← Book details Tsatsuba Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 9

Sashe 9

Tsatsuba Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Lokacin da boka Barwas yazo nan a zancensa sai sarki shardas ya kamu da tsananin farin ciki bai san sa adda ya rungume boka barwas ba yana mai kyalkyala dariya daga can kuma sai ya janye jikinsa daga cikin nasa suka fuskanci juna ya dubeshi yace tabbas yanzu na sami nutsuwa da kwanciyar hankali saboda haka ka zuba idanu kawai kasha kallo zaka ga abin da zai biyo baya, koda jin haka sai boka barwas ya kyalkyale da dariyar farin ciki yayi ta kyakyatawa kamar ba zai daina ba daga can kuma saiya hade fuska tamkar an aiko masa da sakon mutuwa ya dubi sarki shardas cikin alamun tsananin damuwa yace ya shugabana yaya batun alkawarinmu idan bukata ta biya? Koda jin wannan tambaya sai sarki shardas ya bushe da dariya yace ai alkawarina dakai dutse ne babu abinda zai kankareshi face rashin biyan bukatata, daga wannan rana Sarki shardas ya fara aiki da shawarar boka barwas ya zamana cewa ya karbi juna biyun shadila hannu biyu ya rinka riritata da kyautata mata fiye da kowa
.
Al'amarin da yayi matukar baiwa shadila mamaki kenan tun tana ganin abin kamar yaudara ce taga ashe zahiri ne kuma gaskiya domin babu abinda fuskarsa da zuciyarsa ke nunawa face tsananin soyayya da kulawa Abu dai kamar wasa a cikin wata uku kacal sai gashi shadila ta fara sakin jiki da sarki shardas duk da cewar ta daukeshi babban makiyin da babu kamarsa a cikin zuciyarta sai gashi ta fara rayawa a cikin zuciyarta cewar ya kamata ta danne wannan gaba a ranta ta dauki komai a matsayin kaddarar da ta wuce nan fa zuciyarta taci gaba da raya mata cewar ya kamata ta manta da duk rayuwarta ta baya ta fuskanci
sabuwar rayuwar da take ciki yanzu domin samun rayuwa ta gari ga abinda take dauke dashi a cikinta kamar sarki shardas ya san abindake cikin ranta.
.
Wata rana shadila na zaune ita kadai a cikin turakarta bisa wata doguwar kujera ta alfarma irin ta sarakai a wannan lokaci tana sanye da wata doguwar riga fara mai shara shara wacce ke nuna tsiraicin jikinta koda ta dubi cikinta taga ya dan fara girma sai ta shiga shafa cikin tana murmushi ba komaine ya sa ta wannan murmushi ba face tunowa da babban masoyinta wato mahaifin abinda zata haifa nan take ta shiga tunanin irin abubuwan da suka faru a baya tsakaninta dashi tun farkon soyayyarsu kawo izuwa sa adda su sarki shardas suka kawo harin sumame ga sansaninsu lokacin da yake gaya mata cewar kada ta kuskura ta fito daga cikin wannan tanti da take ciki.
.
Koda tazo dai dai inda taga sarki shardas ya sareshi da takobi sai ta kwalla uban ihu, ihun ne sarki shardas ya jiyo a lokacin da dama ya nufo turakar tata cikin firgici da razana sarki shardas ya rugo da gudu izuwa cikin turakarta yana shigowa sai yayi turus bisa ganin cewar babu kowa a cikin turakar face shadila ita kadai
a zaune hawaye na zuba daki daki a kan kyawawan kumatunta cikin sanyin jiki sarki shardas yaje ya zauna akan kujerar dake fuskantar wacce shadila ke zaune ya kama hannayanta biyu ya
rike suka kurawa juna idanu sannan ya budi baki a cikin murya mai taushi da sanyi a lokacin da idanunsa suka ciko da kwalla wannan shine karo na farko da shadila taga kwalla a cikin idanun sarki shardas tun da aka kawo ta gidan sarautar Sarki shardas yace ya ke matata na sani cewar a duniya babu wani mutum wanda kika tsana kuma kika daukeshi babban makiyinki sama dani saboda na kashe miki miji a ranar farko na amarcinku sannan na rabaki da duk zuri'arki na kawoki kasata da karfin tsiya inda nayi miki fyade kuma na maishe dake matata ta dole har abada babu abinda zan yi na goge wannan tabo nawa akan idanunki ko kuma na burgeki bare harna sami gafararki ki sani cewa ni masoyinki ne na har abada duk da nasan bakya kaunata dai dai da tsawon dakika daya ba zan taba so naga rayuwarki da ta abinda zaki haifa ta kasance a cikin farin ciki, alfarma daya nake so na nema a wajanki ina son ki boye laifin da na yiwa mahaifin abin dake cikinki a tsakanina dashi har izuwa kamar tsawon shekaru bakwai nan gaba a sannan zaki iya sanar dashi komai idan yana ganin zai iya daukar fansa a kaina sai ya dauka , kin san cewar ni ba zan taba haihuwa ba face na mallaki Hular lamsara kamar yadda na fada miki a baya burina kawai shine na reni dan mijinki hailur a matsayin dan cikina, wannan zai kawai mini da bakin cikin rashin samun da kuma nayi miki alkawarin cewar daga nan har izuwa tawon shekaru bakwan ba zan taba cutar dashi ba amma fa ki sani cewar a ranar da ya cika shekara bakwai zanyi shiri na bar kasar nan don tafiya neman hular lamsara bokana ya tabbatar mini da cewa shima wannan da naki idan ya zama saurayi zai tafi neman hular lamsara to a sannan ne nake son ki sanar dashi gaskiyar asalinsa da mahaifinsa domin daga wannan rana mun zama ABOKAN GABA na sani cewa a wannan lokaci bana gida don boka barwas ya tabbatar mini da cewar sai mun shafe shekara goma sha daya kafin mu gano inda hular Lamsara take, kinga a wannan lokaci ban san kamannin danki ba shima bai san nawa ba don haka ko da zamu hadu a wani wurin daban ba zamu shaida juna ba zamu iya abokai kuma ko kuma abokan gaba idan kuwa na rigashi mallakar hular lamsara tofa duk inda muka hadu saina gane cewa shine dan hailur kuma nan take zan kasheshi. Sai kiyi tunani bisa wannan alfarma dana nema a wajanki kuma ki tuna cewar kin taba neman alfarma a wajena kuma nayi miki tun da kinsa na 'yanta matan zuri arku daga matsayin bayi sun koma kuyanginki idan har kikayi mini wannan alfarma guda daya dana nema a wajanki babu mamaki ungulu ta Koma gidan ta na tsamiya.
A lokacin da Nikuma AlQuyraemey Zankoma Inda nafi Wayau wato Neman na Aure,,,
..
Anan ne Littafin TSATSUBA NA BIYU YAZO KARSHE
marubucin Littafin yace.
.
SHIN SHADILA ZATA IYA YIWA SARKI SHARDAS ALFARMAR DA YA NEMA A WAJANTA?
.
SHIN SU SARAUNIYA LARBISA ZASU SAMI NASARAR SAMUN ABOKAN TAFIYARSU?
.
WANE IRIN MASIFU DA TASHIN HANKALI ZASU FUSKANTA KAFIN SU ISA KOGON KITABUL SIHIR? SHIN SARAUNIYA LARBISA ZATA CIKA BURINTA NA MALLAKAR LITTAFIN TSATSUBA
Chapter 9 · 0% Book details