← Book details Tsatsuba Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 9

Sashe 8

Tsatsuba Part 2 Complete Hausa Novel · about 10 min read

TSATSUBA
BOOK 2
PART (E)
Na Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi
.
.
Sai gashi nan da nan ya haɗa mashi jini da majina yana bal dashi kamar tamola, ashe duk wannan abu dake faruwa shadila ta leko ta cikin tantin da take tana ganin abin dake faruwa cikin tsananin fargaba da tashin hankali kwatsam sai sarki shardas ya sami nasarar saran kafadar hailur ta hagu hailur ya kurma ihu a lokacin da jini yayi tsartuwa a kafadar tasa amma sai yayi sauri ya rike takobin ta Sarki shardas a lokacin da shi sarki shardas ke son ya danna takobin ta nutse a cikin kafadar koda shadila ta hango abinda ya faru ga mijinta saita kurma ihu bata san sa adda ta fito da gudu daga cikin tantin da take boye ta rugo izuwa inda suke jiyo ihunta da gudun tane yasa sarki shardas ya waigo yayi arba da ita koda yaga irin tsananin kyawunta sai ya dimauce ya juya da sauri ya doke kirjin hailur da karfin gaske saboda karfin dukan saida hailur yayi tsalle sama da baya kamar an janyeshi da majajjawa ashe bayan nasa wani rami ne mai tsananin zurfin tsiya wanda karshensa kwazazzabo ne da magudanar ruwan wata korama koda hailur yaji ya fada cikin wannan rami sai ya kwarara uban ihu irin na wanda ya saddakar mutuwa zaiyi ita kuwa shadila tana ganin abinda ya faru ga mijinta sai ta sulale kasa sumammiya.
.
Sarki shardas ya bushe da dariyar farin ciki ya ruga da baya izuwa inda shadila ke kwance ya dauketa ya azata akan dokinsa nan take dakarunsa suka kwashe gaba dayan dukiyar wannan ayari nasu hailur suka ingiza keyar bayin da suka kama akayi gaba ana tunkarar birnin Romaniya.
.
Ana fara tafiya sai sarki shardas ya sake rufe fuskarsa da bakin rawani kuma ya shakawa shadila banju barcinta ya sake nauyi don haka bata farka ba har aka isa birnin romaniya da tsakiyar dare lokacin da shadila ta farka daga barci sai ta tsinci kan wani luntsumemen gado na alfarma a cikin wani kasaitaccen daki na sarauta cikin razana ta mike tsaye da sauri ta sauko daga kan gadon, ta kama kallon kowacce kusurwa koda tagama ganin kayan kawar dake cikin dakin sai tunanin mijinta da sauran jama arsu ya fado mata ta tuno da duk abinda ya faru a sansaninsu sa adda aka kawo musu sumame na mamayar bazato nan take shadila ta dafe kunnuwanta da hannayanta biyu ta kurma uban ihu tana mai fashewa da matsanancin kuka faruwar hakan keda wuya sai taji an bude kofar turakar ba wani bane ya shigo cikin turakar face sarki shardas a cikin wata irin kyakkyawar shiga ta sarakai fuskarsa cike da annnuri ya durfafeta.
.
Koda tayi arba dashi sai ta razana ainun taja da baya tana mai nunashi da yatsa a lokacin da hawaye ya zubo mata tace ka cuceni ka kashe mini miji kuma ka kashe dukkan mazajen ayarinmu ina sauran yan uwana mata?
.
Me kake nufi dani ka kawoni nan ni kadai kawai ka kasheni na huta da kunci da bakincikin rayuwa tunda ka rabani da masoyina da dukkan zuri ata koda jin wannan batu sai sarki shardas ya bushe da dariya lokaci guda kuma ya turbune fuska ya dubeta yace yake wannan ma abociyar kyawu da cikar zati kiyi sani cewa kece mafi sa a bisa dacewa da zama matar sarkin birnin Romaniya a yanzu duk wata rayuwa da kikayi a baya ki manta da ita ki manta da komai da kowa ki fuskanci sabuwar rayuwar da tazo miki wacce zaki tsinci kanki a cikin daular da baki taba ji da gani ba koda jin wannan batu sai zuciyar shadila ta kama tafarfasa kamar zata kone saboda tsananin fishi taji ta tsani sarki shardas fiye da komai a doron kasa koda idanunta suka kai kan wata wukar dake kan wani faranti babba mai dauke da tuffa masu yawa sai tayi zumbur ta suri wukar ta ritsa sarki shardas da ita tace kada ka kusanceni idan ka matso kusa dani zan kasheka.
.
Sarki shardas ya bushe da mahaukaciyar dariya ya durfafeta kai tsaye ai kuwa yana kusantarta sai ta caka maza wukar a kirji take wukar ta balle gida biyu taji kamar akan dutse ta bugata kawai sai sarki shardas ya hankadata ta fada kan gadon dake bayanta sannan ya bita izuwa kan gadon bai rabu da ita ba har sai da bukatarsa ta biya tana ta faman rusa ihu da kukan bakin ciki daga wannan rana shadila ta zama matar sarki shardas da karfin tsiya ya zamana cewa kullum a cikin daula take babu abinda takeyi da hannunta sai dai kuyangi da barori suyi mata duk da cewar ta tsinci kanta a cikin daula irin wacce bata taba ji da gani ba sai ya zamana cewa kullum a cikin kuka da bakinciki take musamman
idan ta tuno da tsohon masoyinta kuma sabon angonta hailur da kuma sauran danginta da zuri arta lokacin da shadila ta matsawa sarki shardas akan sai taga inda aka kai sauran +yan uwanta mata wadanda aka kama a matsayin bayi sai yayi mata jagora izuwa wani bangare daban na gidan sarautar wannan ranace ta farko wacce shadila ta sami damar fita daga bangaren da turakarta take koda taga yadda girman gidan sarautar yake da yawan dakarun dake tsaro a ko ina sai hankalinta ya dugunzuma ainun domin take burinta na son guduwa ya yanke, haka dai sarki
shardas yaci gaba da yiwa shadila jagora suna ta ratsawa ta cikin lunguna da sakuna har sai da sukayi tafiya mai nisa duk inda suka ratsa sai dai kaga bayi barorim hadimai da dakaru suna risinawa suna gaishesu har suka iso wani katon gida wanda ke cike da bayi mata.
.
Koda shadila tayi arba da yan uwanta mata yan zuri arsu suna ta yin ayyuka na bauta iri iri sai ta ruga garesu tana mai kiran sunayansu daya bayan daya tana zubar da hawaye take suma bayin suka rugo gareta suka rungumeta suna kuka.bayan ta dan jima a kankame dasu sai ta janye jikinta daga cikin nasu ta juyo ta dubi sarki shardas tace ina neman alfarmar ka yanta wadannan yan uwa nawa daga matsayin bayi masu aikin bauta zuwa ga kuyangina.
.
Koda jin wannan batu sai sarki shardas yayi shiru yana mai sunkui da kai ya dubi shadila cikin murmushi yace yake matata kiyi sani cewa babu wani abu da zaki nema a wajena ki rasa saboda tsananin irin son da nake yi miki don haka zanyi miki wannan alfarma bisa sharadi guda shardin kuwa shine wadannan bayi idan suka koma can wajanki ba zasu taba fita ba daga cikin harabar gidanki duk wacce aka kama da laifin hakan hukuncin kisane a kanta.
.
Koda jin haka sai farinciki ya lullube bayin suka fara rungume shadila sunayi mata godiya ita kuwa shadila sai ta dubi Sarki shardas tace na amince da wannan sharadi naka nan take sarki shardas ya sa dakarun dake kula da wadannan bayi suka kwankwance musu sarkokin dake wuyansu da hannayensu sannan aka tafi dasu izuwa can bangaren gidan shadila a nan ne aka basu suturu masu kyau sukaje sukayi wanka suka sanya suturu
.
Tun da aka kawo shadila wannan gidan sarauta na birnin romaniya bata taba yin farin ciki ba sai a wannan rana da aka 'yanta wadannan bayi kuma bata taba yiwa Sarki Shardas murmushi ba sai a yau din nan.
.
Hakika shadila ta tsani sarki shardas fiye da komai a duniya kuma inda tana da ikon kasheshi ko guduwa daga gidan sarautar da tuni ta aikata haka dai dai da rana daya shadila bata taba mancewa da mijinta ba Hailur kusan kullum sai tayi mafarkinshi
sau tari a mafarkin nata ana nuna mata cewar hailur yana nan a raye bai mutu ba amma idan ta tuno da tsananin zurfin ramin da ya fada sai taga cewar mafarkin nata ba zai taba zama gaskiya ba babban abinda take yin nadamar aikatashi shine karya sharadin da tayi a lokacin da hailur ya gaya mata cewa komai tsanani kada ta kuskura ta fito daga cikin wannan tanti da take amma sai ta mance da sharadin ta fito da gudu bisa dimaucewar da tayi a lokacin da taga sarki shardas ya sareshi da takobi a kafada ta kwalla ihu ta fito da gudu ta baiyana kanta.
.
Tabbas inda bata fito ba da sai hailur ya kubuta daga sharrinsa kuma da sai sun gudu tare lokacin da shadila ta sami wata uku a cikin gidan sarautar sarki shardas sai alamun juna biyu suka baiyana a gareta ya zamana cewa tana fama da tashin zuciya, kumallo da zazzafi da ciwon kai ko da sarki shardas yaga shadila bata da lafiya sai hankalinsa ya dugunzuma nan take ya tura aka
kirawo wata likita tazo ta dubata cikin murmushi likitar ta dubi sarki shardas tayi masa bushara cewar matarsa ta sami juna biyu
Koda jin haka sai sarki shardas ya kamu da tsananin farin ciki amma da ya tuno da wani al amari sai hankalinsa ya dugunzuma ainun kuma ransa ya baci take zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone jikinsa ya kama kyarma bai san sa adda yasa hannu ya zabgawa shadila mari ba, saboda karfin marin saida ta fadi kasa bakinta ya fashe jini yazubo sarki shardas ya sunkuya ya kamo kafadunta yana mai daka mata tsawa yace wanene yayi miki ciki ban sani ba a cikin gidan sarautata kiyi sani cewa yau shekara ashirin kenan ina neman haihuwa ban samu ba kuma matana na aure guda goma sha shida ne a cikin gidannan bokana ya tabbatar mini da cewar ba zan taba haihuwa.ba har sai na mallaki wata hular sihiri wacce ake kira LAMSARA.
.
Lallai wannan ciki da kike dauke dashi ba nawa bane maza ki hanzarta sanar dani maishi kona shakeki ki mutu yanzu.
.
Koda sarki shardas yazo nan a zancensa sai shadila ta bushe da dariya al amarin da yayi matukar baiwa sarki shardas mamaki kenan kuma jikinsa yayi sanyi ya mike tsaye yana mai kura mata idanu, shadila ta yunkura ta mike tsaye ta dubi sarki shardas a fusace tace shin kana tunanin ina tsoron mutuwa ne? To ka sani cewa duk wannan daula da nake ciki a wannan gidan sarauta daidai yake da kurkuku a wajena, gaba daya rayuwar duniya ta fita daga raina tun daga ranar da ka wargaza rayuwata ka rabani da babban masoyina hailur kuma ka tarwatsa ayarinmu, ka sani cewa wannan hari da kuka kai mana an kashe uwata da ubana da dukkan dangina a yanzu bani da sauran masoyi a doron kasa face masoyina hailur wanda har yanzu xuciyata ke wasu wasin cewar yana nan a raye bai mutu ba idan har yana raye ina tabbatar maka da cewa sai yazo har nan gidan sarautar ya daukeni mun tafi domin wannan juna biyu da nake dauke dashi nasa Ne bana wani ba, kafin shadila ta gama rufe bakinta ya sake zabga mata mari ta baje a kasa sumammiya nan take kuyangi suka rugo izuwa kanta suka shiga ceto rayuwarta.
.
Koda ganin haka sai sarki shardas ya rude yayi nadamar abinda ya aikata saboda tsananin son da yake yiwa shadila don haka bai san sa adda ya kwarara uban ihu ba har kwallar takaici ta zo masa.
.
A fusace ya baro turakar shadila ya aika aje a kirawo masa babban bokan birnin wanda ake kira da Barwas ibn Mus ab Lokacin da ya isa wajan boka barwas sai ya labarta masa duk abinda yake faruwa nan take bokan yake shaida masa abubuwan
matakin da ya kamata ya dauka yake cewa akan wannan juna biyu data samu ya kasance mai nuna mata kauna kulawa da soyayya irin wacce ma baka taba nuna mata ba ka zamo mai tarairayarta kada ka bari koda kuda ya taba lafiyarta kuyi renon cikin tare kai da ita har izuwa sa adda zata haihu lafiya kuma har izuwa sa adda yaron zai cika shekara bakwai a wannan lokaci kun shaku ainun da yaron kawai saika tsiri tafiya wannan tafiya kuwa nine zanyi maka jagora a cikinta kuma ba zamu dawo ba har sai mun sami nasarar mallakar hular lamsara ina mai tabbatar maka da cewar da zarar mun mallaki hular lamsara tamkar mun dora duniyar nan ne dukanta a tafin hannunka komai da kowa sai ya dawo karkashin ikonka kuma babu wani makiyinka da zai iya samun nasara a kanka
.
Anan zan dakata haka amma kafinnan nake cewa mu kwana lafiya.
Chapter 8 · 0% Book details