bawa banza ajiyata ai gara ki tashi ki tafi"
Asabe ta furta cikin fushi. Bata ga dalilin wannan binbini da Innayo ta fara yiwa yaranta ba. Ta dade da sanin darajar daukar ciki da haihuwa take ci a wurin Munzali amma bata gabansa. Ummakatin da take mace kuma cikin rufin asiri ita kuma bakar rowa gareta a nata tunanin. Amma don neman suna ta dauki kudi ta bawa Innayo.
Gatse ne ko shagube, kalaman ba suyiwa Ummakati dadi ba. Tayi bayanin har ta gaji amma Asabe taki yarda. Surukarta ta ninka Asabe a komai ma. Ga rigima ga fitina. Dan nata ma tsoronta yake ji. Kuma a haka kiris take jira ta saka shi sakin Ummakatin saboda wai gidan da ta fito bai yi mata ba. Daga Alh. Rabi'u har Asabe babu mai daraja a idonta.
"Ki yi hakuri."
Tsaki Asabe ta ja tana mai cigaba da sakin maganganu.
"Bani abin da kika kawo min ki tashi ki tafi kafin babanku ya san kin zo don cewa zai yi sai mun raba. Ko yana ina lokacin da nake fadi tashin gina ku ban sani ba."
"Hmmm" Ummakati ta furta a hankali hannunta a jikin zip din jakarta. Dubu biyar din da ta lalube aljihun mijinta ta dauko ta mika mata. Idan bata bayar ba ta san watan kwasar bakincikinta ne zai tsaya. Har gida za ta dinga zuwa tana zubar da mutumci a gaban jikoki da babansu. Ba za ta yarda cewa Asabe ta manta da yadda suka tashi babu kulawarta ba. Banda tsarewa ta Allah da ta dade da shiga duniya kamar kawarta da suka yi 'yammatanci tare.
A hanyarta ta fita ne ta tsaya yiwa su Innayo sallama. Nan ta ji abin da ke faruwa a bakin Maimuna. Ta ce su taso su tafi tare. Ayaah kawai aka bari a dakin ta kula da Zara da jinjirarta.
Asabe da ta san ba sauraronta Ummakati za ta yi ba ko ta ce kada ta kaisu sai cewa tayi,
"Yau dai ranar ta Innayo ce. Ana ta ganin bacin rai akan 'ya'yan da ake cika mana baki a kansu. An gama gulmata akan tarbiyar 'ya'ya sai gashi sune da arzikin da ake ci. Munzali ya sakar muku bakin aljihu yanzu gashi motar Ummakati za ku shiga. Duk wani asiri kuma da surkullen mutum zai yi ya gama ne. Kurkuwarmu kurrrr....." ta bisu har soro tana fada.
Dama can ba ayi musu tarbiyar mayar mata da magana ba ballantana kuma yanzu da 'yarta take wajen. Hasiya da Maimuna sai suka kama bakunansu. Murja da Ummi su ma basu tanka ba. Yaran Maimuna kuwa basa wurin. Su aka tura shigo da adaidaita sahu kafin shigar Ummakati dakin.
A zaune suka sami Salima da suka isa gidan. Fuskarta a kumbure ta sha kuka. Mata kuwa harda wasu mazan sun cika 'yar tsakar gidan babu masaka tsinke. Kowa bayanin abin da ya sani yake yiwa Innayo.
"Mama ku ma kun yi sakaci tunda abu ne na shekara da shekaru. Ba don tana da tsahon rai ba ma da tuni labari ya dade da shan bamban."
Matar da tayi maganar Innayo ta duba ta jinjina kai. Tabbas da laifinta. Duk da Salima bata fada ba amma ta jima tana hasashen hakan saboda irin ciwukan da take gani a jikinta. Karairayin Saliman na kare Ale Gambo dai ta zabi karba don ta kwantarwa da kanta hankali. Damuwar 'ya'yan sai tayi mata yawa idan kowacce cikinsu bata da sukuni.
"Ina Gambon yake?"
Nan da nan aka shigo dashi a daddaure kamar huhun goro. Bata kula cewa ta wuto shi a waje ba inda samarin layin suka yi cincirindo. Motar 'yan sanda suke jira azo a tafi dashi.
Yana ganin Innayo da Salima a zaune ya fara kici-kicin son a kwance shi.
"Dama na fada! Sharri suke son kulla min ita da 'yan uwanta. Banda haka ai ba yau na fara dukanta ba amma suna tafiya ta zube min a kasa bayan ko rabin dukan da na saba ban mata ba?"
"La ilaha Illallahu..."
Mata suka hau sallallami don ga dukkan alamu bai san asirinsa yake tonawa ba.
"Kin ji yana fada da bakinsa ko Innayo? Wallahi na gama zama da shi ko kotu zamu shiga sai dai aje"
Cewar Salima cike da kwarin gwiwa ganin kowa ita yake karewa.
Don masifa Ale Gambo ji yayi kamar ya kwance daurin yaje ya mareta. Shi fa a tunaninsa bata isa ta taba ketare zancensa ba balle ta kaisu ga sa'insa.
"Ki bar ganin idanun mutane wallahi sai na tattakaki na taka banza idan suka tafi. Ni dake aure yanzu aka fara."
Hasiya da Maimuna harma da Ummakati sun so mayar masa da martani amma fafur Innayo ta hanasu magana. Yaran kawai ta cewa su shiga daki su dauko kayan sawarsu. Washe gari sai a dawo a kwashe kayan gidan.
Hankalin Ale Gambo sai lokacin ya tashi da yaga sun fara fita. Mutane irinsa masu mulkin mallaka ga wadanda suka fi karfi basu fiye son a gudu a barsu ba. Duk wannan power din da yake takama da ita dama na samun wuri ne a jikin Salima. Yau da tayi bore sai yake jin yafi kowa kaskanci. Kiran sunanta ya dinga yi da karfi da kalaman tsoratarwa akan irin hukuncin da zaiyi mata idan ta dawo.
Babu wanda ya waiwaye shi har 'ya'yansa. Innayo ce kadai ta dakata sai da iyalinta suka fice sannan ta dawo inda yake tsaye an daure masa hannuwa ta wanka masa wani irin gigitaccen mari. Kamar an dauke wuta haka mazan da suka yi saura a wajen suka dauke numfashi. Shi kuwa hantar cikinsa sai da ta kada domin bai taba zaton za ta iya yi masa wani abu sama da mugun kallo ba.
"Idan takamarka wanda ya baka aurenta bai san darajarta ba shi yasa kaima kake takawa to kayi karya. Muddin ina numfashi da yardar Allah ka gama taba lafiyar Salima. Shari'a kuma akan hakkinta da ka dade kana dauka ko zamu shekara anayi in Allah Ya so ba za mu karaya ba."
Juyawa tayi ta fita ran ta yana kuna. A bakin kofa suka yi kicibis da 'yan sandan da aka kira. Haka suka bi bayansu domin sun ce dole Salima taje ta bada statement kafin su daure shi.
Daki guda Abbati ya zage da kansa yana gyarawa Baaba Mari. Gidansa kato ne. Akwai rashin adalci idan aka ce matar gidan kullum sai ta bi dakuna da bandaki ta gyara. Shi yasa ya sa rai da ganin kura kadai ta rashin amfani. Shi ma kuma ko don kada kaya su lalace a kalla ko sau daya a sati ne ya kamata ace an share. Sai ya sha mugun mamaki. Datti dakal-dakal ya tarar da kura harda yana. Basu fiye bakin kwana ba saboda kishinta duk da masu zuwan duka 'yan uwansu ne. Bandakin kuwa harda kwari suna yawo wasu kuma sun mutu. Bawan Allah bai hango laifin kowa ba sai nasa. Da bai salwantar da rayuwarsa wurin yawo ba kila da yafi kula da lamuran gidansa. Yanzu kuwa ko sannu bai samu ba daga Hanne tayi hayewarta sama.
'Yashshafa ma duk shirmenta sai da taga rashin dacewar haka. Dukkaninsu sun gaji musamman Hannen da tayi jeka ka dawo a rana daya. To amma har ace ta manta mijinta a ranar aka sallamo shi daga asibiti? Akalla ko da ba yi za ta yi ba ai ta nuna masa cewa tana da hankali ta hanyar cewa ya bata tsintsiyar ta share. A yadda ta fahimti Abbati ta san da kansa zai ce taje ta huta. Jinjina kai tayi ta tashi daga kan doguwar kujerar da ta dan kwanta tabi bayansa bayan ya wuce da tsumman goge-goge.
"Ina zaki kuma?" Deluwa ta tambayeta da sauri.
"Karbar gyaran dakin zan yi."
"Dawo ki zauna ai ba sanin darajarki ya yi ba. Na gano miki miji dan gidan arziki ba taka haye irin na wasu ba."
Ta furta tana kai dubanta ga Baaba Mari wadda maganar ta yiwa dirar mikiya. Ko a farcenta don Deluwa ta hana 'yarta taya Abbati gyaran daki. Abin da ya tsaya mata bai wuce kiransa wanda ya yiwa arziki taka haye ba. Kenan ba ita kadai sauri da habbakar arzikinsa yake yiwa kai kawo a kirji ba? Kamar Deluwa taji tunaninta ta bata amsa tana faman tabe baki.
"Kar fa kiji haushin maganata Mari kin san ba karya nayi ba. Almajiri da tamfatsetsen gida irin wannan akwai ayar tambaya. Anata cewa yana kasuwanci gashi har rana irin ta yau bamu taba ganin samfurin hajar tasu ba."
Baaba Mari bata iya cewa uffan ba har Habi ta shigo daga bangaren Munzali inda aka yi musu masauki. Daki ya basu a cewarsa bai yarda su dawo tare a barshi a nasa gidan shi kadai ba. Iya Kande ba zama take sosai ba indai Qibdiyya bata nan.
Habi ce ta karbi gyaran dakin a wurin Abbati shi kuma ya hau sama. Deluwa ma da 'Yashshafa suka shige dakin da aka basu suna jiran kuku ya gama girki.
Tunani, damuwa da zancen zuci aka bar Baaba Mari tana yi akan tarin dukiyar Abbati. Kasantuwarsa dan fari ba shi ne ya sanya soyayyarsa tafi ta 'yan uwansa a zuciyarta ba. Saukin kansa wanda mutane musamman na gidan suke amfani dashi wurin cusguna masa tun kuruciya ne. Tunda aka gane lagonsa ake saka shi kuka. Tun tana kawaici har ta koma musayar yawo da duk wanda zai taba shi saboda bashi da baki. Wannan saukin kan yasa ta guji ya tafi almajiranci. In an barta ma za ta ce wannan halin zai janyo masa wahalar rayuwa fiye da a gabanta. Sai gashi abin mamaki maimakon ci baya sai ya yi gaba. A gaban ma ya yiwa da yawa fintinkau. Wata irin zabura tayi ta mike lokacin da taji takunsa yana saukowa daga sama. Haka ta kura masa idanu tana kallonsa cike da firgici. Tsoron yarda da hasashenta take yi. A cikin zuciyarta take addu'a kamar haka.
"Ya Allah Kasa ba sata ko fashi yaron nan yake yi ba."
BIYU IDANUN...
Su uku ne zaune a dakin Alh. Rabi'u. Shi, Innayo da Asabe. Tray din abinci ne a gabansa yana ta kwasar girki yana gumi. Hannun malum-malum dinsa yasa ya goge shi bayan gama ya janyo tsintsiyar kwakwa a gefen gadonsa. Dan tsinke ya karyo ya danna a baki yana sakato naman da ya makale yana tofarwa.
Magana ya kirasu suyi wadda gabadaya akan 'ya'yan Innayo ne. Shi yasa taji haushin kiran Asabe da ya yi dakin nasa. Ta san ya yi ne domin neman fada a wurin Munzali tunda dan Asabe ne. Duk tsiya idan ya kyautata mata ta hanyar nuna mata gazawar Innayo za ta yiwa Munzali magana akan bukatunsa. Ya kula yanzu bakin gwargwado Munzali yana dan yi mata magana da tattausan lafazi.
Hirar arzikin Munzalin ya dauko suke ta yi da Asabe har sai da Innayo ta magantu.
"Zan koma idan kun gama tadin ayi min magana."
Mikewa tayi abinta za ta fita Alh. Rabi'u ya dubeta fuska a hade kamar ba shi ya gama yiwa Asabe dariya ba.
"Bakin halin da ki ka koyawa 'ya'yanki za ki gwada min?"
Dadi ya kama Asabe ta karbe zancen don ta kara zuga shi.
"Ka dai bi a sannu kar ka manta da bakinka ka fada min Ale Gambo ya ce ta mare shi."
Kamar an kunno shi kuwa ya hau masifa yana fadawa Innayo maganganu.
"Banda lalacewa ace har kin iya dora hannuwanki a fuskar baligi kamar Ale Gambo kamar baki san haramcin yin hakan ba?"
Saboda yadda take jin ta muzanta sai take gani kamar tsirara ya yi mata a gaban matarsa. Jikinta ya yi sanyi kalau yayinda zuciyarta take tafarfasa. Haka nan idanunta suka rine da bacin rai mara misaltuwa.
"Yanzu Alhaji me ya kawo magana irin wannan? Gambo tamkar dan cikina fa yake tunda ya auri Salima."
"Tamkar 'yar cikinki dai...ke da baki san ma'anar haihuwar namiji ba ina ke ina kwatanta dan wata da naki?"
Asabe ce tayi maganar dankwalinta a gaba tana neman takalar fada. Haushin yadda su Munzali ke bin Innayo take son fanshewa.
"Fada mata dai. 'Ya'yan da ta cusawa kiyayyata basa ganin girmana. Gashi tun ba aje ko ina ba an fara dawo min gida."
Asabe ta murmusa cike da jindadi.
"A'a fa Alhaji. Kar kayi butulci. Nima shaida ce ana kawo maka dari da kwabo idan Hasiya mai lalle tayi ciniki. Su kankamoji (Zara da Uwani) dai ko ita sha-wuyar basa bawa."
Dariya suka kwashe da ita wadda tayi sanadiyar zubowar hawayen da Innayo take ta kokarin dannewa. Habar zaninta ta saka ta goge idanunta amma haka wani hawayen ya maye gurbinsa. Dan kuka mai ja wa mahaifiyarsa jifa. A haka ta fita tana jiyo sautin dariyarsu.
Bata karasa dakinta ba ta juyo a fusace ta koma dakin Alh. Rabi'u. Tuni ta fahimci cewa sadaukarwa da hakuri daban suke da kawar da kai. Ta sadaukar da kuruciya, lafiya da jindadinta a bautar aure da kula da yara. Tayi hakuri da rashin kyautatawar miji da wasu cikin 'ya'yanta. Duka wadannan akwai riba a duniya da lahira. Amma kawar da kai akan abubuwa na bacin rai kam cutarwa ne gareta dasu wadanda take kyalewa. Anyi abin da aka yi a baya. Yanzu kuwa daidai take da kowa. Bata da nufin cutar da kowa, sai dai ba za ta yarda tayi ta hadiyar bakincikin kowa ba.
Bankada labulen tayi ta shiga ta zauna a gaban Alh. Rabi'u. Hannayensa duka biyu ta kamo ta shimfida tafukan akan fuskarta. Asabe mamaki ne ya kamata na zuci da zahiri. Shi kuwa sai ya sami kansa da shiga taitayinsa ya kasa yi mata magana.
Cikin muryar lumana babu wani hargagi kamar yadda ta yiwa su Zara ta soma magana.
"Kaji dumin hawayena?"
Ya gyada kai kamar sakarai.
"Bai kama kafar zafin zuciyata da barazanar bugawar da take a kirjina ba. Alhaji...."
"Na'am" ya amsa da rawar baki.
"Allah zai bi min hakkin hawayen da na zubar maka ba da hakki ba."
Ta tashi ta juya za ta fita sai ta tsaya ta kara da cewa " 'ya'ya amana ne kuma daidai iyawata nayi kokarin sauke wannan amanar. Ba komai da nayi bane zai zama daidai amma nayi imanin Allah zai sakawa kokarina. Zai shirya min 'ya'yana. Zai daidaita min lamurana."
Da ta koma dakinta duka 'ya'yanta suna nan harda Uwani da ta shigo bayan fitarta. Kare musu kallo tayi daya bayan daya tana tuna ranar da ta haifi kowacce. Uwar dakin ta shiga ta barsu ba tare da ta amsa maganganun da suke yi mata ba. Hannu na rawa ta tura kofar ta rufe da sauri sannan ta zube a kasa saboda zafin kirji. Miji babu dadi, kishiya ba zaman lafiya, 'ya'yanta kuma kowacce da tata matsalar. Matsalolin nasu da suka zame mata abin tunani da shiga damuwa.
Kwana biyar kenan da ta dauko Salima. Ga Zara har yau mijinta bai zo ba. Maimuna nata mijin ya ce ya gaji da yawan zarya da take yi zuwa gidan iyayenta, ga talaucinsa da yafi na Ale Gambo. Uwani tun washegarin zuwan Ummule ta fada mata anyi mata kishiya. Gabadaya ta sauya tana neman susucewa. Sai dai taki fada mata ba zuwan kishiyar bane kadai damuwarta ba. Kudin da take yawan cewa babu ta nema ta rasa. Ta kuma kasa cigiya a gida saboda babu wanda ya san dasu. Hasiya kuma nauyi ya mata yawa. Bata morar kudin sana'arta ko kadan yanzu. Duk ta rame saboda wahala da rashin isasshen bacci. Sannan rashin haihuwarta yana matukar damunta.
Ita ce uwa garesu. Bata hango ranar hutun jiki da na zuciya ba kila sai ta bar duniyar.
Alh. Rabi'u da Asabe kuwa har Innayo ta ware a dakinta basu dawo daidai ba. Maganarta takaitacciya ce amma ta zauna saram a kwakwalensu.
"Kace masa Habu ne."
Masinjan ya bishi da wani irin kallon kwaf kafin ya ce "Habun ai da yawa. Baka da inkiya ko cikakken suna?"
Honorable ya yi dan murmushi don fushi ba nasa bane. Satinsa guda yana zuwa ma'aikatar wurin shugabansu Alh. Bala ana jirga shi. Ba kuma zuwan kansa bane. Mutumin ya kasance abokinsa lokacin da yake da abin hannu. Tunda ya sami karayar arziki bai taba bibiyar tsofaffin abokan huldarsa neman taimako ba. Wulakanci ne baya so. Yanzu ma dole ce ta kawo shi. Ya boyewa duka iyalinsa ne musamman Hasiya amma likitan da yake duba Abbas a asibitin kwakwalwa na Dawanau ya tabbatar masa da cewa idan ba ayi masa aiki cikin kankanin lokaci ba da wuya ya warke ko anyi. Jijiyoyin da suka sami matsala sun fara gajiya a yanayin da suke ciki. A wannan yanayin ne ya hadu da tsohon abokin nasa a wajen daurin aure. Bai yi kasa a gwiwa ba ya nemi taimako kuma ya yi sa a ya amsa masa. Fatan samun warakar Abbas din shi ne albishir din da yake ta boyewa Hasiya. Sai gashi har yau ko ciki bai sami shiga ba. Kullum da abin da ake fada masa. Yau ne ma ya yi sa'ar haduwa da masinjan Alh. Bala din shi ne har aka tambayi sunansa.
"Habu Danmalam za ka ce masa. "
Masinjan ya sake kura masa ido kamar me neman wani abu. Cikin 'yan dakiku ya sanya hannu ya bugi kansa da takaicin rashin gane shi da wuri. Sakin fuska ya yi sosai ga mamakin yanayin da ya ganshi.
"Habu Danmalam dai da na sani?"
"Ni ne" ya amsa da murmushi.
"Ikon Allah. Ai wallahi da na san kaine da tun zuwan farko nayi cuku-cukun hada ka da Yallabai" Hannu ya mika masa suka gaisa ya ce " Amma ina zuwa. Bari naje na fada masa idan Minista ya tafi sai ka shiga."
Wani karamin ma'aikaci a wurin yana jin furucin masinjan ya janyo shi gefe.
"Yallabai fa ya ce kada a bar kowa ya shiga yau. Idan Ministan ya tafi shi ma tashi zai yi."
Honorable Habu yana jinsu ya ja gefe da nauyin zuciya. Gwargwadon iyawarsa bai yi amfani da mukamansa na baya ya wulakanta kowa ba. Amma duk da haka yanzu idanunsa sun kara budewa da bambancin masu mukami da talakawa. Mafi yawan masu kawo korafi basu da yadda zasu yi ne. In an barsu ba za sy zabi kaskantar da kai suna roko ba. Amma sai su keta billensu suyi rokon bayan an hanasu a kara da wulakanci.
Masinjan ya amsawa mutumin da cewa "Honorable Habu Danmalam ne fa."
"Kai ka san shi" cewar wancan irin 'yan rijiya ta bayar guga ta hana dinnan.
"Ni kuwa na san shi. Kuma Yallabai ma ya san shi domin tare suka yi siyasa."
Bai kara saurarar mutumin ba ya wuce cikin ofishin Alh. Bala. Ya san suna tare da Ministan (Land, Housing and Urban Development) sai dai kuma idan har bai sanar dashi bakon nasa ba karshenta ya fice ta baya idan sun gama tattaunawa.
Sallama ya yi ya sake gaishe da Ministan kamar ba shi ya yi masa rakiya har nan din ba.
"Yallabai dama na ce bari na leko ko kuna bukatar wani abu."
"Idan ina bukata ma ai ka san Surayya (sakatariyarsa) tana nan."
Masinja ya gyada kai
"Eh haka ne kuma. To ku tashi lafiya." Juyawa ya yi kamar zai tafi sai kuma ya dawo "af...Yallabai kar na manta kana da bako fa."
Alh. Bala ya kirne fuska saboda wannan shishigi zai iya sawa ya rasa alkhairin da Ministan ya zo dashi. Hannuwansa ya dora akan teburin gabansa yana maganar da babu kofar ja'inja cikinta.
"Ba zan ga kowa ba idan mun gama tafiya zan yi. Ko waye ka ce ya dawo gobe."
Ya san za a rina shi yasa ya ce "babu komai. Yau da gobe duk daya ne. Don ya kara kwana daya akan ragowar kwanakin da ya yi yana zuwa babu matsala."
Wani mugun kallo Alh. Bala ya jefa masa kafin ya kai ga ambaton sunan bakon a dole ya fita. Addu'a yake shi kadai yana fatan bai yiwa kansa sanadin aiki ba.
Sai bayan fitar Masinjan Minista ya ajiye karamin kyakkyawan kofin shayin da yake rike dashi tun shigowarsa. Yadda ya buga kofin ya tayar da hankalin Alh. Bala domin alama ce ta bacin rai.
"Kayi hakuri Ranka ya dade. Na san ka ma fini haduwa da 'yan maula masu hana mutane hutawa. Mutumin da ya zo din na san ba kowa bane illa wani tsohon dan siyasa da muka zauna jam'iyya guda a baya. Gwamnatin da ta maye gurbin tamu tun a wancan lokacin tayi watsi dasu. Shi kuma bai iya kwantar da kai irinmu ba...hahahhha"
Har lokacin fuskar Minista babu wani annuri sai ya dora da,
"Harda laifinsa gaskiya da ya kasa samun wani mukami da aka sake samun canji tsohuwar gwamnatinmu ta dawo. Ya dauki girman kai da dagawa shi a dole mai tsantseni. Ashe abin nasa duk buge ne, gashi daga haduwa wurin daurin aure ya makale min."
'Allah na gode Maka da Ka nuna min waye Alh. Bala tun kafin na sanar dashi makasudin zuwana.' Furucin Minista kenan a zuciyarsa.
Idan yawan aiki ne da yawan 'yan maula ya ninka Alh. Bala nesa ba kusa ba. Sai dai shi mutum ne da ya tsani wulakanci. Tarba mai kyau wadda ta dace da matsayinsa ya samu kuma akan idonsa wani ya sami kishiyarta. Wannan abu ne da ba zai iya dauke kai ba. Maganar aure ce ta kawo shi. Ya hadu da wata yarinya a gidan abokinsa wadda bayan gajeren bincike aka fada masa 'yar Alh. Balan ce. Muradinsa na son auren mata biyu yaso cikewa akanta. Dalilinsa kenan na zuwa ya same shi saboda shi mutum ne mai tsari. Ba ya son ya fara yi mata magana a waje ta amince saboda mukaminsa bayan akwai wani. Halin mahaifin nata da ya gani yasa shi yanke shawarar zurfafa tunani da bincike.
Tashi ya yi ya gyara zaman babbar rigarsa.
"Ba dai tafiya ba? Bamu tattauna maganar da ka ce mai mahimmanci bace ba ma" Cewar Alh. Bala shi ma yana tashi tsaye.
"Kada ka damu zan kira ka a waya. Ina da appointment ne da naso mantawa dashi gashi har lokaci ya kusa."
"Au tohhh..." Alh. Bala ya ce yana sakin fuska "ai na zata zuwan dan anacen can ne ya bata maka rai."
Minista bai ce komai ba har suka fito waje. Alh. Bala kuwa sai zuba masa surutu yake yana ta kwantar da kai kamar ya durkusa masa.
Da Masinjan nan ya fito bai iya komawa wurin Honorable Habu ba. Zaman jiran bai dame shi ba. Ya zabi ya fadawa zuciyarsa aiki ne ya yiwa Alh. Bala yawa ba wai da gangan yaki ganinsa ba.
Tashin wasu security da sassarfa suna komawa wurin jerin wasu bakaken motoci da ya samu a wurin yasa shi kallon hanya. Farinciki ya wadatu a fuskarsa yayinda ya yi tozali da Alh. Bala. Da sauri ya tashi yana son yi masa magana kafin ya shiga mota. Da ya tashi sai yaga ba shi kadai bane ya nufi Alh. Bala din da wanda suke tare. Sai kalaman fadanci ake ta zubawa ana cewa
"Allah Ya kiyayeka"
Da dai ya gane ba da ubangidansu suke ba sai ya kalli abokin tafiyar sosai wanda shi ma kallonsa yake yi. Baki ya hangame sai kuma dariya da murna suka hana shi magana.
Ministan ne da kansa ya ambaci sunansa cikin wani irin shauki da kewa.
"Habu Kansila? Honorable Namu? Kai ne?"
Honorable ya dinga gyada kai har suka cimma juna. Hannuwansa Minista ya rike yana ta murmushi.
"Abdulkarim kaine haka?"
Sunkuyar da kai ya yi na kunyar rashin kyautawarsa kafin ya ce,
"Naji kunya sosai Honorable duk da dai wallahi na nemeka sosai bayan dawowata aka ce ka bar unguwar. Laifina shi ne na rashin mayar da hankali wurin binciken inda ka koma din."
Alh. Bala sai yaji kamar an sare masa gwiwoyi. Alamun sanayyar dake tsakaninsu barazana ce a gareshi. Hanyar da suka baro ya nuna da hannu yana kiransu.
"Ku zo mu koma ciki don da alamu kuna bukatar zantawa cikin sirri."
Minista Abdulkarim Mamman Diso bai bashi amsa ba sai nunawa Honorable motar da zasu shiga ya yi.
"Bismillah. Kodayake ban tsaya naji uzurin da ya kawoka nan din ba."
Honorable ya kalli Alh. Bala ya kawar da kai
"Wanda nazo gani bai saurareni ba"
Da haka Minista ya gane shi ne wanda yazo ganin Alh. Bala.
A motar suna tafiya Minista yake sake bashi hakurin yankewar zumuntarsu. Ba abokai bane domin kuwa Honorable ya girme shi nesa ba kusa ba. Lokacin da yake ganiyar cin zamarsa ne su Abdulkarim suka fitini unguwa. Rashin kudi ya hana iyayensa tura shi makarantar gaba da sakandire. Kafin wani ya kai zancen kunnuwan Honorable Habu shi ya gani da idanunsa. Har gida ya tura aka kira masa iyayensu maza ya ce zai dauki nauyin karatunsu shi da abokansa su uku. Haka kuwa aka yi. Suka sake JAMB cikin ikon Allah shi kadai ya haye. Yaji dadi sosai ya biya masa kudin karatun. Abokan masa kuma ya basu jari.
Rayuwa tayi ta tafiya har ya kammala digirinsa na farko. Honourable Habu ya soma cuku cukun nema masa aiki sai ya sami tallafi na zuwa kasar waje karo karatu. A can ya zauna ya yi masters da Phd. Kuma nan ne dai ya hadu da dan wani mai bawa shugaban kasa shawara. Da taimakonsa aka sama masa aiki ya fara yana dawowa. Ya nemi Honorable Habu a ranar da ya sanya kafarsa a unguwarsu Diso sai ya sami labarin ya tashi. Da zuci zucin ya kara nemansa ya koma Abuja. Daga nan kuma kujiba kujibar duniya da kai kawo suka dauke masa hankali. Sai gashi sun sake haduwa a inda bai yi zato ba.
"Ina su Abbas kuwa? Ya gama karatu yanzu ko?"
Tambayar sai ta zama fami ga Honorable. Nan ya labarta masa halin da suke ciki.
Abdulkarim sai ya kara jin haushin kansa. Bai ce masa komai ba amma tuni ya gama yanke shawarar irin taimakon da zai yiwa Hoborable da iyalinsa.
A gidan Alh. Tahir kuwa Mami Khadija ta cigaba da shirye shiryen bikin autansu. Mama Nasima kuma ta matsawa Mardiyya lamba da tambayar yaushe Munzali zai dawo.
"Kinga ya tafi kafin mu samu ayi maganar da ta dace. Ni ba so nake kuyi ta batawa juna lokaci da hirar waya ba." Ire iren zantukanta kenan kullum.
Ita kuwa Jiddo ta shiga tsaka mai wuya a wurin kawaye. Karyar da ta zuga musu akan hadin kai da jindadi da ta samu a wurin Danliti makanike ce take neman tarar da ita. Mutum biyu cikinsu kuma harda shugabarsu a ciki sun nemi ta hadasu dashi. A cewarsu harka da talakawa marasa galihu tafi dadi. Komai kika yi musu yanzu sai su ji kamar duniya babu kamar ki. Ladabi da biyayya da kuma bin hanyoyin farantawa mace sai kin zaba kin darje
. Sannan uwa uba sun fi rike sirri.
Zancen da ake yanzu dai shugabar tasu tana son yaje Abuja ya sameta sati mai zuwa. Mijinta zai yi tafiya kasar waje kuma tana da yakinin da daya daga cikin 'yan matansa zai tafi. To ita ma ta kirkiri tata tafiyar ya kuma amince. Nan kuwa dan gidan holewa ta saya ba tare da saninsa ba inda take kai kwartayenta. Dubu hamsin ta turawa Jiddo ta ce ta bashi ya yi kudin mota.
Jiddo ta rasa inda za ta saka kanta. Tun ranar da ta tura masa hotuna bai kara nemanta ba. Ta saka masa kati na dubu goma babu godi bare na gode. Yanzu kuma har shugabar wadda ake yiwa lakabi da Sarauniya ta fara cewa idan ma taki hadasu ne saboda tana kishinsa zasu saita mata zama. Ai ta san dokarsu babu rowa. Kowacce tana da damar neman saurayin 'yar uwarta. Shi yasa ma suke fadawa juna yadda ta kaya ko wata za ta so.
Uban gayya Alh. Tahir kuwa yana cikin fushin Yakumbo. Ya tsayar da duk wata magana ta auren Yumna saboda abin da tayi masa. A yadda ya tsara idan an fasa akalla nauyin Farha zai ragu a ransa har ya samu su yi magana. Rabin hankalinsa a kwance yake tunda sauran 'ya'yansa babu wanda ya canja masa fuska. Ya san bata fada ba. Ita kadai ce dai har yau bata yarda sun hadu ba. Motsin motarsa ma idan taji daki take shigewa ta kulle kofa.
Yakumbo kuma tayi rantsuwar idan bai auri Yumna ba to ya shirya ganin bacin rai domin babu shi babu ita.
A can wani bangare na zuciyarsa wanda soyayyar 'ya'ya ta rinjaya sai yake jin gara fushin Yakumbo akan na 'ya'yansa. Yakumbo uwa ce. Uwa kuwa a saninsa za ta iya jure komai kuma ta hadiyi komai domin 'ya'yanta. Idan ta kama ya yi mata kuka ne ma zai yi don ya san za ta yafe masa ta janye zancenta.
Dan madaidaicin akwati mai taya hudu Farha ta daga ta saka a booth din motarta. Idanunta ta kai kan motar Abbati wadda take lullube a wurin ajiye motocin gidan taji zuciyarta ta harba. Zai yau zai zo gidan daukar motar amma ba zai sameta kamar yadda tayi masa alkawari ba. Sakon da ya turo mata jiya da daddare ta sake maimaitawa a cikin kanta a hanyarta ta zuwa wurin Maminta.
(Zan zo mu yi magana Ya Farha. Maganar baki da baki kafin nayi shirin daukar mataki na gaba wurin mallakawa Auwal muradinsa. Kin mamaye ko'ina a tare dani. Allah Yasa kina tuna ni ko sau daya ne a rana.)
Wani abu mai kama da ana yiwa mutum yawo a ciki taji ya tsirga mata a lokacin don dadi. Ita kadai ta dinga zuba murmushi tana kuma jin kunya kamar yana gabanta. Ashe sunansa Auwal ta fadawa kanta kamar da wani take. Sai da ya soma fitar da rai da samun amsa sannan tayi masa reply.
(Ban san Auwal ba shi yasa bana tunaninsa)
Da wurwuri ya sake turo mata wani
(Amma dai kin san Abbati?)
Kasa rubuta komai tayi tana dariya kasa-kasa.
A bangaren Abbati shirunta sai ya dame shi. Shi fa kaifi daya ne baya son jan rai. Kiranta ya yi kai tsaye ta dauka da wayar da kusa tsinkewa.
"Ya Farha baki san Abbati ba?"
Yadda ya yi tambayar da damuwa yasa ta fasa cigaba da ja masa rai.
"Na san shi." Ta rage murya sannan ta kara da cewa " Kuma ina tunaninsa kullum."
Ajiyar zuciya ya saki tare da lumshe idanu
"To ai ni ne Auwal din. Suna na na gaskiya na fada miki."
Bata san lokacin da tayi dariya ba har tana tunanin ko dan fari ne. Dariyar da ta dinga kurdawa ko ina a cikin Abbati tana saka shi daukar dumi. Tun yanzu yake fatan idan ya sami Farha Allah Ya bashi ita har aljanna. Da wata irin murya mai dadin amo da tsayuwa a rai ya ce
"Ina sonki Ya Farha"
Yadda ya dauke numfashi yana jiran amsarta haka ta dauke nata saboda girman lafazinsa. Ta dade kwarai da cire rai da jin wannan kalmar a kanta.
"Kin barni da faduwar gaba."
"Nima nawa gaban faduwa yake" ta bashi amsa da dukkan gaskiyarta.
"To yanzu ya za ayi kenan? Da sai nan da kwana uku zan zo daukar motata amma na fasa. Tunda gabanki na faduwa gobe zan zo in sha Allahu."
Kunya ta ji ta sake yin shiru har sai da ya tambayeta me yasa bata son yi masa magana sosai. Bai san hira irin wannan gabadaya bakon abu bane a gareta. Kawar da zancensa tayi ta sako wata hirar daban.
"Yaya su Baaba? Don Allah ka ce ina gaisheta."
Sai da ta yi dariya ya ce "ba damuwa don kin bagarar da zancen. Gobe kinga sai ki bani amsa muna kallon juna. Kinga ni na huta tunda dama ba iya fada zan yi a gabanki ba don nima ina jin kunya. Baaba kuma tana lafiya. Zuciyata tana ninka son mai mutunta Baaba. Ki gaishe min da Maminmu."
Katse wayar ya yi ya barta da murmushin da masana zasu gane na sabon shigar soyayya ne.
Sai dai nishadin da take ciki bai dade ba ya rugurguje. Alh. Tahir ne ya kirata sau biyu bata daga ba sai ya kira Mami Khadija ya fada mata sako ta bata. Suna gama magana kuwa ta kirata ta sanar da ita.
"Abbanku ya ce ki same shi a falonsa goma na safe."
Kuka ta soma tun kafin ta gama jin sakon.
"Mami don Allah..."
Daurewa Mami Khadija tayi domin ta san abin da zata fada mata shi ne daidai.
"Wasan buyar da kike dashi ya isa haka. Kije kiji kiran me yake miki"
"Mami?" ta furta da kyar saboda kukan da yaci karfinta.
"Sai da safe Farha."
Ita ma kukan ne ya taho mata shi yasa ta katse kiran.
A daren Farha ta hada kayanta a akwati. Gari na wayewa ta karasa shiryawa. Ita ta tashi Mami Khadija da ta shiga dakinta.
"Gidan Mama zan tafi na zauna har a gama bikin Kawu."
Ta san za a rina dama. Farha can be stubborn idan abu bai yi mata ba.
"Da izinin wa za ki tafi?"
Zubewa tayi a gaban gadon ta marairaice mata.
"Don Allah ki barni in tafi Mami. Idan naji zuciyata za ta iya daurewa inyi magana da Abba zan dawo." Tayi maganar kwalla na zubo mata.
"Au...bama ki da niyar dawowa in an gama bikin kenan?"
"Please Mami"
"Naji. Allah Ya tsare. Kada dai ki manta duk dadi ko rashinsa ba a canjawa tuwo suna."
Kai ta gyada ta mike. Har ta fita bata bar fassara kalaman Mami na karshe ba. Jinjinawa mahaifiyarta ta tayi domin ta fahimci ko da bata fadi me ta gani ba ita ma ta san ko meye. Ita kam bata son fasiki kuma bata jin zuciyarta tana da kwarin daukar cin amanar namiji. Kofa a bude take yayi aure amma banda yawon bin matan titi. Bata fatan abin da zai zo ya gifta har ya sata hakurin zama da mazinaci!
UKU DUWATSUN...
Da mukulli Jiddo ta rufe kofarta bayan mai yi mata aiki ta fita ta shige daki. Missed calls din Sarauniya sun fi goma. Sai sakwanni wadanda tun bata bude ba ta san kwanan zancen. Surutu ne da zagi duk akan rashin hadasu da Danladi. Kayanta ta cire bayan ta rurrufe tagogi ta haye gado ta dauki hotuna kala kala wanda muninsu yafi na farko. Ta dai tabbatar bata hada da fuskarta ba. Wayar Danladi ta kira yana gani bai dauka ba sai kawai ta tura hotunan tare da sakon magiyar ya amsa gayyatarta. Ta kara da fada masa nemansa da Sarauniya take yi.
(Ta bani dubu hamsin na baka kayi kudin mota zuwa Abuja. Ladan aikinka zai iya fidda kai daga talauci. Ni da kai duka zamu karo da abin da za ta biya. Sai naji shawarar da ka yanke.)
A kwance yake ya gama karewa hotunan kallo ya karanta sakon nata. A gigice ya tashi har ya barar da dan kofin silba din da matarsa ta ajiye masa ruwa a ciki. Dubu hamsin kuma kudin mota kadai?! Hannunsa kaikayi ya kama yi yana son kiranta amma wata zuciyar ta hana. Wai kada ya nuna mata shi din kwadayayye ne.
Jiddo kuwa da ta tabbata yaga hotunan sai ta kira shi. Da irin salonsu na gogaggun mata take masa magana.
"Danladi mata aka sani da jan aji amma sai gashi lokaci guda kana ta dagula min lissafi. Shin ko dai abin da na turo bai burgeka bane?"
Sai da ya hadiyi yawu da kyar saboda muryar ta tuna masa irin hotunan sannan ya dan yamutsa fuska ya amsa mata kamar ba ya so.
"No ba haka bane. Kawai ina busy ne."
Jiddo ta murmusa. Dan hannu ne babu tantama. Kyale shi za tayi ya ja ajin sannan ta fadi bukatunta.
Danladi ya gama kwanakwanarsa ya mika wuya. Ba wai son zuwa ne baya yi ba tun farko dama. Kawai dai yana tsoro ne ganin cewa matar manya ce. In bai manta ba, motar da ya gyara musu da kayan jikinta babu alamar talauci ko kadan a tare da ita.
"Ku sa min rana amma banda satin nan."
"An gama" cewar Jiddo cike da nishadi.
Jan shi ta dinga yi da hira har ya dan saki jiki. Suna gama wayar hankalinsa ya karkata kan Ayaah. Ita ce irin macen da ya dade yana muradi. Irinsu Jiddo sai dai aje aci kudi kawai a dawo. Ayaah kuwa su ake kashewa kudin idan akwai su. Dakin matarsa Raiha ya shiga tana zaune da yaransu biyu tana basu kunu.
Aikin sa yana kawo masa rufin asiri daidai gwargwado amma saboda karya da yawon bin 'yan mata ya kasa wadata gidansa. Yau tashi suka yi babu ko sisi a jikinsa sai makota ta shiga ta karbo bashin kunu. Shi ne suka sha da safe, rana da kuma yammacin yanzu da ya gama sanyi kalau.
"Wani abin kake so ne?"
Ta tambaye shi a ladabce ganin ya tsaya a bakin kofa yana ta binsu da kallo.
Tabe baki ya yi kafin ya ce "bani darin da na baki dazu zan dan fita."
Danne zuciyarta tayi ta ciro darin daga cikin riga ta mika masa. Bai ce mata komai ba ya juya abinsa. Ludayin da take bawa yaran kunu taji ya mata nauyi ya sabule daga hannunta saboda bakinciki. Dan kudin da ya bata take cancanawa za ta saya musu awara suci mai dan nauyi da daddare shi ne ya karbe.
Kamar kiftawar ido da bude shi don ko gyara zama bata yi ba ya sake shigowa ya wuce dakinsa. Katin naira dari ya siyo ya saka a wayar ya dannawa Ayaah kira. Yaci alwashin yau zai fara dorata akan manufarsa. Ba zai bar gidansu ba sai ya rungumeta.
Wanki take ta kunna rediyo tana sauraron wani shiri da akeyi a tashar Freedom mai suna Sabon Shafi. Shirin yana burgeta matuka domin ana hira ne da mata da suka yi fice a fannoni daban daban. Burinta wata rana ace za ayi hira da Hajara Habu Danmalam, fitacciyar....
Tunaninta ne ya katse ba tare da ta gama tsara matakin da take son kaiwa a gaba ba sakamakon shigowar waya. Daga kai tayi kan dan dakalin da suke ajiye guga inda wayar take taga sunan mai kiran. Da sauri ta goge hannunwanta da zanin jikinta ta amsa kafin ta katse.
Sai da tace hello sau hudu Danladi bai amsa ba. Yana jin ciwon tafiyar kudinsa a banza amma dole ya hakura idan yana son cin wannan yakin. Wani jan numfashi ya yi kamar wanda ya yi muguwar gajiya sannan ya kira sunanta da kwantacciyar murya.
"Ayaahhhh. Me na yiwa mata suke guduna haka?"
Daburcewa tayi da salon maganarsa. A lokaci guda kuma kalamansa suna tayar mata da hankali. Duk yadda akayi matarsa ta kuma guma masa wani abin.
"Mata har nawa ke gudunka?"
"Wadda kika sani dai ta gidana, sai kuma ke da na daukeki wata babbar jigon rayuwata. Kwana nawa baki ji daga gareni ba amma ko dan tes dinnan ya gagara ki ji lafiyata."
Kanta yayi gingirin kamar an dora farantin kwai tana tsoron ya fado ya fashe. Zuciyarta kuwa shawagi ta dinga yi mata a kirji saboda tsananin farinciki. Da tattausan lafazi ta soma bashi hakuri. Da ya san katin yana daf da karewa sai ya katseta.
"Na san dai ina takura miki da matsalolina amma don Allah I am sorry. Bana son Mom ta sani. Ke kadai zuciyata ta amince ta dinga fallasawa sirrinta. Idan kina gida zan zo da anyi magariba."
Cikinsa a take ya bada wani sauti kamar yana rokon shi ma a kaishi gareta ya sami abinci. Shu'umin murmushi ya yi ya dan daga murya,
"Dalin, kin dafa min indomie din ne?" Ya dan yi jim kadan "naji. Allah Ya baki hakuri. Idan na fita zan nema. Kina son wani abu ne na taho miki dashi?" Ana fara warning na yanzu kudin zai kare ya ce da Ayaah "sorry na barki ina magana. Idan nazo zan kiraki."
Mace mai tunani za ta fassara hirarsu Ayaah da cewa Danladi (Dani) ya cancanci a tausaya masa saboda rashin samun kulawar iyalinsa. Da kudinsa da komai amma abinci ma sai dai ya saya. Mai zurfin tunani kuwa za ta tausaya masa da farko. Idan an gama wayar sai ta koma tunanin dalilinsa na fada mata laifin matarsa. Daga nan za ta gane akwai wata a kasa. Sauran binciken zai nuna mata shi abin yarda ne ko akasin haka.
Wankin da Ayaah bata gama ba kenan. Inda Hasiya take tare da 'yan lallenta taje ta durkusa. Sosai alakarsu tana ta gyaruwa yanzu sai dai duk da haka aure Ayaah take so. Ita dai ta bar gidan ta huta da zugar su Anti Fati kannen mamanta da kuma mitar yayyenta. Sannan ta kula baban nasu ba iya biya mata zai yi ta cigaba da karatu yadda take so ba.
"Anti me za a dora ne? Naga yamma tayi sosai."
Hasiya tayi murmushin jindadi. Canjin da Ayaah tayi yana faranta zuciyarta sosai.
"Kin manta yau Ummita ce a kitchen? Kice tayi mana jallof din shinkafa."
Ta zaro dari uku ta mika mata ta ce a siyo kifi a saka a ciki.
Ayaah ta karba harda godiya ta shiga ciki. Mayafi ta dauko ta tafi ta siyo kifin ko Ummita bata nema ba.
Kifin dari biyu da hamsin ta siyo sai alayyauhu da albasa mai lawashi na hamsin. Sauran kayan bukatar duka akwai a gidan. Albasa ma suna da ita sai da mai lawashin take bukata. Wankesu tayi ta yanka tare da alayyahun ta sake wankewa ta ajiye ya tsane. Ta debo wake yadda take bukata ta dora. Sannan tayi jajjagen kayan miya da citta da tafarnuwa ta soya ta tsayar da ruwan abinci. Kamshin ne yasa Ummita lekowa daga daki. Tun dazu take son fitowa dora girkin ciwon kai ya hana. Ta dauka Murja ce ta gama kitso ta zo taimaka mata sai ganin Ayaah tayi. Wani dadi ya shigeta na canjin kanwar tasu tayi mata gofiya ta koma ciki.
Da ruwa ya tafasa Ayaah ta zuba shinkafa tare da waken da ya soma dahuwa su dahu tare. Sai da ta kusa gama turara bayan ta rage wutar ta zuba lawashin da alayyahu tare da kifin da ta ciccirewa kaya. Yau ma kafin kowa ya farga ta dibarwa Dani sannan ta kwashe sauran. Tayi sa'ar gama komai kafin a fara kiran sallah. Sai ta fake da alwala ta samu ta wanke fuska taje tayi kwaskwarima.
Honorable yaga ranar taimakawa na kasa a lokacin da bai zata ba. Da suka bar ma'aikatar su Alh. Bala, gidan Minista Abdulkarim suka wuce. Tamfatsetsen gida wanda ko lokacin da yake ganiyar arzikinsa bai taba tunanin mallakar irinsa ba. An kawo masa abinci mai rai da lafiya ga kuma girmamawa ta musamman daga maigidan. Matarsa tana Abuja da yara shi kadai ya zo ganin iyayensa da magana da Alh. Bala. Wannan yasa masu hidimar gidan su ma suka zage damtse anata kai kawo.
"Naga kamar umarninka kadai suke bi. Don Allah ka ce kada ta zubawa wallahi na koshi."
Furucin Honorable kenan bayan duk abin da yaci kuma aka sake kawo masa farfafesun jelar saniya.
Abdulkarim ya dagawa mai aikin hannu da murmushi a fuskarsa sannan ta fasa zubawa. Kallon Honorable ya yi yana mai kara jin tsoron Allah ta yadda rayuwa take jujjuyawa ga bayi.
"Gani nayi duk ka rame. Don Allah ka sake cin wani abu."
Honorable ya tuntsire da dariya "banda abinka kuma sai aka ce a cin abinci guda zan yi kiba?"
Dariya suka yi tare suka taba hira sannan Honorable ya tashi zai tafi. Abdulkarim ya ce bai san zance ba. Yana son jin me ya faru dashi tsayin lokaci har rayuwa ta koma haka.
Tiryan tiryan ya labarta masa komai. Ba kuma don maula ba sai don dalili guda wanda ya fada masa kamar haka,
"Duniya bata da tabbas Abdulkarim. Ba komai ne yake zama tabbatacce ba a rayuwa. Saboda haka ka daure ka rike gaskiya a duk inda ka sami kanka. Idan duniya ta ciyar da kai gaba fiye da nan sai ka dinga kallon kasa kana kara godiya ga Allah. Bana maka fata amma ko da za ta kawoka inda ta ajiyeni to kada ka karaya da samun rahama. Allah ba Ya dorawa bawa abin da yafi karfinsa. Ba zan boye maka ba da farko na shiga kunci saboda rashin sabo da babu ga Abbas a kwance. Da ilimina na fara hasashen ko auren Hasiya ne ya jaza min talauci. Sai gashi ashe ita za ta rike gidana da 'ya'yana. Duk zafin talauci idan Allah Ya baka mace ta gari to tabbas Ya kwashe maka radadinsa."
"Zan so ganinta. Muje da kaina zan kai ka gida." Cewar Abdulkarim, zantukan suna shigarsa da kyau.
Honorable ya dage baya so. Shi ma Abdulkarim ya dage sai yaje. Daga nan ya tashi ya bi wata hanya zuwa bangarensa. Da envelop ya dawo ya mika masa.
Allah Sarki! Yawun bakinsa ya kafe. Idanuwansa suka kada suka yi ja....a wani shudadden lokaci shi ne yake bawa Abdulkarim. Yau duniya ta nuna masa cewa tables can always turn. (Ya Allah Ka rabamu da talauci da karayar arziki. Duk abin da zai taso mana na kudi Allah Kasa mu fi karfinsa.)
"Duk ni kadai? Basu yi yawa ba?" Ya ce da murya tana rawa. Raba kudin ya yi gida biyu ya mika masa rabi.
Abdulkarim sai yaji wani abu mai nauyi a zuciyarsa. Honorable Habu yafi karfin wulakanci a wurinsa. Laifin kansa ya gani da ya yi sakaci da zumunci har ta kai bai san mawuyacin halin da tsohon ubangidansa yake ciki ba. Ace har ya kai matsayin da dubu dari za ta kawo masa kwalla a ido.
"Kada kayi min haka Honorable. Ban kyauta ba a baya na sani amma ka dauka Allah ne bai shirya haduwarmu ba sai a yanzu da muke sa ran alkhairi ya biyo bayanta."
"Haka ne. Nagode.."
Godiyar ma katseta Abdulkarim ya yi suka fita zuwa mota tare. Wannan karon daga su biyu a bayan mota sai direba. A hanya ne yake tambayarsa irin sana'ar da yake son yi. Lokaci ya ja babu batun komawa siyasa. Idan an manta da mutum sai ya zo da kwakkwara kuma kyakkyawan shiri tafiyar take sake armashi. In ba haka ba kudinsa kawai zai yi asara.
"Zan yi shawara da Hasiya sai na fada maka" Ya ce da murmushi a fuskarsa.
Abdulkarim ya kama dariya sannan ya ce "Allah Yasa bata aurar da duka 'ya'yanta ba ta bani guda. Don naga alama idan na auri rainonta kila sai nayi shugaban kasa."
Honorable ya girgiza kai "abin kuma harda zolaya?"
Abdulkarim bai ce komai ba. Ba kuma zai ce ba har sai yaje gidan ya ga 'yan matan da ya sani a baya tun suna yara. Kudurcewa ya yi a zuciyarsa indai ba rashin tarbiya wanda baya tsammani ya gani ba ko su suce basu son aurensa ba zai nemi guda.
Mardiyya da Sauda ne tare da Suhaib da Lilu tsaye a jikin motar Abbati. Sun rako su bakin mota shi da Munzali bayan sun shiga sun gaisa da Mami Khadija. Mama Nasima bata nan kuma Mardiyya sai addu'a take yi su yi su bar gidan kafin ta shigo. Sau biyun da ta zubar da kimarta a gaban Munzali bata yi a gaban yayyenta ba. Ba kuma ta son a fara daga yau.
Hirar motoci suke yi wadda Lilu da Munzali ne karfinta.
Lilu ya shafa motar yana binta da kallon bege
"Ni dai ba don yau za ku tafi ba ai da na dana ko zuwa karshen layinmu ne in kashe arna."
Keyarsa Suhaib ya kwade ya kuma ce idan bai kama kansa ba sai ya fadawa Mami. Mardiyya da Sauda zasu yi dariya ya hade rai zai yi kaza huce kan dami.
"Wai me ma ya fito daku ne? Wurinku suka zo? Ku koma ciki."
Munzali ne ya shigar musu domin Abbati kamar baya wurin. Hankalinsa yana kan hanya yana dakon ganin ta ina Farha za ta bullo.
Da sauri Munzali ya ce "Ya za ka korar min kanne?" Dan nesa kadan da inda suke tsaye ya nuna da hannu yana mai cewa "In ganki mana Diamond girl."
Karashen maganar ya yi ne idanunsa a cikin na Mardiyya. Kawar da kai tayi da sauri gabanta na wata irin faduwa ta daban. Bata san yadda akayi yau take jin Munzali a ranta haka ba. Tun dazu take satar kallonsa sai ta ga shi ma ita yake kallo.
Juyawa tayi za ta gudu saboda kunya Sauda ta rike mata hannu. Shi kuma gogan ya basar kamar ba daga bakinsa maganar ta fito ba. Abbati ma dake son tambayarsu game da Farha amma ya kasa sai da yaji kunyar.
Wato duk yanzu halinsu yake fitowa game da mata da suka hadu da wadanda suke so.
Suhaib ma dai daskarewa ya yi don kusan yafi kanwar tasa jin kunya. Gyaran murya ya dinga yi ba kakkautawa don ya kasa magana. Lilu kuma ya dinga kikkifta idanu na shakiyanci sannan ya ce,
"Diamond dai da na sani mai shegen tsadar nan ka kira Mardiyya?" Hannu ya sakalo a kafadarta ya tako kusa da Munzali dake ta murmushi ya tsaya da ita a gefensa. Hannuwa ya hada kamar mai shirin daukar hoto yana aunosu ta cikin zagayen da yatsunsa suka bayar. Ya dawo kunnenta yayi magana kamar rada amma kowa na ji
"Baby Sis kin matso mana class wallahi." Ya koma ga Munzali " Kai ma Alh. Munzali ka more. Hummm don ma kada ka ce yabon kai da sai in ce duk 'yan matan Kaduna babu kamar na gidanmu."
Hannun Mardiyya ya fara kamawa suka ti musabaha sannan ya saki ya koma kan na Munzali yana faman murmushi gami da nanata kalmar "congratulations."
Suhaib ji ya yi kamar ya daga shi a kafada su bar wurin. Lilu ba ya jin magana ya ce a ransa kafin kuma a zahiri ya biyo shi. Zillewa Lilu ya yi bai bari ya kama shi ba ana ta dariya.
"Baka da kunya ko kadan." Suhaib ya furta yana fuskantar bangaren Abbati. Nauyin Munzali ne ya kama shi saboda a gabansu yake yiwa Mardiyya wani irin kallo. Gashi sun girme shi sosai balle ya yi irin jan idon nan na yayan budurwa.
Abbati kafadar Munzali ya ture da tasa har sai da yasa shi rankwafawa yana mita.
"Munzalin ma ai ba kunyar gare shi ba da ya yi mata magana a gabanmu."
Daure fuska Munzali ya yi cikin wasa yana hadawa da hararar Abbati.
"Ai dama ba ayi maka gwaninta. Sharar fage nayi maka don duk su watse kafin ta fito."
"Wa?" Lilu da Suhaib suka hada baki wurin tambaya.
"Ya Farha" Sauda da Mardiyya suka basu amsa a tare.
Suhaib bai san lokacin da wani irin murmushi mai cike da tsantsar annashuwa ya bayyana akan fuskarsa ba. Farha ce yau da kunnuwansa yaji ance namiji yana jiranta? Ganin murnar na neman yi masa yawa kuma bashi da tabbacin me yake faruwa sai ya ce,
"Yanzu duka nan dama zance ku ka zo ba daukar mota ba?"
Sauda da Lilu har ma da Munzali sai dariya.
"Diamond girl kanwata ce kuma abokiyar shawara ko?" Munzali ya yi magana yana kannewa Mardiyya ido sannan ya dora da cewa "wasu ne dai har a cikin bacci za ka ji suna kiran Ya..."
Bakinsa Abbati ya rufe da hannu su Lilu aka sami nayi sai dariyarsu suke. Munzali na kokarin kwatar kansa Abbati kuma yana faman yi masa alkawura akan idan ya kama bakinsa zai cika masa su.
"Zan tuka motar har Kano!" Ya fadi abin da ya san zai yiwa Munzali dadi.
A take Munzali ya daina kokarin janye hannun Abbatin ya nutsu. Yana sakinsa yasa dariya. Da gaske wautar Abbati bata wani buya lokuta da dama.
"Riba biyu kenan. Kaga dai kowa ya fahimci menene baka son na fada. Alkawari kuma dole ka cika tunda ban fada da bakina ba" Mukullin ya dorawa Abbati a tafin hannu ya yafito Mardiyya da hannu.
"Kina ta sani dibar kunyar Ya Suhaib kuma kin ki zuwa."
Gate din gidan aka wangale direban Alh. Tahir ya shigo ciki. Wurin ajiye nasa motocin ya dan yi nisa da inda yake hango 'ya'yansa da wasu baki biyu suna dariya. Motar da ya gani a kusa dasu kuma a bude ce tasa ya gane su waye. Mami Khadija bata tauye masa hakkinsa na maigida ba, ta sanar dashi game dasu tun ranar da suka ajiye motar a gidan.
"Ga sirikinku nan" cewar Lilu yana yin gaba wurin mahaifinsa.
Mardiyya da Sauda ma da sauri suka mara masa baya suna kiran "Abba" tamkar wanda ya yi tafiya. Kafin su karasa ya ware hannuwansa ya rungume kowacce a bari daya. Kirjinsa yaji ya takure saboda rashin Farha. Indai su uku suka zo tarbarsa to ita a bayansa take tsayawa ta riko wuyansa da hannuwanta biyu. Daga nan haka suke raka shi har daki. Wani lokacin ma su taya shi cin abinci. Lilu kuma idan yana gida shi yake dauko masa jaka da wayoyi. Yanzu ma ya dauko harda babbar rigar da ya bari a motar ya ratayota a kafada. Tun tashinsu Suhaib baya zuwa sai suke ganin kamar irin abin nan ne na babban yaya. Farha kuma tunda taga bidiyon nan take kirkirar abin da zai hanata fitowa idan ya dawo ko ya aika a kirata.
Yanayin soyayyar uban da 'ya'yansa ya burge Munzali da Abbati matuka saboda basu tashi a haka ba. Gara ma Abbati ya san nasa mahaifin yana dan kokartawa amma babu zancen wata runguma ko sakin fuska makamanciyar wannan. Duk ranar da suka kwatanta haka karshenta Mal. Sa'idu sai ya tsire masa uba. Shi kuwa Munzali ina ma suka hadu balle a nuna an damu dashi.
"Manyan yayye basa zuwa oyoyo?"
Munzali ne ya tambayi Suhaib amma Abbati ne ya lura da yanayinsa a lokacin da yake bayarda amsa.
"Mu ai mun girma an barwa kanana"
Ba da niyar nuna musu komai ya yi ba amma bakidaya annurin fuskarsa ya bace. Irin kallon da ya yiwa mahaifin nasa ya kawar da kai Abbati ya kasa fassarawa. Kamar kallon tsana, kiyayya ko jin haushi. Kallo mai nuni da cewa akwai wani kwamtaccen abu na bacin rai tsakanin uban da d'ansa. Bai bar tunanin ma ya zauna masa ba ya kawar dashi ta hanyar sakin fuska suka karasa wurinsu shi da Munzali.
Da fara'a ya tarbesu ya kuma dinga jansu da hira. Dama ransa a bace yake daga office amma ganin yaransa kadai ya wanke masa komai. Wata sabuwar ma'aikaciya suka dauka shi ne daga zuwanta ta fara nuna masa alamun tana so su kulla mu'amala. Matsalarsa da Farha ta janyo masa rashin kwanciyar hankalin neman yarinyar duk da ya kwadaitu da ita tun farkon zuwanta. Abin da ya bashi haushi kuwa bai wuce kukan da ta saka masa a office ba bayan ta gaji da dabarunta ya daka mata tsawa ya ce ta fita.
"Amma sauran duk sun ce ba haka kake yi musu ba. Ni me na rasa?"
Wannan magana ta hana shi hadiyar yawu a lokacin saboda dacin da ya taso masa. Sauran da take nufi ba wasu bane illa matan kamfanin nasa da ya nema a baya. Kenan duk kudaden da yake kashe musu da gargadin su rike bakunansu ya tashi a iska. Suna hirar da juna harda yi masa cune...in ba cune ba ta ya akayi yarinyar ta san ta nemi jan ra'ayinsa tunda ba shi ya fara nemanta ba? Har suka iso gida yana tunanin mutum nawa aka fadawa? Mutane nawa ne suke yi masa kallon tsirara mara kima ba tare da ya sani ba?
Farha da baya tsammanin gani a cikinsu ya tambaya Sauda ta fada masa tana gidan Mama.
Ba shi kadai yaji babu dadi ba harda Abbati da suka yi alkawarin haduwa yau.
Alh. Tahir murmushi ya yi ya ce "ta fi ku dokin bikin nan naga alama."
"Abba bata fada maka za ta tafi ba?" Mardiyya ta tambaye shi don tayi mamakin tambayar tasa.
"Yau meeting muka yi tayi amma naga missed calls dinta zan kira."
Sallama ya yiwa su Munzali ya wuce nasa bangaren kafin a kara wata tambayar da za ta fallasa karyar da ya musu. Abbati kam jikinsa ya yi sanyi tunda bata sanar dashi ba kuma ta san zuwan a yau dominta ne. Farha ta fi karfinsa ta kowacce fuska idan ya dubi tarayyarsu. 'Yar masu kudi duk da dai ya san indai don kudi ne ba zai wahala ba. To amma cikakkiyar 'yar boko ce mai tsaftataccen asali. Sirrin rayuwarsa ya sanya bai sami damar jin bacin ran kin fada masa ba. Zuciyarsa dai ta raya masa cewa bashi da wannan matsayin. Tunani ne ya yi masa yawa sai kawai ya yi sallama dasu Suhaib ya shige mota bangaren direba . Munzali dake son magana da Mardiyya sai ya fasa ya ce zai kirata.
"Mutumina kayi hakuri. Karshenta inda taje din ba za ta iya haduwa da kai ba shi yasa bata fada maka bata nan ba ko ta ce ka biyota" Munzali ya fadi a kokarinsa na kwantar masa da hankali bayan ya zauna.
Da sanyin jikin da bai so ko Munzali ya gani ba ya ce "Kar ka damu."
Suna tafiya Suhaib ya tafi wurin Mami Khadija. Albishir ya yi mata don yafi kowa sanin damuwarta akan Farha.
"Amma Mami yarinyar nan don wulakanci sai ta tafi gidan Mama bata fada masa bata nan ba? Wallahi duk yadda yaso boyewa sai da na gane rashin jindadinsa."
"Ai kuwa zan gamu da ita. Ta barmu da damuwa Allah Yasa ba ita take korarsu ba muke tunanin su suke kin zuwa."
Zancen yana da mata da kuma tsoron kada a sami matsala a gaba ta fara yi masa suka shiga wata hirar daban.
A waje kuwa sai da kowa ya tafi sannan Lilu ya nufi dakin Abbansu da kayansa da ya dauko a mota. Tunawa ya yi da katin daurin auren wan abokinsa a dakinsa ya juya. Ya san ba zuwa zai yi ba tunda rana daya ne da na kanin Mami da za ayi a Kano. Duk da haka amintarsa da abokin nasa tasa yana son Abban nasa ya sani kuma ya kira baban angon ya masa fatan alkhairi.
Akan gadonsa ya ajiye kayan Alh. Tahir ya bude durowar gaban madubi ya dauko envelop din katin. Jakar office din ya fara dauka sannan wayoyin. Ya dago babbar rigar biruka da wallet suka fado daga aljihun jakar. Guntun tsaki ya yi na bata lokaci ya duka ya daukosu. Hannu kawai ya zura a aljihun ya mayar dasu sannan ya kama zip din zai ja sai yaji ya rike yaki motsawa. Jibge kayan hannunsa ya yi ya juyo da jakar yadda zai ga zip din da kyau. Abu ne kamar takarda ya makale yasa taki zuguwa. A lokacin da ya zube kayan hannunsa akan gadon ne wayar Alh. Tahir wadda yake amfani da ita wurin kiran 'yan matansa ta fado daga aljihun babbar rigarsa. Lilu bai kula ba ya gama gyara zip ya kwashe wayoyin da yazo dasu a hannu ya yi gaba.
Alh. Tahir bai tashi sanin wayar bata nan ba sai dare bayan Jiddo mai girki a ranar tayi bacci. Hankalinsa kuwa a take ya tashi. Ko a office ba zai so barinta ba saboda gudun fadawa hannun da zai ji kunya, ballantana kuma gida. A daren nan wurin daya saura ya fita yaje motar ya dudduba tunda ya san a hanya ma ya amsa waya da ita.
Motsin wucewarsa Lilu yaji a lokacin yana kallo ya tashi ya leka taga. Ya yi mamakin me Abban nasu yake nema a mota a daren. Kamar ya fita tambayarsa sai yaga ya koma. Laptop dinsa ya kashe ya kade bargonsa ba tare da kula da wayar da ta fado daga kai ba ya haye gado ya kwanta.
Wurin karfe tara ya fito zai tafi makaranta yaga Alh. Tahir tsaye da jallabiya ga direbansa yana ta bankade mota yana dube dube. Karasawa ya yi ya gaishesu duka.
"Abba me ake nema ne? Jiya ma cikin dare na ganka kana duba motar nan."
Murmushin dole Alh. Tahir ya yi saboda kada ya nuna ya damu da wayar.
"Babu komai jeka abinka" ya ce masa. Shi kuma direban ya ce "wayar Alhaji" a lokaci guda.
"Abba ka duba. Jiya duka wayoyinka na kawo maka daki."
Kamar gaske Alh. Tahir sai ya saki fuska "bari naje na duba. Sai ka dawo."
Ana rufe gate din gidan ya dawo da idanunsa da suke nuna tsantsar bacin rai ga direbansa. Hankalinsa ya matukar tashi.
"Idan wayar nan ta fada hannun wani saboda sakacinka a bakin aikinka."
Direba cigaba da bincike ya yi yana mamakin wannan abu. Shi ko kalar wayar ba zai ce ya sani ba amma an dora masa laifin batanta.
Ana gobe zasu tafi Kano Mami Khadija ta kafa sharadin duk wanda bai gyara dakinsa ba babu inda zai je. Kamun amarya ne wanda aka hada da mother's eve da dinner za ayi a Kanon. Babu mai son a barshi da kallon hotuna yana cizon yatsa. Ita kanta ta san da wa take dama. Lilu ne dakinsa sai tayi da gaske yale gyarawa. Alh. Tahir ya so masu aiki su dinga gyara musu ta ce sam bata yarda ba. Tana barin wurin ya fice daga gidan. Shawarma ya siyo guda biyu manya manya da robobin yoghurt ya shige wurinsu Sauda. Mardiyya ce ta fara jin kamshin shawarmar ta tashi da murna za ta karbi ledar ya boye abarsa.
"Kun dai ji me Mami ta ce. A gyara min palace dina a ci dadi. Bari na saka muku yoghurt din a fridge kafin ku gama."
Da gudu gudu suka bi bayansa. Wasu kaya ya dauka a leda ya tafi dakin Suhaib ya shirya. Dinner din gidansu abokinsa ya tafi.
Sauda ta fada toilet aka bar Mardiyya da uban shirgin kayansa. Tana cikin ninki taci karo da waya a kasan gado. Lilu bai san da ita ba balle ya kula da faduwarta. Daukewa tayi ta jona masa tunda taga chaja a jikin bango. Da suka gama aikin ta kunna masa kafin ta fita. Shi kuma da ya dawo ko bi ta kan wurin bai yi ba ya kwanta saboda gajiya. Da safe bayan sun gama shiri sun dauki hanya Yumna ta dinga kiran wayar.
AFAFFUN...
Flashing ya kai shida Danladi ya yiwa Ayaah. Tsabar kwarewa wasu a ciki ma bata jin karar wayar sai dai taga haske kamar walkiya ya bace. Hakura tayi da son dauka ta kira shi da kanta. Abin da ya fara cewa yana daukar wayar shi ne,
"Gaskiya kuna da matsalar netwok a unguwar nan. Zuwana nan na kira ki ya fi sau goma. Har na fara tunanin turo yaro a kira min ke tunda ba zan iya tafiya ban ga murmushinki ba."
Da sanyin murya ya yi magana. Cikin wani irin yanayi mai sa mutum ya ji kamar ya aikata gagarumin laifi. Ayaah taji babu dadi ta shiga bashi hakuri duk da a bangare guda tana cike da farinciki game da kalamansa. Da ya nuna mata kamar komai ya wuce sai ta ce ya ajiye mota a bayan layinsu za ta zo nan ta same shi.
"Yanzu Babanmu ya kira Anti cewa yana hanya tare da bako. To ban sani ba ko bakon da zai kai ciki ne ko mai tsayawa a soro. Kuma kaga baku taba haduwa ba zai fi kyau ku hadu yana shi kadai."
Cije lebe Danladi ya yi ransa na kuna. A soron nan nasu mai dan duhu ya so ya fara koya mata gurbatacciyar soyayyarsa. Gashi bai sami motar da tayi masa a garejin ba. A ina zai sami wannan damar idan suka hadu a filin Allah? Da muryarsa da ya kware wurin kwantarwa domin ya sanyawa 'yan mata tausayinsa ya yi mata magana.
"To babu komai Ayaah. Ba zan so na takuraki ko na sanyaki cikin yanayi mara dadi ba. Banda zuciyata da ta kasa sukuni saboda tunaninki da na hakura sai lokacin da kike so na zo."
Numfashi taja wanda ya bashi damar yin murmushin samun nasara tun kafin ta furta ta bakinta. Yadda yaso haka ta ce za ayi. Duk da tana jin nauyi haka ta daure taje ta fadawa Hasiya za tayi bako. Murmushi Antin tasu tayi gami da 'yar tsokana.
"Gilashi zan saka domin na tantance ko ya cancanci zama surukina. To amma wani hanzari ba gudu ba. Ki bashi hakuri ya jira zuwa gobe. Kinga Babanku yana hanya da bako."
Ko kadan Ayaah bata son batawa
Dani rai. A tunaninta zai fassara rashin sauraronsa daidai da abin da yake fada mata matarsa tana yi. Zai shiga damuwa idan basu hadu ba kuma bata son haka.
"Anti ko inje gidan Mal. Tasi ya sameni a can sai na bashi hakuri tunda ya riga ya zo?"
Katangarsu daya da ta gidan Mal. Tasi din. Yadda ta marairaice fuska sai Hasiya ta amince. Dakin Abbas ta koma suna hira da Murja mai bashi abinci. A zuciyarta take tunanin lallai Ayaah tana son bakon nata. Za ta sanar da Honorable tun wuri ayi binciken da ya dace.
Ayaah kuwa da saurinta ta sake kiran Dani ta fada masa inda zasu hadu. Ba haka yaso ba amma ya fiye masa waje. Tana cikin gaisawa da matar Mal. Tasi tare da fada mata abin da ya kawota taji sallamarsa. Wani iri ta dan ji tunda ta zata zai kirata ne. Da babu alaka mai kyau tsakanin gidan da nasu kuma ba ayi mata izini ba haka zai zo kenan? Ta tambayi kanta. Haka nan dai ta tashi da ledar da ta sako madaidaicin filas din da ta zuba masa abinci. Tana doso soron kamshi ya dinga hawa kanta. Yau ma turaruka 'yan duri ya bulbula sai dai hannu ya so zarcewa. Kamshin ya yi yawa har yana neman sakawa mai shaka mak'ak'in wuya.
Suna hada ido ta manta da komai sakamakon murmushin da ya sakar mata. Yana da nashi kyawun amma babban abin da ya zame masa jari bai wuce yanayin jikinsa ba. Ga tsayi ga kaurin da bai kai a kira shi kiba ba. A idonta gani tayi kamar ya fad'a. Haushin matarsa ya kamata. Ta yaya mace za tayi sake mijinta ya dinga ramewa saboda rashin kulawa da abinci?
"Mom dina tana gaishe ki"
Rausayar da kai tayi gefe tana murmushin jindadi ta ce "ta sanni ne?"
Dariya ya yi mata yana mai cewa babu wani abu nasa da mom din bata sani ba.
"Idan ta dawo daga Dubai har gida zamu je ki gaisheta."
Ayaah sai tayi murmushi. Ina ita ina zuwa gaishe da uwar saurayi? Ba Anti Hasiya da Babansu ba ko su Anti Fati da kakarta Larai sai sun kusa yankata. Yawo ba tarbiyarsu bace. Idan ya sake tayar da zancen a gaba za ta kirkiro hanyar fitar da kanta don babu inda za ta je.
Ledar hannunta ta mika masa ya dinga godiya da shi mata albarka. Harda cewa wai ya akayi ta san yana jin yunwa? Filas din wan can karon da na yau ya yi mata alkawarin kawowa duka a washegari.
Wurin karbar ledar ne ya samu ya hada da hannunta ya matse. Gabanta taji ya yi mummunar faduwa taja hannun da sauri amma ta kasa kwacewa saboda ya rike gam. Ja ta sake yaki saki sai ma wani irin shafawa da ya dinga yi a hankali yana mai bin kwayar idanunta da kallo da nasa da suka yi alamun tausayi. Ilahirin jikinta babu inda baya rawa kamar mazari. Cikin dabara ya rage tazarar dake tsakaninsu.
"Ki dago ki kalleni Ayaah" ya ce a kasalance.
Kasawa tayi sai girgiza kai da take yi tana son cewa ya saketa. Danladi sai ya saka yatsunsa biyu ya dago kanta. Runtse idanu tayi da sauri taji ya yi karamar dariya.
"Kunya ki ke ji? Gashi ni kuma mutum ne mai son kulawa. Kulawar da na rasa a gida. Ina fata da addu'ar ki cike min wannan gurbin ki hanani tunawa akwai kowacce mace bayan ke. Idan kin amince min zan yiwa Mom magana kawunnai na su zo ganin Baba."
Runguntsumi sunan abin da Danladi ya yiwa Ayaah domin yaji dadin isar da mummunan kudurinsa. A lokacin da yake son bude mata ido da haramtacciyar mu'amala ya kama zuciyarta a hannu ta hanyar nuna mata yana sonta. Banda haka ya hada da maganar aure da mata ke so a wannan zamani. Sannan ya rufeta ruf da ya nuna mata cewa za ta zo gidansa a matsayin mai share hawaye. Wannan tunani ke sanya mata mugun tausayin namiji da ganin ba zai rayu babu su ba.
Da kyar ta iya mallakar tunaninta ta ja jikinta baya. Muryarta ko fita bata yi sosai ta ce,
"Ka sakar min hannu don Allah. Kaga babu kyau."
"Nima ba zan so yin abu mara da ke ba. Kiyi hakuri" ya ce yana sakin hannun.
Ko sallama bata yi masa ba ta fita daga soron. Ya kwashe da dariya
"Kin kusa samuwa."
Ficewa ya yi abinsa da ledar abinci ya tafi gida. Yana zuwa ya bawa Raiha yana wani cin magani.
"Sai ki saki ran ai. Baki san irin kokarin da nake domin samar muku abinci ba. Don na karbi darin dazu ki ke ta kumbure kumbure. Ki zuba min ku ci sauran"
Bude filas din tayi ta ganshi shakare da abinci sai kamshi yake. Cikinta ya bada wani uban sautin yunwa. Da sauri ta samo faranti ta dibar masa sannan ta taso yaranta tana basu tana ci. Tambayar inda ya samo abincin bai zo mata ba don ta zata sayowa ya yi.
A dakin Abbas iyalin Honorable Habu suka hadu ya nuna su ga Abdulkarim wanda tausayin Abbas ya kusa saka shi kuka. Addu'ar samun lafiya ya yi masa tare da jaddadawa Honorable lallai ranar litinin a mayar dashi asibiti. Duk abin da ake ciki a sanar dashi. Hasiya tsabar farinciki sai da tayi kuka. Da zai tafi tayi masa tayin abinci sai ya ce a zuba masa ya tafi dashi. Dan filas din da yake madaidaici mai kyau shi Ayaah ta kai wa Danladi. Aka yi neman duniya aka rasa. Murja sai rantsuwar ta wanke shi take yi. Hasiya ta ce babu komai su bar maganar kada bakon yaji. Na maigidan ta saka a leda aka bashi. Bayan tafiyarsa ne ta rutsa Ayaah a kitchen ta tambayeta inda ta kai shi.
"Lokacin da zaki fita wurin bakonki na ganki da leda da abu kamar shi sai dai ban zata abinci ki ka diba ba shi yasa ban miki magana ba."
Sunkuyar da kai Ayaah tayi. Hasiya ta daure fuska saboda bata so hasashenta ya zama gaskiya ba.
"Na zata mun wuce wannan matakin Ayaah. Kin sani sarai rowa ba halin gidan nan bace amma ba zan lamunci yiwa saurayi girki ba! Wato dalilinki na karbar girkin Ummita kenan? Bai ji komai ba ya karbi abinci a hannunki ko mahaifinki bai taba gaisarwa ba?"
Tuni zuciya ta soma tunzurata. Ba za ta iya jure kalamai marasa dadi a kansa ba. Idan ba a tayata tausayinsa ba ai bai dace a aibata shi ba.
"Anti matarsa ce fa bata girki. Shi ne na zuba mishi ba roka ya yi ba. Bata yi masa komai ko ya roka sai taga dama."
Hasiya sai ta hadiye fadanta ta kirkiro murmushi ganin abin ya girmi abincin da ta bayar.
"Kin kyauta da ki ka taimaka masa amma nan gaba ki dinga tambayata kinji ko? Kuma ki ce lallai zuwa na gaba ya zo mu ganshi."
Ayaah sai murmushi. Tasa hannu ta rufe fuska sannan ta tashi a guje tana yiwa Hasiya godiya. Ita kuwa bayan tafiyar Ayaah daki ta koma ta rafka tagumi. Gabadaya saurayin bai yi mata ba daga jin furucin Ayaah. Maza masu tonawa iyalansu na gida asiri ba mazan kwarai bane mafiya yawan lokuta. Ta kuma fuskanci ya riga ya fara dasa mata wani tunani. Tashi guda idan ta nemi rabasu za a iya samun matsala. Gida za taje suyi shawara da Salima don ta fita fahimtar halayyar yara. Shawarar data bata kwanaki ita ce ta taimaka wurin kara kusantasu da juna.
Ginin shopping mall din su Abbati ya yi nisa. Hankali kwance komai yake tafiya yadda suke so. Ga tafiyarsu Italy asibiti tana ta matsowa. A lissafi nan da kwanaki goma sha bakwai zasu tashi. Suna fata idan an dace babu wani abu da zai yi saura a tare dasu na bukatar jinsinsu. A gefe guda suna cike da farincikin daina jin motsin Shazali. Tun zuwan da Munzali ya yi gidansa ya masa dukan nan akan tafiyar Abbati bai sake nemansu ba. A zatonsu an rabu kenan...
Yau ta kama Alhamis suna site din gininsu tare da masu aiki ana ta lissafin kudaden da zasu kawo domin siyan wasu kayan aikin. Hankulansu sun raja'a kan abin da ke gabansu wayar Abbati ta soma ringing. A hannunsa take ya juyo da ita yaga sunan Farha ya bayyana a screen din. A take zuciyarsa ta doka dan tsalle sai kuma ta koma ta kwanta. Tun zuwansu Kaduna da bai hadu da ita ba yake kiran wayarta a kashe. Yau kwana biyar sannan za ta kira shi. Yana son dauka yana jin tsoron me za ta ce. Muryar Munzali yaji wanda ya zuro kai ta kafadarsa.
"A haka dai kamar za kayi abin arziki amma daukan waya ya gagareka. Tsoron me kake ji ne?"
"Ni kar ka kara min tension ka matsa ka bani wuri" Abbati ya bashi amsa yana kokarin matsawa gefe domin yaji dadin amsa wayar.
"Ita ma fa tana sonka"
Tsayuwa Abbati ya yi ya juyo ya kalli Munzali da murmushi kamar Farha da kanta ta fada masa.
"Ai fa na kasheka da dadi to dauki kada ta kuma tsinkewa" Munzali ya ce yana kara yi masa dariya.
"Kaima ka ce wani abu. Bari na sallameta zan gamu da kai."
Gefe ya matsa don idan Munzali ya saka shi a gaba kila hirar ba za tayi armashi da kyau ba. Yana dauka yaji zazzakar muryarta mai taushi tana magana.
"Ya Auwal"
Shiru...Abbati ya sake nutsewa cikin kogin son Ya Farha.
"Ko dai wrong number na kira?" Tayi tambayar da murmushin da yake kan fuskarta tun lokacin da ta yanke shawarar kiransa da sunan gaskiyarsa idan ya dauki wayar.
"Ki ka ce baki san shi ba" Abbati ya fada a hankali da ya rasa me zai ce.
"Na san shi. Kararsa ma na kawo maka"
Sai da ya jingina da bango ya cigaba da sauraron bayaninta. Korafi tayi masa na rashin nemanta ranar da yaje Kaduna a wurin 'yan uwanta. Ta tabbata da ya yi hakan dole zasu kai shi gidan kakaninta. Ita kuma wayarta ce gida na taro aka nema aka rasa a ranar. Ba ita tayi sabuwar waya ba sai da safe kafin su taho Kano. Kin fadawa Alh. Tahir wanda zai saya mata sabuwa a guje tayi. Sai da safen Mami Khadija ta bata kudi ta saya.
"Kina nufin iskar gari daya muke shaka? Shi yasa yau nake jina daban."
"Uhummm. Wane canji aka samu?"
"Iska mai dadi, gari yana kamshi, zuciya kuma sakayau."
Farha sai ta kama dariyar yadda yake magana. Kwatancen inda suka yi masauki ya nema ta ce ba za ta iya gane komai a hanyar ba. Wata 'yar uwarsu ta samu 'yar gidan da suke tayi masa kwatancen. Hira suka yi inda take fada masa daurin auren kanin Maminsu ne za ayi ta kuma gayyacesu. Hoton IV din za ta tura masa ta whatsapp don bata san unguwannin Kano ba.
"Idan kun fita ki dinga kallon hanya tunda zama ya kusa kawo ki."
Kunya kuwa ta kamata ta ce "Ni sai anjima".
"Mu jima da yawa Ya Farha sarkin kunya. Yau dai tunda bikin na yamma ne ba zan zo ba. Amma gobe da jibi kafin ku koma in sha Allahu zan zo."
Anyi kamu ranar Alhamis din tare dasu Mami Khadija da suka iso ita da sauran yaran. Ranar Juma'a kuma sai bayan magariba za a tafi wurin dinner. Farha ta sami Lilu tayi masa famfo akan ya tambayi Mami ko zasu sami kati guda biyu tunda event din card admit ne. Shakiyanci ya yi mata kuwa son rai tana shanyewa sannan ya tafi wurin Mami. Yana gama fada mata zancen da ya tsara ta girgiza kai tana murmushi.
"Dama kai ai ko ba aiko ka aka yi ba nayi tunanin za ka iya nema musu."
Shafa kansa ya yi yana dariya "wallahi Mami don ba ki yi musu kallon kwaf bane amma sun hadu."
"Allah Ya tsareni da yi musu kallon kwaf" ta ce tana mikewa da dariya. Babu wanda ya san irin farincikin da take ciki sakamakon soyayyar da taji akwai a tsakanin Abbati da Farha.
Sun yi sa'ar samun katuna a wadace daga wurin dangin amarya masu shirya dinar. Hakan kuwa ya faru ne saboda suma zasu yi tasu a Kaduna idan an kai amarya. Yadda suka basu da yawa shi ne aka ramawa kura. Guda biyun ta bashi ya tafi yana murna. Suhaib ya kaiwa domin su ji dadin karbar gayyatar shi kuma ya kira ya fada musu.
Kafin lokacin masallaci dama Munzali yake da nufin zuwa dauko Qibdiyya yau. Tunanin zuwansu dinner din gashi Kande bata dawo ba sai washegari sai ya kira Abbati ya fada masa.
"Kada ma ka fara tunanin soke daukota zuwa gobe. Ko so kake a fara ganin kamar akwai uzurin da za ka dinga fifitawa akanta?" Cewar Abbati yana tsaye a cikin wani bakery. Duk wani cake da ya san tana so ya saya yana jiran turn dinsa ya biya.
Munzali ya sha kunu kamar suna tare ya ce "Ka gama kashewa yayarmu murya ni kuma ka dinga yi min masifa. Ya yi kyau!"
Daga inda Abbati yake har hasko fuskar tasa ya yi. Dariya ya dinga yi masa,
"Ai kaine da wani zance kawai don za ka je tsara budurwa baka son babyna ta bata show."
Shi ma dariyar ya yi "Dadin abun kaima tsarin nan dai zaka je. Tun wuri na fada maka idan mun tafi da ita a wurinka zata zauna ku kare kalau."
Da haka suka yi sallama. Munzali ya kira Mardiyya shi kuma Abbati gudun kada Munzali ya shashantar da dauko Qibdiyyan yau ya kira Zakiyya ya ce mata yana hanya.
Abu ne da suka saba dama. A wajen kaita gidan ko daukota daya daga cikinsu ke zuwa ko suje tare. Tunda Zakiyya ta san da tafiyar tun kwanaki biyu ta riga ta hada mata 'yan kayanta. A can dinma tana da kaya domin dakinta guda. Hatta uniform akwai koda watarana dalili zai sa ba a mayar da ita da wuri ba. Fitowa tayi daga daki tana kwala mata kira domin ta zo ta shiryata.
Duk inda take tunanin samunta ta duba babu Qibdiyya babu dalilinta. Hankalinta tuni ya fara tashi tunda ta tabbatar tare suka shigo gidan daga gidan kitso. Dakin mahaifiyarta ta sake shiga ta gama tashin hankalinta.
"Umma kamar fa bata gidan nan. Kuma ga kofar gida a rufe."
Umman tasu kanwa ga Asabe ta mike ita ma cikin firgici.
"Taso min Daddy ya zo ya fita a dubota. Ba har gara Munzali ya zo ace bata nan ba da wannan Abbatin."
Daddy din kanin Zakiyya ne. Hanyar dakinsa ta nufa da gudu gudu sai gashi tana kama kofar dakin shi ma ya kama ya bude. Wata mayyar jallabiya ce da ya nacewa a jikinsa yana murmushin yake. A gefensa kuwa Qibdiyya ce tayi tsilli tsilli da ido.
Dariyar da bata kai zuci ba Daddy ya yiwa yayarsa.
"Oji-oji (hide and seek) muka yi miki kuma baki kama mu da wuri ba ko Qibdiyya?" Ya furta yana tsare yarinyar 'yar shekara biyar da idanu.
"Eh" ta amsa babu wani kuzarin kirki a tare da ita.
Zakiyya haushi ya kamata duk bata kula da yanayin fuskokinsu masu dauke da labarai iri-iri ba. Hannunta tasa ta tankado kan Qibdiyya gabanta.
"Bana son irin wannan wasan, kada ki sake. Wuce muje ki canja kaya."
Tana sake turata Qibdiyya taji wani irin azababben ciwo ya tsirga ta tsakanin kafafunta.
"Washhh Mama."
Kafin Zakiyya ta gama juyowa har Daddy ya sunkuceta ya yi gaba.
"Daga yi miki wasa sai ki dinga hankadeta? In wasan ne ba kya so an daina yi dake."
"Ku wasa ya dama. Kayanta suna kam gado. Kayi sauri ka shiryata kafin azo daukarta, dama karatu nake Abbatin ya kirani."
Falo ta koma inda ta bar wayarta ta dauka ta cigaba da karanta novel din da aka yi update gabanin wayarsu da Abbati. Bata ji komai ba ta nutse cikin karatun ta bar kankanuwar 'yarta a hannun baligin namiji wai ya shiryata don kawai tana takamar shakikinta ne.
Ba yau ta fara ba. Son jiki ne ko sakaci? Allah Masani.
"Saka mata pant."
"Jeki Uncle Daddy ya yi miki wanka kafin na gama."
"Daddy shafa mata mai."
Aikin Zakiyya kenan. Idan ka bibiya kuma zaka samu ba wani abin kirki ne ya tsareta ba da har kula da tilon 'yarta yake yi mata wahala. Gashi bata son takura. A haka ma don anyi sa a Ummansu tana tsawatarwa duk lokacin da ta gani. Ta kan ce mata wannan zamani da uba yake haikewa 'yar cikinsa bau dace tana sakacin sakarwa kaninta ragamae Qibdiyya haka ba. Kowane dan Adam baya rasa makusa. Wannan dabi'ar ita ce ta Zakiyya.
To shi ma Daddy ba yau ya fara latse 'yar yayar tasa ba tare da barazana. Na yau dinne sai yaso wuce gona da iri. A cikin dakin daure fuska ya yi katamau yana yiwa Qibdiyya kallo mai ban tsoro.
"Kina fadawa wani zan sani kuma sai nasa wukata mai kaifi na yanka wuyan Daddy dinki (Munzali) da Papa (Abbati)."
Girgiza kai tayi da sauri tana mayar da kwallarta. Bidiyo din da yake nuna mata na yadda aka yanka wani mutum ta tuna ta runtse ido
"Allah ba zan fada ba."
"Ko kefa " Ya dan kalli jikinta "babu zafi ko?"
"Uhmm" ta ce da saurinta tana gyada kai.
"Good girl."
Abbati na zuwa Daddy ne ya rakota har mota suka gaisa sannan ya ja suka tafi. Abin mamaki a gareshi bai wuce rashin kuzari ko digo a tattare da Qibdiyya ba. Kafin su isa gida ta cure jikinta a bayan mota tayi bacci.
BIYAR NA YATSUN...
A kafada Abbati ya saba Qibdiyya daya hannun kuma ya dauko ledar kayan ciye ciyen da ya siyo mata suka shiga gida. Hanne tana zaune a falo tana kallo. Ganinsa da 'ya a hannu da kaya bai sa ta tashi ba balle ta rage masa wani abin. Sannu kawai ta ce masa ta mayar da idanunta kan tv.
Ko ta kanta bai bi ba ya shiga dakin da Baaba Mari ta zauna kafin su koma Kirikasamma ya kwantar da ita akan gado. Sama ya haye ya yi shirin masallaci ya sauko har lokacin Hanne bata motsa ba. Shi ya fara yi mata magana yana daura links. Sallahun kula da Qibdiyya ya bar mata ya fita.
Tsaki ta buga bayan taji tashin motarsa. Yadda ya bata mata rai shekaranjiya da tafiyarsu Baaba Mari ita ma ba zai ji dadinta ba kuwa. Sama ta haye ta bar Qibdiyyan har suka dawo. Allah Yasa Munzali gidansa ya shiga da tare zasu ji kukanta tana ta kiran Abbati da Anti Hanne. Ransa kuwa ya sosu ba kadan ba. Yana gama rarrashin ya kaita wurin Munzalin sannan ya dawo ya sameta rai a bace.
"Idan Qibdiyya 'yar cikinki ce haka zaki tafi ki barta ta tashi tana kuka?"
Baki ta murguda bata san ya gani ba ta bashi amsa da rashin kunya.
"Sai kaji in da dadi mutum ya nemi abu aki yi masa bayan akwai halin yin hakan."
Ya fara gane inda ta dosa amma ya kyaleta ta cigaba da magana domin ya tabbatar. Zancen shekaranjiyan ne dai ta tayar. Tunda Baaba Mari ta zo tayi 'yan kwanaki ita ma sai tata uwar ta zo.
"Ai uwa bata fi uwa ba"
Daure fuska ya yi da takaicin halayenta.
"Gwaggo Jumai ba kishiyar Baaba bace kina jina. Haka kawai idan ta so zuwa gidan nan ba zan hana ba. Amma ba zan yarda ki tsiro min da abin da zai iya zama rigima a gaba ba. Zuwan daya ba zai zama dalilin zuwan daya ba."
"To kuwa wallahi...."
Dan murmushi ya yi sannan ya katseta "ki cigaba da biyewa Gwaggo Deluwa ta kashe miki aure."
Gabanta ne ya dan fadi saboda bai yi kuskure ba. Gwaggo Deluwa ce zugata akan cewa ya kamata innarta ta zo ta kwashi romon arzikin gidan. Abbati sai ya sami damar cigaba da fadin abin da yake jin zai taimaka masa ya dan dawo da ita kan hanya.
"Ki bar ganin tana ta cewa ta samarwa 'Yashshafa miji a Kaduna. Idan yaki aurenta kin san ni din dai za a kuma kawowa. Shi yasa take so tayi sharae fage yadda idan can bai samu ba nan din ba za ki kawo musu matsala ba."
"Cabdijan" ta furta cikin bacin rai "amma Gwaggo Deluwa ta raina min...."
Bai tsaya jin sauran sababin nata ba ya sake ficewa yana murmushi. Sai da suka yi magariba suka tashi shiryawa zuwa dinar. Hanne da rawar jiki yana cewa ta shirya Qibdiyya ta kamata tayi mata wanka. Wurin tsarki ne ta kula tana kanne ido sai ta alakanta hakan da zafin ruwan. Tsaf ta shiryata cikin riga da skirt na lace tayi mata dauri. 'Yar kwalliyar da taso yi mata da ja gira a hada da jambaki da foundation ba tun yau Abbati ya hana ba. Ya kan ce mata komai da lokacinsa. A bar yarinya taci kuruciyarta idan ta isa adon ba sai an koya mata ba.
A mota kwanciya Qibdiyya tayi a jikin Munzali, Abbati kuma yana tuki.
"Wai ni baka ga canji a wurin Mamana ba? Dan taba wuyanta ko zazabi take yi? Shirun ya yi yawa."
Dago kanta Munzali ya yi ya taba wuyan da goshi.
"Babyn Daddy akwai inda yake miki ciwo?"
Kamar ta nuna masa sai ta tuna kashedi ta fasa. Yanzu ma dai da sauki sosai tunda bai yi mata mai gabadayan ba. Firgici ne ya zauna mata a rai ta rasa walwala saboda bidiyo din da Daddy ya nuna mata. Kai ta girgiza ta sake kwanciya.
Gajeren tsaki Abbati ya yi yana cewa "ka gani ta sake kwanciya ko? Kawai kar mu dade mu biya a dubata. Ni dama saboda shirun ne ma nace mu fito da ita ko ta sha iska."
"Nifa ba soyayya muke ba" Mardiyya ta sake nanatawa Farha da Sauda mai bada labari.
"Shi yasa naji yana kiranki Diamond girl" Sauda ta fada tana harararta ganin za ta raina musu wayo.
"Saboda a diamond plaza muka hadu ko kun manta?"
Sauda bata hakura ba ta sake cewa "Amma ai ke ya fadawa zasu zo da 'yarsu."
"Saboda yaga kamar na fiki son yara ne."
"Tunda a rubuce yake a goshi ba! Ke dai idan biki ya tashi kada ma ki nemeni don ba zan miki komai ba tunda tsakaninmu an fara boye boye."
Farha dariya tayi yadda suke hararar juna kowacce tana son a yarda da zancenta. Su ukun sanye suke da skirt da riga na lace fari da purple. Kowacce kamar sauran 'ya'yan dangi taci gwaggwaronta da kwalliya irin ta zamani saisa-saisa. Dokar Maminsu kuma ta tabbata a kansu don bata yarje musu yawo babu lullubi ba saboda biki.
"Duk wadda ta ajiye tarbiyarta tayi yadda take so a bayan idona Allah na kallonta."
Da haka ta kashe musu jiki domin da fari har Sauda da Mardiyya sun fara son bin sahun 'yan mata 'yan uwansu. Da suka kiyaye mutumcinsu kuwa sai suka dinga jinsu a sama a wurin bikin sabanin marasa mayafi. Sun yi matukar kyau kamar a daukesu. Hankalinsu kwance basu da damuwar komai. Jiddo da Mama Nasima ma duka sun zo saboda biki dai na kanin Alh. Tahir ne ko bai auri Mami Khadija ba.
Inda suka zauna ma dai taron 'yan uwa ne daga masu sabbin goyo sai marasa aure anata hira. Kiran Abbati da sanarwa Farha da ya yi cewa sun iso ya kara karfin shewarsu.
"Farha da saurayi? Lallai yau zamu yi farin gani a wurin nan." Cewar wata sa'arta wadda a yanzu take da ciki na biyu.
Idanu suka dawo gareta kowa na fadin albarkacin bakinsa. Abin ne da mamaki saboda duk lokacin da ake haduwa irin haka ana hirar samar sai dai tayi murmushi. Idanu suka saka mata suna jiran ganin waye ya ciri tuta. 'Yar kwallarta ta samu ta danne saboda ganin yadda suke ta murna. A baya din ma basu san babu bane ba wai tana boye shi ba.
Zuga guda ce ta biyo su suka tsaya daga bakin kofar shiga inda ake nuna kati ana jiran su shigo da bakinsu. Farha da ta fisu tsiya sai ta fadawa Lilu ta ce ya shigo dasu. Idan akwai saukin mutane ma ya fara kaisu su gaisa da Mami Khadija. Shi kuma sai ya kira Suhaib saboda katinansu suna wurinsa.
Ba tare da wata shan wahala ba Danliti ya iso venue din da Anti Jiddo ta fada masa ya zo ya sameta. Yau bai yi karambanin daukar motar garejinsu ba saboda ta san ko shi waye. Gara ma ya nuna mata fakirancinsa da kyau domin ta kara sakar masa bakin jaka. Yana sauka daga adaidaita sahu ya kirata ta fito waje. Ba karamar kwalliya tasha ba. Mayafinta a kafada daya ta rataya shi sai karamar jaka a daya hannun. Ba ciki take son su shiga ba. Hasali ma idan ta sami faraga so take su dan zaga hotel kafin a tashi daga taron. Shi yasa ma ta san yadda tayi Alh. Tahir ya yarda aka taho da motarta. Dan kanwarsa ne ya tuko kuma ana zuwa ta karbe mukullinta.
(ZINA kenan. Ma'abocinta baya taba cin bulus. Da wuya ne idan bata dawo jikinsa yadda zai yi masa ciwo ba.)
Kasa dauke ido daga kallonta Danliti ya yi har ta iso tana girgiza masa jiki.
"Ka san kana so amma nake turo maka hotuna kana ja min aji" Jiddo ta furta tana kashe masa idanu.
Busassun labbansa ya lasa cike da shu'umanci a zuciyarsa ya ce "ba so ne bana yi ba karfina kawai aka fi."
A kagauce ta ce "Akwai inda zamu iya zuwa kurkusa don na dawo da wuri?"
Da ka ya amsa mata saboda irin kallon da take masa da motsin jikinta duk sun hargitsa masa lissafi.
Danna remote tayi motarta dake gefe tayi kara alamun lock din ya bude. Da ido ta nunawa Danliti ya shiga tana wani irin kakkashe masa idanu kamar wadda ta sha kayan maye.
Danliti ya kama hannun kofa zai bude kenan Suhaib ya isko su. Ta gabansa Anti Jiddo ta fito tana waya da Danliti ya zo bata kula dashi ba. Fitowarsa kenan zai shigo dasu Munzali. Uzurinsa yaso karasawa da ta wuce sai dai karairayar da ya hango tana yi da girgiza jiki ya matukar kada hanjinsa. Yau ko mahaifinsa ne baya jin akwai dacewar tayi haka a gabansa a waje irin wannan ba. Jikinsa ya yi matukar sanyi da yaga irin kallon da Danlitin yake binta dashi shi ma. Maganganunsa basu isa kunnuwansa ba sai dai ganin suna neman shiga mota ya karar da hakurinsa. Baya son dasa musu zargi bisa hasashe amma duk da haka baya jin zai iya dauke kai.
"Anti Jiddo ina zuwa haka ana ta nemanki a ciki."
Sakin mukullin tayi ba shiri sakamakon gumin da ya karyo mata ba shiri har tafin hannu. Daburcewa tayi gabadayanta ta juyo.
"Me ya fito da kai ana tsakar taro Suhaib?"
Kallon tuhuma ya yi musu duk suka ji kamar ya yi musu tsirara a waje.
"Baki gareni zan shiga dasu."
"Oh...to sai ka dawo." Anti Jiddo ta ce da murmushin yake tana fatan ba zai yiwa Danliti magana ba.
"Kai kuma fa?" Ya ce da Danliti fuska a murtuke.
"Am, ammm"
Wani mugun kallo Suhaib ya dinga yi masa sai ya rasa abin fada duk kwarewarsa a karya. Anti Jiddo da ta san koma meye ita ce a ruwa sai ta ce makanike ne zai duba mata mota.
"Waye ya turo miki shi?"
Tambayar ta fito babu digon fara'a a fuskar Suhaib gareta.
"Kawata. Eh kawata ce ta turo shi." Ta amsa da rawar murya.
Hannu kawai ya mika mata "bani mukullin naki. Idan na raka bakin ciki sai na bi shi. Gani ga Lilu ace kin tafi gareji a daren nan Abba ma ba zai barmu ba."
Jikinta sanyi ya yi ga wani irin bacin rai da yake cinta. Danliti zuciyarsa kamar ta fado don tsoro. A haka ya daure ya ce,
"Kawo na tayar na fara dubawa kafin ka dawo. Idan dole sai mun je garejin zan gani."
Shiga motar ya yi ya tayar ya shiga danna totir ya leko da kansa da ya jike da gumi.
"Ina jin ma ba sai mun je ba." Ya dubi Anti Jiddo "Hajiya bakin mai kawai za ki canja."
A firgice ya mikawa Suhaib mukullin ya kara gaba ko waige babu. Suhaib ma sai ya bawa Anti Jiddo ya tafi inda su Abbati suka yi parking ko kallon kirki bai kara yi mata ba. Kwafa kawai tayi tana tsine masa a ranta. Uban da ya haife shi ma yawo yake bata ga wanda zai hanata more rayuwarta ba.
Gaban Farha ne ya fadi da su Abbati suka shigo hall din. Bata jin rashin samun masoyi da wuri ne yasa take ganin ya burgeta a komai. Yanzu kam shigarsa take kallo. Kayansu iri daya da Munzali. Yadi ne ruwan toka anyi musu dinki mai gajeren hannu. Kawunansu da hula ita ma iri daya babu bambanci. Wurinsu Mami Khadija Suhaib ya fara kaisu suka gaisheta. Lilu yana wurin ya dauki Qibdiyya wadda take makale a hannun Abbati yana tambayarta sunanta.
"Lilu sarkin yara. Tun yanzu zan fara yi maka addu'ar bibbiyu da uku uku." Cewar matar wani kanin Mami din.
"Ai kuwa matata ba sai ta dauko mai raino ba Anti. Ta dauki daya na dauki daya."
Mami Khadija ta girgiza kai tana kiransa mara kunya su Abbati suka yi murmushi. Iyayensa dake wurin kuwa dariya suka dinga yi masa anata tuna kuruciyarsa da yadda yake daukar musu yara yana musu wasa.
"Kaisu su zauna mana" Mami ta ce da Suhaib wanda ya kafe Anti Jiddo da ido a inda take zaune.
Bayan sun zauna Lilu ya kira Farha ya kwatanta mata inda suka zauna. Tare suka mike da yan uwanta har mutum hudu. Duk yadda taso sai da suka bi bayanta suna dariya.
"Gashi can mai sajen" Sauda ta nuna musu shi.
Kan kace meye wannan sun riga Farha isa. Kunya ta kamata da taji suna ta yi masa tsiya.
"Allah banga laifinki ba Farha. Wannan da ya bayyana da wuri ai da tuni an miki kwace." Wata mai baki ta fada.
Abbati kuwa sai ya kada baki ya ce "ba zan kwato ba fa. Ni nan sai Ya Farha."
Kafin kowa ya farga Suhaib ya bar wurin saboda wata irin shewa da suka saka. An tara masu baki ne a wurin wadanda duk taro sune iyayen zance. Farha kamar ta nutse a kasa ta juya zata bar wurin.
" 'Yan uwanmu kunga ban gama shigar da kaina ba kuna neman korar min ita ko Mun...."
Yana waigawa babu alamun Munzali a wurin sai Lilu da yake bawa Qibdiyya meatpie. Ashe wurin zama daban ya ce Mardiyya ta sama musu tun kafin su shigo. 'Yan matan suka gama dariyarsu suka watse. Ya rage su hudu har Qibdiyya.
Lilu ma sai ya mike ya dorata akan cinyar Farha.
"Zan bika" ta ce da sauri tana daga hannuwa.
(ABIN LURA: Yaran da kan gamu da sharrin makusanta ta fannin fyade ko koya musu munanan dabi'u sukan saba da abin fiye da tunanin iyaye. Ba ranar Daddy ya fara taba Qibdiyya ba sai dai ranar ne ya fara nufin zarcewa. Wannan ne ya haddasa masa tsoronsa har ta kaishi ga yi mata barazana. Idan uwa bata kula da 'yar alawa da biskit kadai ake toshe bakunan yara musamman masu wayo ace kada su fadawa kowa. Ba tare da sani ba kwakwalwar Qibdiyya ta saba da abin da Daddy yake yi mata. Lilu da yake kusan tsaransa kuma lokaci guda ya jata jiki sai wancan abu yake neman tasiri a kan karamar yarinya. Gani take abin da Daddy yake mata shi ma kila zai yi. Kuma tunda ya fara da kyautatawa me yiwuwa ba zai kaisu da zancen yanka iyayenta ko ya yi mata mai zafi ba.)
Girgiza kai Lilu ya yi ya bata hakuri cewa zai je ya dawo ne sai ga Sauda tazo ta dauketa.
Shiru kan Farha yana kasa haka kawai take jin kunyar Abbati fiye da ta kullum. Nasa shirun bashi da nasaba da kunya sai nazarin yanayinta. Zuciyarsa ce take kara nanata masa lallai yabi a hankali saboda ba lallai bayan anyi binciken asalinsa a mallaka masa ita ba.
"Ya Farha dago kanki muyi magana"
Kayan daki gabadaya Uwani tasa Mubasshir fitar mata wurin neman kudadenta. Ko digo bata zargin Salihi saboda haka bai taba faruwa ba. Mubasshir din kuma ta san da wuya yake shigar mata daki. Tafi yarda da cewa wuri ta canja musu amma har yanzu shiru. Ga dadin bakincikinta yadda Ummule take tararta gaba da gaba babu shakka ko tsoro. Da taga wankin hula yana neman kaita dare kawai sai ta nemi Habibu. Ta kikkira wayarsa a iya kwanakin da take neman kudin bata samu ba. Shi ne yau kawai ta same shi a office.
"Hajiya, Hajiya" ya dinga yi mata kirari tun kafin ta iso gabansa.
Murmushi tayi kanta na fashewa ta sami wuri ta zauna. Bayan sun gaisa ta bijiro masa da bukatarta. Kudinta take so na Hajji ta fasa zuwa. So take ya bata taje ta karasa gyaran gida ta tashi.
"Ikon Allah. Metiron lafiya kuwa? Wannan indai ba fitar rabo ba waye ya taba fasa Hajji saboda gyaran gida?"
Cike da bacin rai ta ce "ba za ka gane bane Habibu. Wai ni Salihi ya yiwa kishiya? Kishiyar ma kuma wai gida daya zamu zauna. Bana son yin wani tashin tashina dasu domin nafi karfin haka. So nake ya gani a aikace cewa na haifu cikin uwa da uba. Sannan wannan aikin ba gumin banza nake fitowa nayi ba."
Yawu ya hadiya. Ta ina zai fara nemo wadannan makudan kudade yanzu? Dama jira yake a fara kiran maniyata ya samfe ba za ta kara jin duriyarsa ba sai an gama dawowa. Wannan ba za ta har ina?
"Gaskiya Metiron akwai matsala. Kudi ba zai dawo ba. Na fada miki cewa na riga na biya har Agents sun gama komai. Lokaci ake jira a baku passport dinku."
Huci ta kama sai ta ya tsorata. Ta buga ta raya ya daure ya cigaba da cewa sai dai tayi hakuri. Haka ta hakura ta koma wurin aikinta tana ta tufka da warwara. Da shigarta ba dadewa aka kawo mai haihuwa. Matan manyan mutane sun fi ganewa asibitin kudi akan na gwamnati. Yau sai ga tsuntsuwa daga sama gasashshiya. Matar kwamishinan raya karkara ce da kanta ta kawo surukarta. Nakuda ta kamata kuma suna ganin kafin su isa asibitin da take awo za a iya samun matsala saboda ta soma zubar da jini. Shi yasa suka kawota nan saboda yafi kusa. Uwani kuwa sai tayi uwa tayi makarbiya ta hana kowa tsayuwa kan mai nakudar.
Kafin likitoci biyun da aka sanar su shigo har ta gama shirinta. Kudi kawai take gani har ta samu indai tayi aikinta yadda ya kamata.
"Haihuwa ta nawa ce?"
Da kyar yarinyar ta amsa mata "ta biyu."
Rage murya tayi ta matsa kusa da ita kamar cikin za ta taba sai ta duka yadda za ta ji ta sosai.
"Naga babu dinki a haihuwarki ta farko kuma da alama da kanki ki ka karu."
"Washhh Allah..."
"Ko"
"Likitan ta ce ban karu shi yasa ba ayi ba."
Uwani ta dago kai kamar gaske "wace irin likita ce wannan mai neman kashe miki aure? Ke baki dinga jin jikinki a sake ba?"
"Innalillahi...wayyo Mamaaa"
Jira tayi ciwon ya dan kara sauki ta kuma ingizota.
"Zan taimaka miki. Idan kin haihu yanzu da kari kada ki yarda ko kadan ayi miki dinki. Zan jira ki haihu na baki nambata. Wallahi gyara zan miki giredi amma a gida. sai kinfi budurwa a wurin mijinki."
"Lahaula wala quwwata illa billah....ki rabu dani don Allah" yarinyar ta furta cikin tsananin azabar ciwo.
Ana haka likitocin suka iso. Kafin ma su fara dubata kan d'a ya danno. Ba haka Uwani taso ba haka tana ji tana gani likitocin suka karbi haihuwa. Abin dadi ga maijego wannan ma bata karu ba ko kadan. Uwani sai ta makale a dakin da sunan taimaka mata ta gyara jikinta kafin a fito da ita.
"Kar ki cuci kanki na san zafi ne babban abin da yake saka ku gudun dinki. Allura zan miki wadda zata kashe duk wani ciwo. Mazan yanzu masu dan banzan yawo sai da gyara ake samun kansu."
Bacin rai muraran ta gani a fuskar yarinyar a lokacin da ta tashi za ta fita daga dakin haihuwar tana cewa
"Baiwar Allah ki kyaleni don girman Allah"
Tana fita Uwani ta ciji lebe za ta fara zaginta sai ji tayi ance "ni ina so. A nawa za ki min na dawo kamar budurwa?"
"Dubu ...." ta soma cewa bayan ta bude labulen da ya raba gadon wadda ta haihu da na mai maganar. Ita ma tsohon ciki ne da ita. Ta sanar da ira cewa an kawota tun dazu anyi inducing amma har lokacin bata fara jin ciwo ba.
"Barshi ma. Zan baki dubu hamsin kiyi min aiki mai kyau." Sama ta kalla tayi kwafa "sai na shayar da kai mamaki. Wallahi nafi karfin zama da kishiya."
An tabo inda yake yiwa Uwani masifar kaikayi. Nan ta zauna tana yiwa matar da bata sani ba famfo da nuna mata illar rashin gyara irin wannan ga matan aure.
Ranar fafur taki tafiya gida sai wuraren uku na dare matar ta haihu. Ta so suyi magana tun lokacin amma ganin
manyan likitoci suna ta kai kawo sai ta hakura. Ranta fari kal domin ta tabbata dai matar wani ce.
Bayan ta kimtsa an kaita dakin hutu da kanta ta ce a kira mata Metiron Uwani. Da zumudinta kuwa ta shiga ta kara yi mata barka. Matar ta karbi nambar wayarta.
"An riga anyi min dinki amma."
"Karki damu. Kwancewa zanyi nayi miki nawa. Wallahi na yiwa mata sun fi a kirga masu haihuwa a nan da haihuwar gida ko wasu asibitocin."
Ajiyar zuciya ta samun nutsuwa matar tayi sannan suka yi alkawarin ana sallamarta washegari za ta kirata ta bata kwatancen gidanta. Jikin Uwani har rawa ya dinga yi saboda taji kudi. Tana fita matar nan ta dauki waya ta kira maigidanta. Hakuri ta bashi saboda yana ta kiranta lokacin da suke maganar da Uwani bata dauka ba. Farincikinsa na sake samun karuwar zuri'arsu ya nuna mata da tambayar bukatunta idan akwai a lokacin.
Murmushi tayi ta gyarawa jaririnta kwanciya sannan ta ce "Akwai mai girma CMD (Chief Medical Director). Ana badakala a asibitin nan karkashin shugabancinka baka sani ba. Nayi karambani na kama maka daya. Za dai muyi maganar a gida. Amma please my dear ya kamata kasa ido sosai."
Dariya ya kwashe da ita ta tausayin mai tsautsayin da tayi shuka a idon makwarwa. Matarsa lauya ce mai zaman kanta wadda take hadawa da aikin sa kai na kare hakkin bil adama.
Karfe shida da kwata a kofar gidan Alh. Rabi'u ta yiwa Salihi. Garin da sauran duhu hasken rana bai fara fitowa ba. Wasu magidantan ma basu riga sun koma muhallansu daga masallaci ba. Daga ganin yadda ya ajiye mota zaka san baya tare da nutsuwa. Kasheta kawai ya yi ba tare da ya rufe ba ya fita ya soma doka sallama a kofar gidan.
Sallamar tasa ba karamin tsinka zuciyar Salima wadda ko tashi daga kan abin sallah bata yi ba tayi. A hanzarce ta mike suka kusa yin karo da Zara don ita ma ta gane muryar waye. Innayo kuwa iccen da take kokarin turawa a murhu tayi jifa dashi su ukun suka hado a kofar gidan da ko budeta ba ayi ba.
"Karbo min mukulli a wurin Alhaji"
Innayo ta furta muryarta tana fallasa fargabarta. Babu wani abu ko daya da zai kawo Salihi gidan nan da duku dukun asuba mai dadi.
Tare da Alh. Rabi'u Salima ta dawo ya sako babbar riga yana murza idanu don ko sallah bai yi ba. Innayo ya kalla ta jingina da bango zuciyarta tana ta dukan kirjinta.
"Aka ce Salihi ne yake sallama."
"Ni ne Alhaji" ya amsa daga waje.
Nasa hannun ma rawa ya kama yi sai Zara ce ta iya budewa Salihi ya shigo. Daga soron ya durkusa ya gaishesu sannan ya dan sosa keya.
Salima da Zara sai suka bar wurin tunda kowa ya fahimci ba tashin hankalin da suke taraddadi bane.
"Innayo ki bata hakuri tazo mu koma. Indai akan Ummule ne zan raba musu gida."
Alh. Rabi'u ya kalli Innayo kallo na wulakanci sannan ya yi wata irin banzar dariya.
"Hajiya Hauwa kenan. Kin nunawa kowa a gidan nan cewa kin fi kowa iya tarbiya da kyawun hali. Rannan har magana ki ka fada mana ni da Asabe akan 'ya'yanki. Sai gashi a tsukin abin da bai kai wata guda ba uku sun dawo gida. Allah Ya kyauta."
Wucewarsa ya yi ko waige babu. Salihi kunya ta lullube shi yaji kamar ya nutse a wajen.
Numfasawa Innayo tayi ta dube shi da murmushin da ya tsaya a fatar bakinta saboda bacin ran Uwani.
"Salihi aure kayi?"
Da sauri ya kalleta ba tare da ya iya boye mamakinsa ba.
"Uwanin bata fada miki ba?"
"Bata fada ba. Allah Ya sanya alkhairi. Sai dai kuma bata zo gidan nan ba."
Kansa da ya yi niyar yin kasa dashi ya sake dagowa da sauri hankalinsa a mugun tashe. Jiya bata da aikin kwana. A ka'ida ma kafin la'asar take dawowa a ranaku irin wannan. Sai gashi har bayan isha babu duriyarta. Ya dinga kiran wayarta babu amsa, wanda kuma tana sane don kada ya katse mata jiran mai haihuwar da zata zame mata alkhairi. Abu kamar wasa har goman dare. Nan fa yaji ba zai iya bacci ba dole ya tafi asibitin nemanta. Nos din da suke da aikin kwana ranar suka ce masa ta tafi. Basu san tana nan ba tunda kafin zuwansu ma 'yan yamma sunyi nasu sun tashi. Sai da ya tafi ne daya daga cikinsu ta ganta take fada mata wani yazo nemanta. Haka nan taji a ranta maigidanta ne amma sai taki kiransa. Dole zai yi mata ta dawo gida ita kuwa bata cikin masu wasa da neman kudi. Haka ya koma gida ko runtsawa bai yi ba. Tunaninsa ya tafi akan ko tayi yaji ne saboda zuwan Ummule. Shi ne ya taho gidan da sassafe saboda baya son kowa ma hatta Ummule ta fuskanci da b'araka irin wannan tsakaninsu.
"Ikon Allah" ya ce lokacin da yake jin wani irin tsoro a ransa "nima nayi jinkirin zuwan ne saboda tunanin ko ta karbarwa wata aikin kwana ne..."
Innayo ba shiri tayi 'yar dariya tana cewa "banda abinka Salihi yaushe zaka dinga magana kamar yau ka san Uwani? Ita da ba wasu kawayen kirki ba ai da wuya ne ta karbarwa kowa aiki."
Murmusawa ya yi shi ma. Wayar suka sake kira shiru dai ta ma daina shiga. Innayo daurewa kawai take yi amma gabanta sai faduwa yake yi. Salihi yana tafiya taje ta ballo magungunan hawan jininta tasha. Sun yi dashi zai koma asibitin ya sake dubawa. Idan an tabbatar masa ba a nan ta kwana ba zai kirata ya sanar da ita su san matakin dauka na gaba. Jiri ne ma ya yi mata sallama dole ta nemi wuri ta kwanta.
Wuraren bakwai da rabi Metiron Uwani ta fito daga dakin Haj. Salma wato matar CMD. Bakinta kamar gonar auduga domin Hajiyar tayi mata alkawarin idan aiki ya yi kyau tana da mutane a kalla shida wadanda zata hadata dasu. Duka kawayenta ne a cewarta da suka hayayyafa ana neman tayar da komad'a. Kudin aikin kowacce sun tsayar a dubu talatin. Nuna mata tayi duka matan manya ne sannan ai suna sayen kayan gyara na sama da wannan kudin sosai. Kai tsaye dakin da suke kwanciya ko ajiye kayansu ta nufa ta dauko wayarta. Tabe baki tayi ganin yawan kiran da Salihi ya dinga yi mata. Da yana sonta ba zai munafunceta ya karo aure ba ta ayyana a zuci. Kiransa tayi yana bakin danja zai karaso asibitin.
"Naga missed calls ne" ta ce dashi da ya dauki wayar da yanayi na nuna kosawa da kiran nasa.
Haushi ya kama shi ya daure ya boye fushinsa.
"A ina kika kwana?"
"Wace irin tambaya ce wannan bayan ka san ina zuwa aiki? To ina asibiti yanzu zan taho gida."
"Sai kin dawo"
Yau kam ya yi niyar nuna mata idan ma da gangan take wannan rashin hankalin to bashi da juriyar cigaba da dauka. Ace ko kadan bata ma san tayi masa ba daidai ba? Ta kwana a waje ba waya ba text sai amsa waya da gadara. Wayar Innayo ya kira ya fada mata sun yi magana sai ta roke shi da ya kawo Uwanin gidanta idan ta koma.
Ita kuma Uwani wayar kafintanta ta kira cikin sa'a kuwa ya dauka. Kayan gado da kujerun da ta saya a wurinsa ta ce tana bukatar aje a kafa mata yau. Dama ta saya ne saboda tayi gyaran daki idan ta dawo daga Hajji.
"Idan kun kusa titin Kofar Famfo ga nambar dana ku kira zai kaiku gidan."
Bayan ta gama dashi ta kira mai labule shi ma ya dinka mata ne na iya falo da dakin baccinta. Karin yadi ta ce ya nema irin wadancan za ta zo bayan la'asar suje ya auna labulen sabon gidan a kara. Kafin nan ta san masu gado sun yi nisa a nasu aikin. A son ranta a gama komai cikin kwana biyu ta tare.
Ginin da kuma wadannan kayayyakin da ta saya su suka cinye mata kudade. Dalilin da yasa ta shiga rudani kenan akan bacewarsa sarka da kudadenta na daki. Shawarar da ta yanke tun kwana biyu da bacewar kudin ce ta sake fado mata taji kwarin gwiwa. A jikin Salihi za ta fanshi kudinta komai runtsi.
Da wadannan lissafe lissafen ta kama hanyar BUK oldsite inda Mubashir yake karatu. Da ta kira shi a waya tsorata ya yi da farko sai yaji ba zancen kudinta bane. Haduwa suka yi ta bashi mukullin gidan nata da bayanin abin da zai yi. Saboda halin rayuwa ta jima da nuna masa gidan tun yana fuloti. Daga nan gida ta nufa zuciyarta kamar an yayyafa ruwan sanyi. Tana tura gate din suka yi ido hudu da Salihi.
"Fita zaka yi ne?" Tayi masa tambayar rainin wayo a zuwan ita har lokacin bata san tayi masa laifi ba.
"Ke nake jira"
Kallonsa tayi shekeke ta wuce ciki tana cewa "wai meye ne kake ta wani bata rai don na kwana a asibiti kamar wani bakon abu?" Dan tunani tayi ta dawo da baya ta ce "Idan saboda ban kiraka bane aiki ne ya min yawa. "
Tsabar takaicinta bai bashi damar amsa mata ba. Daki ta wuce tayi wanka ta fito ta sha shayi a gurguje saboda kada Haj. Salma ta kirata bata gama ba. Tana tashi Salihi da Ummule suka fito daga dakinsa. Dakin nata ya bita shi kadai ya sameta tana sauko da akwatuna.
"Lafiya?"
"Lafiyar kenan" ta ce a yayinda ta dauko wata leda da 'yan mukullaye a ciki. Kwancewa tayi ta dauko wasu masu guda hurhudu ta cirar masa d'ai-d'ai ta damka masa.
"Gasu nan mukullin gate ne da na kofar gida. Idan kayi kwanakin cin amanarka a nan sai ka dinga biyoni nawa muhallin ranar girkina."
Mamakinta yana neman zarta bacin ransa. Sam ya kasa fahimtar inda ta dosa.
"Ban fahimceki ba."
Kugu ta rike da hannu daya bayan ta turo dauri gaban goshi.
"Na gama gini na ina shirin saka 'yan haya kazo min da waccan abar wai kishiyata kuma kana sa rai na karbeta mu zauna a nan. Sai dai ina so ka sani cewa nafi karfin wannan wulakancin. In Allah Yaso ba zan kara sati ba a gidan nan zan koma nawa. Ba kuma zan yafe maka hakkina ko daya dake kanka ba."
"Yanzu Uwani har gida ne dake ban sani ba?"
Kwaikwayonsa tayi tana dariya "yanzu Salihi har aure ne da kai amma sai da matar tayi ciki na sani?" Ganin ya kasa cewa komai ta dora da cewa "da ne maza suke taka mata su zauna lafiya amma yanzu kan mage ya waye. Ko an fada maka kudin da nake nema ina yi ne don na mutu ku ci gado kai da 'ya'yanka?"
"A tare lafiya Uwani"
Daga yanayin fitar muryarsa ma ta gane ba da niyya ya yi mata adduar ba. Shi yasa ita ma ta amsa masa yadda zai ji haushi.
"Amin dai. In ka sami sukuni sai ka kawo kudi ko ka sayo gadon da zaka sa a dakinka na can."
Ya daina mamaki kamar yadda ya daina jin bacin rai. Hukuncinta sai ya zauna ya yi shawara da kwakwalwarsa sosai. Tafiya ya soma yi ta biyo bayansa da sauri.
"Af...baka ji ba. Na ce akwai lissafin da zan maka na abubuwan da bakuwarka ta sace min." Dage gira taga ya yi sai ta hau bayanin cewa ranar da ya kawo Ummule gidan bata ga alamun bakunta a tare da ita ba. Shiyasa rake ganin ba ranar ya fara zuwa da ita ba. A takaice tana zargin ita tayi mata satar kudi da sarka.
Katse zantukan da yake ganin matsalar kwalwalwa ce ta kawo mata su ya yi
"Idan kin gama shiryawa ki zo muje Innayo tana nemanki."
"Ina da uzuri zan biya idan na gama. Maganar sark...."
"UWANI!"
Hadiye sauran maganarta tayi ba shiri saboda karfin tsawar da ya daka mata.
"Ki dauko mayafinki yanzun nan ina jiranki a mota."
Bata gama dawowa daidai daga firgicin da ta shiga ba Mubashir ya kirata. Saurin dawo da nutsuwarta daga tunanin me ya sami Salihi tayi ta amsa wayar.
"Umma gamu a bakin gate amma KNUPDA sun yi alamar a dakatar da aiki a gidan."
Kwakwalwarta ce ta toshe na 'yan dakiku ta dinga maimaitawa Mubashir tambaya daya kamar mai bitar karatu.
"Su waye kuma KNUPDA?"
Farha bata dago da kanta ba har Abbati ya gama fada mata asalinsa da musabbabin zuwansa Kano. Labarin nasa ya sami sauyi ne a wurin silar arzikinsa inda ya ce mata kasuwanci suke yi amma yanzu sun balle daga jikin ubangidan nasu. Ya fada mata unguwar da suke ginin shopping mall da ire iren kayayyakin da suke son zubawa a ciki.
A lokacin da yazo gabar da dole karya ce kadai za ta iya rufa masa asiri sai da ya hadiyi yawu mai daci. Da kansa yake jin tsana da kyamar dabi'ar da suka rayu cikinta. Yana son Farha so mai girma. Burinsa idan har ya mallaketa su zamewa juna tamkar warin takalma masu cike junansu. Yadda bashi da sirri da Munzali yana fatan kusancinsa da ita yafi wannan. Ba don komai ba kuwa face sanin cewa duk matsayin aboki matar aure ta fishi. Ita da mijinta aminai ne, masoya kuma ma'aurata.
Kimanin minti uku da yin shirunsa amma har lokacin bata dago kanta ba. Tuni ya fara sarewa yana jin ya rasata kenan har abada. Magana mai girma irin wannan ya so ace a gida aka yita. Sai dai kuma tazo masa bagatatan ne da Farha tayi masa tambayar cikin hirarsu.
"Don Allah ki dago kan ki ko sallamata zaki yi kada ki ce ba za ki sake iya kallon wannan almajirin dan kauyen wanda ko kwalin primary bai mallaka ba." Muryarsa ce tayi wani irin rauni mai fallasa ruhi da zuciya tana raurawa saboda tasirin soyayyarta a zuciyarsa. Bai gaji ba ya sake yi mata magana domin ya kagara ya san matsayinsa duk da ya gama sallamawa.
"Ni ba tsaran aurenki bane Ya Farha, amma wallahi ina sonki da dukkan zuciyata."
Farha bata san yadda zata kwatanta halin da Abbati ya jefa zuciyarta ba da kalamansa na karshe. Zuciyarta kara fadi take a cikin kirjinta tana kuma cikewa da wannan bawan Allah dake gabanta.
Kosawa ya yi da rudanin da zuciyarsa ta shiga a sakamakon shirunta.
"Ko in tafi?"
Sai lokacin ta dago da taji ya dan tura kujerarsa baya alamun zai tashi.
"Idan ka tafi kana tunanin tsaran auren nawa zai zo?" Ta ce a raunane.
Kansa ya gyada da murmushin da ya tsaya a labbansa. Wurin kawai yake son ya bari kafin ya tsinci kansa a kan gwiwoyinsa yana rokon soyayya.
Hawaye ne ya zubo mata ba shiri da ta hada ido dashi. Wannan wace irin zazzafar soyayyace suke yiwa juna haka? Da jikakkun idanunta ta dube shi.
"Yazo ya aureni kana ji kana gani?"
"Kin yarda idan yazo na kore shi ko waye?"
Ita ma kai ta gyada masa amma nata murmushin mai sauti ne da jindadi.
"Kina ganin su Mami zasu yarda ki aureni?" Ya tambayeta da sabuwar damuwa.
"In sha Allahu babu matsala."
Gyara zamansa ya yi gami da sakin ajiyar zuciya. Suka kalli juna suka yi murmushi a tare. Abbati ya kasa dauke ido daga kan kyakkyawar fuskarta.
"Kin san me?"
"Ina dai so in sani" ta lumshe idanunta sannan ta bashi amsa.
"Na dan kware a Ingilishi."
Farha bata san lokacin da ta kama dariya ba.
"To ko mu kara ne?"
"Me ya yi zafi daga wasa"
Dariya suka yi tare a idanun Mami Khadija wadda ta zo wucewa can nesa dasu da kawayenta. Murmushi tayi ta dauke kanta kafin su farga cewa ta gansu. Fatanta Allah Ya cikawa 'ya'yanta farincikinsu.
A zuciyar Abbati kuwa tunani yake kada Allah Ya kawo abin da zai raba shi da Farha. Shi kan shi tsoron girman soyayyar da yake yi mata yake yi. Idan ya rasa ta......baya son sanin halin da zai shiga idan ya rasa ta.
Can daya bangaren inda Munzali da Mardiyya suka zauna suma tasu hirar suke gwanin sha'awa. Hirar irin son da Abbati yake yiwa Farha yake mata tana bashi amsa da tabbacin yayarta ita ma tana kaunar aminin nasa.
"Da gaske dai ba sona kike ba ko Mardiyya?"
Ya furta daga sama suna tsakar magana. Gabanta ne ya fadi domin tun haduwarsu bai taba kiranta da sunanta ba. Kallon ma kamar tayi masa laifi haka ya tsareta da idanu duk sai ta daburce.
"Me nayi don Allah?"
Yanayin tsoratar da tayi sha'awa ya bashi. Yarintarta ta fito sosai sai kara shiga zuciyarsa take yi.
"Tunda muka zauna nake yi miki zancen su Abbati amma ko ki bata rai ki ce a canja hira. Kamata ya yi nima naci ribar lokacin nan nayi miki hirar zuciyarta da yadda take kaunarki."
Sunkuyar da kai tayi tana wasa da wayar hannunta. A haduwarsu da yawan wayarsu ta gane Munzali yana da son wasa da tsokana. Wannan ma yana daga cikin abubuwan da suka sa take son sa.
"Baki ce komai ba."
Mardiyya sai ta zabi ta rama ita ma ta nuna masa wace ce ita.
"To ni me zan ce? Ka kebe 'yar karamar yarinya kana yi mata zancen soyayya."
Dariya sosai ya dinga yi yana bude baki ya rufe kafin ya ce "kin ce wani abu. Wato yarinya ko? Bari na tashi na nemi daidai dani a cikin taron nan"
Hannuwanta ta daga kamar mai addu'a da ya mike ta soma cewa "Allahumma..."
Tsayuwa ya yi yana kallonta cikin wani irin yanayi mai kashe jiki "karasa mana."
Sai ta daure fuska ta cigaba
"Allah Kasa duk wadda Daddyn Qibdiyya ya gani ya yiwa magana ta ce an kawo kudin aurenta."
"Diamond girl" ya ce yana dariya sosai "I love you."
A guje ta tashi ta bar wurin har tana tuntube da kujera akan hanya.
Munzali ya dinga murmushi yana mai mamakin yadda zukatansu suka zama mallakin yaya da kanwarta lokaci guda.
Filin rawa Lilu yaje ya yi abarsa son rai ya dawo inda Sauda take tare da Qibdiyya. Yarinyar ta sake abinta tana ta yi musu hira. Tana ganin Lilu ta gudu wurinsa. Sauda ta ce.
"Baban yara ita ma ka sayeta kenan"
Ranar har su Abbati suka tashi tafiya Qibdiyya tana hannun Lilu. Kowa sai da ya shaida yadda tasu tazo daya daga haduwa. Da ya zo sakata a mota shi da iyayen nata babu wanda ya kula cewa kiss ta so yi masa a baki. Dama ce bata samu ba saboda tana yunkurowa ya sauketa a jikin Abbati.
Kuruciya bata barta ta dauke shi komai ba. Uncle Daddy ne kadai yake yi mata. Sai kuma mutanen cikin ire iren bidiyo da yake kunna mata ya ce tayi masa abin da ta gani. Ta fanin kallo Zakiyya tana matular kokari don ko fim ta daina kallo a gaban 'yarta saboda kaifin basirar yarinyar. Shi yasa bata da aiki sai karatun waya. Sakacinta a bangaren saka ido ne a cikin gida. A zatonta tunda suka fito ciki daya da Daddy ba zai taba cutar da ita ba balle 'yarta.
(Ya ke UWA mai dimbin daraja da martaba. Ba a ce ki sanya zargi da kokonto a tsakanin mu'amalar 'ya'yanki da 'yan uwanki ba. Nagari masu sonmu da gaskiya sun ninka shaidanun. Yana da kyau amma ki kula da irin shakuwarsu ko tsoronsu da yara ke ji. Idan tayi yawa to wajibi ki bi abin cikin laluma ki gano musabbabinsa. Ita alakar da aka gina da taba jikin juna a waje tana da wuyar bari. Shi yasa ma yaran da ake yiwa fyade ko koya musu mummunar dabi'a ake samun wahalar hanasu. Sai kin dinke baraka tsakaninsu da mai koya musu sai suje suna nema a wurin wasu da kansu. ZINA MASIFA CE GA BABBA DA YARO! Rabuwa da ita sai an dage sosai.)
KIRIKASAMMA
Dakin Baaba Mari babu haske sosai saboda ta gama shirin bacci. A kwance take tana ta juye juye akan gado. Jikarta ta wajen Atine da suke kwana tare sai munshari take abinta. Gajiya tayi da tunanin da ya addabeta ta tashi za ta dauro alwala kamar yadda aka koyar dasu a islamiyya. Babu wani abu da ya gagari addu'a, musamman a hada da qiyamul laili.
Alwala taje ta dauro a bandakinta wanda Abbati ya yi mata a falo. Da yake fitilar chaji ta kunna tana iya hango tsakar gidansu sosai. Maigidanta ne har yanzu shadaya da kwata na dare zaune tare da Mal. Sa'adu wanda ya yi uwa ya yi makarb'iya akan bakon da suka yini dashi. Su uku har bakon hira suke suna dariyar wani abu da ya fada.
Daki ta wuce ta dauki hijabi da abin sallah. Komai a sanyaye take yi saboda wani kwantacwn abu da bata san a ina yake ba yana fada mata akwai matsala. Ko Munzali bai taba zuwa Kirikasamma shi kadai ba. To me zai sa 'yan satittika da nad'in sarautar Abbati shi wannan Shazalin ya dawo?
SHIDA RANAKUN...
Gari ya waye, rana ta fito tun karfe shida da rabi. Zuwa goma na safiyar Asabar jama'ar dake waje har sun fara jin zafinta. Sai dai wannan zafin ba zai hana masu uzuri a waje fita su gabatar dashi ba. Kamar kowacce rana ga dan Adam, ita ma wannan Asabar ta zo a matsayin ranar kuka, farinciki, dariya, bakinciki, fargaba, alhini da kowane irin yanayi da mutane ke tsintar kawunansu.
A safiyar wannan Asabar din ne Uwani ta amsa wayar Mubashir mai tafe da mummunan labari akan gininta.
A ranar ne kuma Shazali ya wayi gari a Kirikasamma bayan ziyarar bazata da ya kaiwa gidansu Abbati.
Ita ce kuma ranar da Hasiya ta zaba domin kai wa Salima kukanta akan saurayin Ayaah.
Duka dai kuma a wannan ranar ne Abbati da Munzali suka je daurin auren kanin Mami Khadija bayan dinner din da suka je ranar Juma'a da daddare. Dinner din da basu baro ba sai da suka tabbatar an sami musayar zukata tsakaninsu da 'ya'yan Alh. Tahir guda biyu.
Ana kiraye kirayen sallar Magariba Shazali ya isa Kirikasamma. Girkin abokiyar zaman Baaba Mari ne. Tana jin an ce abokin Abbati ne ta fito daga rumfar da suke girki tana fadin maganganu. Ciki har tana cewa
"Ban san da zuwan bako ba saboda haka ban girka dashi ba."
Baaba Mari ko tari bata yi ba har ta juya ta tafi. Bakinciki da hassada ba bakon abu bane gareta daga wurin kishiyar dake morar arzikin Abbati. Niyarta idan an kawo mata nata abincin ta bashi. Sai gashi an hada masa gara guda daga bangaren Mal. Sa'adu. Atine da Habi su ma ba a barsu a baya ba saboda kada mahaifiyarsu ta wahala. Kowacce ta aiko da abinci.
Ashe kusan karfin girkin ma 'Yashshafa ce tayi. Deluwa ta rasa inda za ta saka ranta domin a burge wannan bako. Mahaukaciyar motar da yazo da ita kadai ta ishi bawa shiga rudani. Akan Shazali ita mai iya hakura da Sha'aib ce kamar yadda take kiransa.
Kafin lokacin kwanciya baccin da Baaba Mari ta kasa runtsawa Mal. Inuwa ya shigo dakinta. K'aidarsa ce zaga matansa da asuba da kuma bayan Isha. Da murna ya shigo mata yana yabawa baiwar dansu wanda har masu kudi ke ziyartar iyayensa.
"Idan aka kirani da Uban Abbati sai naji duk garin nan babu ya ni. Dubi dai ace mutum mai arziki kamar wannan ne a gidanmu..."
Kula ya yi hankalinta ba ya gare shi ya bata rai.
"To yanzu kuma me ya faru? Tunane tunanenki na banza akan arzikin danki ne ya sake dawowa?"
Murmushin yake tayi tare da kawar da kai domin ko za ta kwana tana bayani baya taba fahimta.
"Malam kenan."
Komawa ya yi ya zauna yana dubanta cikin yanayin da yaki jinin ganinta.
"Ki fadi damuwarki tunda nayi imanin akwai. Yau da ace ba Inna Mairo ce ta karbi haihuwar dan nan ba sai ince ba naki bane shi yasa kike gwada masa halin matar uba ko dan riko. Ni ko da wasa ban taba jin uwar da take yiwa dan cikinta bakincikin samun arziki ba sai ke Mari."
"Har yanzu kana ganin laifina don na damu da son sanin silar kudin da mu da danginmu muke ci? Daga zuwa almajiranci sai kudi kamar suna zuba daga sama?"
Ransa ya soma baci amma ya danne domin baya son rigima a daren nan.
"To meye a ciki? Arziki ba na Allah bane? Kuma yana baiwa wanda ya so bi ghairi hisaba. 'Yan kasuwa nawa ne suka fara a matakin da yafi bara kaskanci amma yanzu sun wuce sa'a?"
"Cikinsu kuma kowanne idan an tashi zaka ji an cewa abu kaza yake sayarwa ko yake kerawa. Shin ka taba tambayar kanka me Abbati yake sayarwa? Ka taba ganin wani abu cikin kayan sayarwarsu ya kawo gidan nan?"
Shirunsa ya bata damar cigaba da magana cikin lumana.
"Malam ni da kai mun sani cewa yaron nan duk fadi tashinsa yana yi ne domin ya inganta rayuwarmu. Kafatanin gidan nan babu wanda Abbati bai shiga rayuwarsa ba." Muryarta sai ya karye tun kafin ta fadi abin da ke zuciyarta "dan nan yaron kirki ne ba don ni na haife shi ba. Amma ina tsoron kada haram..."
"Ya isa!" Mal. Inuwa ya furta yana mikewa. Zargin ta dasa masa wanda ko kadan bai so ba. A duk lokacin da son bincikar dan nasa ya bijiro masa sai tsoron abin da zai tarar ya hana shi. Amma yau yaji wani irin nauyi ya sauka a zuciyarsa mai tayar da hankali.
"Allah Ya huci zuciyarka. Mu kwana lafiya."
Daga wadannan kalaman ya shige uwar daka ta barshi. Ya fita zuciyarsa tana ta wasiwasi. Amma yana zuwa wurin Mal. Sa'adu da ya same shi da Shazali suna hira sai ya tura zarginsa baya.
Da safe Deluwa har dakin da aka sauke Shazali
ta tura 'Yashshafa ta kai masa abinci. Ta hada mata da hudubar kwarkwasa domin daukar hankalinsa. To 'Yashshafa ko kadan baiyi mata ba daga kallon farko. Akwai kudi ta gani daga sutura da motarsa. Bashi da wani muni amma mummuman nufin dake zuciyarsa ya tasirantu a cikin ji da ganinsa. Ko murmushi yake idan ka kalle shi zuciya sai ta harba saboda shaidan ya gama dashi. Da zumbura baki tayi sallama kuma yana amsawa ta ajiye a bakin kofa ta gudu abinta. Gara dai a mayar da ita Kadunan ko sa saba da Suhaib. Matsalarta daya akansa bata wuce kaninsa da ya kirata Iya duba-duba ba. Idan ta auri yayansa sai ta tashi tsaye ta saita shi don kada ya rainata.
Wajajen biyu da rabi aka raka Shazali
bangaren Baaba Mari zai yi mata sallama. Ita kadai ce a falon nata tana sauraron rediyo.
'Saboda ke Abbati bai isa ya jika min aiki ba. Munzali baya ketare maganarsa. Idan ya ce su komo gareni karshenta da gudu zai biye masa ya amince.'
"Zauna mana"
Baaba Mari ta furta da dan karfi domin ta dawo dashi daga duniyar da ya luluk'a. Jikinta har sanyi ya soma yi da ya shigo saboda kallon da ya kafeta dashi yana tunanin yadda zai bata mata da.
Gaisheta ya yi da girmamawa da zai tafi ya kawo dubu hamsin ya ajiyeta a kusa da ita. Kudin ma tsoro ya bata tunda bata san manufarsa ba. Haka kawai ya zo ya kwana kuma gari ya waye zai tafi ya hadata da kudi.
"Daukesu don Allah."
Nunawa ya yi kamar bai ji dadi ba ya yi magana cikin rashin walwala.
"Don Allah ki dauka kisa mana albarka. Na san da Abbati ne ba za ki ce ya dauke ba."
"Duk da haka ai kai bakonmu ne. Ni dai don Allah ka dauke nagode."
Wayarsa ya zaro yana cewa "tunda baki daukeni d'a ba bari na kira Abbati da kansa ya fada miki matsayina."
Matsawa tayi daga inda kudin suke tana sauraron alamar shigar kira saboda speaker ya saka. Sau hudu ya kira Abbati bai dauka ba saboda suna zaune da Munzali suna amsa tambayoyin Alh. Tahir da wasu yayyensa. Sakon text Shazalin ya tura masa wanda ya saka shi kira hannu na rawa bayan ya tashi ya fita.
(Ina dakin Baaba Mari a Kirikasamma)
Shazali sai ya dauka ya kuma danna speaker a lokacin da Abbati yake magana hankali a tashe. Ya gama birkicewa gami da tsorata. Magana kawai yake yi yana mai jin inama zai iya bude ido ya ganshi a gidan.
"Ban gane kana dakin Baaba ba? Shazali me zai kaika gidanmu."
"Zumunci mana."
"Zumunci? Ko da can ka taba jin na nemi yin zumunci da kai da balle yanzu?"
Shazali sai ya kalli Baaba Mari ya marairaice kamar kalaman sun bashi mamaki shi ma.
"Ka bari na fita nan ba wurin wannan maganar bane. Ni kararka na kawo mata akan kasuwancinmu. Sana'ar tana kawo kudi kana neman durk'usar damu."
Daga bayan fage (background) Abbati yaji ana kiran sunan wata ya kuma gane muryar mai kiran da sunan wadda aka kiran duka 'yan gidansu ne. Hankalinsa sai ya nemi gushewa saboda tsananin tashin hankali da ya gane da gasken yana gidan. Gargadin da yake yi masa ma a raunane ya fito domin yana daf da fita daga hayyacinsa.
"Shazali! na rantse idan ka fada mata wata magana sai ka raina kanka. Hummm....Kai bari kaji in fada maka, idan ka sake ka fada mata abin da zai tayar mata da hankali sai na dauki mummunan mataki a kanka."
Baaba Mari tana daga zaune amma jiri ke dibarta. Hannuwanta ta sanya ta rike gefe da gefen kujerar two seater da take kai a zaune. Idanunta a rufe taji muryar Shazali yana bawa Abbati amsa. Tasa muryar a nutse take fita da wani abu da za a iya kira da nasara.
"Kwantar da hankalinka ni hanya ce ta biyo dani na zo muka gaisa. Ban san sadar da zumunci da iyayen aboki laifi bane da ban zo ba."
Kashe wayarsa ya yi ya juya ya fita ko sallama bai yiwa Baaba Mari ba. Bukatarsa ta riga ta biya. Ko yanzu kasuwa ta tashi Dankoli ya ci riba. Bukatunsa akan Abbati biyu ne. Ko dai tsoron tonon asiri a wurin mahaifiya da danginsa yasa shi komawa ruwa ko kuma asirin ya tono ya zubar masa da mutumci kamar yadda ya hana shi cigaba da samun kudi. Yadda ya san Munzali yana jin maganar Abbati ko uwar da ta haife shi baya jin ta isa dashi. Umarnin da hani a hannunsa suke. Shi yasa ya zabi biyo masa ta bayan gida.
Abbati ya dinga kiransa wani kiran na tarar da wani amma yaki dauka sai da ya shiga mota. Idanunsa na kallon Mal. Inuwa da Mal. Sa'adu tare da wasu kawunnan Abbatin suna ta dago masa hannu. Murmushin mugunta ya yi sannan ya amsa wayar. Shi ya fara magana bai ma saurare shi ba, kuma yana gamawa ya katse kiran.
"Zabi ya rage naka Abbati. Kafi kowa sanin cewa ina da abubuwan da zan nunawa tsohuwarka wanda zai sa ta tsine maka yau dinnan ba gobe ba. Ka fadawa Munzali na ce ku same ni a Port Harcourt jibi."
Awanni uku da rabi kafin waccan mummunar wayar sun zo wa Abbati da Munzali tare da masoyansu da abubuwa daban daban. Ga Abbati da Farha, wata kofa ta karin sani da fahimtar juna ce ta bude musu bayan an dawo daga daurin aure.
Sai ta kurewa Suhaib a waje yake yarda magana ta hada shi da mahaifinsa. Sai dai yau ta sha bamban da kowacce rana. Jiya bayan sun dawo daga dinner Farha ta fada masa yadda suka yi da Abbati. Shi da Mami wadda ya fadawa zancen duk sun yi mamakin jin bai yi karatu ba sai na yaki da jahilci.
Tabbas Mami Khadija za ta so 'yarta ta auri mai ilimin boko bayan na addini sai dai kuma ta duba abubuwa da yawa. Na farko dadewar Farha a gida babu wanda ya taba cewa yana sonta (kadan daga cikin shukar Alh. Tahir da zuri'arsa suke girbewa). Yabawa da hankalinsa da mutumcin mahaifiyarsa. Sai kuma ganin girman soyayyar da Farha take yi masa.
Dasu aka daura auren sannan suka bi su Lilu gidan Kawunsu inda aka shiryawa Ango reception. Suhaib ya hango Alh. Tahir cikin mutane. Sai da yaga ya bar jama'ar dake tare dashi ya fito daga karkashin katuwar canopy din ya bishi a baya.
"Ga bakin Farha da Mardiyya zasu gaisheka."
"Suhaib kenan. To ina kwana?" Cewar Alh. Tahir yana mai jindadin maganar da dan nasa ya yi masa ko a wane yanayi ne.
Shi ma Suhaib sai yaji kunya ya dan rissina da murmushi a fuskarsa. Murnar alakar dake tsakanin Abbati da Farha ta cire masa damuwa sosai. Wannan kuwa ya biyo bayan nishadin da yake ganin Mami Khadija tana yi saboda ganin walwalar 'yarta. Kansa ya dan shafa ya ce,
"Abba ina wuni? Ya taro?"
Bai iya boye jindadinsa ba kuwa "Lafiya kalau. Suna ina bakin? Ko na rannan ne da suka zo gida?"
Da Suhaib ya tabbatar masa su din ne sai ya ce su dan jira shi minti kadan zai je ciki ya gaisa da kakaninsu da suka zo. Sannan tunda akwai 'yan uwan Alh. Tahir din mazauna Kano, zai fi son su gaisa dashi a gabansu domin a taya shi bincike.
Munzali ya kasa nutsuwa da Suhaib ya fada musu zasu gaisa da Alh. Tahir da kawunnansu.
"Idan wani ya san mu ko wanda ya san mu fa?"
Ya ce jikinsa a sanyaye ga wani tsoro yana shigarsa. Idan ka cire Qibdiyya, to Mardiyya ce mace ta biyu da yake matukar so. Asabe darajar haihuwa kadai ta samu a wurinsa saboda watsi dashi da tayi.
"In sha Allahu babu komai"
Abbati ya sami kansa da karfafawa Munzali gwiwa duk da a zahiri ya fi shi jin tsoro.
Manyan mutane sun halarci daurin auren saboda baban amaryar dan siyasa ne. Shi kuma ango danginsa manya ne a ma'aikatun gwamnati daban daban. Dole su tsorata saboda ire irensu sune abokan mu'amalarsu a baya.
Mardiyya ta gama shiri za ta fito su gaisa da Munzali kafin Alh. Tahir ya kirasu Mama Nasima ta tsayar da ita. Dakin da babu kowa ta shigar da ita ta damka mata wata 'yar leda.
"Yi maza ki bude ki saka kwallin kafin wani ya shigo."
"Kwalli kuma? Kinga idona fa na saka." Ta matso da fuskar gaban mahaifiyarta sosai.
Mama Nasima ta daure fuska da sauri ta kwance ledar ta miko mata abubuwan dake ciki.
"Kwallin mallaka ne. Ki saka sannan ki shafa hodar ki fita wurin Alh. Munzali."
Ja da baya Mardiyya tayi da sauri bayan ta mayar da kullin ledar tafin hannun mamanta.
"Ba zan saka ba."
Kiris ya rage Mama Nasima ta mareta
"To shashashar banza. An fada miki mazan yanzu ana sanya a kansu ne? Tun yanzu idan bamu tashi tsaye ba kina ji kina gani wata za ta kwace shi a hannunki. Yau da sassafe Dini (kaninta) ya shigo mota domin ya kawo amma za ki fara yi min shirme."
Kwalla sai ta taru a idon Mardiyya. Tana son mahaifiyarta amma taki jinin halayen da ta tashi ta ganta a kansu.
Mama Nasima da ta fuskanci kamar abin bai mata dadi ba sai ta wayance ta koma lallabata.
"Kafin ki fara yi min wa'azi tun wuri ki sani ba kayan boka bane. Haba Mardiyya, kamar baki sanni ba? Wannan wani malami ne wanda ya dogara da Qur'ani. Ko kasa zai buga miki sai ya kama sunan Allah."
"Mama ni dai ki daina wasa da lahirarki a kaina. Malamin Allah babu ruwansa da duba ko buga kasa."
Ba don bakunta da idanun mutane ba da
Mama Nasima ta kai mata duka don haushi.
"Baki ji na ce yana Bisimillah kafin ya fara don ya kori shaidanu ba?"
Cigaba da maganar zai iya saka Mardiyya yi mata rashin kunya wanda ba halinta bane. Sai kawai ta zabi fita daga dakin cikin kunar rai ta iske Munzali da Abbati a inda Suhaib ya ce suna tsaye.
Tun daga nesa Munzali ya gane tana cikin bacin rai. Wurin wata mota ta tsaya ya ka a ya sameta. Yana isowa wayarta ta hau ruri. Sunan (Mama) ya gani a jikin wayar kafin tayi saurin kashewa. Murmushin yake tayi masa wanda akan ce yafi kuka ciwo. A zuciyarta kuwa tana tararrabin kada Maman ta biyo bayanta. Yanayinta na mai son boye zahirin halin da take ciki ya fi komai damunsa. Karamar yarinya ce da ta dauki nauyin saita mahaifiyarta da boye aibunta. Abin da shi Munzali mai shekaru da suka kusa rubanya nata bai yi ba duk kuwa da shawara da fadan amininsa. A lokacin da Abbati yake masa wannan fadan yana ganin tamkar bai gama fahimtar matsalarsa bane tunda ya tashi gaban uwa tagari. Sai gashi ya hadu da Mardiyya cikin yanayin dake kusanci da wanda ya taso a ciki. Kuma tana gwada sabanin abin da y
a dinga yiwa tasa mahaifiyar.
Girmanta ne ya karu a idanunsa tare da wata irin soyayya mai ratsa zuciya. Murmushi ya yi mata ganin duk ta takura kanta tana ta waige waige.
"Ashe nayi kuskuren tunanin zan zama mai baki shawara game da abin da ya shafi rayuwarki Diamond girl."
A razane ta dube shi sai ta sadda kanta kasa saboda kallon da yake mata ya nuna maganarsa ta jindadi da yabawa ce.
"Idan baka bani ba wa ka samu da zai bani?"
Ido cikin ido ya kalleta ya kuma kada yatsansa yana mai gargadinta da kada ta kaucewa kallonsa. Daurewa tayi ta cigaba da kallonsa zuciyarta tana rawa.
"Zuciyarki ce za ta dinga bamu shawara Mardiyya. Da ka nake tafiyar da personal matsalolina. Amma na gane kan yana kuskure domin a zuciya ne akwai jin kai da tausayi. Tawa zuciyar kuma karama ce akan taki ta wannan fanin. Shin za ki karbi amanar wannan bawan Allahn dake neman hasken bin iyaye ki gyara masa rayuwa? Kin amince na gabatar da kaina a matsayin manemin aurenki? Za ki iya aurena nan da wata hudu da kin kammala secondary?"
Murmushi tayi ta cukwikuye fuskarta cikin mayafi. Ga duka tambayoyinsa tana gyada kai na amincewa.
Farha kuwa da ledoji biyu masu dauke da abincin da aka raba na reception ta fito. An yi packaging abincin cikin mazubin roba mai kyau sai lemon ginger da zobo a robobi suma duka masu kyau da dadin rikewa. Ledar da aka saka su a ciki ta gaba sunan ango ne da amaryarsa. A baya kuwa tana dauke da tambarin /D Delight/ kwararru wajen girkin taro tare da abin sha (online cooking classes for Ramadan coming soon in sha Allah. Come and patronize Batul Mamman please.)
Abbati kadai ta hango saboda Munzali yana tare Mardiyya. Tun kafin ta karaso suke yiwa juna murmushi.
"Ya Farha kin tayar min da duka kishina da wannan kwalliyar. Ina tafiya ki je ki goge indai ba a ciki zaki zauna ba."
Dariya tayi a hankali "so ka ke na dauka da gaske kake har na fara jin nima na isa?
Harararta ya yi da jin furucinta ta cigaba da yi masa dariya. Dolensa ya soma tayata domin
gabadaya yana neman shagala da kallonta.
"Kin yi yawa ma. Kin kuma san da haka. Fatana kawai kada Allah Ya kawo abin da zai iya shiga tsakaninmu."
"Kana ganin akwai?" Sai kuma tayi murmushi "kodayake yawancin kullum sai naci karo da sakon Malama hide my ID idan an kawo kararku."
"In sha Allahu ba zan taba yi miki abin da zaki kaini kotun social media ba." Ya furta da alamun tsoron da ta zata na wasa ne.
"Allah Yasa"
Kasa hakuri ya yi ya dora da cewa "ko kin ji wani abu nayi miki rantsuwa ko meye ya zama tarihi. Zan zame miki miji nagari in Allah Ya so."
"Allah Ya yarda" ta amsa da karamar murya.
"Da gaske nake sonki Ya Farha. Burina na zama mijin da babu abin da zaki ji a kaina ki yarda kai tsaye ba tare da bincike ba."
Kalaman nasa sun fara bata tsoro. Shi kuma firgicinsa akan tunanin idan gaskiya tayi halinta watarana ne. Rokonsa tayi da sigar da bai ga kofar kubucewa ba.
"Kayi min alkawari daya Ya Abbati..."
"Kina son wani abu ne bayan ni?"
Girgiza kai tayi tana murmushi "kwantar da hankalinka ba mutum bane."
"Au tohh. Ina jin ki. Nayi alkawarin."
"Babu zancen sirri ko rufe wani abu da zai zo tsakaninmu nan gaba. Ko aure ka ke son karawa ka fada min da wuri ba don neman izini ba sai don bani da boye boye kuma bana son ayi min."
Jikinsa ya yi sanyi kalau yaji tsana fiye da ta baya game da rayuwarsa.
"In sha Allahu irin zaman da zamu yi kenan. Kuma tunda kin amince min zan sanar da iyalina game dake tun kafin iyaye su zo."
Hira suka soma gwanin sha'awa basu ankara ba ashe Alh. Tahir ya fito kiran Suhaib domin kiransu Abbati cikin falon. Da ya hango Farhansa tare da Abbati sai da yaji zuciyarsa ta wani takure a kirjinsa. Abu ne dai bai taba ji ko gani ba tun tasowarta. Damuwar da suke da ita shi da Mami akan wannan matsala yana sa ran cewa ta kau. Tahowa ya yi garesu fuskarsa a sake ya ma manta da fushin Farha.
Ita ta fara ganinsa ta daure fuska sosai. Bata da yadda zata yi da zuciyarta akan bakincikin
hoton da kwakwalwa ta kasa gogewa. Mahaifinta dauke da kawarta akan cinya daga shi sai dogon wando da singeleti. Wannan abu har ta koma ga Allah bata jin zai taba fita daga ranta. A yadda kuma abin yake mata ciwo har yanzu ta san bata da karfin gwiwar fuskantarsa ba tare da tayi abin da za ta yi nadama a gaba ba.
Gajeren tsakin da zuciya tafi karfinta a kai ne ya fito ba shiri a lokacin da take cewa Abbati,
"Don Allah zo mu koma daga can saboda idon mutane."
Yaji tsakin sannan kuma muryarta ta sauya lokaci guda. Juyawa ya nufi yi domin ganin wanda ya bata mata rai sai yaji ta ce,
"Kar ka juya mana.."
Sai dai ya riga ya ga Alh. Tahir din wanda fuskarsa take tamkar gonar auduga. Ya juya ga Farha ita kuma tata babu annuri ko digo sai ma kwalla da ta cika mata ido. Sai yaki motsawa daga inda yake.
Yana ganin ta fara tafiya bai san lokacin da tasa muryar ta fito da sigar umarni ba.
"Dawo ki tsaya."
Sau daya ta kalli fuskarsa wadda ta sauya shi ma babu wasa ko kadan taji kafafunta sun daskare a wurin.
Alh. Tahir yana karasowa Abbati ya durkusa cike da ladabi ya gaishe shi. Ya amsa masa tare da mikar dashi tsaye ta hanyar dago hannuwansu da suka yi musabaha. Wanda kuma Alh. Tahir din ne ya mika masa.
"Tashi tashi ai ka zama dana."
Wajen sati guda sai yau yasa Farha a idonsa. Amfani ya yi da albarkacin idon Abbati ya janyota barin jikinsa.
"Farhan Abba wato tun yanzu za ki min ritaya ko?"
Da kyar ta saki jiki ta rabu da jikinsa amma har runtse idanu tayi saboda tsigar jikinta da ta tashi. Mahaifi! Sanin mahaifinka yana zina daban da ganin mahaifinka a yanayin da ya kusanci zina. Yanayi mai nuni da cewa anyi ko ana gabar yi. Its devastating! Kada Allah Ya hadamu ko zuri'armu da mummunan gani irin wannan.
Abbati dake dariyar kalaman Alh. Tahir bai fasa la'akari da yanayinta ba. Hakan ya tuna masa da abin da Suhaib ya yi rannan a gabansu na kin zuwa gaishe shi. Ko ba a fada ba ya gane akwai matsala kenan.
"Ki bamu aronsa kakaninki da baffani zasu gaisa dashi." Cewar Alh Tahir. Sannan ya dubi Abbati "ina fata kai da abokinka da gaske kuke akan 'ya'yana. Idan akasin fahimtarmu ne a gabanku don Allah kada ku yaudaresu."
"In sha Allahu ba za mu baka kunya ba" Abbati ya furta kai a kasa.
Alh. Tahir sai ya murmusa "Allah Ya muku albarka. Bari na nemi Suhaib a waya ya shigo daku wurin 'yan uwana."
Da haka ya tafi. Farha ma sai ta daga kafa tana shirin barin wurin. Da muryar dazu ya ce,
"Farha."
Kiran ya fadar mata da gaba. Ya tuna mata cewa Abbati babba ne ta kowacce fuska akanta. Ko Suhaib bai isa ya kara dashi a shekaru ba balle ita. A hankali ta juyo suna hada ido sai hawaye ya soma gudu a kumatunta. Kallon roko da magiya tayi masa sannan ta fadesu da baki.
"Don Allah kada ka tambayeni komai."
Sai ya sami kansa da yin murmushi "bani da niyar tambaya. Amma duk da haka ina da abin cewa idan kin bani dama."
Sai ta dawo ta tsaya sosai lokaci lokaci tana goge hawayenta da bayan hannu.
"Yanzu kin ga idan ba ni ba babu wanda zai ce kin burge shi da wannan fuskar da ta baci da kwalli."
Sai da yaga murmushinta ya soma magana a nutse.
"Ya Farha darajar mahaifi da mahaifiya ta girmi komai da kowa banda da'a ga Allah da ManzonSa SAW."
"Na sani" ta ce a raunane wani hawayen yana zubowa.
"Ina mai baki shawara da kiyi amfani da wannan ilimin ki bi hanyar da ta dace ta mu'amalarki da Abba."
Babu wasa ko damar tayi masa musu a maganganunsa. Cigaba ya yi har sai da ta fashe da kuka sosai.
"Allah SWT Ya yi mana dukkan gata da bai watso mu cikin duniya ba tare da iyaye ba. Daga Mahaliccinmu sai Annabinmu sannan iyaye a girman daraja. Allah Ya ambaci yi Masa biyayya tare da da'a ga iyaye a wurare daban daban cikin littafinsa mai tsarki. Karshe ma dai iyayen nan kin sani saboda adalcin musulunci ya horemu da kyautata musu ta kowacce siga koda mushirikai ne. Illa iyaka kada mu yi musu biyayya wurin saba Masa. Tunda sune abu mafi kusanci da suke tuna mana da Girma da Buwayar Allah. Cikin hikimarSa ya hado mutane biyu mabanbanta jinsi da komai Ya ce musu ga amanar bayiNa wato 'ya'ya. Sai ki ga mutum har sata ya kan yi domin ciyarwa ko dauke wata lalurar wannan amanar. Wani ayi ta cin zarafinsa a wurin aiki amma ya yi ta jurewa saboda albashinsa shi ne abincin 'ya'yansa. So many things dai da ba sai na fada ba. Wasu irinmu mu da bai bawa 'ya'yan ba har kuka muke muna fargabar ko girman zunubanmu ne yasa Allah bai bamu amanar bayinSa su zo a matsayin 'ya'yanmu ba..."
Kuka ta fashe dashi domin ya gama daureta da jijiyoyinta. Ta san Qibdiyya ba 'yarsa bace kuma bai ce mata yana da d'a ba. Amma da ya fada da bakinsa sai da ya tabata fiye da zato.
"Kayi shiru don Allah, za ka haihu in Allah Ya so....na fahimci kuskurena kuma Allah zan gyara."
"A yau ba gobe ba?"
"A yau ba gobe ba."
Murmushi ya yi ya ce "Allah Yasa ke dinnan rabona ce ta duniya da lahira"
Amin ta ce yadda zai ji domin ita kam bata jin kunyar ya san cewa tana yi masa soyayya mai girma. Duk mutumin da zai gan ka a irin yadda ya ganta ya kuma zauna yana kokarin ganin ka gyara lahirarka baka da na biyunsa.
Basu gama hirar ba Suhaib ya zo suka wuce cikin falon tare da Munzali. Da wasa da dariya
dattijan suke yi musu tambayoyi har aka gangaro kan sana'a. Bakinsu a hade suka ce kasuwanci suke yi. Iyayen sun yaba da halayyar da suka gansu
a kai aka shiga barkwanci.
Wannan lokacin Shazali ya zaba ya kira Abbati. Kiran da Munzali ya fito ya same shi a mawuyacin yanayi a dalilinsa. Jijiyoyin kansa duka sun fito sai gumi da yake tsatstsafo masa saboda firgici.
"Allah mun tuba. Allah Ka rufa mana asiri"
Kalmominsa kenan har suka shiga mota a gigice suka tafi ko sallama basu koma sun yiwa kowa ba.
"Idan ya fada mata wallahi da kyar in bata tsine min ba. Munzali yaya zanyi da rayuwata kuma? Me zai rage min idan Baaba taji wannan zancen?"
Abbati kuka yake yi. Kuka kamar karamin yaro. Irin kukan da ya manta rabonsa da yin makamancinsa. Bai hada iyaye musamman Baaba Mari da kowa ba. Ita ce mafi girman gatan da Allah Ya bashi domin ba don ita ba kila bayan waccan dabi'a sai ya hada da wasu munanan alfashar.
Munzali ma kukan yake yi ya kuma kasa rarrashin Abbati. In ta kwabewa daya ta kwabe musu ne su duka. Hanyar Kirikasamma ya dauka ba tare da tunanin komai ba.
BAKWAI RANAKUN...
Kallon jan fentin da aka yiwa alamar (
) a jikin gidanta Uwani tayi taji jiri yana dibarta. Tambayar Salihi ta dinga yi cikin sarkewar harshe kamar ya san wani abu a kai.
"Me nayi? Ina da takardun filin nan da sa hannu wanda na saya a wurinsa. Kai hatta Mai unguwa sai da muka je yasa hannu a matsayin shaida."
Duk da yana cike da haushinta sai ta dan bashi tausayi a lokacin. Ba kuka take ba domin tana da bala'in dakakkiyar zuciya. Jikinta ne kawai ya saki sannan sautin muryarta ya fallasa tsoro da tashin hankalinta.
"Ki kwantar da hankalinki tunda akwai takardu za a warware cikin sauki in sha Allahu."
Sambatu ta dinga yi kamar ba da ita yake ba. Katangar gidan ta nuna masa inda tasa aka yi baya da ita kawai don tana son ayi mata rela samma tana tsoron kar ta shiga filin gwamnati. Shi dai hakuri ya bata har suka koma mota tare da Mubashir a baya. Niyarsa su je gida ta amsa kiran Innayo sai ta kafe akan lallai ofishinsu can Ministry of Health zata je ta sami Habibu.
"Shi ne ya jagoranci sayen filin da komai. Zuwa zai yi ayita ta kare don wallahi asara bata kamani ba."
"Waye kuma Habibu?" Salihi ya tambayeta. Bacin ransa na dawowa sabo fil.
"Abokin aikina ne. Shi ya tallata min filin ya kuma shige min gaba."
"Tunda kin auri lusari ai dole wani kato ya fini sanin halin da kike ciki Uwani."
A kausashe Salihi yayi maganar wanda yasa Uwani shan jinin jikinta. Borin kunya ta soma yi masa saboda ta san bata da gaskiya.
"Damuwa kayi dani da zaka san me nake ciki? Ko kai ba aure kayi ba tare da sanina ba? Habibu duk inda yaji harkar karuwa zai nemeni. Kafin ka ce ban fada maka ba ma shi na bawa ya biya min kudin Hajji. Bana damu za ayi 'yan bakinciki su daina hura mana hanci."
Da kannensa mata take ya sani. Shi yasa bai ce komai ba har suka isa gate din BUK ya sauke Mubashir. Kai tsaye ministry din ya nufa sai ga waya an kirata. Koda ta duba sunan (Costumer) ta gani ya bayyana. Murmushi a take ya maye gurbin bacin ranta. Amsa kiran tayi taji muryar Hajiyar nan da ta haihu tana yi mata magana cikin nutsuwa. Uwani ta ajiye komai a gefe ta saurari kwatancen gidan da matar tayi mata.
"Ka saukeni 'Yan Kaba zani" cewar Uwani ga Salihi.
"Ai ko direba nake ya kamata ki rissina lafazinki gareni."
Yatsina fuska tayi ta gyara lullubi sannan ta hayyako masa da fada tana jin kanta daidai da kowa tunda ta tabbatar zata sami kudi. Cikin kudin za ta bawa Habibu a kashe kurar dake neman tashi a gidanta su sallami KNUPDA.
"Sau nawa nake cin arzikin shiga motar taka da har zaka min gori? "
Girgiza kai kawai ya yi "wurin wa zaki a 'Yan kabar?"
"Stitches zan yiwa wata."
"Allah Ya kiyaye hanya."
Sauketa ya yi ta fita ta shiga adaidaita sahu. Yadda yake jin bacin rai ba zai juri ja in ja da ita ba. A yau kadai ya gane har yawon dinke mata take zuwa bai sani ba. Sai yake jin kamar ma bai san wace ce yake aure ba. Karya kwana ya yi ya nufi Ministry din yana son ganin wannan Habibun domin zuciyarsa taki nutsuwa. Ba wai zarginta yake ba domin ya yarda da ita dari bisa dari. Duk bakin halinta ya yarda za ta tsare mutumcinta duk inda take. Harka dai ta kudi ce bashi da tabbas. Idan yana son gyara lamuranta ya kamata ya fara da sanin abokan huldarta.
Da kwatance da kiran waya Uwani ta isa gidan CMD. Bata wani sha wahala ba saboda kwatancen dalla dalla ne duk da ba a fada mata sunan maigidan ba. Hankali kwance ta shiga wani makeken falo bayan anyi mata iso. Gida ne babba irin wanda take burin mallaka wataran. Nan da nan ta sake ganin kimar hajiyar tana tunanin yadda za ta tatsi naira jikinta da kawayenta matan masu kudi.
"Haj. Umma ta ce ki shigo ciki"
Muryar mai aikin da ta shigo da ita ta katse tunaninta. Sai lokacin taji sunan matar. Wata kofa suka bi sai gasu a wani falon da ya shafe shafin inda ta baro. Sai da ta zauna akan wata luntsumemiyar kujera sannan matar ta tafi. Kimanin minti bakwai sai taji sallamar Hajiyar. Fuska ta saki tana mai kara raina kanta. Kama daga sutura zuwa su sarka babu ta inda Haj. Umma bata burgeta ba. Tashi tayi cikin girmamawa tana yi mata sannu.
"Ya karfin jiki da jaririnmu?"
"Alhamdulillah Matron Uwani. Ya gajiyarki?" ta amsa fuska a sake.
Zama suka yi Haj. Umma ta ce bari ta kira Maigidan su gaisa sai su shiga daki ayi. Uwani taji kamar kakarta ta yanke saka yau. Idan tayi sa'a mijin mai alheri ne ai kila shi ma ya bata wani abu. Irin wannan mutanen idan sun yi maka kyauta baka cewa a'a.
Kamshi ta fara ji kafin sallamar babban mutum cikin wani irin yanayi na seriousness. Kasa dagowa tayi har ya zauna ta gaishe shi.
Muryarsa babu alamun wasa ko digo taji ya kirata da cikakken sunanta. Wani abu da yasa hanjin cikinta kanannadewa da juna cikin azama.
"Matron Uwani Rabi'u!"
Haka ta daga kai jiki na tsuma. Fuskar da ta gani sai da ta kusa sakin zawo. Basu taba haduwa kurkusa ba amma karya take ta ce bata san kamannin CMD dinsu ba.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta dinga maimaitawa ba ji ba gani da karfi ga gumi yana bin sassan jikinta.
Dakewa ya yi domin ba abu bane mai wuya ya tausaya mata ya fasa hukuncin da ya dauka. Bai manta da zantukansu da maidakin nasa ba. Inda take cewa yiwa Uwani sako sako tamkar an ce ita ko wasu su cigaba da haka ne. Dole ne ya tauna tsakuwa domin aya taji tsoro. Laifin Uwani mai girma ne. Gara ace matan ke nemanta da abin da take yi. Akalla idan su suka nemeta a waje babu ruwan asibiti. Yanzu kuwa ana samun tangarda basu da mai kwatarsu a hannun hukuma tunda ma'aikaciyarsu ce.
Envelop ya nuna mata akan karamin teburin gilas na gabanta.
"Dauki ki tafi."
"Ranka. Ranka. Ya dade. Ranka ya dade.." ta soma magana tana waigawa ko matar tasa zata fito.
Katseta ya yi ganin za ta bata masa lokaci. "Idan hukuncin da yake ciki bai yi miki ba kina iya kai batun Ministry."
Kafin ta samu bakin magana ya fice abinsa. Kasa bude takardar tayi saboda faduwar gaba. Kafafunta kamar an kwashe mata kasusuwa don kiris ya rahe ta zube a kasa. Kirjinta kawai ke dukawa tare da azababben ciwon kai. Ko a mafarki abubuwan da suka faru yau suke samunta ta san cewa sai ta tashi da hawan jini. Shigowar Haj. Umma wannan karon fuska a tamke ya kara tayar mata da hankali.
Ita mamakin kasadar Uwani ma take yi.
"Allah Yaso ki duk wadanda kike yiwa aiki ta wannan sigar babu wadda nata ya baci ta shigar da kara kotu. Da license dinki ya dade da barin hannunki. Idan private practice kike son budewa kin san akwai hanyoyi da matakan da ya kamata ki bi domin samun sahalewar gwamnati. Amma son zuciya ya hana. Ace mace tana tsakar nakuda don tsabar rashin tausayi kina tallata mata muguwar sana'arki?"
Kalaman cin mutumci ne suka taba fita daga bakinta ga abokiyar aikinta lokacin da ta taba
yunkurin hanata wannan sana'a. Ashe kura ta san gidan mai babbar sanda. A gaban Haj. Umma ko tari bata iya yi ba har ta gama magana.
"Ki bashi hakuri Hajiya. Tunda ki ka ga ina wannan abu kin san cewa kudi nake nema."
"Kiyi me dashi? Yasa anyi bincike akanki Uwani don kar ya dauki hukunci bisa rashin uzuri. Kina da miji mai rufin asiri. Har mota gareki balle ace kuncin rayuwa ne ya tasoki a gaba. Neman kudi ba hauka bane so kar ma kiyi kokarin justifying laifinki. Ko kina da wata kebantacciyar bukata hanyar da kika biyo bata dace ba."
A shekaru wannan matar bata fi kanwarta ta uku ba Salima. Don tana auren maikudi shi ne za ta tasata a gaba da bakaken maganganu? Wannan abu ya tunzura zuciyarta taji ba za ta bar gidan bayan an koreta daga aiki ba tare da ta rama ba.
Yatsina fuska tayi tana hura hanci ita a dole girmanta bai zube ba.
"Don kin sa an koreni daga aiki kina tunanin zan daina walwala ne? Ana kiran ciwon 'ya mace na 'yar uwarta ne kamar ba a san mata sun fi kowa son ganin karshen junansu ba? Banda munafunci ai bake nake yiwa tallan ba jiya amma kika yi katsalandan kika ce kina so. Auren maikudi ba zai raba mace da talauci ba ehe. Idan kina son burgewa ki nemi na kanki ki wuce wulakancin namiji."
Tun farko Haj. Umma bata ga alamun mutumci a tare da Uwani ba. Sai dai ko kadan bata kawo a ranta abin ya kai haka ba. Ranta ya sosu matuka amma haka ta daure taki magana har Uwani ta dire tana yi mata kallon banza. Hannu ta kai ta dauki envelop din da Uwanin bata kai ga dauka ba ta yaga shi gida hudu ta watsar a kasa.
Uwani tabi takardun da kallo tana kissimawa a ranta rashin nuna tsoronta ya yi rana. Karshenta matar ta tsorata ne taga gara a bar mata aikinta. Murmushi ta soma yi sai dai bai kai ko ina ba idanunta suka soma cikowa da kwalla sa'ilin da Haj. Umma ta soma magana.
Tsaye take kyam kana ganinta ka san mace ce da ta san kanta. Sai tayi mata wani irin kwarjini.
"Suspension ne na wata hudu hukuncin da aka yi miki ba tare da kai zancenki ministry ba. Anyi miki haka ne domin kada mu rabaki da aikin da bamu san irin WAHALAR DA IYAYE suka yi wurin karatunki ba. To amma Uwani kin yi kuskuren fada min maganganu son ranki a cikin gidana. Ki koma bakin aikinki daga yanzu idan kin so. Sai dai ina so ki sani cewa in sha Allahu indai ni Barr. Umma Jibril ina numfashi sai kin rasa license dinki ba ma aiki ba."
Wuta ce dif ta dauke a kwanyar Uwani
'Barr. Umma Jibril din da kusan duk mai jin Rediyo Kano ya sani?' ta tambayi kanta a zuci. Amsa ta bawa kanta domin tana jin sunan ta alakanta muryar da wadda take ji a rediyon.
Da tangadi ta bar gidan don ji take kamar duniyar da ta sani aka kifar. 'Yan uwa da iyaye da mijinta bata ga wanda ba zai yiwa halin da take ciki dariya ba. Zasu samo mafita ko ta wane hali ita da Habibu. Ya san manya a matakai daban daban na gwanati. Idan ta rasa aikinta ta rasa matattakalar rayuwarta ne. Shi ne abin da ta dogara dashi wanda zai kangeta daga talauci.
Habibu ta kira. A lokacin yana tsaye a gaban Salihi yayi tsilli tsilli da idanu. Tambayarsa ya yi akan ya hada shi da ainihin dillalan filin da tayi gini sannan ya bashi shaidar biya mata kudin kujera.
Mintuna arba'in da suka wuce Salihi ya tambayi masu gadi ko akwai Habibu a wurin. Tashi daya suka amsa da cewa akwaisu har uku. Biyu manyan ma'aikatane. Daya kuwa sub-staff ne mai shigewa manyan. Yana jin haka ya ce a nuna masa shi. Da ya sanar dashi cewa shi ne mijin Uwani ba karamin mamaki da tsoro ya gani a tare dashi ba. Tambayoyin da ya yi masa suka sashi daburcewa ya kasa bada kwakkwarar amsa. Sai gashi ta kira a wannan lokacin. Gefe ya dan matsa da niyar bude mata wuta da borin kunya.
"Habibu akwai matsala. Zan shigo ministry yanzu."
Tana cikin tashin hankali a yadda yaji muryarta. Sai ya fasa fadan ya ce
"Don akwai matsala sai ki turo min mijinki ya titsiyeni a cikin mutane?"
Adaidaita sahun da ta tare ta hau. Abin da ya dameta daban da zancen da yake yi shi yasa ta amsa shi ba tare da nuna damuwa ba
"Zuwa ya yi? Yace maka me?"
Habibu sai ya murmusa ya zabi amfani da amsarta ya tada tarnaki tsakaninsu. In ba hakan ya yi ba yau shi za ta karewa.
"Takardun filinki ya ce na bashi da kuma kudin kujerarki. Har yana ikirarin ban isa na fishi sanin matarsa ba. A matsayinsa na mijinki yaba da hakki akan dukiyarki amma ke ce harda yin gini bai sani ba."
Abin ya zo mata bambarakwai saboda sanin Salihi shi yasa ta ce "inji Salihin?"
"Yasin gashi a nan, na baro shi a gefe da zan amsa wayarki. In kin ce na bashi kwafin takardun sai na bayar." Ya rage murya yadda za ta tausaya masa.
"Ka barni dashi. Kada ka bashi komai. Kai kaga ma yi tafiyarka ka bar saurarensa. Wannan wace irin masifa ce?"
Maimakon ya wuce gaba sai ya dawo gaban Salihi ya tunkuda hularsa gaban goshi.
"Da kai bada izinin matar taka kazo yi mata kutse a harkokinta ba? Ta ce kada na baka komai. Ko kunya baka ji ba bayan kayi aure matar ta sami ciki sannan ta sani, shi ne za ka lallabo rabata da arzikinta. Ku kuke janyowa ana zaginmu ace bamu da tausayi. Haka fa kwanakin baya ka matsa mata da sai ta ranta kudin makarantar yara."
Salihi bai taba danasanin auren Uwani kamar yau ba. Banda barin Habibu ya zama uwa da uba gareta yana juyata da sunan shawara harda sirrin gidansa duk ya sani. Allah Kadai Ya san yawan abubuwan da ta sanar dashi. Kala bai iya sake cewa ba ya kama hanyar motarsa yana jiyo dariyar Habibu. Yana hanya
Uwani ta kira shi da tambayar rainin hankali.
"Me kaje yi wurin Habibu?"
"Na baki rabin awa duk inda kike ki sameni a gidan iyayenki."
Da ya ajiye wayar sai kawai ta kama a'uziyya domin ta yarda dari bisa cewa jifa ne ko sihiri aka yi mata. Idan komai zai kwaba bata taba kawowa harda Salihi ba. A zatonta har abada zai kasance tare da ita yana hadiyar bacin rai. Kwafa tayi tare da mugun tsaki lokaci guda da wani tunani ya fado mata.
"Tsafi gaskiyar mai shi. Lallai Mulmule kike ko wa? Ni zaki tarwatsawa rayuwa daga zuwanki?"
Sai kawai ta soma dariya wanda har ya janyo direban adaidaitan ya dinga kallonta ta madubi. Ita kuwa karfin halin amaryar Salihi ne ya saka ta dariyar. A bayyane yake gareta Ummule ce tayi mata asiri. Banda haka me yasa komai bai faru ba sai da tazo gidan? Wata kwafar tayi ta ce da direban Adaidatan ya kaita Dala.
"Hummm inji mai ciwon hakori. Ka magantu azo a fara narai-narai da ido ana neman janyo maka zunubin da ba naka ba."
Furucin Asabe kenan bayan Hasiya da 'yan matanta sun gaisheta sun wuce dakin Innayo. Alh. Rabi'u sai ya zata dashi take saboda sun yi sa'in'sa akan
'yar dangin wa ya kamata a sake hadawa da Munzali cikinsu.
Labule ya daga ya leko da kansa ya watsa mata mugun kallo.
"Dake da Munzalin duka kuna karkashin ikona. Sannan Zakiyyan da suka rabo ba 'yar kanwarki bace ciki daya?..."
Dakatar dashi tayi ta nuna masa dakin Innayo da bakin da ta turo gaba.
"Maida wukar. 'Ya'yan matarka ne naga suna ta sintiri a gidan nan abin ya soma yawa."
Ta tashi ta koma dakinta yana biye da ita. So tayi ta daga murya wurin fadin maganganu amma Munzali ya ce mata ko labari yaji ta sake takalar Innayo sa rigima zai hanata kudin wata.
"Kwanaki Zara ce ta haihu kullum sai sun zo. Auren Salima ya mutu shima kamar wata uwar zasu iya yi mata suka dinga zuwa. Dazu kuma akan idona Maimuna tazo ta wuce da ledoji harda jakar bacco. Ga Hasiya ita ma ta wuce yanzu. Kar ka manta zuwan mijin waccan kankamojin Uwani shi ma ya ce bai ganta ba. Ni dai ka dauki mataki kafin a fara zaginmu a unguwa."
Buguzum buguzum ya fice daga dakinta ya tafi na Innayo. Ta saka dariya ta zauna jiran tashin muryarsa idan yana fada.
Hira ya samu suna yi ga kayan kad'in miya danginsu kuka da daddawa ana ta zuzzubawa a ledoji. A gefe ma akwai ledojin viva biyu cike har baka da danyar masara. Sai kwan zabi cike da katuwar kwarya.
Fuska a sake Innayo ta nuna masa uban kayan dake gabansu.
"Idan kun hadu da Musbahu (mijin Maimuna) kayi masa godiya. Kauye yaje shi ne ya hadomu da abin arziki."
"Ya hadoki dai ke da kike shagwaba shi. Duk wata dawainiyarsu kin dauka kamar ke ki ke auren Maimunan" cewar Alh. Rabi'u cikin fushi yasa kafa ya shure ledar masara guda daya "wai masara kamar wasu mabarata?" 'Ya'yan nasa yabi da kallo saboda duk sun dinke fuska yaja dogon tsaki. Duk tsiyarsu dai shi ne ubansu. Kuma dadin abin yana da Munzali. Tabe baki ya yi kamar anyi masa dole kafin ya fita ya ce "In kun dafa ki miko min inji idan noman ya yi kyau dai."
Tun a gida Maimuna take cikin farincikin wannan kyautatawa ta mijinta ga iyayenta. Kullum sune masu karba a hannun Innayo ko Hasiya, yau gashi ita ma tana da abin kaiwa g
da asa albarka. Sai gashi tun ba aje ko ina ba Alh. Rabi'u ya yi nasarar kawar da murmushinta. 'Yan uwanta duk sun kawar da kai basa son hada ido da ita don kada su karasa sarar mata da gwiwa.
"Ina da itace. Zara tashi kije ki dora masarar nan."
Idanuwan sai suka koma kan Zara. Salima ta mike da hanzari tana cewa bari ta dora. Ga mamakinsu sai Zara ta tashi da rawar jiki. Irin rawar jikin nan na mai son burge wanda ya bashi umarni ba na tsoro ba. Ledojin ta kwasa tayi waje ga uban murmushi ta kasa dainawa.
Sai da ta fita Innayo tayi murmushi tana girgiza kai ta furta kalmar "Zara kenan" da kulawa.
Ita kuwa Zara tana isa waje sai da ta share kwalla. Shareta da Innayo take yi yafi duk wani abu da ya sameta ciwo a yanzu. Daki daya suke kwana amma takaitattun kalmomi ke shiga tsakaninsu. Ta riga ta sauke duk wani dakon rashin albarka da ta dauka akan ahalinta. Shiri take nema da kowa a cikinsu. Da ta dora kin komawa ciki tayi tana ta faman tura icce don tayi saurin dahuwa. Sa'arta daya ma iccen bai nuna mata kurenta ba. Tashin farko ya kama ba tare da ya hada mata hawaye da majina na yaushe gamo ba. Tana jin kukan jaririyarta taki shiga ciki har sai da Hasiya tazo ta kirata.
"Ke kuma daga hura wuta sai kiyi zamanki ki barta tana kuka?" Cewar Maimuna tana mika mata 'yar.
"Naga duk kwadayin cin masara ya kamaku shi ne na zauna ina ta fifita don ku samu da wuri."
Wasa take son shigarwa tsakaninsu. Basu sace mata gwiwa ba kuwa suka dinga dariya suna cewa ko dai akwai sauran bebi a cikinta.
"Ku barta dani take tunda ni na ce a dora."
Zara sai idanu suka raina fata. Gabanta ya fadi. A tsorace ita dasu Mqimuna suka kalli Innayo ta fara cewa
"Wallahi, wallahi..."
Innayo sai tayi dariyar da ta bawa 'ya'yan nata mamaki.
"Lallai ma Zara. Ke ki tsokani 'yan uwanki amma ni ba zan tsokaneki ba?"
Ajiyar zuciya Zara ta sauke su Hasiya ma duk sai suka saki rai. Sun san yadda Innayo ta dauki zafi da ita. A gaban ido da baya duk suna bata hakuri da son ganin ta sakarwa Zara.
"Tsoron bata miki rai nake Innayo." Ta ce a sanyaye wanda ya soki zuciyar mahaifiyar da bata da tamkarta.
Harararta tayi cikin wasa ta ce "Ai kuwa dai ya soma baci tunda kin bar min jika da yunwa."
A gaggauce Zara ta gyara zama ta rungume 'yar a jikinta sosai. Ta kalli su Salima kowa murmushi yake mata. Innayo ta sake shayar da ita mamaki da ta ce,
"Komai ya wuce Zara ki daina saka damuwa a ranki. Allah shaida na yafe miki duniya da lahira. Rashin zuwan maigidanki da yara duk ba wani abu bane indai kin sami lafiya. Muna nan da yardar Allah zaki ganshi dasu."
Allah Sarki, Zara sai hawaye "na gode Innayo. Salima kuma ku yafe min. Don bakin halina yarinyar nan ko suna bai saka mata ba har yau."
"Allah Ya san sunan da Ya halittota dashi. Kada ki sake tambayarsa." Cewar Innayo ta sake sako wasa don ta kawar da damuwarsu "ni dai a dafa min masara in mayar da mugun yawu."
Kusan tare yaran nata da ita kanta suka saka dariya. A zuciyarta tana jin wani irin farinciki wanda yafi kudi da duk abin da kudi zai saya.
Dariyarsu ce ta kawo Asabe wadda take mamakin ko Alh. Rabi'u bai yi musu yadda ta ce ba. Zuwanta ya yi daidai da tambayar da Hasiya ta yiwa Innayo akan dalilinta na cewa a dafa masara bayan abin da babansu ya yi mata. Su duka sun kasa gane dalilin rashin nuna fushinta da abin da ya yi. Asabe ta kasa kunne da kyau domin kwasar gulma ta kara hada fada.
"Allah ne fa Ya ce kada mu zata don mun ce munyi imani ba zai jarabcemu game da 'ya'ya da dukiyoyinmu ba. Da rayuwa tana tafiya da burin dan Adam da babu wanda zai yi kuka da komai. To amma yawan jarabawa da hakuri da ita karin daraja ne a aljannah. Tunda Allah bai bani kudin yin sadaka ba ba zan butulce don Ya dora min wannan rayuwa ba."
Hawaye ta sanya 'ya'yan nata. Suka kara ganin kima da darajar mahaifiyarsu. Ana haka
Salihi ya iso. Bai jira isowar Uwani ba ya ce da Innayo idan ta zo ta ce mata ta zauna.
Abin da ya fadi ya tabata sai dai dama ta san dole akwai ranar da tura zata kai bango. Ya yi hakuri na ban mamaki a zamansa da Uwani.
"Wani abin ta sake yi?"
Murmushin bacin rai ya yi "ta dai zauna. Idan zuciyata ta sanyaya zan zo ki mana hukunci. Mubashir zai kawo mata kayanta."
Bata taba ganin suruki irin Salihi ba. Nauyinsa ta kara ji. Yana da iyaye da 'yan uwa amma har kullum bai gazawa wurin kokarin rufa asirin matarsa. Ta rasa wace irin zuciya ce a kirjinsa mai matukar hakuri da zurfin tunani. Ba shi ta haifa ba amma ya iya zuwa debe mata kewar 'yarta yana kuma bata hakuri akan halayyarta. Yau kam ta tabbatar Uwani bata yi masa da wasa ba wajen bata masa rai. Za ta bashi hakuri ya ce don Allah ta bari. Uwani ce mai laifi don ta haifeta ba za ta dauki nauyin laifinta ba. Bai jima da fita ba uwar gayyar ta iso.
Innayo taji kamar ta rufeta da duka akan amsar da ta bayar bayan ta fada mata abin da Salihi ya ce.
"Ba zan yi mamakin duk wani abu da zai yi min ba yanzu tunda ya auro matsiya... "
"Rufe min baki shashashar banza. Kina girma halinki yana kara tabarbarewa. Akanki ni ba sai dai na ce banga ranar boko ba? Ke kadai kika same shi mai yawa a cikin 'yan uwanki amma banda hauka bai kareki da komai ba."
Haukan ta nuna ziryan inda ta kada baki tana hurawa kannenta hanci ta ce "ai kuwa boko ya min komai Innayo. Na sayi mota, nayi gini sannan na biya kujerar Hajji."
'Ikon Allah' Innayo ta sami kanta da cewa cikin wani irin yanayi a zuciyarta. Bata cikin iyaye masu saka ido akan kudin 'ya'yansu amma bata jin duk hakurinta zata so ace bata san cigaban yaranta ba. Babu abu daya da Uwani ta lissafa wanda zata yi mata shamaki da mallakarsa. To me ya hanata fada mata ko addua ta tayata da fatan alkhairi. Abin bai yi mata dadi ba ko kadan. Murmushin fatar baki tayi mata tare da fadin,
"Sai ki wuce gidan naki kafin mijin naki ya sakko."
"KNUPDA sun kwace" Uwani ta ce tana tura baki kafin kuma cikin sauri ta dora da yi musu bayanin cewa zata je a daidaita don kada suyi mata dariya.
Dariyar da ta guda ita Innayo tayi.
Bayan tafiyar kimanin awa daya da rabi sai ga wayar Suhaib. Munzali ya samu a lokacin. Ya jima yana kiran layukansu shi da Abbati amma duka sun ki shiga saboda raunin service na hanya. Da ya same su kuma aka rasa mai daukar wayar cikin su biyun. Gara ma Munzali tuki yake. Abbati kuwa ragowar karfin halinsa ne yaji yana neman kufce masa da yaga sunan mai kiran. Kira hudu ya musu a jere ta wayar kowa sau bibbiyu sannan ya hakura.
A gidan bikin iyayen nasu duk sun damu saboda an san cewa wayar da Abbati ya amsa ce ta tayar musu da hankali har suka tafi.
Yayinda Mardiyya take ta kiran Munzali saboda halin da ta shiga na taya shi jimamin damuwar da ake tsammanin suna da ita, Farha
bata kira Abbati ba ko sau daya. Ko ma mene ne ta fahimci gagarumi ne tunda ya bar gidan ba tare da ya yiwa iyayensu da suke tare sallama ba. Za ta jira zuwa gobe idan ba a ji daga garesu ba ta bangarenta ko 'yan uwanta kafin ta kira. Addu'a kawai ta zauna tana yi don bikin ya fi
ce mata a kai. Da Suhaib ya ce wayoyinsu na shiga ba a amsawa sai ta tura masa text.
(Allah baya dorawa bawa abin da yafi karfinsa. Wannan alkawari ne daga
Mamallakin dukkan halitta. Ina fata Allah Ya kawo muku saukin abin da yake gabanku. Luv, Ya Farha)
Karar shigowar sakon ya kada duk wani abu dake yawo a jikin Abbati. Fargabar barnar da yake tunanin Shazali ya yi masa ta shafe komai a kwakwalwarsa. Wayar tana aljihunsa amma jikinsa ya bashi daga ina sakon yake. Jiki a sake ya dauki wayar ya bude sakon. Numfashi kawai ya dinga ja yana saukewa da sauri da sauri.
"Shazali ne? Me ya ce?"
Munzali ya tambaye shi da yaga yadda ya kara birkicewa.
"Farha ce."
"Nima tun dazu Mardiyya take kirana."
Shiru suka yi na lokaci har suka isa Gumel. Fadan irin tashin hankali da tsoron da suka sami kawunansu a tsukin lokacin ma bata baki ne. Gidan mai suka shiga suka kara mai tare da yin sallah. Sun kusa barin garin Abbati ya ce da Munzali ya yi parking. Gefe ya gangara ya fuskanci Abbati ba tare da kashe motar ba.
Yana tsayawa Abbati ya kama kofar ya bude. Kafarsa daya a waje ya juyo ya kalli Munzali mai binsa da ido da alamun tambaya.
"Ka koma Kano zan wuce ni kadai."
A razane Munzali ya dube shi maganar tana dukansa ta ko ina.
"Me ka ke nufi?"
Kadaici yake bukata? Tsoron haduwarsa da Baaba Mari? Tabbacin rasa Farha na har abada? Hasashen girman tashin hankalin da zai wanzu a gida da garinsu? Babu abin da ahi kadai bai isa ya haukata tunanin shi ba. Sai gashi su duka da ma wasu suna jiransa. Bai san ta ina zai fara ba, amma gara ko meye ya tunkareshi shi kadai tukunna.
"Don Allah Munzali ka koma. Tunda kaji na ce ka barni ni kadai ka san bani da zabi ne."
Yawu mai daci ne ya wuce ta makoshin Munzali. Ko ba a fada ba ya san cewa Abbati ya gama sarewa da komai. Yau din rana ce da za ta zama mafarin wani abu da bashi da suna a rayuwarsu. Kuma har ga Allah Yafi kowa sanin cewa tonowar asirin Abbati ba kamar nasa bane. Abbati ya tashi cikin dangi da iyaye. Duk wani rikicin cikin gida bai raba kan iyayensa ba. Shi kuwa ko yau iyayensa suka ji bashi da abin da ya wuce dora musu alhakin komai. Darajar Qibdiyya da kuma 'yan uwansa da ya fara sabunta zumunci dasu ne ababen dubawa. Sai kuma masoyiyarsa Mardiyya wadda ko kadan baya son abin da zai shata layi tsakaninsu. Mafi girman damuwarsa kuwa tana tattare da bakincikin shi ya batawa Abbati rayuwa. Numfasawa ya yi bayan ya dan yi nazari.
"Kana nufin za ka je ka tonawa kanka asiri ne ni kuma na zauna? Waye silar shigarka wannan rayuwa."
Hannu Abbati ya nuna masa "kada muje nan wajen."
Rai ya soma baci Munzali ya ce "to ina zamu je? Ba ni bane? Ba don ka hadu dani ba da yanzu kana rayuwarka cikin kwanciyar hankali."
Kafin ya gama maganar idanunsa sun yi jajir. Zuciyarsa a kuntacce take yana jin yadda take zafi. Ya sake bude baki zai yi magana Abbati ya dakatar dashi da cewa,
"Don Allah kayi tuki a hankali."
Duk yadda Munzali yake son yi masa musu haka ya hakura ya tafi bayan shigar Abbatin motar haya.
Mummunan faduwar gaba ne ya sami Baaba Mari har ta saki butar hannunta da taji muryar yaran gidan suna yiwa Abbati barka da zuwa. Sake dibar ruwa tayi cikin rawar jiki duk tana zuzzubarwa ma ta kuma cika botar ta zauna za tayi alwalar Isha'i. Jikinta har wani karkawa yake saboda tashin hankali. Tunda ya iya biyo dare ya taho garin a yau da basu kwana da shirin zuwansa ba ta san babu lafiya. Tabbas babu ko tantama Abbatinta bashi da gaskiya. Da babu wata a kasa tun dazu zai kirata ya karyata zantukan da taji sunyi a waya da Shazali. A yadda zuciyarta take dakan lugude a kirjinta kuwa a lokacin ko me ya fada a waya zata amince. Yardar ta zame mata wajibi ko don kada bakincikin jin gaskiya ya kwantar da ita.
Shi kuwa a bakin kofar da zata sada shi da sashen mahaifinsa ya tsaya tun shigowarsa. Idanunsa da suke cike da kwalla suka sauka akan Baaba Mari tana alwala. Ya gama karanta da fahimtar duk wani motsinta. A firgice take! Alwala take yi amma sam hankalinta baya jikinta. Shafar kai kadai wadda da wuya ake kuskure adadinta saboda sau daya ce sai da tayi biyar akan idonsa. Ya lura duk gabar da ta kama sai ta dawo hayyacinta take tafiya ta gabanta. Bai san kuka yake ba sai da yaji ruwan da zafinsa yafi wuta a zuciyarsa yana bin kumatunsa. Asalin kunci da damuwa ne suka rufe shi ya juya a hankali ya fita daga gidan.
Kofar gidansa yaje tun daga dan nesa yake hango hasken tocilan din wayoyi guda uku a wurin. Bai yi mamakin ganin 'Yashshafa da wasu 'yan mata sa'o'inta biyu ba. Su ma duka kannensa ne kowcce da tsintsiya a hannu.
"Gwaggo Deluwa ce ta aikomu muyi maka shara kafin a kawo abinci."
Guda cikinsu ta fada bayan ta gaishe shi. Mukullin kawai ya mika musu ya juya masallaci. 'Yashshafa bata manta gargadin Deluwa ba tayi saurin cewa a dawo lafiya.
"Ki kwantar da kai ki kyautata masa domin mu sami biyan bukata."
Cewar Deluwa mintuna kalilan da sallamar Abbati cikin gidan.
'Yashshafa tana dirzar kafarta da dutsen goge kaushi ta daga kai tana zumburo baki.
"To wai ni Inna haka za kiyi ta min ne? Yau ki ce in daina sakar masa fuska gobe in saki? Yaushe zai soni a haka?"
Deluwa ta murmusa tana wani jijjiga kai
"Yaro man kaza. Banda abin ki 'Yashshafa idan baki kwantar da kan ba ta yaya zamu samu ya baki lambar shi Sha'aib din cikin sauki?"
Cigaba da dirzar kafarta tayi cikin yanayin ko in kula ta ce "Inna ki bar batunsa don a ranar ko kallo ban ishe shi ba."
Harara mai kyau ta samu kuwa sannan cikin fushi Deluwa ta ce mata,
"Ta yaya zaki san me yake faruwa a lokacin nan kina can kina kukan shanu? Kar ma ki zata dominki na damu. Tausayin yaron da mutumcin uwar tasa ne yasa nake ta kokari. Ni kadai na san me na gano a kwayar idanunsa game dake. Jikina ya bani suna ta nemanki ta wurin Abbati. Amma don mugunta yaki hadaku. Su kuma 'yan birni ba wuya ciwon zuciya ya kwantar dasu saboda da gaske suke soyayya."
Tabe baki 'Yashshafa tayi bayan tafiyarsa tabi 'yan uwanta cikin gidan. Daga Abbatin har Suhaib ta san bata gabansu. Ita din ma ta turesu daga gabanta. Kwanakin nan mutum daya take yawan tunawa tana jin ina ma zasu hadu ta rama dariyar da ya yi mata.
Da Abbati ya dawo bai koma gidansu ba. A waje ya gaisa da sauran iyayensa maza ya ce kansa ne yake ciwo zai kwanta. Harda nanatawa Mal. Inuwa ya sanar da Baaba bashi da lafiya kada ta ji shi shiru. Nan kuwa karfin gwiwar hada ido da ita a daren ne bashi dashi. Abinci kala biyu ya gani a falonsa. Wanda ya tabbata daga wurin Baaba Mari aka turo ya tsakura kadan ya yi shirin bacci. Sun dan taba shawarwari da Munzali a waya sannan ya kwanta.
Tafiyarsu Munzali ta gaggawa ta dagawa iyaye da 'yan uwan Alh Tahir wadanda Allah Yasa suka gamu dasu jiya hankali. Saboda haka suka dinga kiransa ana tambayar ko yaji daga garesu. Shi ma ya damu haka Mami Khadija da Mama Nasima. Wuraren tara na safe yaci sa'a Munzali ya dauki waya.
TAKWAS GOMA BA BIYU.
Tafiyarsu Munzali ta gaggawa ta dagawa iyaye da 'yan uwan Alh Tahir wadanda Allah Yasa suka gamu dasu jiya hankali. Saboda haka suka dinga kiran Alhajin ana tambayar ko yaji daga garesu. Shi ma ya damu haka Mami Khadija da Mama Nasima. Wuraren tara na safe yaci sa'a Munzali ya dauki waya. Munzalin kwanan zaune yayi inda yake ta tufka da warwara. An wayi gari kansa yana wani irin ciwo saboda rashin bacci da alhinin me zai faru tsakanin Abbati da Baaba Mari. Irin wannan lokacin sallah da kankantar da kai a gaban Allah SWT
shi ne yafi dacewa da bawa. Sai aka yi rashin sa a munin dabi'ar da suka rayu cikinta ya danne tunaninsu daga shi har Abbati. Asalin kalmar da bature yake kira despire ita ce ta wanzu a kawunansu. Suna jin tamkar basu da sauran rabo. A duniyar sai sun ji kunya sannan a lahira da wuya su sami dacewa da rahama. Wannan shi ne tunanin kowannensu. Shi ne fargabar da suke da yakinin ganin ranar faruwarsa.
Da farko bai yi niyar amsa wayar kowa ba sai ta Abbati. Amma karar kiran da ya shigo tamkar ana kada kararrawa a cikin kansa ya saka shi mika hannu ya daukota a gefensa.
Katse kiran yaso yi tunda bai san nambar ba, bisa kuskure sai ya zamana ya amsa ne.
"Alhamdulillahi ya dauka"
Shi ne abin da Munzali yaji an fada daga dayan bangaren. Bai sha wahalar gane mamallakin muryar ba. Hakan ya tilasta masa tattaro duk wata nutsuwarsa ya gyara murya suka gaisa sosai.
"Me ya faru jiya Munzali? Kun tafi kun barmu da fargaba. Ina shi Abbatin?"
Murmushin fatar baki Munzali ya yi da ya hasko tonuwar asirinsu da irin yadda zasu wulakanta bayan rabuwa da masoyansu. Karya ce kadai rufin asirinsu kuma ita ya gilla kamar yadda suka saba domin kare kai.
"Ku yi hakuri. Wan Baban Abbati ne aka kira babu lafiya ...."
Alh. Tahir ya katse shi tun kafin ya gama da cewa "Subhanallahi, ciwon ya yi tsanani kenan duba da yadda ku ka tafi."
"Eh suma yake yi kamar ba zai tashi ba."
"Kuna ina ne yanzu?"
Munzali sai da ya dauke wuta na wucin gadi kafin ya iya bayar da gamsashiyar amsa. A yadda suke dai bai kamata ya ce Abbati ne kadai ya tafi ba. Sannan idan ya yi gaggawar binsa yanzu bai san me hakan zai janyo ba. A takaice ma dai dole ya zauna domin ya dakile yunkurin da yake hasashen Alh. Tahir ya fara.
"Muna Gumel nima aka kirani Qibdiyya ta fadi ana zaton karaya ce." (Da safe ranar ta fadi amma ko kuka bata yi ba)
"Sannunku kaji. Ya jikin nasu?"
"Kawu Sa'idu ya fara samun sauki. Qibdiyya kuwa mai kula da ita ce ta firgita. Buguwa ce kawai."
Nutsuwar da Alh. Tahir ya rasa tun jiya ce ta dawo masa. Ya sake jajantawa Munzalin sannan suka yi sallama.
Munzali har ya fara jin sanyi a ransa na rabuwa dashi lafiya sai ya sake kira. Bayan ya fada musu me yake faruwa ne Mama Nasima ta ce ayi musu kwatance zasu je dubiya. Ita a nufinta taje har gidan Munzali ta kara gane ina zata kai Mardiyya. Alh Tahir bai ki ba saboda shi ma baya son wadannan zaratan matasa su kufcewa zuri'arsa. Tunda Allah Yasa suna Kanon gara ma da aka yi haka. Sai suje domin a karfafa magana.
"Amma ya dace muje gidansa? Babu mace fa a ciki. Idan akwai ma kuma ai bai kyauta iyayen wadda yake son aure suje duba mata 'ya ba."
Mami Khadija ce taja hankulansu kan kuskuren zuwa gidansa. Mama Nasima sai ta hau borin kunya.
"Mutum kullum burinsa ya nuna yafi mu sani da iyawa. Da an fimu din kuma da bamu zo gidan ba. Ki kwantar da hankalinki bance sai kinje ba. Yanzu nake shirin cewa a fada masa ya kaita gidan iyayensa sai muje can."
Mami Khadija sai ta girgiza kai kawai. Ba don tayi magana ba tsaf gidansa zasu je. Yanzu kuwa ko don a bata kunya dole a canja salo.
Ba bata lokaci Alh. Tahir ya kuma kiransa ya fada masa shawararsu. Suna gama wayar Munzali ya tashi a gaggauce ya fada bandaki. Cikin mintuna biyar har kaya ya saka. Yana makala links din hannun riga wayarsa tana gefen kunne ya danneta da kafada. Asabe ya fara kira ya tambayeta ko tana gida ta ce ta tafi sunan wata 'yar uwarsu a kauyen Kuyen Ta'inna da sassafe.
"Idan zuwa zaka yi bari in taho gida yanzu. Ka san kauyen a cikin gari yake zan iso da wuri."
"A'a yi zamanki. Zan zo da daddare ko gobe."
A wurinsa gara ta zauna kada su hadu da Mama Nasima ayi abin da shi da Mardiyya zasu dade basu manta ba. Zara ya kira ya fada mata bakin da zai yi da matsayinsu.
Asabe kuwa sai ta kasa zama. Idan kudi ne gara ta koma gida tayi masa waya ya zo ya kawo mata. Kada tayi sake goben ya ce ya taba. Takalmanta ta saka ta sallami maijego ta fito neman abin hawa.
Yau ma Abbati ya kasa shiga bangaren Baaba Mari. Ya leka ya gaisar da kawunnansa. Ita kuwa yana zuwa kofar dakinta ya tambayi wani yaro dan wajen Habi ko ta tashi.
"Ta tashi tun dazu. Kunu take sha."
Kirjin Abbati ya sake matse zuciyarsa saboda tsoron hada ido da ita. Cikin hanzari ya ce da yaron
"Tunda kunu take sha ka ce ina gaishe ta. Bana son shiga in katseta. Zan dawo anjima."
Daga cikin dakin Baaba Mari tana sauraronsu tun farkon tsayuwarsa a wurin. Maganarsa ta karshe tasa ludayin hannunta ya yi mata nauyi a hannu. Abbatin da ko wanka take yi yana jiranta shi ne mai cewa baya son katse mata shan kunu? So take ya bata dalilin karyata duk wani zargi da ya darsu a zuciyarta amma ya kasa. Daga wayarsu ta jiya kafin yazo zuwa yanzu bai yi komai ba sai tarwatsa mata zuciya da fargaba. Akwai matsala ta riga ta sani sai dai bata san girmanta ba. Wannan shi ne tashin hankalinta.
Tsayuwa Abbati ya yi a jikin bangon dakin ya kasa tafiya. Komai na duniya ya tsaya masa cak. Baaba Mari kawai yake so ta dube shi, duba na tsausayi da soyayyar uwa ta ce masa ta yafe. Ta roka masa rahamar Allah wadda a yanzu yake taraddadin samu. Idanunsa ya rufe sa'ilin da kwala ta cikasu har tasa suke zafi. A sanyaye ya juya zai tafi sai yaji wayar Baaba Mari tana ruri.
Sautin ne ya dawo da ita daga duniyar tunani tayi saurin share kwallarta sannan ta dauka da sallama. Muryar mace mai kamala ce ta amsa mata cikin walwala da son janta a jiki.
"Wa alaikum salam wa rahmatullah. Allah Yasa baki manta Khadija kanwarki ta Kaduna ba."
Baaba Mari tayi murmushin jindadi "yaushe zan manta mace mai kirki da mutuntunta dan Adam kamar ki Mami Khadija?"
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Cikin sakan daya Abbati ya bayyana a gaban Baaba Mari a hargitse.
Kallo guda taji ya matukar bata tausayi. Duk ya sauya babu komai a idanuwansa sai fargaba da tashin hankali. Bakinsa na rawa saboda bai san me aka ce musu ba tunda ya gama tsorata da Shazali ya ce,
"Baaba kashe wayar don Allah" a hankali.
Dauke kai tayi kamar bata ganshi ba tana tambayar Mami Khadija yara.
"Kowa lafiya kalau Alhamdulillah. Ya mai jiki kuma? Jiya Abbati ya tafi ya barmu da fargaba. Ashe kawunsa ne babu lafiya."
Kallonsa Baaba Mari tayi ta tabe baki. Abin har ya kai ga karya kenan. Shi da bai ma san abin da Munzali ya fada musu ba sai ya daburce ganin tana masa kallon tuhuma. Da bakinsa ya kasa hada kwakkwarar kalma balle ya yi magana sai ta cigaba da wayar.
Rufa masa asiri tayi kamar yadda kowace uwa za ta yi ta ce "Ai jiki ya yi kyau sai hamdala. Tsorata muka yi shi yasa aka kira shi."
Cikin jimami Mami Khadija ta ce "haka Munzali ya ce. An kira an ce yana suma ai dole hankula su tashi. Don Allah kiyi masa sannu."
"In sha Allahu Mami. Mun gode sosai."
"Haba ai an zama daya. Allah Ya kara hada kawunansu."
Amin ta ce sannan suka yi sallama. Abbati ya kalleta cikin sauri ya sauke ido. Inda ya tashi ya koma ya gurfana gabanta hankalinsa ya sake tashi.
Baaba Mari ta kasa tambayarsa komai. Tsoron amsarsa take ji ga kuma tausayin yadda ya firgice mata. A hasashenta ma daga maganganun Mami Khadija ta fahimci akwai alaka tsakaninsa da daya daga cikin 'yan matanta. Wayarsu ta karshe kafin zuwan Shazali dama ya fada mata akwai maganar da yake son yi da ita. Kawar da tunanin tayi domin bashi da muhalli a yanzu cikin damuwarsu. Can ta nisa tayi masa tambaya amma a sakaye.
"Kai da Munzali sana'arku daya?"
Sai da taji hadiyar yawunsa tare da hawa da saukar Adam's apple dinsa kafin ya iya bata amsa.
"Eh" ya dora da cewa "amma wallahi Allah mun tuba mun daina" yana mai nunin girman maganar da yatsansa.
Hannu ta daga ta dakatar dashi nata jikin yayi sanyi kalau. Kunnuwanta kuwa kamar an toshesu domin bata jin komai sai karar bugun fargabar zuciyarta.
"Bana son jin koma mene ne Abbati. Duk wanda yake kan tafarkin gaskiya ya sani. Wanda ya saba ma yana sane. Ka tashi ka koma gida. Zamanka a nan ba zai karemu da komai ba."
Samun kansa ya yi da fashe mata da kuka. Babu sauti sai dai ilahirin jikinsa duka rawa yake kamar an kwara masa ruwan sanyi.
"A tare dake aljannata take Baaba. Idan kin yafe min ina sa ran samun gafarar Ubangijina."
Nata kukan ta danne. Ya zama wajibi a gareta ta karfafi zuciyarta indai tana son danta ya sami karfin gwiwar tuban da yace ya yi.
"Na yafe hakkina idan akwai a cikin sana'arka. Sai dai ban san yadda zaku yi da hakkin mutane ba."
"Baaba ban fahimta ba." Ya tambayeta da dukkan gaskiyarsa. Rikicewarsa ta kai ya manta bata san ainihin sana'ar ba.
"Ba da sana'arku ku ka yi kudi ba?"
"Da ita ne." Ya amsa kansa a kasa.
"Kuma sana'ar haramtacciya ce?"
Kai ya sunkuyar ya gyada shi a hankali.
Yanayinsa sai ya soma bata haushi. Yafi ta sanin me suke aikatawa to don me zai nuna mata rashin sanin girman laifin? Duk mai daukar kayan da ba nasa ba yafi kowa sanin hakkin wasu ne yake dannewa. Hakkin da sai an tambayeshi ranar lahira.
"Kafi ni sanin cewa dukiyar haram ce kake kwance a kai. Idan akwai halin ka mayarwa wasu cikinsu dukiyoyinsu gara ka gaggauta yin hakan."
Abinka da dan fari kuma mutum wanda tun asali bashi da saurin fahimtar abubuwa makamantan wannan. Da Munzali ne tabbas zai cigaba da tafiyar da Baaba Mari ne akan zarginta na cewa sata ce suke yi. Abbati kuwa cikin kidima da tsoron zargin da take musu sai cewa ya yi bai taba satar kudin kowa ba.
Baaba Mari taji zuciyarta ta daka wani mugun tsalle a kirjinta yana fadin haka. Da sassarfa ta tashi ta tura kofar dakinta ta saki labule sannan ta dawo ta kama hannunsa suka zauna. Kallon ido cikin ido take yi masa cikin yanayi na fargaba da taraddadi.
Muryarta a shake ta fito saboda nauyin tambayar da take shirin yi masa.
"Yankan. Yankan? Kai? Yankan kai? Abbati ku 'yan yankan kai ne?" Bata jira amsarsa ba ta shiga yarfe hannuwa "na shiga ukuna ni Mariya. Abbati rashin imanin naku ya tsallake sata ya hada da zubar da jini?"
Sakin hannuwansa tayi ta hanyar bigesu daga cikin nata tayi baya a zabure. Hakan yasa shi yaji kamar ba za ta kara son ya kusanta gareta ba. Ita kuwa zafi ta soma ji fiye da kima ga gumi yana tsatstsafo mata kamar an kunna famfo. Wannan kaddara da nauyi take. Dan cikinta ne a gabanta amma bata san shi ba. Tana tuhumarsa da daya daga cikin masifun wannan zamani amma yaki cewa komai sai ido da yake binta dasu. Tana hawaye ta doki gefen kirjinsa, cikin gunjin kuka ta ce,
"Bakinka zaka bude kayi min magana. Wato da baka da niyar fadin gaskiya sai ranar da aka bukaci jininmu a kungiyar ...."
"Baaba ki yarda dani wallahil Azeem bana cikin kowacce irin kungiyar asiri ko yankan kai" ya fada dalla dalla duk da kukan da yake cinsa domin ta yarda da gaskiyarsa.
Komai ya kulle mata. Ta rasa tudun dafawa. Tsoron abin da zai fada yasa take jin gara ma ace satar ce. Sassauta murya tayi ta sake mika hannu ta damko hannunsa daya. Da dayan hannun nata ta share kwallarta sannan ta fuskance shi da kallo na tausayi garesu baki daya.
"Fada min sana'arka!"
Saukar aradu yaji. Zuciyarsa ta tsaya na 'yan dakiku kafin ta cigaba da bugu cikin yanayi na faduwar gaba.
"Baaba...."
Sai kuka. Kuka. Kuka...sannan ya fayyace mata komai tun daga haduwarsa da Munzali. Ko da ya gama ya sake kiran sunanta bata amsa ba. Dama kansa a duke yake sai ya dago a hankali. Shi take fuskanta amma ba shi take kallo ba. Bakin kwayar idanunta a birkice ya gansu, sun juye kamar babu su. Suman zaune tayi bai sani ba.
Datar MTN ta dari uku wadda suke bayar da 1GB na kwana daya Danliti ya saka a wayarsa. Whatsapp ya bude cikin rashin sa'a bai ga sunan Ayaah ba. Guntun tsaki ya yi domin ya so ganin hotunanta yau. Kwana biyu kenan da zuwansa wurin dinner inda ya hadu da Suhaib amma har yanzu bai manta da fuskarsa ba. Sai da ya koma gida haushi ya ishe shi. Da gani ya girme shi wai amma shi ne ya yi masa barazanar da ta tsorata shi haka.
"Idona idon matsiyaci sai na nuna masa tashancin 'yan Kano."
Danliti ya yi kwafa gami da jinjina kai cikin bacin rai. Duk da cewa baya jin akwai wata mace da ta kama kafar Ayaah cikin matan da yake son mu'amala dasu, amma yaci burin samun hajiyar Kadunan nan wato Jiddo.
Da bukata bata samu ba. Ya laluba babu halin ganin hoton Ayaah a yau. Sai kawai ya saka katin dari biyu ya kirata.
Shirin fita suke ita da Murja zuwa gidan Innayo. Murja ce za ta yiwa Zara kitso kamar yadda ta fadawa Hasiya jiya. Shi ne ita kuma ta hadasu da Ayaah ta ce su tafi tare.
Shake murya ya yi yana magana ciki ciki irin na mayaudara.
"Baby nayi missing dinki da yawa. Anjima zan zo. Me ki ke so na taho miki dashi?" Ya fada a karshe don ya san ba za ta ce komai ba.
Ita kuwa sanyi taji a ranta da sabon sunan da ya rada mata.
"Babu komai. Fita ma za muyi da Murja."
"Ina zaku je baki fada min ba? Nifa gaskiya bana son kina fita ana gane min ke. Da kin fada min sai na zo na kai ku. Anywhere dai ku jirani please zan taho now now."
Satar kallon Murja tayi ta bar wurin da sauri kafin taji me yake cewa.
"Ka barshi bani kadai bace. A gida fada za ayi min. Gidan kakanninmu zamu."
A lissafinsa anci rabin kudin wayar sai kawai ya fake da nuna bacin rai ya mata sallama. Hankalinta sai ya tashi tayi maza ta kira shi da ragowar canjinta.
"Kayi hakuri mana don Allah."
Kamar ba zai ce komai ba har ta fara kosawa sannan ya ce "Naji. Amma har ku isa muna chatting. Ki kwatanta min gidan sai na sameku a can ko fuskarki na gani naji dadi. Da kudi a wayar ko na turo miki?"
"Akwai" ta bashi amsa duk da ta san sun kare.
A danja ta sayi kati ita ma na dari biyu ta saka ta tura masa amsar sakonsa wanda ya rubuta kamar haka,
(Wane kaya ki ka saka?)
(Atampa ce)
(Kwatanta min daga sama har kasa domin naji kamar kina gabana.)
Kwatancen tayi masa na riga da skirt da hijabin da ta saka mai hannu wanda ya zarta gwiwarta kadan. Abin bai yi masa armashi yadda yake so ba. Wanda a idon namiji mai mutumci zai ga tayi matukar kyau. Canja salo ya yi cikin kwarewa da iya hillata.
(Da wane irin kaya ki ka fi son yin bacci?)
Kallon wayar tayi kamar ba tata ba na dan lokaci har sai da Murja ta tambayeta ko akwai matsala ne. Dena juya wayar tayi a kasan ranta tana yi masa uzuri da cewa kila lefe yake tunanin fara hadawa.
(Doguwar riga)
Danliti yaja tsaki ganin taki daukar haske.
(Ni kuwa kinga nafi son kwanciya da wandon bacci kadai. Idan ma sanyi ake nan gaba kadan na san kina kusa dani ba zai dameni ba. Kema ki shirya ba zaki zo min da doguwar riga bed ba.)
Wani dumi dumi Ayaah ta fara ji. Ita kadai ta dinga tsarguwa ko Murja ta fahimci irin sakwanin da yake turo mata. Hirar ta daina yi mata dadi amma ta rasa me ya hanata dakatar dashi ko ta daina bashi amsa. Wani sakon ne ya sake shigowa sai da ta dan zabura da ta karanta.
(Ina son mace mai kunya. Shirunki yasa na kara sonki. Amma fa ki sani nan gaba kadan zaki nemi kunyar ki rasa. Zaki fara rungumeni da kanki ba sai na nema ba. Kafin aurenmu ina son mu sake da juna sosai ta yadda tun yanzu zamu san abubuwan da zasu faranta mana.)
Ayaah bata iya sake tura masa amsa ba. Tambayoyin nauyi suka yi mata. 'Yar fara'ar da ta soma ta nema ta rasa.
Danliti da kansa ya gano zai yiwa kansa sagegeduwa ta wannan hanyar. Kifin rijiya ce ba kamar yadda ya yi zaton irin makwadaitan 'yan matan nan bane masu mummunar wayewar zamani a soro.
(Kiyi hakuri Baby. Ina jin kamar na dauko hirar da bata kamata mu fara tun yanzu ba. Ina tsananin kewar irin wannan kusancin da iyalina. Ke kadai ce zan iya fitowa da damuwata hankali kwance domin nayi imanin zaki saurareni kuma ki fahimceni. I love you)
Shi kenan! Kyakkyawan tunanin da ya fara ginuwa a zuciyarta ya rugurguje da sakonsa na karshe. Tausayinsa ya sake kamata. Ta kara jinsa a rai fiye da kullum. Matarsa kuma ta sha bakaken addu'o'i domin har gani take ba don haduwarsa da ita ba kila da yanzu ya fara bin matan titi.
Dubu ashirin Alh. Tahir ya baiwa Mama Nasima domin yiwa Qibdiyya sayayyar dubiya. Ita da Mami Khadija zasu je. Sai 'ya'yansu. An nemi Jiddo a waya bata dauka. Tana can gidan wata 'yar kungiyarsu 'yar Kano an kawo musu samari suna keta dokar Allah. Ta gama tsara karyar da zata yi idan ta dawo kafin lokacin tafiyarsu Kaduna.
Mota biyu suka yi. Daya direban gidan da ake bikin ne yake jan Mama Nasima da Mami Khadija tund shi dan gari ne.Ta bayan kuwa motar gidan Alh. Tahir ce. Suhaib ke tuka kannensa suna biye dasu a baya.
A son ran Mami Khadija su biyu kadai zasu je sai ko 'yan mazan. Saboda mata da kunya aka sansu. Tana ganin iyaye da 'yan uwa sun isa su wakilci 'yarsu kafin a daura aure. Dadin dadawa ma maganar bata riga ta zama ta gemu da gemu ba. Zai iya zama kamar suna son cusa 'yarsu ne ta karfi. To Mama Nasima ta dage sai Mardiyya taje. Shi yasa ta hada da Farha da Sauda don kada ido ya yiwa Mardiyyan yawa idan aka fahimci matsayinta.
Kayan tarbar baki lodi guda Munzali ya kawo dakin Innayo. A nan ya sami Uwani tana ta buge bugen waya tana tsaki. Tun safe take kiran Habibu waya taki shiga. Za ta fita kuma Innayo tayi rantsuwar idan bata nemi izinin mijinta ba in ta fita kar ta dawo. Ita Salima dama yaji labarin komai. Sunyi magana da ita a waya ya kwantar mata da hankali tare da goyon bayanta akan son raba auren.
Zara ce ta gyara falon Innayo ta sakewa Qibdiyya kaya sannan ta jera komai a tray. Salima ta shimfida tabarma saboda basu san mutum nawa bane. Haj Uwani tana uwar daka ta kira Mubashir a waya tana kwatanta masa kamanin Habibu. So take yaje ministry ya kira mata shi. Innayo kuma tana gefe ita da Munzali yana yi mata bayanin Mardiyya da iyayenta.
"To amma duk wannan bayanin da kake ni banga farinciki a fuskarka ba. Baka son
yarinyar ne ko akwai wata matsalar ne daban?"
Ta tambaye shi bayan ya gama. Bata ga wani doki ko murna a tare dashi ba. Kusan ma kamar rabin hankalinsa yana wani wajen daban.
"Ba haka bane Innayo. Abbati ne ya ce min zai taho daga Kirikasamma yau. Shi ne nake tunanin zuwan bakin da isowarsa. Kada ya iso basu tafi ba. Kinga babu mai dauko shi daga tasha."
Zancen bai yi tasiri a kanta ba saboda bashi da madogara. Abbati ba yaro ba kuma ba bako ba me zai same shi idan ya shiga mota daga tasha zuwa gida? Akwai damuwa sosai tana gani a idanunsa. Munzali mai yawan fara'a yau idanunsa kamar an dauke wuta. Rabuwa zata yi dashi har bakin su tafi sai ta kuma tuntubarsa. Idan ba abin da ya kamata ta sani bane zata bishi da addua.
Uku da rabi saura suka isa kofar gidan Alh. Rabi'u. Sauda ce mai tsokanar Mardiyya tana cewa,
"Ke zaki shiga gaba mu take miki baya tunda gidanku ne."
"To parrot kaddai mu shiga ki dinga nunata."
Farha da tayi maganar ita ma bata tsira daga tsokanar kanwarta ta ba.
"Kai Ya Farha daga wasa? To ko daga nan a biya garinsu ne shi ma."
Suhaib da Lilu aka bari da dariya. Suka taka zuwa inda iyayensu suke tsaye bayan sun fito daga mota. Tsayuwarsu keda wuya Munzali ya fito tare da Ayaah a gefensa. Ita za ta rakasu dakin Innayo shi kuma zai shiga dasu Suhaib falon Asabe tunda babu kowa a ciki.
TARA DAGA KE SAI GOMA.
Innayo da 'ya'yanta sun karrama su Mami Khadija fiye da zaton Munzali. Shi ya kawo duk wani abin ci da sha to amma bai kai rabi rabin kyautatawar su Salima garesu ba. Farha tana ganin jaririyar Zara ta karbeta. Mardiyya da Sauda suka karaci nacinsu suka hakura. Uwani har lokacin tana daki ko lekowa a gaisa bata yi ba. Duniyar ce take ta hajijiya da ita. Bata da lokacin kanta balle na wani.
Lokacin da suka shigo Murja tana ta sauri sauri ta kai karshen kitso biyun da ya rage musu, saboda haka kan Zara a bude yake. Suna sallama ana gamawa. To bayan sun zauna an gama gaisawa Sauda ta dinga taba Mami Khadija har sai da Innayo ta kula da hararar da Mamin take yi mata. Da hannu ta kira Saudan fuskarta dauke da murmushi. Bakin da gani sun baiwa kalmar 'babu' hutun shekara da shekaru ma. Amma babu alamun wulakanci ko girman kai. Mama Nasima ce ma dai ta hadiye rashin gamsuwarta ta hanyar kama bakinta tana jiran tabbatacen bayani game da gidan da matar dakin.
"Zo ki fada min me kike so ake hanaki kamar ba dakin mamanki ba."
Mami Khadija tayi saurin cewa "don Allah kar ki biye mata."
"Sai dai a tari gaba."
Yadda Innayo tayi maganar sai ya basu dariya. Sauda na tsoron batawa Mami Khadija wadda bata daina hararta ba, sannan tana kunyar badawa Innayo kasa a ido.
Su biyun duka idanunsu na kanta. Ta kalli wannan ta kalli waccan ta dukar da kai. Farha da Mardiyya da ma su Zara da Ayaah wadda 'yan matan suka burgeta ana ta dariya. Mama Nasima kuwa cin magani take rai a bace sai ga Munzali ya shigo. Sauda ta hau murmushi da ajiyar zuciya.
"Yauwa don Allah taimakeni."
"Da me?" Ya amsa yana dube duben fuskokin mutanen dakin.
Mami da Innayo ma sai da suka yi dariya wannan karon. Salima ce ta labarta masa me yake faruwa.
"Saboda haka ka taimaketa idan ba haka ba daya daga cikinsu zata hukunta ta."
Halin rashin nutsuwar da yake ciki bai hana shi
biye musu ya yi murmushi ba.
"Nima dai babu ruwana. Kawai ki kwato kanki don duka ina tsoron fushinsu."
"To ke kinji, kin kama kafar wala" cewar Mami Khadija da murmushi.
Sauda ta turo baki ta soma cewa "Ai don dai ba Mar....."
Kafin ta gama shi da Mardiyya sun kama kansu domin cikin sauri suka dinga cewa ta fadi abin da take so. Nan da nan dakin ya sake kaurewa da dariya. Sai da suka nutsu ne ta fada musu kitson da ta gani ne ya burgeta.
Ayaah ta mike da sauri tana cewa "bari na kirawo miki wadda tayi."
Sauda ta kalli Mami ita kuma ta ce ba za su jira ayi mata kitso ba.
Munzali na jin haka ya ce "Mami ba a waje za a nemo mai kitson ba. 'Yata ce ita ma. Bari su zo na gabatar muku dasu" ya kare maganar da murmushi.
Zara da Salima harda Innayo ne suka hadu suna rokar alfarmar Mami ta bari ayi kitson. Murmushi kawai tayi domin nauyinsu ne ya kamata ta kasa kafewa akan bakanta. Halayyarsu ta burgeta matuka don daga uwar har 'ya'yanta sun iya saka bako yaji kamar a gida yake. Shi yasa ta ce ba hanawa tayi ba sai dai da kunya zuwan farko su zauna ayi kitso.
"Duk gida ne Hajiya kuma na fahimceki sosai. Amma don Allah ki bari ko manya tayi mata. Ki ajiye dalilin zuwanku ki dauka mu daku
daya ne."
Mami Khadija ba yadda ta iya da furucin Innayo wanda tayi cikin sigar rarrashi da sanin ya kamata. A dole ta ce ta hakura amma fa manyan za ayi kuma tun wuri Innayo ta sani cewa idan sun je gida sai ta yiwa Sauda fada.
"Ba zan hana wannan ba. Amma dai kar kiyi da yawa. Na tabbata jin da tayi kamar tana tare da 'yan uwanta ne yasa bata boye abin da take so ba. In wani gidan ne ita ma ba za ta soma ba ko Saudatu?".
Sauda ta gyada kai tana kallon kasa. Farha ta tashi ta ce bari ta fadawa Suhaib. Saudan sai ta bita aka bar Mardiyya da ta karbi baby din Zara da Munzali tare da sauran mutanen falon.
Mardiyya kunyar kasancewar Munzali a wurin ta hanata sakat. Sau biyu suna hada ido. Murmushi yake mata wanda a kasan ransa yake jin zai iya zama na bankwana. Tunda Shazali ya kunno musu wuta yanzu basu san iya inda zata tsaya ba. Don kada kowa ya fahimci kallon me suke yiwa juna sai ta dubi Zara ta tambayeta sunan baby.
Kafin Zara ta san me za ta ce mata Mami Khadija ta sako tambayar waye babba tsakanin Munzali dasu Salima. Ba kuma haka kawai tayi ba sai don ta kawar da hankulansu daga tsakin da Mama Nasima take yi jifa jifa. Sautin na yanzu yafi karfi shi ne tayi tambayar da dan karfi ita ma. Har kasan ranta bata da niyar idan sun zo ta zake da yawa tunda ta san halin abokiyar zaman nata. Kar ta ce surukanta ne Mamin take shige musu. Kyawun mu'amalar 'yan uwan Munzalin ya bata sha'awa amma ta kula ba haka bane a wurin mai shirin zama surukarsu. Yatsine yatsine take ta yi da tsaki na gajiya da kosawa daga zamansu. Dalilinta kenan na jan maganar kitson da Sauda ta nuna mata kawai don kada su kunyata kansu.
Munzali ya nuna mata Salima ya ce ta girme shi amma Zara kanwar bayansa ce. Ai fa nan suka soma musu da Zara akan waye babba har ya hakura ya karbi kankantarsa.
Da Ayaah ta fito kiran Murja samunta tayi tana waya. Gira ta dage tana yi mata dariyar shakiyanci saboda gane wanda ake wayar dashi. Mahiru ne saurayin da ya kai kudin aurenta.
"Haba nifa naji shiru daga kaiwa baki abin sha baki dawo ba ashe ashe..."
Sallama Murja tayi da Mahiru tayi dariya "gulmammiya indai ba labe ki ka yi min ba me ki ka ji na ce da zaki gane da wa nake waya?"
Ayaah ta rausayar da kai hannunta daya akan kugu ta ce "gani nayi kina ta bin bango kina malalewa kamar ruwa irin abin nan na Indiyawa a lambun soyayya. Na ce duk yadda aka yi Yaya Mahiru ya fadi abin da ya susuta Murjanatu 'yar Baba."
Haushi ya kama Murja da Ayaah ta kwatanta irin tsayuwarta a jikin bangon harda waka.
Iska ce ta debi maganganunsu har falon Asabe saboda sun fi kusa da wurin. Lilu ya kama dariya harda rike ciki. Suhaib ya kai masa duka yana nuna masa alamar ya yi shiru da dan yatsa. Shi ma hirar nishadi ta sanya shi har yaji yana son ganin fuskar mai tsokanar.
"Kai fa baka da kan gado wallahi."
A lokacin wakar da Ayaah take yi ta shiga kunnuwansa sai da ya murmusa. Gyara zama ya yi yana saurarensu tare da kallon Qibdiyya da Lilu yana biye mata kamar yaro dan uwanta. Waka take abinta babu kyakkyawan kari. Duk baitin da yazo kanta take fada.
Sai ruwa ruwa na malaleeeee. Ashe ruwan bana ya ci su Murjaaaa. Kinsan ya dade yana sonki ruwa na ...."
"Zan malale bakinki a wurin nan" cewar Murja a fusace tana galla mata harara sai kuma ta kama dariya "murya kamar gogen tsumma."
Ayaah ta sha kunu tsiwar ta motsa ta ce "kin dai fada ne kawai don kiji dadi amma ke kin san muryata da dadi. Idan ina magana Dani kasa dauke ido yake daga kaina."
"Waye kuma Dani kamar wani arne?"
Furucin Murja kenan domin yau ta fara jin sunansa. Ran Ayaah in yayi dubu kuwa a take ya baci. Maganar tayi mata zafi don sai da taji kwalla na neman kwace mata. Dani din nata ake kamantawa da arne.
A bangaren su Suhaib ma sai suka hada ido da jin kalmar Murja ta karshe da shirun Ayaah. Ba tantama ya da kanwa ne. Sai da Farha ta fito tana tambayarsu inda su Lilu suke sannan Ayaah ta fadawa Murja sakon da ya kawota.
Rashin sanin da mutane a kurkusa dasu ya sake bawa Ayaah haushi da Murja ta nuna falon Asabe. Da suka fito bayan gama jin bayanin Farha suka fito Ayaah ta basu baya tayi hanyar kofar gida da waya a kunne. Danliti ne ya iso yana neman karin kwatance. Basu ga fuskarta ba har suka karasa ciki wurinsu Innayo.
Mami Khadija bata son barin 'yan matan dasu Lilu kadai a gidan. Sannan take taken Mama Nasima tun farkon zuwansu ya nuna mata zasu iya samun matsala akan jiran kitso. Cije lebe tayi ta rasa me zata ce da Innayo ba tare da ta bata mata rai ba.
To ita ma Innayo din duk ta karanci rudanin da Mami Khadijan ta shiga. Ita kadai a zuciyarta ta yabawa wannan uwa. Tunanin maslaha ta tayata inda bayan dan nazari na kankanin lokaci ta bude baki tayi musu magana.
"Munzali ko zaka bisu da Murja sai Ayaah ta rakata. Kitson mutum daya dai na san kafin Magariba in Allah Ya so sun gama. Ko kuwa? Kunga sai a sami zumunci sosai tsakaninsu ko?"
Kai Mami Khadija ta daga ta kalleta da murmushi sannan tayi mata godiya sosai.
"Haka ne. Nima ba zaman kitson ne bana so ba amma kinga ..." tana son cewa su matsayin dangin mata suke kuma gashi ko iyaye maza basu gana ba. Ita da tun farko bata goyi bayan zuwan ba kuma harda Mardiyya bai kamata ta assasa dadewarsu ba.
"Karki damu duk na fahimta. Bari ta kirawo kanwarta sai su biku tare."
A lokacin Lilu ya bukaci Suhaib ya bashi mukullin mota yana da chakulet zai daukowa Qibdiyya. Nan ta soma tsalle. Munzali ya ce shan zakinta ya yi yawa kada ya dauko. Da ido Lilu ya yiwa Suhaib alamar ya taimaka ya dauko masa. Shi kuma sai ya sami kansa da biye masa yabi bayan Murja da ta fito kiran Ayaah.
Turare Danliti ya sake mitsikawa a hannunsa yabi jikinsa ya shafe sannan ya sako kai soron da Ayaah ta shiga bayan ta hango shi. Tuni ya ce mata a bakin titi ya ajiye mota saboda ya zata layin nasu mota bata shiga. Ita ma a ciki hijabinta ta gyarawa zama tasa hannu ta dan goge fuska. Idanun iyayenta da bakin dakin Innayo ne suka hanata sabunta kwalliya domin tarbarsa.
A tare suka sakarwa juna murmushi da ya shigo. Idanunsu sarke da juna kunya duk ta kamata.
"Baby kin yi min kyau sosai."
Kalman da Suhaib yaji kenan da ya tunkaro kofar. Can ya baro Murja tayi cikin gida tana ta kwala kiran Ayaah. Bai san wace ce ba amma zuciyarsa ta bashi abokiyar fadanta ta dazu ce wadda aka ce zasu tafi tare.
Fari tayi masa da ido sannan tayi godiya.
"Na gode Dani."
'Dani?' Suhaib ya ambaci sunan a ransa yana mai tuna abin da ya hada 'yan uwan rigima. Curiosity bai barshi ya cigaba da tsayuwa inda ya dakata ba. Yanke shawarar wucesu don yaga fuskokinsu su biyun ya yi. Murmushi ya bayyana akan fuskarsa da ya ayyana me Lilu zai yi da shi ne ya fito. Ya daga kafa zai cike tazarar dake tsakaninsa da kofar soron sai yaji abin da bai zata ba. Muryar mai suna Dani ce take fita a raunane cike da makirci irin wanda ba kowa zai gane ba.
"Baby yau ma ina cikin damuwa. Shi yasa ma kika ga na matsa sai mun hadu." Bai kuma jira jin cewarta ba don ya kula ta fara yi masa kallon tausayin nan ya dora da "wai ko kinsan yanzu matar nan ta daina zuwa shimfidata sai na biya?"
A saukar aradu maganar ta shiga kunnuwan Ayaah da Suhaib. Ita nauyi da kunya ne suka kama ta gami da fara jin haushin me yasa hirarsa bata wuce irin wadannan maganganun. Suhaib kuwa zuciyarsa yaji ta soma tafarfasa.
Ya yiwa zina da duk wani ma'abocinta mummunar tsana. Salon hirar nan kuwa ba komai bane illa dauko hanyar bude kofar da za a iya fadawa gareta. Yarinyar da yaji muryarta kila ba za ta wuce sa'arsu Sauda ba ita ake fadawa wadannan kalamai. Jikinsa har yana tsuma don bacin rai ya iso daidai bakin kofar amma sun juya masa baya sannan yaji amsarta.
Muryarta har raurawa take yi saboda an kure rashin kunyarta ta ce "Dani ina ga ba ni ya kamata ka fadawa wannan matsalar ba. Gara dai ka kaiwa magabatanku a nemi mafita."
Danliti ya gane ta fara jin tsoro daga muryarta ya yi murmushin gefen baki. Da tsoron wanda bai hana cigaba da soyayya ake samun kan irinta. Sake kwantar da murya ya yi abinsa harda langabe kai.
"Wa zan fadawa matsalata bayan Mum idan ba ke ba? Ita kuma saboda bata kasar bana son yawan tayar mata da hankali. Kece dai wadda nake shirin aura nake ganin ya dace ki san matsalolina tun yanzu domin ki tanadi hanyoyin magancesu."
Maganar tasa tana fita ne daidai da takunsa da yake ta kusanto shi gareta. Idanun Ayaah sun yi wuri wuri amma ta rasa me ya hanata ja da baya. Tausayinsa take ji har kokon ranta tana kuma gudun kar ya nemi wata idan taki taimaka masa. Bata yi aune ba ta ji shi daf da ita har tana jin dumin numfashinsa.
"Baby ko dan huk (hug) ne don Allah in samu domin na rage zafi. Ina tsananin bukatar mace. Jiya na tura mata dubu dari ta ce ya mata kadan. Ni kuma shi ne naji haushi ban sake yi mata magana ba. Kudin bai dame ni ba amma na gaji da rainin wayo."
Sai ga Suhaib yana tafa hannuwa kamar mace saboda tsabar mamakin da ya sarke shi. Bai taba ganin dan is... kamar wannan mai sunan arnan ba. Duk da haka ya tsaya yana son ganin irin tarbar da Ayaah zata yiwa yunkurinsa domin ya san matsayin da zai ajiyeta. Duk abin da ake yi ko fuskarta bai gani ba har yanzu.
Akan idonsa ta ja baya kadan tayi magana kamar mai shirin kuka.
"Ka kara hakuri. Ba ka ce idan Mum din ta dawo za a turo ba? Ka bari ayi auren."
Hannu ya daga yana son shafa fuskarta ta goce da sauri. So yake su wuce wannan matakin ya sami yadda yake so. Yawancin mata wuyarta a sami kansu na farko. Daga basu da zabin da ya wuce amincewa a gaba saboda gudun kada a ki aurensu. Ya dade da yadda da wannan shi yasa yake cin karensa babu babbaka.
Cikin muryar dake nuni da tsantsar karaya da neman agaji ya ce
"Har sai wannan lokacin Ayaah? Idan na shiga wani hali kafin nan ba laifinta bane ita kadai har dake. Naki ma yafi nata domin zuciyata da gangar jiki duka ke suke so.
Nayi zaton zuwa yanzu nafi karfin komai a wurinki. Ashe ni kadai nake haukana. Yadda na daukeki daban da matsayin da kika bani."
"Ba haka bane. Kai ma ka san ina sonka."
"To ki nuna min a aikace. Ki mantar dani bakincikin da matata take kunsa min. Ki cire tsoro a ranki domin wallahi ko raina ki ka nema zan iya baki. Sannan kada ki manta dama ya halatta na ganki tunda maganar aure ce tsakaninmu. Gani babu hijabi balle mayafi. Hakkina ne kike neman dannewa Baby. Kin yi min adalci kenan?"
Runtse idanu Ayaah tayi da ya sake daga hannu zai shafa fuskarta. Bata so ko kadan amma zuciyarta ta gama aminta da halatta haramun din da yake neman yi. Ba zina zata yi ba. Nutsuwar da yake nema kawai take son taimaka masa ya samu.
Suhaib bai san lokacin da ya iso gabansu ba. Danliti da ya gama sakawa ransa cewa daga shafa fuskar zai zarce da koya mata wani karatun daban sai ji ya yi hannunsa ya makale a iska. Daga kai ya yi yana kallon gefen fuskar mutumin da ya rike shi a firgice.
Ayaah kuwa da taji shiru bai taba ta ba sai ta bude idanunta a hankali. Nan suka yi ido hudu da mutumin da bata sani ba. Kwayar idonsa tamkar maganadisu aka zuba saboda yadda ta kasa dauke nata. Mugun kallo yake yi mata mai kama da na tsana. Zuciyarta sai da tayi wani irin tsalle don tsoratar da tayi. Suhaib ya kuma ware mata idanuwansa da suka kara firgita ta.
"Get out of here (bar wurin nan)" ya umarceta da tsawa.
A guje tayi cikin gida tana haki. Murja har ta fitar da rai da ganinta suka yi karo. Bata kula da yanayinta ba ta fada mata sakon Innayo.
Bayan tafiyarta Suhaib ya kalli Danliti wanda yake ta kokawar kwace hannunsa ya kasa. Tuno inda ya san fuskarsa ya yi ba shiri ya saki hannun baki a bude.
"Kai? Ba kai bane makaniken...."
Bai iya karasa magana ba sakamakon ture shi da Danliti ya yi da karfi ya kwasa a guje ya fita daga soron. Tunda ya fita ba shi ya tsaya ba sai da yaje titi. Ya tsaya mayar da numfashi bai yi aune ba wani mai kurar ruwa ya kwashe shi ya watsar a gefe.
Innayo da iyalinta har bakin mota suka rako su Mami Khadija. Su suna godiyar ziyara ita tana ta kyautata musu da aka yi. Ita dai Mama Nasima mota ta shige kai tsaye ko waige babu. Tuni ta fara musu da zuciyarta akan amincewa alakar Munzali da Mardiyya. Ta raina gidan da ahalin gidan.
An rarrabu kowa ya shiga mota. Ayaah kamar wadda ta yiwa Sarki karya gabadaya ta kasa sakewa. Duk inda ta motsa sai taga kamar idanun mutumin da taji Kawunta ya kira Suhaib suna kanta. A gaban motar Munzali ta zauna ta hade hannuwanta a tsakiyar cinya. Murja tana baya suka bi bayan motar Suhaib din. Ita dai har suka isa gidan bata san inda tunaninta yake ba. Tsakin da taji lokacin da ta fito daga motar ne ma yasa ta karewa gidan da suka iso kallo. Ido suka kuma hadawa da Suhaib ya sake yin tsaki a karo na biyu sannan ya kawar da kai tamkar yana kyamar kallonta.
Hawaye taji yana neman sauko mata ta daure ta hadiye shi. Da tabi 'yan matan cikin gidan shi tsayuwa ya yi wurin Munzali suna magana. Hankalinta a tashe tana tsoron ko abin da ya gani yake fada masa. Ana ta janta da hira sai dai tayi yake. Cikin abin da bai kai minti talatin ba har an gama kitson. Mami Khadija ta basu kudi suka ki karba. Har ta nuna bacin rai amma suka ki. Sai suka sake burgeta. Dama da a gida suka hadu ba kudi zata bayar ba. Kyauta zata yi musu irin wadda ta dace da 'yan mata.
"Ku karbi nambar juna ku dinga gaisawa. A haka ake fara zumunci."
Abin da tace musu kenan sannan ta juya ta barsu dasu Sauda. Da yake 'ya'yan nata babu girman kai a take suka fara aiwatar da shawararta, aka yi musayar nambobi tsakaninsu. Ayaah jiki ya kasa daina rawa saboda ganin har lokacin Munzali da Suhaib suna magana. Da Munzali ya kallo inda take kuwa sai da taji kamar ta saki fitsari a wurin.
"Ku zo mu tafi"
Kasa daga kafa tayi sai da Murja ta ja hannunta. Da suka isa bakin motar Suhaib ya bata mamaki da ya bude mata gaban sannan ya hada da yi mata murmushi. Kura masa idanu tayi ba shiri domin tabbatar da abin da take gani. Ya kuwa sake yi mata murmushi a karo na biyu. Farha tana yi musu sallama shi ma ya yi harda cewa su gaida gida.
Murmushinsa bai hanata satar kallon Munzali ba a hanya tana jiran ya fara fada. Gani take
kamar na mugunta yake mata bayan ya gama hada mata bomb.
Kallon hanya da zurfi cikin tunani da take ganin Munzali ya yi bashi da alaka da abin da take tunani. Suhaib ya yi masa magana ne akan baffaninsu maza da suka yaba dasu har suka bukaci a sanar dasu cewa su turo iyayensu indai da gaske suke. Ya kira Abbati yafi sau shurin masaki amma bai dauka ba tunda gari ya waye. Abin ya karu domin yanzu wayar ko shiga bata yi. Haka ya rufe ido ya kira layin Baaba Mari shi ma shiru. Kafin ya isa kofar gidan Hasiya ya kira mutum ya kai shida a gidansu Abbati. A kalla kowanne ya kira sau uku ko hudu. Hankalinsa ya tashi sosai har ta kai kwatancen gidansu da Murja take yi masa baya ganewa sosai. Sau biyu yana yin kwana sabanin wadda take fada masa.
Tsayuwarsa da mota ke da wuya Ummita ta fito rike da Hasiya a jikinta. Tangadi suke duk su biyun. Hasiya na ciwo, Ummita na firgicin irin aman da taga tana yi. Cikin kankanin lokaci ta fita daga hayyacinta. Ko kashe motar bai yi ba Ayaah da Murja suka fita da sauri.
"Me ya sameta?"
Ummita tana kuka ta fada masa yadda Hasiya ta dinga amai daga kwabin lalle. Babansu kuma tun safe Abdulkarim ya turo aka tafi dashi asibiti tare da Abbas. Duk wannan bayanin a hanya aka yi shi. Gudu irin na
ganganci ya dinga yi saboda kakarin da Hasiya take yi a galabaice.
Kiran Abbatin da bai sake samun damar yi ba kenan a ranar domin suna zuwa asibitin emergency aka nufa da ita.
"Gabadaya na kasa fahimtar bayaninka Abbati. Haka kawai ta suma bayan bata kwana da ciwon komai ba?" Mal. Inuwa ya furta hankalinsa yana ga Baaba Mari dake kwance akan gadon asibiti rai kwakwai, mutu kwakwai.
Atine ce tayi karfin halin cewa "Ya ce magana suke fa yaji ta daina amsawa"
Duka 'ya'yan Baaba Mari suna dakin da aka kwantar da ita a babban asibitin garin Kirikasamma. Abbati ya rasa me yake masa dadi a duniya. Gefe guda ya samu ya zauna ya hada kai da gwiwa cikin tunani. Tare suke da mahaifinsu Mal. Inuwa da wasu cikin Gwoggoninsu matan 'yan uwansa. Shi Mal. Inuwa yafi kowa nuna gigita saboda yadda yaga Abbati ya fito da ita waje a hannu ko motsi bata yi. Daga shi har 'yan majalisarsa sun dauka bata da rai.
Kowa yana tofa albarkacin bakinsa game da ciwon da ba a san silarsa ba likita ya dawo. Wasu gwaje gwajen jini ya sake rubutawa ya bukaci Abbati ya biyo shi waje.
Da sauri Mal. Inuwa ya ce "Fadi ko ma mene ne Dafta. Nan wajen duka babu bare. Me ya sami Mari?"
Likitan ya dubi Abbati wanda ya gyada masa kai sannan ya fada musu abin da suka gano.
"A gaskiya jininta ya hau fiye da kima har yana barazanar taba mata zuciya. Idan ba a dauki matakin da ya dace ba zata iya samun stroke (mutuwar barin jiki) ko ...."
"Allah ma Ya kiyaye" cewar Mal. Inuwa da rawar murya "indai kudi ne sha Allahu ba zai gagara ba. Ayi mata duk abin da ya dace ga danta nan."
"Malam. Malam"
Ba Mal. Inuwa da ta kira ba, duka wanda yake dakin sai da ya juya da farincikin ganin Baaba Mari ta farfado.
Da hannu ta yafito shi ya matso kusa da gadon ya duka kansa ganin tana ta motsa baki.
"Ku mayar dani gida."
Wani irin kallo ya mata cikin tashin hankali ya daga kansa ya yiwa Abbati inkiya da ya matso. Su Habi duk sai suka fice.
"Kaji taurin kan mata ko? Wai a mayar da ita gida."
Murmushi tayi masa "Idan an kaini asibitin waye zai biya kudin?"
"Wace irin magana ce wannan? Ko kin sami makuwa ne saboda ciwo?"
Muryarta ta kara dusashewa ta ce "kana da sauran kadara ne Malam da zaka sayar ka nema min magani?"
Duk da ya soma harzuka haka ya daure saboda ba lafiya gareta ba ya ce
"Wai ba ga Abbati ba? Mari lafiyarki kuwa?"
Idanun Abbatin ta lalubo da nata. Ya zabge tamkar shi ne kwance a gadon asibitin. Kalamanta na gaba a gareshi ita kanta basu yi mata dadi ba sai dai babu gudu ba ja da baya.
"Ban yafe ba idan ya sake kashe min kwandalarsa. Ban yarda kaima ka kashe min daga kudin da ya baka ba. Sannan idan ban tashi ba ka isar da sakona ga dan uwanka Sa'idu. NI MARIYA BAN YAFE MASA BA!
TARA DAGA KE SAI GOMA.
"Anya Mari baki yi gamo ba? Yaya Sa'idun kike ja wa Allah Ya isa?"
Wani bacin rai ne ya turnuke kirjinta. Wato bai ma damu da abin da tace akan dan cikinsa ba sai yayansa wanda ya zama silar rushewar rayuwar 'ya'yanta maza.
"Ko in hada da kai ne?"
Mal. Inuwa ba arziki ya saita fuskarsa daga fushin da ya yi da farko
"Ni kuma me nayi?"
Ko kula shi bata yi ba ta dubi Abbati da murmushi. Wannan karon kallon yana cike da soyayyar uwa da danta. Yadda ya koma yafi mata ciwo akan shi kansa. Dukiyarsa take son ta raba shi da ita domin babu amfani su cigaba da ninkaya cikin haram. Sabuwar rayuwa za ta tura shi da taimakon Allah wadda bai taso cikinta ba tunda ya fara sana'arsa. A yanzu yafi bukatar soyayyarta da tausayawa kuma a shirye take ta nuna masa domin yaji dadin tuba.
"Kirawo 'yan uwanka su taimaka min na tashi."
Kai ya gyada daidai da saukowar hawaye a idanunsa. Tana kallon yadda yasa bayan hannunsa ya dauke hawayen sai dai bai hana wasu gudana suna maye gurbin wanda yake sharewa ba. Haka ya fita bai yi musu akan rashin son zamanta ba. Ya fahimceta sarai. A shirye yake ya bi umarninta. Da hannu ya kara goge idanunsa sannan ya kira kannen nasa.
Da ya fita Mal. Inuwa kallon tuhuma ya dinga yi mata. Tabbas akwai abin da yake faruwa tsakaninta da Abbati. A matse yake da son ji. Sai dai yanayin fuskarta ya sanya tayi masa kwarjinin da ba zai iya yi mata titsiye ba.
Likitan da ya dubata har bakin mota ya bisu yana nanata musu gangancin dake tattare da dauketa a yanzu.
"Bai kamata ku biye mata don ta ce ba za ta zauna ba" ya dubi matan da ya tabbatar 'ya'yanta ne saboda kukan da suke da rokon yayansu akan su zauna "za ta iya shiga yanayin da dukkanku nan sai kun yi dana sanin kin karbar shawarata."
Habi sai ta koma kusa da mahaifinsu tana kuka.
"Kaji abin da yake cewa Baba. Don Allah ka tilasta mata ta zauna."
"Abbati?"
"Baba muje gidan. Da kaina zan dawo da ita asibiti in Allah Ya yarda."
Iyakar abin da yace kenan ya shiga gaban motar da zata mayar dasu gida.
Deluwa ce kan gaba wurin zuwa bangaren Baaba Mari bayan sun dawo. Daga ita sai daurin kirji da dankwali a ka. Tabe baki tayi tana soshe-soshen jiki.
"Yo aka ce mana ranga- ranga aka fitar dake ashe ma ciwon ba wani na azo a gani bane."
Ci-kan-ki wannan bata samu daga bakin kowa ba. Ta gaji da maganganunta ta kama hanya za ta fita.
"Ki kirawo min mijinki idan kin fita"
Wata irin juyowa Deluwa tayi ta kalli bakin Baaba Mari da ya furta wannan maganar. Har wani duka ta kaiwa kunnenta domin tabbatarwa.
"Ki ka ce?"
"Ki turo min mijinki! Da jikina da kwari da kaina zan je na same shi."
Mal. Inuwa dama ya matsu yaji me yake faruwa. To amma shi ma yadda tayi maganar ba karamin tsorata shi ya yi ba. Musamman da ta sallami duka 'ya'yanta da jama'ar gidan da suke sashen nasu ta bar Abbati shi kadai. Dadin dadawa kuma sai shi ma Abbatin ya yi wata magana da ta sabule masa kuzarinsa ya kara shiga firgici akan me yake faruwa.
Hadiyar yawu mai masifaffen daci ya yi, idanunsa duk sun shige ciki ya dubeta.
"Baaba tona min asiri zaki yi? Na rantse miki ba yau na tuba ba. Ni da Munzali har..."
Runtse idanuwa tayi da ya ambaci sunan Munzali. Allah Ya sani ko sunansa bata son ji balle ayi hirarsa. Ya fice mata a rai lokaci guda kamar anyi ruwa an dauke. Akwai laifin mijinta da yayansa dumu dumu amma nasa mai girma ne. Bata jin zata taba manta cewa shi ya koya masa....karshenta ma har yanzu suna yi. Tsigar jikinta a take ta mimmike da wannan tunanin.
"Idan ban yiwa tufkar hanci ba ka san irinka nawa zasu samar mana a dangi?"
Abin da ta ce kenan. Sai ya koma jikin bango ya tsaya tare da jingina bayansa. Babu wani abu ko digo da yake yi masa dadi a duniyar nan. Nadama iyakar nadama ya kara yi. Ya tsani ranakun da ya mika jikinsa ga marasa tsoron Allah cikin manyan mutane masu fada a ji a kasar nan. Farincikin da kudaden suka saka shi ya koma bakinciki.
Sallamar Mal. Sa'idu da kakkaurar murya mai nuni da girman bacin ransa sai da tasa hanjin cikinsa kanannadewa. Zazzabi mai zafi har cikin 'bargo ya afka masa. Daga wannan lokacin zai sanya kafa guda da sabon shafin rayuwa. Idan har zai iya cigaba da rayuwar.
Shikenan!
"Wa nake gani kamar Mariya?"
Asabe ta takawa kafafunta burki a daidai kofar dakin Innayo. Laluben dakin da yake sakale akan dokin kofa ta sake dagawa da hannunta ta leka ciki. Tabbas jikarta ce take hangowa zaune akan cinyar Salima tana ta zuba surutu. Ranta ya sosu ta taka cikin falon ko sallama babu sai ganin hannunta Salima tayi tana kokarin fincikar Qibdiyyan.
"Tashi ki wuce muje."
Noke kafada tayi ta kwace hannunta. Salima ta murmusa kawai ta ce mata "tashi mana Qibdiyya. Sannu da zuwa Asabe."
"Ban son munafunci. Ki rike sannunki ki sakar min jika"
Sababi ta hau yi akan dalilinsu na riketa a dakin.
"Shi ma Munzalin zai zo ya sameni. Akan me zai kawota bai fada min ba?"
Innayo da Zara duka suna falon amma yadda bata nuna ta gansu ba haka su ma basu kulata ba. Ta gaji da fadanta ta dauki Qibdiyya da karfi ta nufi bangarenta.
Ihunta suka ji da ta tura kofar ta bude ba tare da ta saka mukulli ba.
"Jar uban nan! Wallahi gidan nan baku so zaman lafiya ba. Wace mai kokarin ce ta bude min daki?"
"Daddyna ne ya budewa su Uncle Lilu."
Asabe ta gatsina fuska "waye kuma Unku Lihu?"
"Uncle Lilu da yake min doki a bayansa... " Cewar Qibdiyya da mamakinta irin na yara idan aka kasa gane abu mai mahimmanci a wurinsu.
Asabe hakura tayi da neman ba'asi. Duk inda yake ta san dole zai dawo daukan 'yarsa. Zata nemi karin bayani a wurinsa. Sannan kuma ta samu ta karbi kudin da take tunanin shi ya zo bata.
Mayafinta ta kama za ta cire Qibdiyya ta ce zata yi fitsari. Sunkutarta tayi gabadayanta ta shiga bandaki. Yarinya fes da ita amma saboda son burge mahaifinta kamar ba dan cikinta ba ta tube mata kaya.
"Wanka zan miki kada ya dawo ya ganki haka kamar wadda tayi dambe."
Bata da ruwan dumi amma don kar ya dawo bata gama ba idan ta tsaya dafawa sai tayi mata da mai sanyi. Qibdiyya harda kukanta don garin babu wannan zafin da zai sa mutum wanka da ruwan sanyi. Aka zo shafa mai tabi ta mulketa da man kadanya sai kyalli take. Ta kawo kwalli aka rambada mata a ido. Ta tafi dauko pant din da ta cire mata a bandaki Qibdiyya ta kai hannu gabanta tana susa. Wanka ne aka yi aka koro maikon jiki amma ba ayi mata tsarki ba. Dan datti da ruwan sabulun da ya wuce ta wajen da fitsarin da tayi ba a wanke ba.
Wannan susa akan idon Asabe da ta dawo daga bandakin.
"Kalau kike kartar jiki haka da karfi? Kwanta mu gani ko kurji ne a wajen."
Da kanta ta kwantar da ita ta kai hannu za ta raba kafafunta taji ta cafke mata hannun. Idanuwa Qibdiyya ke binta dasu tana yi mata kallon tsoro.
"Kema hannu zaki saka min a nan? Kiyi min a hankali ba mai zafi ba. Kuma ba zan fadawa kowa ba don kada ki yanka min Daddy da Papa."
Asabe ido kawai ta zuba mata ta kasa kwakkwaran motsi saboda firgici.
Qibdiyya kuwa tuni ta rufe ido tana jira ayi a gama. Da taji shiru sai ta bude idon a hankali. Da karamar muryarta ta ce da Asabe,
"Ni ce zan yi miki?"
Kamar wadda aka kwadawa mari sai lokacin Asabe ta dawo hayyacinta. Kuka ta kama yi ba tare da ta sani ba ga jikinta ya soma rawa kamar mazari. Furucin Qibdiyya ya matukar tayar mata da hankali fiye da tunani. Shi yasa bata ma san lokacin da ta d'aka mata wani mugun duka a cinya ba.
"Ki yi min uwar me? Na bonu ni Asabe. Kiyi min me? Tashi don uban...."
Qibdiyya ta tashi zaune a razane tana son yin kuka amma tsoro ya hana. Daddy ya hanata kuka ko taji zafi idan yana yi mata abu irin wannan. Cewa yake hawayenta na fita za a saka mamanta a rami a rufe da kasa. Tun bata iya ba har ta kware wurin danne hawayenta. Idanu tsilli tsilli ta kafe Asabe dasu babu alamar kuka duk zafin dukan.
"Daina kallona" wani tunani tayi ta sake kwantar da Qibdiyya ta soma dubata. Allah ne kadai Ya taimaketa bata suma ba akan abin da ta gani. Kankanuwar yarinya ta kusa gama budewa.
Kafafunta kasa daukarta suka yi bata ankara ba tayi zaman 'yan bori a kasa. Kai ta dago dankwalinta ya karkace saura kadan ya fadi ta kalli jikarta.
"Waye yake taba miki nan?" Ta nunawa Qibdiyya inda take tambaya da hannu.
Razanar da tayi a dalilin dukan da tayi mata dazu da kuma tsoron kada a rufe mata uwa a rami sai taki fada. Jikinta yana bata cewa idan ta fada din ma ba tsira zata yi ba.
Asabe ta gaji da tambaya ta soma dukanta. Amma ko digon hawaye babu sai ajiyar zuciya. Hargagin muryarta tana cewa "ba za ki fada min ba?" har tsakar gida. Uwani ta fito tana waya taji. Hanyar dakin ta nufa sai dai kafin ta isa Innayo ta fito daga nata dakin ta ce mata kada ta soma zuwa.
"Bana son gulma ki zo ki wuce naki uzurin kada ki ja min magana".
Komawa tayi din amma haka kawai taji ta kwadaitu da son sanin me yake faruwa. Maganar dai kamar da Qibdiyya ake yi amma bata ji ko tarin yarinyar ba.
"Munzali kana ina?"
Sautin muryarta banda alamun tashin hankali harda kuka yake iya ji.
"Muna asibiti da Hasiya ne amma na kusa tahowa. Wani abin ne?"
Karo na farko a rayuwar Asabe da ta dakata tayi tunani kenan da kwakwalwarta. Wannan sam ba maganar waya bace.
"Ka taho da sauri ina son ganinka yanzun nan."
Bayan ajiye wayar hankalinsa ya kasa kwanciya. Yasa rai da jin mitarta akan zuwa wurin 'ya'yan Innayo. Kudi ya damkawa Ummita kafin shigowar Hon. Habu ya ce musu zai je gida ya dawo.
Akan hanya ya dinga kiran Abbati shiru bai dauka ba. Kansa ya sake daukar chaji kamar ana buga guduma. Ya san Abbati ba yaro bane da za a zane bayan ya fadi gaskiya. To amma me ya biyo bayan fadin tunda ya tabbatar da wahala idan bai fada din ba.
Sanyi da daddadan kamshi ke tashi a wani katafaren falo. Duk inda ake neman ni'ima mai shiga zuci an gama samu a nan. Mazauna wurin maza ne su biyar wadanda shekarunsu suka tura. Ga kuma shaida a jikinsu na cewa sun kama kasa. Daga 'yan siyasa sai 'yan kasuwa sai kuwa masu manyan mukamai a gwomnati.
Dukkaninsu sanye suke da manyan kaya harda babbar riga illa mutum daya. Daga gani shi ne mai masaukin baki saboda yadda ya bararraje. Hula da babbar rigarsa duk suna gefe guda can nesa dashi. Bayani yake yiwa babban bakonsu. Amininsu ne ta fanin harkokin 'yan mata. Sai gashi a Kano garin yake gida ga sauran hudun.
"Yanzu sai da kana shirin komawa Kaduna zaka sanar damu zuwanka Alh. Tahir? Karramawar nan da ake yiwa manyan baki ma baka bamu damar yi maka ba."
Cewar mai gidan hutun (guest house) din da suke ciki.
Dariya Alh. Tahir ya yi masa "banda abinka ni da na taho da taurarina guda uku ina ni ina bin kwararo?"
Kwashewa suka yi da dariyar shakiyanci suna zolayar juna. Nan hira ta kacame da ciye ciyen kayan abinci na alfarma. Maigidan aka kira ya amsa ya bayar da umarni ga mai kiran da ya shigo.
Alh. Tahir na jin haka ya san ba zai wuce mace aka kawo ba. Murmushi ya yi yana gyada kai.
"Ni dai bari na gudu don na tuba."
Wani Alhaji mai tulun ciki ya tafa da na kusa dashi suka yi masa dariya "Kowa ya tuba don wuya ba lada."
Alh. Tahir ya kada kai "da lada fa. Abubuwa sun cabe min. 'Yar banzar yarinyar nan kawar Farha da nake fada muku yanzu fa Yakumbo ta rantse sai na aureta. Yarinyar da take yawonta da kananan yara kuma duk na sani."
Mai gidan yaja guntun tsaki "duk laifinka ne. Na fada maka wallahi Malamina yana aiki akansu maganar nan zata bi ruwa. Ita Yakumbon da kanta za ta ce a bar maganar. Yarinyar kuwa duk iskancinta sai an sauke mata shi. Ba za ta sake yin wani yunkuri domin bata maka suna ba."
"Wai kai Alh. Tahir tsoron me kake ne? Ka amince mana ka yar da kwallon mangwaro. Yarinyar nan a bariki ta sameka tayi kadan ta kawo maka cikas da girmanka da komai." Wani da bai ce komai ba tun dazu ya tofa albarkacin bakinsa.
Mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki. Basu wani jima ba suka shawo kansa. Nan take Maigidan wanda aka fi sani da Comared ya kira Malamin tsibbunsa a waya. Suna kan magana wani mutum sanye da kufta da wando ya zo ya shige cikin dakin Comared din da dan matashi da bai fi shekaru sha takwas ba.
Bayan ya gama wayar ne Alh. Tahir ya tsare shi da idanu yana nuni da dakin nasa.
"Comared ba dai kaima ka fara daya harkar ba da maza?"
Kkamar dazu, yanzu ma dariya sauran suka yi masa. Comared ya gyara zama yana shafar gemunsa.
"Wannan Malamin da na kira shi ya dorani a harkar nan. Naki fada maka ne kawai saboda naga kamar kana kyamar abin. Magana ta gaskiya wani aiki aka yi min shi ne yace na nemi namiji. Washegari aikin ya ci to amma abin ya zarce...." Ya kare da shu'umar dariya.
Alh. Tahir ya kada kai "kace ya hadani da mata goma ni dai akan namiji guda."
Wata dariyar Comared ya yi domin aikinsa kenan. Dariya kamar dan akuya.
"Ai kuwa ka makaro domin kuwa namiji ya ce ka nema ranar laraba kafin rana tayi zawali. Indai kayi yadda ya ce da kanka za ka nemeni. Zai aiko da magani da zaka hada kafin kayi abin."
Hula Alh. Tahir ya cire ya shafi sumar kansa wadda ta fara samun bakin furfura. Ko kadan baya son auren Yumna musamman saboda abin da ta nunawa Farha. A bangare daya kuma ko yana shan giyar wake ba zai so tsinuwar Yakumbo ba. Sau daya dai don ya nemi namiji ba zai rage shi da komai ba. Yana tunanin abin yaji tsigar jikinsa ta mike har amai na neman taso masa. Wayarsa ya dauka ya tashi yana yi musu sallama.
Comared ya dakatar dashi daga tafiya "bari nasa ayi maka booking wanda ya san me yake yi tunda kai sabon shiga ne" waya ya dauka ya sake kira sai ga mai kuftar da ya shige dakinsa ya fito.
Zubewa ya yi kamar mai rokon gafara a gabansa "Yallabai kana da wata bukatar ne?"
Kofar dakinsa ya kalla ya hadiyi yawu "yaron da ka kawo daga gani ya yi kawai. Kwararre a harkar nan nake so kayi min booking ranar laraba mai zuwa. Ina son irin wanda idan sabon kamu ya samu gobe da kansa zai koma. Daga aljihuna kadai zan baka dubu dari biyar. Shi kuma uban gayyar ba mai rowa bane. Ka sa rai da farin gani."
Shazali ya saki murmushi har hakoransa suka fito. Ya san inda zai samo musu kalar wadanda suke so. Shi da yake da shaidar da zata tarwatsa musu rayuwa, dolensu su zo ko sun ki ko sun so.
GOMA
AYA GOMA.
Akwai uwa kuma akwai uwa! Wadansu uwayen sun san cewa 'ya'ya amanar Allah ne kuma suna kokari wurin ganin sun sauke in nauyin. A cikinsu wasu suna yin nasara wurin aikata daidai a wannan tafiya mai dadi da wahala. Wasu kuwa kuskure suke aikatawa wanda soyayyar 'ya'yan ne yake zama sanadiyarsa. A shagwaba 'ya'ya fiye da kima. A kasa tsawatarwa kurakurensu, sannan a karshe a biyewa ra'ayoyinsu koda zuciya da kwakwalwa sun san hakan bai dace ba. Kaso na biyu cikin uwayen bayan wannan rabe raben na masu son sauke nauyi sune masu fifita kawunansu da bukatunsu akan na 'ya'yansu. Irinsu ake yiwa lakabi da ballagaza.
Kwakwalwarta kalau take balle ace lalura ke hanata bawa 'ya'yanta kulawa. Ita bata ma san cewa kuskure take aikatawa ba. A lissafinta kodayaushe ita ce farko kafin danta. Shi yasa take gabatar da farincikinta kafin na danta. Ita fa ko yunwa ke damunsu ita da 'ya'yanta sai ta fara koshi take tunawa dasu. Idan abincin babu yawa sai su kare da sudin hannu. Kulawa wadda ke karkata zukata ga nuna tausayi da damuwa ga mai bayar da ita bata fiya shiga tsakaninta da nata ba. Wannan sakacin nata zai iya zama kalubale kuma babbar jarabawa ga 'ya'yanta da duk wanda ya rab'e su. A karshe da za ta rigasu komawa ga Allah da wahala su ji kewa irin wadda 'ya'ya ke ji idan sun rasa uwa. Albarkacin wata tara, nakuda da shayarwa kadai za ta ci.
Ya ke Uwa!
Ki koyawa 'ya'yanki sonki ta hanyar kulawa, tausayi, jinkai, ladabtarwa da soyayya. Idan a gaba kin sami sabanin tarbiyar da kika yi musu ki sani cewa kowane bawa yana tafe da kaddararsa. Ke dai ki tabbatar cewa kin yi iya yinki har a gaban Allah ta yadda ba za ki zama wata Asaben ba. Kin bata naki ki bata na wasu da basu ji ba basu gani ba.
Kada ku manta laifin ba na Uwa bane ita kadai.
Ya dauki kimanin minti goma sha biyar a dakin bata ce komai ba. Hasali ma ko motsi daga inda take bata yi ba. Qibdiyya ce a gefenta idanunta a kumbure sun yi ja, da gani tasha kuka. Ya yi mata magana bata amsa masa ba. Tun shigowarsa da ta taso a guje Asabe tayi mata tsawa ta koma ta zauna.
Gajiya ya yi da shirun. Ya san halin mahaifiyarsa. Karshenta kudi take son karba a hannunsa take ta kirkiro wannan dabarar. Hannu ya zira a aljihu ya zaro dubu goman da ta rage a hannunsa ya dora mata a hannun kujera.
"Qibdiyya taso mu tafi" ya furta a yayinda ya mika mata hannunsa don ta kama.
Sannan Asabe ta tashi da fada bayan ta kwashe kudin "ince ka zo amma don raini baka tsaya kaji me ya faru ba za ka tafi."
Hannu yasa ya matse kansa da yake ciwo. Haka ya soma magana kamar zai yi kuka. Bai san wata damuwar da ta zarce rashin ji daga Abbati ba. Washegari yake son bin sa, ko ma me za ayi gara ayi musu tare. Ko kuma ya bishi a yau....tunaninsa ne ya katse lokacin da Asabe ta sakar masa harsashin da ya bula kwakwalwa da zuciyarsa.
"Ban san wane irin sakaci kake yi da 'yarka har wani tsinanne ya..ya" sai taji bakinta ya sarke sakamakon idanun da Munzali ya zuba mata.
"Me aka yi?" Ya furta da sautin da yafi kama da umarni. Bai ma san ya yi amfani dashi ba saboda yadda ya soma tsorata tun kafin yaji karshen zancen.
Asabe ta hadiyi yawu "ina jin fyade aka yi..."
"Qibdiyyan???" Ya tambaya a razane kafin ma ta kai karshe. 'Yarsa ya dauka da zafin nama yana neman dubata mata jiki.
Asabe tayi azamar karbeta "baka da hankali ne za ka bude mata jiki? Na riga na duba kuma wallahi namiji ya kusanci..."
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un....hawaye ne suka ballewa Munzali. Zancen ya dinga bin sassan jikinsa tamkar ana huda shi da alluran da aka kona a wuta. A wurin ya durkushe yana kuka mai sauti. Kuka irin wanda bai taba yin kwatankwacinsa ba. Da z
ai ci karo da ko ma waye ya tabbata sai dai ayi masa takwara a dangi domin shi kam tasa ta kare. Kashe shi zai yi idan ya so shi ma a hukunta shi.
Asabe gani tayi ya dora hannu a kahon zuci yana bugun kirjinsa. Idanunsa basu bar fitar da hawaye ba.
"Kashe kanka zaka yi ko kuwa zaka tambayeta waye ya mata wannan aikin?" Sannan ta kara da cewa "kuma ina zargin ba abin kwana daya bane domin kuwa alamu sun nuna ta soma sabawa."
Runtse idanuwansa kawai ya yi. Yawancin maza idan 'ya'yansu mata suka isa aure sai kaga suna ja wa manemansu aji. Ba don komai ba kuwa illa tunanin cewa idan ka auri 'yata fa ga abin da zaka yi mata. Wannan kishin yadda uba yake yiwa 'yarsa haka 'ya'ya maza suke yiwa uwayensu idan kaddarar sake aure ta gifta musu. Munzali yaji zuciyarsa tana suya a kirjinsa. 'Yarsa mai shekaru biyar ake cewa ta saba...ta saba da namiji a kananun shekarunta. Shi da ransa, mahaifiyarta ma da ranta. Garin yaya???
(Zina bashi ce Munzali. Kaga Allah Ya bamu 'ya. Idan bamu tuba ba wata rana ita za ta girbe abin da muka shuka)
Kalaman Abbati a wani lokaci da yake yi masa maganar tuba daga wannan alfashar suka dawo masa. A hankali ya tashi yaje gaban Qibdiyya ya durkusa. Ya mika hannuwansa gareta duk ta firgice. Asabe tayi mata dukan da ba a taba yi mata ba a dalilin kin fadan wanda yake mata. Shi yasa ta tsorata ko shi ma dukanta zai yi. Ga mamakinta da Asaben sai ya rungume Qibdiyya. Riketa ya yi sosai a jikinsa yana jin kamar ranar suka fara haduwa bayan haihuwarta. She will always be his baby duk girmanta. Kasancewarta tsatsonsa bai kara mata komai ba sai masifa. Ya cuceta cuta ta har abada domin an bar mata tabo daga barnar da ya kasance yana aikatawa.
"Ki yafe min Mariya. Ki ce kin yafe min."
A razane Asabe ta taso har tana tuntube da kujera.
"Me kake cewa. Na shigesu. Munzali kai ne ka bata..."
Magana ya cigaba da yiwa Qibdiyya da taushin murya.
"Ki yafewa uban da bai bar alkhairin da zaki mora a rayuwarki ba sai sharri. Nayi miki alkawarin gyarawa. Zan yi ta tuba har karshen rayuwata. Ina fatan Allah Ya haskaka rayuwarki Ya wanke miki duhun da na janyo miki."
"Munzali kayi min gwari gwari don Allah. Shin kai ne ka bata 'yar nan?"
"Allah ba zai dora min wannan kaddarar ba in sha Allahu."
"Washhh har hankalina ya kwanta" tace tare da sauke ajiyar zuciya "yadda ka ke magana ne sai a zata kai ne."
Da Qibdiyya a hannunsa ya juyo ya fuskanceta
"Hankalinki kar ya kwanta Asabe. Ke ki ka assasa komai."
"Kar ka dora min laifin da ba nawa ba. Dubata fa kawai nayi na sanar da kai. Banda sakarci ita kadai kwal amma kun kasa kula da ita."
Murmushin bacin rai ya yi "kamar yadda ki ka kasa kula dani da 'yan uwana?"
Ba ta zaci wadannan kalaman daga bakinsa ba shi yasa ta dinga bude baki tana rufewa don mamaki. Da kyar ta iya yin magana muryarta tana fita kamar an shake mata wuya.
"Me kake nufi?"
"Bayan haihuwata da suna da ku ka saka min ke da Baba kuna da wani abin kare kai a wajen Allah game da tarbiyyata? Kin san sana'ata? Kin san silar arzikina?" A yanzu sababbin hawaye sun cika idanunsa har suna zuba amma dariya yake yi "ina dauke da zunubina ga na Abbati da nayi silar fadawarsa mummunar rayuwa. Ba mamaki shi yasa Allah Ya jarabceni akan Qibdiyya."
'Kada kayi sab'o' ya fadawa kansa da ya tuna da cewa da a gaban Abbati ya fadi wannan maganar haka zai ce masa.
Tunanin Asabe sai ya luluka da ita duniya daban da wadda Munzali yake son haska mata. Gani take kamar abin da ya sami Qibdiyya ne yake neman taba masa kai. Banda haka kaf zantukansa basu yi ma'ana ba a cewarta. Tana kallo ya murda kofar dakinta ya fita. Sai dai me?
Yana fita suka yi ido hudu da guda cikin 'yan uwansa mata. Idanunta kadai ya kalla ya san ta gama jin komai. Abin mamaki shi ne yadda zuciyarsa bata ji komai ba. To me zai ji bayan ciwon da yake ciki a yanzu? Matsalarsa bata wuce rashin sanin halin da Abbati yake ciki ba. Sai kuma tunanin irin hukuncin da zai yiwa wanda ya soma ketawa diyarsa haddi.
Zaune akan kujera Mal. Sa'idu ne yana karkada kafafunsa. Su hudu ne a falon Baba Mari. Daga ita sai Abbati, Mal. Inuwa da shi babban bako na musamman. Bacin ransa baya bukatar ya bude baki ya yi magana. Yanayinsa kadai ya isa tsorata jama'ar gidan.
Mal. Inuwa kansa a takure yake don idan fadan ya tashi babu mai tsira. Da ya dubi Baaba Mari sai ta bashi tausayi. Duk yadda aka yi zafin ciwo ne ya kaita ga yin wannan kasadar.
Gyaran murya Mal. Sa'idu ya yi gami da yin kwafa.
"Inuwa gani a gaban isasshiyar matarka. Ka umarceta da ta fadi abin da yasa ta aika NI SA'IDU in zo inda take."
"Mari..." Mal. Inuwa ya fada a hankali kamar yana rokonta da ta kawo karshen zaman nan.
Mal. Sa'idu ne ya katse shi
"Idan kuma takamarta haihuwar Abbati ne to ka tuna mata cewa ni da ake zagi, ni ne silar arzikinsa. Bayan duk tijarar da ta gama yi akan tura shi karatu gashi tafi kowa girbar samunsa" ya daga hannu yana kadawa domin kashedi "duk da haka babu wata mace da ta isa ta nuna min iko da danta domin iyayensu maza ma umarni na suke bi. Abbati da duk abin da ya samu nine sila..."
"To Alhamdulillahi..." Baaba Mari ta katse shi.
Kowa sai ya kalleta da tayi magana. Abbati kuwa ji yayi kamar kasa ta bude ya shige ciki kada a sake jin ko da sunansa balle labarinsa. Ya amince da ko ma me zata yi amma hakan ba zai hana shi jin tamkar tsirara yake a gabansu ba.
Kamar tana jin rurin da zuciyarsa take yi sai ta kira shi da hannu. Kafafunsa da yake ji kamar ba nasa ba haka suka kaishi gefenta ya sulale ya zauna. Dan murmushi tayi masa wanda ya sake nutsar da zuciyarsa sannan ta fuskanci Mal. Sa'idu.
"Fashin baki nake son yi muku akan wani abu da kuke yi mara tushe kafin na fadi illar da ya janyo min."
Mal. Sa'idu ya yi dariya
"Magana kike son yi akan zuwa almajiranci ko? Ke a dole ba za ki karbi addini a yadda ya zo miki ba?"
"A yadda yazo muku dai. Wannan fitinar da kuka farlanta bata cikin shika shikan musulunci. A takaice ma dai baku yiwa addinin komai ba sai bacin suna."
"Mari wai sai yaushe zaki daina janyowa kanki matsala da Yaya Sa'idu?" Cewar Mal Inuwa cikin fushi.
"Kila yau! Yau din da nake so kai dashi ku san cewa kun dade ana rubuta muku zunubi a matsayin wadanda suka jagoranci aikin alfashar da dansu yake yi saboda mummunar akida."
Falon sai ya yi tsit. Baka jin komai sai hawa da saukar numfashi. Kan Abbati a kasa yayinda Mal. Sa'idu yaji lokaci ya yi da zai saurari Mari. Kalamanta ba karamin zargi bane wanda yake jin dole sai da hujja za ta yi shi.
"Addinin Musulunci da kalmar Karatu ya fara zuwa garemu. Wannan yake nuni da cewa ko kadan jahilci bashi da muhalli a cikinsa. Allah ma Ya ce mu san Shi kafin mu bauta Masa. Duk musulmin kwarai bai dace ya yi gaba da neman ilimi ba."
Mal. Inuwa ya ce "to amma ai ke kina yi."
"A fahimtarku ba" ta nuna Abbati da yatsanta "ga danku nan. Kamar kowane bawa shi ma da tasa kaddarar yazo duniya amma kune sila. 'Ya'yanmu amana ne. Babu inda aka ce mu sakesu da kananun shekaru neman karatu ba tare da kyakkyawar kulawa ba. Kun turasu gidan malamai da sunan neman ilimi amma babu abinci. Yunwa ba kanwar uwar kowa bace. Idan ta taso dole a kawar da ita ko a ji jiki. Babba ma idan ka kai shi karatu babu abinci ka hada shi da jidali balle yaro. Wani sai ya wuni yana barar bai samu ba. Mutane su ci karo dasu wasu su zagesu wasu su tsine musu tare da mu iyayensu saboda sun dame su da bara. Ba dole su nemi abinci ta hanyar da ta fi musu sauki ba? Wasu su dace da halal, da yawa su fadawa haram. Hatta masu kwacewa na kasa dasu kana ganin laifinsu? Sun yi girma da bara kuma da gaske babu abincin. Sannan sun tafi babu tunanin ranakun da zasu tashi ba lafiya. Waye zai kula dasu idan suna ciwo? Wa zai basu magani? Ko kun manta ranar da na shigo garin nan da gawar Sani ba tare da na san ya rasu ba?" Sai ta fashe da kuka. A haka ta cigaba da cewa "Uwa uba baku ajiyesu a inda za a basu tarbiyya ba. Iyakarsu da malamansu a biya musu karatu su bayar da hadda. Idan sun yi laifi a zane su. To amma tarbiyyar fa? Sai abin da suka tsinta a titi? Da yawansu basu tashi sun ga jinkai da tausayi ba. Dan shekara shida yana yawo a unguwa neman abinci a lokacin muku-mukun sanyi ko damuna. Wani idan ka ganshi saboda rashin kulawa da zama cikin hazo sai dai ka dinga ja masa Innahu min Sulaimanu. Wallahi zato zaka yi aljani ne. A makarantar babu mai tausaya musu sai kalilan idan anyi sa'a. Mu da muka haifesu mun riga mun bata rawarmu da tsalle da muka rabu dasu da kuruciya. A karshe zukatansu su bushe. Idan anyi dace yaro ya zama nagari, idan ba a dace ba ya buwayi al'umma."
"Yanzu ki ka ce kowa da kaddararsa. Ni tun tasowata banda Sani da jikan Mai-adua ban taba jin labarin yaron da yaje karatu ya rasu ba. Gidan nan yara nawa muka tura kuma gasu nan duk sun dawo kamar ba ayi ba?"
Mal. Sa'idu kenan. Ya fadi haka ne ba don zuciyarsa bata soms zuwa inda Baaba Mari take son kai shi ba. Ba dai ya son ya karbi gyaran ne daga gareta.
"Ashe baka ji lokacin da nace kowane bawa da kaddararsa yake zuwa ba? Amma akwai sila. Kuma dole ne silar ya karbi sakamakon abin da ya zama tushen faruwarsa mai kyau ko akasinsa."
"Kai Abbati. Wace irin sana'a kake yi? Sata ko fashi?" Cewar Mal. Sa'idu muryarsa ta soma sauyawa daga dakiyar da yayi da farko.
Abbati bai iya amsawa ba. Ba zai iya cewa ga takamaimai abin da yake cikin zuciyarsa ba.
"Ba da kai nake ba!" Ya daka masa tsawar da zata firgita mai karamin tunani "nace wace irin sana'a kake yi?"
Baaba Mari ta daga masa hannu duk da kwarin jikinta yana ta raguwa.
Tsawar da ya yi ta bata rai itama ta koma yi masa magana tana daga murya.
"Baka da hurumin yiwa dana tsawa Yaya Sa'idu. Wannan damar ta saraya a wuyanka. Abin da ya rage tsakaninmu bai wuce ALLAH YA ISA ba. Ni da d'ana bamu yafe mak...."
"Mari!" Mal. Inuwa ya kirata da karfi.
"Kaima da ka kasa tsayawa 'ya'yanka ka tanadi amsar fitar da kai ranar lahira."
Dakin ya yi shiru na wani lokaci. Iyayen maza biyu mamakin kalamanta ya ishe su. Baaba Mari kuma ciwo ke neman dawowa sabo. Abbati ya matsa kusa da ita da sauri. Filo ya kara mata a bayanta domin ta zauna da kyau.
Mal. Sa'idu ya rasa me zai ce ya kare kansa sai "Yanzu ke da ace barinki aka yi da yaran nan za ki iya kula dasu ba tare da uba ba? Uwa ai ba ita kadai ce madogarar 'ya'yanta ba. Sannan karatun nan da kike ta suka ba shi ne yake taimaka musu wurin iya rike kawunansu a duk inda suka sami kansu ba saboda sun horu?" maganar ma a hankali ta fito.
"Rike kai..." Baaba Mari ta furta da murmushin da tun dazu take yawan yi domin ragewa Abbati damuwa "Allah bai halicci kananan yara domin su rike kawunansu ba. Da haka ne kuwa to kowannemmu zai fado daga sama idan lokacin haihuwarsa ya yi. Yaya, cikin daukar ciki da haihuwa akwai mabanbatan wuya irin wadda bakunan mata kadai ke iya labartasu. Wannan azabar mai kama da mutuwa bata taba hana uwa mai cikakken hankali son 'ya'yanta ba. Ashe baka san.." ta dubi idanun Mal. Sa'idu babu tsoro ko shayi "soyayyar uwa da 'ya'ya aya ce cikin ayoyin Ubangijinmu ba? Cikinsu ya hanamu lafiya, haihuwarsu ta gadar mana da ciwo da sauyin halitta, tarbiyarsu ta janyo mana zagi da aibatawa komai kokarinmu amma duk da haka bamu fasa son kayanmu ba. Me yasa karatu yazo mana da cewa Allah Yana kunyar wadanda bai bawa haihuwa ba? Kuma Ya umarcemu da kyautatawa marayu domin samun lada. Lallai Ubangijin da Ya samar da wannan ladan ba zai so a tauyewa uwa zamewa 'ya'yanta uwa ba. Munfi kowa son cigaban 'ya'yanmu. Idan suka zama manyan malamai sai nafi kowa cikinku farinciki. Amma zama malamin ko wani kwararre a fannin da Allah Ya dorasu yana tafe da kulawarmu. 'Ya'yanmu suna bukatarmu kafin su shiga duniya su iya rike kawunansu. Baka bani damar kulawa dasu a lokacin da suka fi bukata ta ba. Yaya Sa'idu jawabina da yawa. Gashi na gaji bana jindadi. Kuje kai da dan uwanka na barku da ...."
Caraf Mal. Inuwa ya hanata karasa magana "haba Mari karki karasa mana. Ni duk zancen ma baki fada mana me yake yi ba."
Ta kalli fuskar Abbati sai kawai ta tashi ta barsu a wurin ta shige dakinta. Shi da ta bari taji nauyin karasa labarin da kansa ya zayyane musu komai. Mahaifinsa ya dinga kukan da ko ranar da iyayensa suka bar duniya bai yi irinsa ba. Daga cikin dakin Baaba Mari tana jinsa ita ma kukan take yi. Hawaye wani yana min wani babu kakkautawa. Mal Sa'idu ne ma bata ji koda tarinsa ba sai daga baya taji alamun faduwa da kuma kiransa da karfi da Abbati da Mal. Inuwa suka yi.
Honourable ya kai ya kawo a dakin asibiti ya kasa zaune ya kasa tsaye har likitan da ya sake shiga ya fito.
"Baku yi min bayani ba sai shiga kuke kuna fita. Me ya sameta?"
"Alhaji muje ofis muyi magana."
'Yan matan aka bari a kanta yabi bayan likitan. Ana cewa ya zauna bai ji ba don hankalinsa baya tare dashi.
"Yallabai matarka ciki gareta na wata uku."
Cikin wani gigitaccen farinciki Honourable ya ce
"Allah Hakimu, Hasiya ke da ciki? Alhamdulillah. Allah Ka karawa Annabi SAW daraja."
"Amin" cewar Likitan "sai dai akwai 'yar matsala."
Nan da nan Honourable ya zauna hannuwansa akan teburin likitan. Murna tana neman komawa ciki.
"Zubewa ya yi?"
Gamsashen bayani likitan ya yi masa akan halin da take ciki. Mahaifarta bata da kwari ne tana barazanar zubar da cikin. Idan ba a daure mahaifar ba zai iya zubewa. Sannan tana bukatar bed rest na wani lokaci. Kuma ta daina komai har ya yi kwari a gani.
Honourable ya ce musu ya amince ayi duk abin da ya dace. Yana fitowa masallacin asibitin ya nufa ya yi sallah raka'a biyu domin godiya ga Allah. Hasiya ke rike da gidansa da sanaarta. Da ace wata biyu da suka wuce ta sami cikin nan mai matsala bai san yadda zai yi ba. Yana neman kudi sosai amma kamar kofofin samun sun toshe masa. Yanzu gashi tayi cikin a lokacin da yake da abin kula da ita. Minista Abdulkarim ya bashi kudi a hannu banda wanda ya zuba a account din asibitin da aka kai Abbas.
"Allah Ka kara mana hakuri da kaddara kowace iri."
Daga nan bai koma cikin asibitin ba. Adaidaita sahu ya tare ya ce a kai shi Dala. Sai dai akira shi duk abin da aka ga dama amma da bakinsa zai yiwa Innayo wannan albishir. Ita ce mutum ta farko da ya san Hasiya za ta so gani idan ta tashi. Kuma bai ga wanda zai yi masa tattali da jinyarta kamar mahaifiyarta ba.
Kankanin daki ne kamar akurkin kaji, ba taga ko daya sai kofar shigowa. Babu komai a cikinsa sai tarkacen gyaran mota irinsu spanner, sukun direba da matattun tayoyi. Iskar dakin kuwa warin fetur take da bak'in mai. Daga bayan inda aka jere wasu tayoyi suka yi tsini muryoyi ke tashi a hankali. Daya tana magiya dayar kuma tana bayar da hadin kai. Cikin sassarfa Suhaib ya shigo dakin ya isa bayan tayoyin ya leka. Mummunan gamun da ya yi bai sa shi ja da baya ba sai ma cakumo wuyan rigar namijin da ya yi.
Dani ne sanye da kayan makanikai ya yi duqun-duqun. Suturarsa da fatar jikinsa duka suna neman agajin wanka da wanki. A tare dashi kuwa ba kowa bace illa Ayaah. Fuskarta babu kwalliya amma tayi kyau. Hijabin jikinta kuwa dama shi Dani ya kamo saura kadan ya gama cire mata shi. Ya gama hillatarta da alkawarin aure idan ta yarda ta bashi hadin kai kamar yadda Suhaib yaji.
Kunnenta Suhaib ya murde iya karfinsa yana yi mata fada cikin bacin rai.
"Ban yi miki magana ba dazu?"
Ayaah ta turo baki "wai kai ina ruwanka? Kuma ba ya ce zai aureni idan Mummy ta dawo."
"Mooooommiiii"
Yaji an ce daga gefensa. Kunnen Ayaah ya saki ya juya. Yarinyar nan mai kwalliyar aljanu cousin din Abbati ya gani. Bata fasa kiran Mooomiii ba. Lilu a kusa da ita ya dinga dariya yana kiranta Iya duba duba.
A zabure Suhaib ya tashi daga bacci yana salati. Kansa ya yi wani irin nauyi kamar an dora masa dutse. Baccin dauke shi ya yi bai sani ba. Fuskar Ayaah ce ta zauna masa daram a kansa lokacin da ya gansu Dani zai cire mata hijabi. Murmushi take yi kamar abin da suke niyar yi daidai ne.
"You have the guts to smile (har kina da damar yin murmushi)" ya furta tare da yin kwafa ya yi wurgi da filo.
Sake kwanciya ya yi niyar yi wani tunanin ya fado masa. What if yarinyar nan ta bi mutumin yaje ya bata mata rayuwa? Daga hirarsu ta dazu ya fahimci kamar yanzu ne yake neman amincewarta.
"Wannan kanta baya ja da gani"
Tsaki ya yi ya tashi a gurguje ya zura takalmi ya fita zuwa cikin gidan. Yawancin 'yan biki sun watse tunda yau aka tafi da amarya Kaduna. Yana shiga suka yi kicibus da Mardiyya.
"Bani wayarki."
"Wallahi Ya Suhaib babu komai a ciki mara kyau."
Murmushi ya mata duk hankalinsa yana kan wayar.
"Karki damu Auta na yarda dake."
Wayar ta bashi ya laluba contact dinta. Da yazo kan numbar Ayaah da sunanta da ya zauna masa daram a ka ya ganeta. Yana wurin suka karbi nambar juna. Kallo biyu ya yiwa numbar ya haddaceta. Mardiyya tana jiran taga me zai yi sai gani tayi ya miko mata wayar.
Dakin da suka yi masauki ya koma ya samu wuri ya zauna a gefen gado. Yana danna kira ta shiga. Sai yaji wani bakon yanayi ja sarkewar harshe ya ziyarce shi. Me zai ce mata matsayin dalilin kiran?
Kunyarku nake ji wallah. Haka dai zaku dinga hakuri dani saboda Son So dake tsakaninmu. Allah Ya barmu tare har aljanna. Amin
Chapter 1 · 0% Book details