← Book details Tsatsuba Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 9

Sashe 2

Tsatsuba Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Kashe gari da safe bayan sarauniya larbisa ta yi wanka ta kimtsa sai ta ga shumaira bata kawo musu abincin kalaci ba kawai ta zauna tana jiranta ta gama kimtsawa tana gama kimtsawa kuwa sai shumaira ta mike tsaye ta dubeta tace iyayena suna jiranmu acan turakarsu domin muyi mude baki tare dasu kuma mu sami damar tattaunawa akan abubuwan da muka sa a gaba koda jin haka sai sarauniya larbisa ta mike da sauri cikin murna ta bi shumaira a baya suka fice daga cikin dakin suka nufi hanyar da zata kaisu bangaren da iyayen shumaira suke, sai da sukayi yar tafiya mai dan tsawo kadan sannan suka iso wani babban falo mai dauke da Wani faffadan tebu A karkashin teburin kujerune guda biyar
tsoho Imshal tare da matarsa larisa na zaune akan kujeru biyu ga abinci nan wajen kala uku akan teburin dake gabansu, da isowar shumaira da larbisa sai tsoho imshal da larisa suka mike tsaye suna musu girmama sarauniya larbisa gami dayi mata barka da isowa nan take larbisa da shumaira suka janyo kujeru daga cikin karkashin teburin suka zauna aka fara cin abincin.
.
Tsawon yan dakiku da fara cin abincin dayansu baice uffan ba daga can sai tsoho Imshal yayi gyaran murya yace yake wannan sarauniya mai daraja yanzu saiki gaya mana abin da ya kawoki garemu kafin muma mu
gaya miki bukatar da muke da ita a wajanki.
.
Koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa tayi murmushi sannan tayi gyaran murya tace ba wani abu bane ya sa na baro kasata ba mulkina da jama ata face don na riski kogon Kitabul sihir inda littafin TSATSUBA yake, littafin da shine kadai zai cika mini babban burina na duniya na samun damar yin aure gami da samun magaji kuma na mallaki komai da kowa dake cikin wannan duniya ba zan iya isa inda kogin yake ba face na ratsa ta cikin dazuzzuka guda uku;
.
Daji na farko shine ake kira da Shajarul Shaljuma wanda ke dauke da mugayen dabbobi da mugayen tsuntsaye. Bokaye sun tabbatar mini da cewa babu wani mahaluki wanda zai iya wucewa dani ta cikin wannan daji a raye face wannan ya taku shumaira daga nan ne zamu wuce izuwa dajin Ujurul Majnun bisa jagorancin Jaruma Larifat, daji na uku kuwa wanda ake kira darul maut zamu shigeshine bisa jagorancin jaruma Lubaina muna wuce wadannan dazuzzuka sai kuma mu tunkari dajin da kogon Kitabil sihir yake shi kuwa kogon babu mai iya yi mana jagora izuwa cikinsa face jarumi Ruhaisu dan sarki Zaiyanu na birnin kufa. A cikin kogon kitabul sihir ne zan iya dauko littafin TSATSUBA domin na lalata duk sihirin tsafin dake cikinsa don na sami damar yin aure na sami da ko yar da zata gajeni idan ban lalata sihirin dake cikin wannan littafi ba na tsatsuba har abada burina ba zai cikaba.
.
Koda sarauniya larbisa tazo nan a zancenta sai tsoho Imshal ya tuntsire da dariya Al amarin da ya baiwa larbisa dasu shumaira mamaki kenan daga can kuma sai Tsoho Imshal ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da sakon mutuwa a lokacin da idanunsa suka ciko da kwalla har hawaye ya zubo masa..
.
Nan fa sarauniya Larbisa ta kara cika da tsananin mamaki ta dubi tsoho Imshal tace yakai Abul Shumaira ina dalilin yin dariyarka gami da zubar hawayenka a bisa
abinda kaji na fada??...
.
Ni nima zan dakata ana sai Allah Ya kaimu gobe inda za mu ji abin da tsoho Imshal sai fada a huta lafiya.

TSATSUBA
BOOK 2
Part (B)
Na Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi
Chapter 2 · 0% Book details