← Book details Tsatsuba Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 9

Sashe 3

Tsatsuba Part 2 Complete Hausa Novel · about 11 min read

.
Yayinda tsoho Imshal yaji wannan tambaya sai yayi Ajiyar numfashi ya dubi sarauniya larbisa cikin nutsuwa yace yake wannan sarauniya mai daraja kiyi sani cewa ba wani abu bane ya sakikaga na bushe da dariya ba sai saboda nasan cewa kin daukowa kanki gagarumin aikin da sai kinyi nadamar yinsa domin aikine wanda babu tabbacin samun nasara a kansa, sannan kuma zaki iya shan bakar wahala da bata da misali kuma dake da duk abikan tafiyar taku zaku iya rasa rayuwarku ko lafiyarku. Ke a takaice dai fiye da shekaru dari baya ba a taɓa samun mahalukin da ya ratsa ta cikin wadannan dazuzzuka guda uku har ya isa kogin sihir a raye
ba don haka ni yanzu ina kallonki ne a matsayin wacce ta gaji da rayuwar duniya take neman mutuwa ruwa a jallo! Ko kuma ince wacce ta sami tabin hankali !!
.
Dalilin da yasa kikaga ina zubar da hawaye kuwa shine biwa wannan TAFARKI da kike son bine na rasa iyayena da kakannina domin suma sun bar gida sun tafi izuwa kogon kitabul sihir domin magance wata matsala data addabi gaba daya zuri armu tsawon shekaru masu yawa amma dayansu bai dawo a raye ba, wannan matsala kuwa ba komai bace face wani sihiri wanda wani abokin gabarmu ya yiwa kakanninmu, shi dai wannan abokin gaba namu mafarauci ne kuma takadarin boka ne tunda akayi GASAR FARAUTA a birninmu kakanmu ya lashe gasar sai wannan
boka yayi masa sihiri ya kasa ci gaba da zama a cikin gari shi da iyalinsa yaji kamar ana konashi da wuta. Matansa da 'ya'yansa da jikokinsa ma haka suka rinkaji ya zamana cewa ba shiri suka hada nasu 'i' nasu suka koma cikin daji da zama bisa dole kakan namu ya hakura da sarautar sarkin daji da aka bashi ya daina zuwa fada gaba dayan zuri armu sai suka tsani cikin gari daga wannan rana kawo iyanzu babu sauran mutum daya daga cikin zuri armu wanda ke rayuwa a cikin daji duk mun watsu a cikin dazuzzuka har yau har gobe ni din nan da matata da yata shumaira da kike ganinmu bamu taba shiga cikin gari ba mu tsaya tsawon rabin sa a sai dai muyi siyayya a kasuwa mu fito babu irin kokarin da bamu yi ba wajan neman yadda zamu karya wannan sihiri amma abu ya gagara kafin mahaifina ya rasu ya shaida mini cewa ba zamu taba iya samun nasarar karya wannan sihiri ba face mun bude littafin TSATSUBA mun karanta wata kalmar tsafi guda daya wadda ke shafin tsakiya, yake wannan sarauniya mai daraja kiyi sani cewa bukatarki kusan iri daya ce da tamu amma ni ba zan iya barin yata shumaira tayi wannan tafiya ba tunda ita kadai gareni a wannan duniya kinga nidai tsufa ya riskeni mahaifiyar tama gata nan ta fara manyanta , yau idan babu ita shikenan zuri armu gaba daya ta shude kenan tunda mu ne kadai mukayi saura kafin tsoho Imshal ya gama rufe bakinsa sai jaruma shumaira ta mike zumbur ta durkusa bisa guiwoyinta a gabansa ta rike hannayansa biyu a lokacin da hawaye ya zumo mata tace ya kai abbana kayi sani cewa ko ka barni ko ka hanani yin wannan tafiya watarana sai mutuwa ta daukeni shin ka manta cewar ka gaya mini cewa dukkan mai nema yana tare da samu lallai ina son na karya wannan asiri wanda ya gagari iyayenmu da kakanninmu domin na barwa birninmu abin tarihin da baza a taba mancewa dashi ba ka tuna cewa har yanzu sarautar sarkin daji tana hannun zuri ar babban makiyinmu boka zarratu tunda mu mun kasa zama a cikin gari lallai ta kowanne hali saina kwato mana yancinmu na dawo mana da sarautarmu mun koma mun zauna a cikin wannan gidan sarauta namu na sarkin daji wanda kai kanka rabonka da shi tun kana jariri ina mai rokonka daka bani wannan dama ayi wannan tafiya dani da izinin iyayenka dake kwance cikin kabari saina sami nasara na kwato mana yancinmu.
.
koda jaruma shumaira tazo nan a zancenta sai tsoho Imshal da matarsa larisa suka kamu da tsananin tausayinta suka rungumeta sunamasu fashewa da kuka itama saita tayasu kukan.
.
Al amarin da ya karya zuciyar sarauniya larbisa kenan a karon farko a rayuwarta taji tausayin wani ya kamata har itama idanunta suka ciko da kwalla kuma ba komai bane ya janyo hakan ba face ganin matsalar ta tazo iri daya da tasu.
.
Saida tsoho Imshal da larisa suka dan jima a kankame da shumaira sannan imshan ya janye jikinsa daga cikin na shumaira ya dubeta cikin Alamun tsananin damuwa yace yake yata hakika kinzo mini da babban Al amari wanda ya dugunzuma hankalina kuma wanda a halin yanzu ba zan iya yanke hukunci ba a kansa lallai ina bukatar ki bani lokaci daga nan zuwa gobe muyi tunani da nazari akan al amarin nida mahaifiyarki koda jin wannan batu sai hankalin sarauniya larbisa ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe domin ta fara tunanin cewa tsoho Imshal ba zai yarda da wannan tafiya ba don haka duk shirinta ya rushe.
.
Nan dai shumaira ta mike tsaye ta kama hannun sarauniya larbisa ta jata suka fice daga cikin falon duk su biyun jikinsu a sanyaye, lokacin da dare ya sakeyi sai shumaira da sarauniya larbisa suka kasa barci saboda zulumi da fargabar sakamakon shawarar da iyayen shumaira zasu yanke akan wannan tafiya suna cikin wannan hali ne shumaira ta mike zaune daga kan gadonta ta dubi larbisa tace ranki ya dade ni fa tunda ina cikin zulumin abinda zai biyo baya ba zan iya barci ba, ina mai tabbatar miki da cewar rayuwata gaba daya yanzu babu wani abu da ya shiga raina sama da yin wannan tafiya koda kuwa ina da yakinin zan mutu nafi son na mutu jaruma akan na mutu raguwa a cikin rashin yanke wannan bakin ciki na zuri armu saboda haka yanzu zanje na gana da mahaifina domin naji hukuncin da ya yanke koda gama fadin hakan sai shumaira ta mike tsaye ta fice daga cikin dakin ita kuwa sarauniya larbisa saita bita da kallo kawai cikin alamun tsananin damuwa, jikinta na tsuma zuciyarta na dukan uku uku tana fargabar abinda zaije ya dawo lokacin da shumaira ta isa falon mahaifinta saita iske mahaifiyarta zaune akan kujera tayi tagumi kanta a sunkuye tana zubar da hawaye shi kuwa tsoho Imshal yana tsaye yana kai kawo duk su biyun fuskokinsu na nuna alamun tsananin damuwa da fargaba.
.
Koda shumaira taga iyayenta a cikin wannan hali sai hankalinta ya dugunzuma ainun taji kamar ba zata iya tunkararsu da maganar ba tunda su ma suna cikin irin halin da take ciki kawai sai shumaira ta juya da nufin ta koma izuwa dakinta.take tsoho Imshal ya kira sunanta shumaira , kada ki koma kizo mu tattauna wata muhimmiyar magana koda shumaira ta juyo tana mai amsa kiransa saita ga fuskar tsoho Imshal ta juye izuwa murmushi da annuri cikin mamaki shumaira ta tunkari mahaifin nata ta iso daf dashi yadda har suna iya jin numfashin juna tsoho Imshal ya dafa kafadar shumaira yace, yake yata ki kwantar da hankalinki kiyi sani cewa ba zan iya hanaki yin wannan tafiya ba saboda ganin muhimmancinta.
.
Amma akwai sharadi guda daya da zamuyi dake wannan sharadi kuwa shine ba zamu yarda kiyi wannan tafiya ke kadai ba sai tare damu koda jin wannan sharadi sai idanun shumaira suka zazzaro hankalinta ya dugunzuma ainun ta dubeshi tace haba yakai Abbana tayaya zanyi wannan tafiya tare daku alhalin girma ya kamaku baku da karfin jiki gami da jarumtaka irin tawa koda jin wannan batu sai tsoho Imshal ya sake yin
murmushi a karo na biyu yace Ashe kin manta da cewar nine na koya miki yadda ake farauta a cikin daji da yadda ake yin yaki a cikin dandazon mayaka??
.
To kiyi sani cewa ko giwa ta fadi tafi gaban a dasa mata wawa malami har abada malami ne akan dalibansa ina mai tabbatar miki da cewa ni da mahaifiyarki zamu baku gagarumar gudumawa a cikin wannan tafiya yadda zaku sha dumbin mamaki saboda haka ki koma dakinki ki gayawa sarauniya larbisa cewar ku fara shirin wannan tafiya tun a daren yau amma ina son ta turo mini babban abokin tafiyarta tsoho Huzallatul marwas yanzu take kuma ta gaya masa cewa ya taho tare da jakar sihirinsa shumaira ta juyo jikinta a sanyaye ta koma izuwa can turakarta zuciyarta cike da zulumi. Fargaba da tsananin damuwa lokacin da shumaira ta isar da wannan sakon mahaifinta izuwa ga sarauniya larbisa ta firgita kuma ta kamu da tsananin mamakin yadda akayi tsoho Imshal ya san da batun jakarsa ta sihiri alhalin bata gabatar dashi ba a wajansam nan take larbisa ta gano cewar lallai shi ma tsoho Imshal ya cika boka masanin abinda ke boye ba tare da boye komai ba sarauniya ta tashi ta tafi izuwa masaukinsu tsoho huzallatul marwas ta jashi izuwa gefe daya ta sanar dashi sakon tsoho Imshan, koda jin hakan sai huzallatul marwas ya bushe da dariya.
.
Al amarin da ya baiwa larbisa mamaki kenan kuma ranta ya baci ta dubeshi a fusace tace menene kuma abin dariya a cikin wannan Al amari??
.
Huzallatul marwas ya numfasa yace hakika mahaifim shumaira ya cika hatsabibin boka domin ban taba zaton zai gano da batuna ba a cikin wannan tawaga taki bare ma har ya san da batun jakar sihirinsa babu komai ki kwantar da hankalinki yanzu jamuje na riskeshi domin naji dalilin da yasa ya bukaci ganina, koda gama fadin hakan sai tsoho huzallatul marwas ya yunkura da nufin ya juya ya nufi hanyar da zata kaishi inda turakar tsoho Imshal yake. Tsulum sai suka ga aljani subauratu ya baiyana a sama daf da fuskarsa yana mai kyalkyala dariya lokaci guda kuma sai ya hade fuskarsa ya risina ga huzallatul marwas yace ya shugabana kayi sani cewa zuwanka kai kadai izuwa ga tsoho Imshal yana da hadari don haka duk yadda za ayi ka tafi tare da sarauniyarka komai rintsi da tsanani kada ka yadda kayi wata magana dashi sai sarauniya na kusa tana sauraronka, kafin tsoho Huzallatul marwas ya budi baki ya tambayi subauratu dalilin da yasa ya bashi wannan shawara tuni subauratu ya bace bat, sai jin motsinsa yayi a cikin jakarsa ta sihiri Huzallatul marwas ya dubi larbisa yace ranki ya dade menene abinyi?
.
Larbisa tayi murmushi tace yadda Aljani subauratu ya fada haka za ayi, nan take suka dunguma su biyun suka koma can turakar tsoho Imshal inda suka iskeshi tare da yarsa shumaira da matarsa larisa a zaune koda Isham yaga larbisa ta biyo tsoho huzallatul marwas sun dawo tare sai ya murtuke fuskarsa tamkar an aiko masa da sakon mutuwa ya dubi larbisa yace ai sai ku bamu wuri don ina son na gana da huzallatul marwasu koda jin haka sai huzallatul marwas ya matso gaban Isham ya mika masa hannu suka gaisa sannan yace yana daga cikin sharaddan tafiyarmu nida sarauniya cewar komai tare da ita zanyi, ba zan boye mata komai ba koda jin wannan batu sai jikin tsoho Isham yayi sanyi kawai sai ya kyalkyale da dariya ya rungume huzallatul marwas yana mai cewa lale marhaban da babban aboki ma abocin hikima da hangen nesa shi kenan kuje ku kwanta domin ku dan rintsa kafin gari ya waye mu kama hanya dajin haka sai larbisa da tsoho Huzallatul marwas marwas suka dubi junansu suka yi murmushi nan take suka yiwa su tsoho isham sallama suka juya suka fice daga cikin falon, fitarsu keda wuya sai jaruma shumaira ta dubi isham fuskarta cike da alamun tsananin damuwa tace ya kai abbana yanzu ta yaya kenan zamu san shafin da ya kamata mu karanta a cikin littafin tsatsuba domin kawai da wannan matsala tamu tunda gashi sarauniya larbisa taki yarda ta barka ka kebe da tsoho huzallatul marwas bare har kuyi wannan yarjejeniya damu ka tsara?
.
Koda jin wannan batu sai tsoho isham ya bushe da dariya yace ai maso abinka ya fika dabara kuma masu iya magana sunce samu yafi iyawam idan har muka mallaki littafin tsatsuba a hannunmu munyi mai wuyar da sannu zamu gano duk wani sirri dake cikinsa da jin wannan batu sai hankalin jaruma shumaira ya kwanta zuciyarta ta cika makil da farin ciki amma da ta tuno irin mugun hadarin dake cikin tafiyar da zasuyi kuma gashi tare da iyayen nata za ayi wannan tafiya sai hankalinta ya dugunzuma ainun ta rasa abinda yake yi mata dadi haka dai ta yiwa iyayen nata sallama cikin sanyin jiki ta tafi izuwa turakarta kashegari kuwa tun kafin Alfijir ya keto kowa ya gama shirin tafiya nan take aka hau dawakai aka kama hanya aka nausa cikin daji tsoho huzallatul marwas, sarauniya larbisa da sadauki humaisu ne akan gaba jaruma shumaira da iyayenta kuwa sune a karshe domin dakarun larbisa ma suna gabanta bayan an shafe sa a guda ana tafiya sai tsoho huzallatul marwas ya dubi sarauniya larbisa a lokacin da suke tafiya kafada da kafada bisa dawakansu yace ya shugabata kiyi sani cewa ruwa baya tsami banza lallai akwai wata hujja mai karfi wacce tasa iyayen shumaira suka siyar da rayuwarsu wajen biyomu a cikin wannan tafiya mai hadarin gaske. Yayinda sarauniya larbisa taji wannan batu sai tayi murmushi tace koma menene a ransu ai zamu gani tunda dai sannu sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba a jeba
.
Kamar yadda sannu sannu ba zata hana AlQuyraemey xan ci gaba da rubuta muku wannan littafi saidai a jima ba ajeba..A nan nake cewa sai Allah ya kaimu Gobe dominmjin Yadda zata kaya a cikin wannan Littafi Na tsatsuba
Chapter 3 · 0% Book details