← Book details Tsatsuba Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 9

Sashe 4

Tsatsuba Part 2 Complete Hausa Novel · about 10 min read

TSATSUBA
BOOK 2C
Na Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi
.
Yayin da sarauniya larbisa taji wannan batu sai tayi murmushi tace koma menene a ransu ai zamu gani tunda dai sannu sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba aje ba, Tsoho Huzallatul marwas ya gyada kai yace tabbas zancenki Dutse ne Larbisa tace wai shin yanzu ina Muka dosa ne?
.
Huzallatul marwas yayi murmushi yace in banda abinki ya zaki tambayi kaza hanyar rafi, ni kaina ina bin jagorancin jaka ne, duk inda naga ta nuna nan nake bi damu. Amma ai idan baki manta ba zamuje neman jaruma larifat ne wacce zata yi mana jagora a cikin daji na biyu wanda shine dajin Ujurul majnun ki kwantar da hankalinki don nasan cewar ba zamu dauki wani dogon lokaci ba muna tafiyar zamu riske ta bisa taimakon wannan jakar sihiri nawa.
.
Koda jin haka sai Larbisa tayi shiru bata kara cewa komai ba haka dai aka ci gaba da wannan tafiya ba dare ba rana babu abinda yake sawa a tsaya ko a yada zango face gajiya ko yunwa da kishirwa, har tsawon kwana uku sannan suka iso wani babban birni mai kyau gaske wanda aka kawatashi da gine gine masu kyau da kawa ita kanta sarauniya larbisa sai da wannan birni ya birgeta ta raina kyawun nata birnin harma tana cewa a cikin ranta lallai duniya da fadi hakama abin cikinta a iya tunanin sarauniya larbisa ba za a taba samun birnin da
yafi nata girma da kawatuwa ba a duniya da yafi nata girma da kawatuwa ba a duniya amma sai gashi tun kafin ma tafiya tayi nisa ta fara ganin cewar ba haka
bane.
.
Tun daga nesa da masu gadin kofar birnin suka hango tawagar sarauniya larbisa sukaga alamar cewar manyan mutane ne masu daraja sai suka bude musu kofada sauri har daya daga cikinsu yayi musu jagora izuwa fadar birnin tun akan hanya kafin a isa fadar sai jaruma shumaira ta matso kusa da larbisa ta dubeta tace to wai shin mu yanzu menene yashigo damu cikin wannan gari alhalin mun zo ne neman jaruma larift kuma ga yadda aka bayar da labarinta ba zata yi rayuwa ba a cikin gari sai dai a daji?
.
Koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa tayi murmushi tace ai da dan gari akanci gari, yanzu idan muka ce zamu tafi neman jaruma larifat bamu san a cikin dajin da take ba amma da zarar mun shiga cikin birnin zamu sami labarin inda take wata kilama mu sami karin haske akan yadda zamu tunkareta ba tare da mun fuskanci wata matsala ba. koda shumaira taji wannan batu sai tayi ajiyar zuciya tayi shiru bata kara cewa komai ba...
.
Fada ce kasaitacciya abar kwatance domin lokacin da aka shigo dasu sarauniya Larbisa cikin fadar sai gaba dayansu suka kama kalle kalle suka zama kamar yan kauye saboda ganin irin kyan fadar da kawatuwarta.
.
A wannan lokaci ne larbisa ta dada tabbatar da cewar gaba da gabanta Aljani ya taka wuta Ita dai a iya saninta a can nahiyoyin dake bangarenta babu wata kasa mai girma da karfin Arziki kamar kasarta don haka sai ta fara tunanin cewa a duniyar ma gaba daya ba a taba samun kamarta ba amma a yanzu da ta tsinci kanta a cikin wannan birni da wannan bakuwar fada sai ta karyata kanta, wani kyakkyawan saurayi ne na kwatance bisa karagar mulkin wannan fada ya yi babbar shiga ta alfarma irin wacce attajiran sarakai da suka gawurta ne kadai ke iya yinta domin tufafin dake jikinsa darajarsu takai jarin wani mashahurin attajirin, hatta takalminsa da kwagirin dake hannunsa na lu'u lu'u ne a yatsun hannayensa na hagu da dama akwai zobuna guda shida kuma duk na zinare ne masu tsadar gaske, shi kansa rawanin dake kansa da falmaran din dake jikinsa da zaren zinare a aka dinkasu.
.
Koda jaruma shumaira da sarauniya larbisa sukayi Arba da wannan sarki sai kyawunsa da kwarjininsa ya dimautasu sukaji nan take sun kamu da tsananin sonsa. Hakika babu wata 'ya mace da zata ga wannan sarki bataji ta kamu da tsananin sonsa ba, saboda baiwar da allah yayi masa ta kyau da arziki, gashi idan yayi ado sai kaga tamkar dawisu ne koda shigowar su sarauniya larbisa cikin fadar sai sarkin ya dubesu sau daya ya kau da fuska kuma babu annuri akan fuskar tasa, Al amarin da ya dugunzuma hankalinsu kenan domin a tunaninsu kyawunsu kadai zai iya sawa sarkin yayi marhaban dasu bare kuma ga matsayi na sarautar larbisa, cikin sanyin jiki suka karasa kusa da karagar mulkin sukayi cirki cirko caraf sai tsoho isham ya zube kasa gaban sarki ya kwashi gaisuwa sannan ya gabatar da sarauniya larbisa da jaruma shumaira ya kara da cewa yakai wannan sarki mai daraja kayi sani cewa ba wani abu bane ya kawomu birninka ba face neman jaruma Larifat ma abociyar basira da hangen nesa saboda muna son tayi mana rakiya izuwa dajin ujurul majnun domin biyan
wata muhimmiyar bukata ta sarauniya Larbisa.
.
Koda jin wannan batu sai sarkin ya mike tsaye zumbur daga kan karagarsa ta mulki. Fuskarsa cike da annuri ya kama kafadun tsoho Isham ya tashe shi tsaye
ya jashi har kan karagarsa suka Zauna tare, su sarauniya larbisa ma sai yasa aka basu kujeru na alfarma suka zauna sannan aka kawo musu abinci da abin sha na alfarma suka kama kimtsa cikinsu suna masu murna da mamakin yadda akayi nan da nan ra'ayin sarkin ya sauya bisa jin abindake tafe dasu sai da kowa ya gama kimtsawa ya sami natsuwa sosai, sannan kyakkyawan sarkin ya dubi tsoho isham yace yakai wannan dattijo kayi sani cewa yau shekara bakwai kenan ina fama da tsananin so da begen wannan jaruma larifat amma ko sau daya bata taba kallona ba tayi mini murmushi bare ta karbi tayin soyayyata sai dana kwanta rashin lafiya sau bakwai sakamakon ciwon sonta da ya kayar dani amma bata taba zuwa ta dubani ba ni da ita bata taba yi mini magana ba kuma bata taba amsa gaiyatata ba izuwa wannan gidan sarauta ba.
.
Lokacin da na dameta da aika manzanni da kyaututtuka iri iri na duniya sai ta tattaro duk abinda nake bata na tsawon shekaru bakwan ta dawo mini dasu gami da wasika.
.
A cikin wasikar ne ta shaida mini cewa na daina bata lokaci na da tunanina a kanta domin ta daukarwa kanta alkawari cewar ba zata taba yin aure ba ko soyayya har sai tayi gagarumin abin gwanintar da wani bai taba yi ba a duniya lokacin da naji wannan batu sai na kamu da tsananin bakin ciki kuma na fashe da kuka na takaici domin banga ranar da larifat zata cika wannan buri ba daga wannan rana ne nima na yi alkawarin na daina cin abinci mai dadi na daina kwanciya a wuri mai kyau kuma na daina murmushi da sukuni har izuwa karshen rayuwata face a ranar da naji cewar ta sami damar da zata cika burinta.
.
A tsawon shekaru bakwai da suka gabata wannan dama bata samu ba sai yanzu naji kunzo mini da wannan batun na zuwa kogon Kitabul sihir inda littafin tsatsuba yake sai naji a jikina cewar lokacin samun yardar larifat yayi a gareni
domin a yanzu ne zata iya yin jarumtakar da har abada ba za a mance da ita ba a duniya, ko shakka babu na san cewa larifat zata karbi wannan tayi naku domin bata tsoro ko shakkar wani abu mai rai akan biyan bukatarta, babu wani abu wanda zaku iya biyanta da shi domin ta wuce daku ta cikin dajin ujurul majnun face kwadayin cika na ta burin ba wani abu da yake burge jaruma larifat a cikin wannan duniya, saboda ta rasa iyayanta yan uwanta da dukkan danginta bisa wannan daliline ta kebe kanta daga cikin mutane ta koma cikin daji da zama inda ta zabi ta karasa sauran rayuwarta gaba daya yanzu dai a gajiye kuke, don haka zan sa a kaiku masauki ku huta washe gari da safe ni da kaina zanyi muku jagora izuwa dajin Da jaruma larifat take domin ku gana da ita, ku sanar da ita bukatar dakuka zo da ita a gareta. Amma ina neman wata alfarma guda daya a wajanku? Alfarmar kuwa itace ina son nima nayi muku rakiya a cikin wannan tafiya domin idan kuka tafi kuka barni fargaba tunani da begen halin da larifat ke ciki zai iya jefani cikin wani mugun hali.
.
Koda sarki AYUBUL HASNU yazo nan a zancensa sai kowa ya cika da mamaki musamman sarauniya larbisa da shumaira. Sarauniya larbisa ta dubi sarki Ayubul hasnu cikin mamaki tace yakai wannan sarki mai daraja kayi duba izuwa wannan daula da kake ciki ka dubi girman kasarka da tarin arzikin dake cikinta ka sani cewa akwai mata da yawa masu kyau a sassan duniya wadanda zaka iya mallakarsu da karfin dukiyarka da mulkinka saboda me yanzu zaka siyar da rayuwarka don baiwarka?
.
Lokacin da sarki ayubul hasnu yaji wannan tambaya daga bakin sarauniya larbisa sai ya bushe da dariya kamar ba zai daina ba daga bisani kuma sai ya hade fuska tamkar an aiko masa da sakon mutuwa nan fa fadar tayi tsit kamar babu mai rai a cikinta kawai sai aka ga idanun sarki ayubul hasnu sun ciko da kwallah har hawaye ya zubo masa, sarki ayubul hasnu ya dubi sarauniya larbisa cikin nutsuwa yace yake sarauniya larbisa kiyi sani cewa a duniya babu wani abu wanda yafi soyayya karfi da hadari masoya da yawa sun rasa rayuwarsu akan tafarkin mallakar masoyansu ba komai ne ya janyo hakan ba face duk rayuwar da babu masoyi dai dai take da zama a cikin kurkukun daurin rai da rai kisan sani cewa ke da jaruma shumaira duk kun kasance kyawawan matan da babu kamarsu a duk cikin fadin kasata da nahiyarmu amma kuma baku kama farcen kafar jaruma larifat ba a fagen kyau kunga kenan a yanzu babu wata ya mace da zata iya maye gurbin larifat a wajena banda fagen kyau a bangaren jarumta kuwa ina mai tabbatar muku da cewa in daku biyun nan zaku hada karfinku ku yaketa ba zaku taba samun galaba a kanta ba koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa da jaruma shumaira suka bushe da dariya domin su a ganinsu ma tatsuniya ce abinda sarki Ayubul hasnu yake fadi shumaira ta dubeshi tace aiko yarima RUHAISU dan sarki ZAIYANU na birnin kufa wanda masana da masu bincike suka tabbatar da cewar babu mai karfin damtsensa da sa arsa idan muka hada karfi nida larbisa sai mun gama dashi bare wata jaruma larifat wacce ta kasance 'ya mace kamarmu yayinda sarki Ayubul hasnu yaji wannan batu sai yayi murmushi yace ai shi kenan inda babu kasa nan ake gardama Kokowa, ni dai shawarata guda daya ce a gareku duk abinda zakuyi kyi shi da cikakkiyar hujja domin banson ku yi irin kuskuren da SADAUKI HULKAS MAI HULAR LAMSARA YAYI. Koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa da jaruma shumaira suka dubi junansu cikin mamaki larbisa ta juyo ta dubi sarki Ayubul hasnu tace wanene kuma sadauki Hulkas mai hular lamsara?
.
Koda jin wannan tambaya sai sarki Ayubu hasnu yayi ajiyar zuciya gami da sauke dogon numfashi sannan yace labari ne mai tsawon gaske sai dai nayi iya kokarina na gani ko zan iya gajarce muku shi...
.
SADAUKI HULKAS YANA DAGA CIKIN MANYAN JARUMAN DUNIYA GUDA UKU wadanda akayi musu lakabi da MAZAN JIYA jarumai ne wadanda ba a taba yin kamarsu ba kuma ba za ayi ba a yanzu da nan gaba domin sun bar abin tarihin da ba za a taba mancewa dasu ba sai dai kash! Duk su ukun rayuwarsu ta salwanta ne a tafarkin soyayya. Yanzu dai saiku saurara da kyau kuji wannan labari domin akwai dumbin darasi a cikinsa, nan take sarki AYUBUL HASNU ya shiga basu labari kamar haka......
.
Hm yanzu ne zamu shiga cikin labarin gadan gadan a yayinda zakuji Labarin sadaukin sadaukai Hulkas mai hular lamsara kuma daya daga cikin jaruman duniya Mazan jiya saboda haka sai ku gyara zamanku Amma fa sai gobe idan Allah mai kowa da komai ya kaimu.
Chapter 4 · 0% Book details