← Book details Tsatsuba Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 9

Sashe 6

Tsatsuba Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

. Nan take sarki Ayubul Hasnu ya shiga basu labari kamar haka ”kimanin shekaru Ashirin da hudu da suka shude a birnin Romaniya anyi wani azzalumin sarki mai suna SHARDAS IBN KAUMIL sarki shardas ya kasance gawurtaccen jarumin sadauki mai tarwatsa maza a filin daga yana da tsananin karfin damtse na Allah ya isa don ance ko giwa ya yiwa naushi daya saita fadi kasa kisan kai kwace da cin zali kuwa bai maidasu komai ba. . A cikin wata daya yakan shirya dakarun sumame su kai mamayar bazato izuwa ga ayarin fatake ko izuwa ga manyan garuruwan da suke da karfin arziki cikin bad da kama su kwato bayi da dukiya da mata ba tare da an shaida ko su waye ba, a bisa wannan halaiya ne ya addabi gaba dayan kasashen dake nahiyar gaba daya kuma gashi an kasa gano mutanen dake yin wannan barna, babu irin matakin da sarakuna basu dauka ba kuma babu irin binciken da bokaye basuyi ba don gano rundunar dakarun dake wannan mummunar barna amma abu ya gagara babban abin bakin cikin ma shine sarki shardas ya tara dukiya mai tsananin yawan da jikokinsa ma da tattabakunnansa ma ba zasu iya cinyeta ba amma duk da haka bai daina yin wannan fashi da kwace ba. . Masana da masu bincike na wannan zamani sun tabbatar da cewar duk duniya babu wani sarki da ya kai sarki shardas tarin dukiya kuma babu wani gidan sarautar da yakai nashi girma da kawatuwa, duk bayin da ya kamo da mata ana boye sune a gidajen gonarsa da wani bangaren daban na gidan sarautar inda har abada ba za a sake ganinsu ba bare ma wani ya shaida dayansu asirinsa ya tonu a gane cewa shine dan fashin da ya addabi Mutane a nahiyar. . Tunda yake kamo Bayi da mata ba ataba samun wanda ya taba guduwa ba daga cikinsu ya tsira da rayuwarsa face sarki shardas yasa anbi bayansa an kasheshi saboda tsananin tsoron da ake yiwa dakarun sarki shardas ne yasa aka musu lakabi da suna DAKARUN AJALI. . Wata rana sarki shardas tare dakarunsa kimanin mutum dubu uku sun fito mamayar bazato izuwa wani babban kauye da ke gefen wata makociyar kasa da ake kira salmas sai suka kai hari izuwa ga ayarin wadansu matafiya masu yawan gaske wadanda suka yada zango a gefen kauyennwanda ake kira Malgur. . Su dai wadannan matafiya suna da tarin shanu tumaki da raguna masu yawan gaske kuma Allah ya albarkacesu da kyawawan mata ababan kwatance ga kuma tarin zuri'a. . Al amarin ya faru ne da yammaci sakaliya daf da faduwar rana shugaban wannan ayari saurayi ne ma aboci kyau kwarjini da jarumtaka ana kiransa da suna Hailur, a wannan rana ne hailur yayi aurensa na farko a duniya kuma matar da ya aura budurwace yar shekara goma sha takwas a duniya wacce babu mai kyawunta a duk cikin zuri ar ayarin gaba daya. . A wannan lokaci wannan ayari sun shagala a cikin bikin auren hailu ana ta kade kade da raye raye saboda murna kowa da kowa ya zage yana ta rawa maza da mata yara da manya gaba daya dakarun ayarin dake tabbatar da tsaro sun ajiye makamansu sun shiga cikin taron 'yan rawa suna cashewa kwatsam ba zato ba tsammani sai gani akayi dakarun Ajali sun bullo daga kowace kusurwa gabas da yamma kudu da arewa bisa dawakai aguje kuma sun zare makamai suna ihu da kururuwa nan fa taron biki ya watse mata, yara da tsofaffi suka kama ihu da guje.guje suna neman maboya, a dai dai wannan lokaci ango Hailur na tare da amaryarsa shadila a cikin tantinsa suna more amarcinsu kwatsam sai suka jiyo iface iface da guje gujen jama arsu a rude ango Hailur da amarya shadila suka mike tsaye zumbur daga kan shimfidarsu suka suri suturarsu suka sanya hailur yayi waje ya dauko takobinsa da garkuwarsa ya dubi shadila yace komai wuya komai rintsi kada ki fito daga cikin wannan tanti indai kika kiyaye wannan umarni nawa ni dake duk zamu tsira daga sharrin wadannan yan harin bazati kada ki kuskura kiyi ihu ko maganar da wani zai jiyoki shadila ta kada kai cikin alamun tsananin damuwa tace lallai zan kiyaye wannan umarni naka nan take hailur ya sumbaci goshin shadila sannan ya juya zai fice daga cikin tantin sai tayi wuf ta ruko hannunsa ta rungume shi tana mai fashewa da kuka ba komai ne ya sa tayi hakan ba face taji a jikinta cewar abune mawuyaci su sake ganin juna, ba komai ne ya tabbatar mata da hakan ba face ta dan leka wajan tantin daga tsananin yawan dakarun sumamen da suka kawo musu hari tasan cewa tabbas an shammaci nasu dakarun ba zasu iya kare kansu ba. . Cikin hanzari hailur ya janye jikinsa daga cikin nata ya sake dubanta cikin yanayi mai nuna yarda dakai yace ki barni kamar yadda kika saba ni nasan dabarar da zanyi na kubutar da rayuwarki da tawa, shin kin manta ne da cewar irin wannan ta taba faruwa shekaru uku baya sa adda wata rundunar yan fashi suka ritsamu a daji mu biyu rak nidake muna kiwo? . Ko dajin wannan batu sai Shadila ta gyada kai cikin murmushin karfin hali tace haba ya masoyina ai ba zan taba mancewa da wannan gagarumar jarumtaka da kayi ba, koda jin haka sai fuskar hailur ta fadada da murmushi yace to wannan karon ma abinda zai faru kenan baya ga wannan ina mai yi miki wani babban albishir cikin matukar mamaki da zakuwa shadila ta zaro idanu tace wane irin albishir kuma zakayi mini yanzu? . Hailur yace boka zaifur ya gaya mini cewa a ranar farko dana sadu dake juna biyu zai shiga don haka yanzu ina mai tabbatar miki da cewa kina dauke da cikin dana kona mutu a wannan yaki bani da nadama ko takaici na san cewa na bar wanda zai kula dake. . Yayinda shadila taji wannan batu sai hawaye ya zubo mata tace lallai ina son ta kowanne hali ka rayu a wannan yaki kuma mu tsira tare domin babu abinda na tsana a wannan duniya sama da dana ya taso maraya. hailur yayi murmushi yace nayi miki alkawari cewar danki ba zai taso a maraicin rashin uba ba yana gama fadin hakan sai ya juya da sauri ya fice da gudu daga cikin tantin. Ai kuwa yana fitowa yaga yadda ake ragargazar jama arsu ana saransu da sukarsu suna ihu jini na tsartuwa fallatsi da malala suna zama gawa sai ya fusata ainun ya kwarara uban ihu ya zare takobinsa daga cikin kufenta ya afkawa dakarun sumamen ya hausu da sara da suka ya zame musu guguwar annoba a wannan lokaci hankalin sarki shardas yana kan bayi mata da ake ta kamawa da kuma dukiyar da ake diba amma ko da yaji ihun dakarunsa ya yawaita a wani bangare daban sai ya juyo da sauri izuwa wajan take ya hango jarumi Hailur yanata ragargazar dakarunsa duk inda hailur yasa gabansa sai dai kaga maza na Zubewa kasa tamkar ana sassabe a gona Al amarin da yayi matukar baiwa sarki shardas mamaki kenan dimin tunda yake fita sumame da yaki bai taba ganin jarumi mai irin zafin naman hailur ba gami da tsagwaron jarumtakarsa duk da cewar a wannan lokaci dakarun sarki shardas sun kashe kaso takwas daga cikin kaso goma na jama ar jarumi hailur sai da ran sarki shardas ya baci ainun zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone cikin tsananin fishi sarki shardas ya takarkare ya kwarara wani uban ihu wanda ya firgita komai da kowa dake cikin dajin aka daina yakin aka tsaya cak tamkar babu abu mai rai a wajen a lokacin da amon ihun sarki shardas ke tayin amsa kuwa a dajin gaba daya shi kansa jarumi hilairu sai da ya firgita bisa jin wannan kururuwa ya kura idanu izuwa sashin da kuwar ta fito da yake a sannan ne kurar yakin take lafawa sai da yan dakiku suka shude sannan ya hango sarki shardas ya tunkaroshi daga can nesa kadan take zuciyar jarumi hailur ta buga da karfi ya ji tsoro ya darsu a cikin ransa a karon farko a duk gwagwarmayar da yakeyi da mazaje a rayuwarsa bakomai ne ya haddasa hakan ba face a iya rayuwar jarumi hailur bai taba ganin mutum mai kirar sadaukai da kwarjininsa ba kamar sarki Shardas duk da cewar fuskar sarki shardas a rufe take cikin rawani sai da jarumi hailur ya gane cewa lallai wannan sadaukiba saurayi bane shekarunsa sun kai arba in da 'ya'ya kuma idanunsa ya kalla kawai ya gane hakan abinka da jarumi mai dakakkiyar zuciya kuma wanda baya fidda rai ga samun sa a da rabo sai hailur ya gyara tsayuwarsa ya rike takobinsa da garkuwarsa da kyau koda ganin haka sai sarki shardas yayi murmushin mugunta kawai sai shima ya zare takobinsa daga cikin kufenta wata irin takobi ce mai tsawo da kaifi kuma anyita ne da wani irin karfe na musamman wanda sai kwararren makeri ne zai iya gano hakan take sarki shardas ya falfalo da gudun tsiya izuwa kan jarumi hailu duk sa adda sawun kafafun sa suka taba kasa sai kaji kamar takun giwa ne saboda nauyinsu. . Koda jarumi Hailur ya hango sarki shardas ya rugo izuwa kansa cikin mugun nufi haka sai shima ya ruga izuwa gareshi duk su biyun suna ihu da karaji yayin da ya rage saura baifi taku biyar ba su hadu sai kowannansu ya daka tsalle sama yakai wawan hari sarki shardas ya kaiwa hailur sara a wuya da nufin ya cire masa kai hailur ya kare saran da garkuwarsa take garkuwar ta rabe gida biyu tamkar an yanka tsakiyar tufa da wuka cikin zafin nama hailur ya kaiwa shardas suka da takobinsa a ciki shardas yasa garkuwarsa don tare sukan amma duk da haka sai da takobin ta huda rigarsa ta tsargeta in ba don ma ya kare harin ba cikin zafin nama dasai takobin ta huda cikinsa koda suka duro kasa sai kowannansu ya cika da mamaki shi dai sarki shardas bai taba karo da jarumin da ya taba samun nasarar ko da lakutar rigar jikinsa ba amma yau gashi ya hadu
Chapter 6 · 0% Book details