Sashe 7
Tsatsuba Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
da wanda ma ya tsargeta da takobi shi kuwa jarumi hailur firgita yayi ainun bisa ganin yadda takobin sarki shardas ta tsarge garkuwarsa gida biyu don haka ya tabbatar da cewar duk sa adda takobin shardas ta sami jikinsa ba karamar illa zata yi masa ba, nan fa Hailur ya fara tunanin hanyar da zaibi ya iya kare kansa koda ya dubi garkuwar dake hannun sarki shardas sai yaga anyi tane da irin karfen da akayi Takobin, cikin sauri hailur ya dubi kaifin takobinsa sai yaga she har ta dan dakushe a wajen tsininta sakamakon haduwa da tayi da garkuwar sarki Shardas. . Al amarin da ya kara dugunzuma hankalin hailur kenan ya tabbatar da cewar babu wata hanya da zai iya kare kansa a wajen sarki shardas face ya kwaci garkuwar dake hannunsa yin hakan kuwa yasan cewa ba karamar sa a bace da nasara. . A wannan lokaci gaba dayan dakarun sarki shardas da tsirarun dakarun su hailur da sukayi saura a wajan sun zuba idanunsu a kansu kawai kowa so yake yaga yadda karshen wannan gumurzu zai kasance tamkar dacan ba yaki ake ba a wajan su kuwa matan da aka kama amatsayin bayi aka daddauresu tuni sun fara kuka tare da ya yansu kananan yara wadanda kusan su duka an kashe iyayansu maza an mai dasu marayu sai da kimanin dakiku dari da arba in suka shede ana kallon kallo tsakanin sarki shardas da jarumi hailur kowannansu tunanin dabarar da zaiyi ya cutar da abokin gwaminsa yake sannan suka sake rugawa izuwa kan juna a karo na biyu suna haduwa asama sai sarki shardas ya kawowa hailur sara a cinya shi kuma yakai masa sara a ka kowannansu yayi iya kokarinsa wajan kaucewa harin cikin zafin nama amma sai da takobin sarki shardas ta yanki hailu ta dara naman cinyar jini yayi tsartuwa hailur ya kwala uban ihu sakamakon tsananin zafi da zogin da yaji shi kuwa sarki shardas bai ankara ba sai gani yayi hailur ya tuje rawanin dake kansa ya fado kasa sai ga fuskarsa ta baiyana a fili karara kafin su duro kasa gaba daya tuni hailur ya doki hannun sarki shardas mai dauke da garkuwa garkuwar ta subuto kasa cikin bakin zafin nama hailur ya fada kan garkuwar ya sureta kuma yayi 'yardungure sau uku izuwa can gaba yana mikewa tsaye yayi sauri ya yagi rigar jikinsa ya daure raunin cinyar tasa don tsaida jini. . Shi kuwa sarki shardas ko da yaga tsirarun dakarun su hailur sunyi arba da fuskarshi kuma sun shaida ko shi wanene sai ya dakawa dakarunsa tsawa yace su karasasu gaba daya take dakarun suka hau tsirarun dakarun da sara da suka suka karkashesu a cikin 'yan dakiku kadan koda ganin abinda ya faru sai jarumi hailur ya kurma uban ihu ya ruga izuwa kan sarki shardas har dakaru sun yunkura zasu tareshi sai sarki shardas ya tsaidasu yace ai wannan nawa ne ba naku ba kuma abin kunya ne a ce nidaku munyi masa rubdugu ku zuba ido kamar yadda kukayi da farko kuga yadda zamuyi dashi koda gama fadin hakan sai sarki shardas ya tari jarumi hailur suka ci gaba da kaiwa juna mugayen hare hare wannan karon dai sarki shardas yana kaiwa hailur sara da suka ne da dukkan karfinsa cikin azababben zafin nama na gaban kwatance. . Kaico mai karfi sai Allah ya isa kuma na gaba yayi gaba na baya sai labari duk da irin tsananin juriya da jarumtaka irin ta hailur wannan karon sai da ya raina kansa domin bambancin a baiyane yake kuma sarki shardas ya shammaceshi wajan sauya salon fadan, a lokaci guda ya hada da kai masa naushi da bugu da hannu da kafa sai gashi nan da nan ya hadawa hailur jini da majina yana bal dashi kamar tamola... . Tab ganin wannan yanayi da hailur ya shiga ya sa ni tsaya wa cak! Da typing ɗin da nake, kuyi haƙuri bisa jin shiru na wasu kwanaki da kuka jini InSha Allahu zamu ci gaba a gobe idan Allah ya kafin