← Book details Tsatsuba Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 9

Sashe 1

Tsatsuba Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

TSATSUBA
BOOK 2
Part (A)
Na Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi

Lokacin da takobin Shumaira ta isa kirjin sarauniya larbisa sai ta dan soketa a kirji, tana kokarin danna takobin a cikin kirjin nata kafin larbisa tayi kara sai shumaira taji an daka mata tsawa daga baya bisa dole ta fasa dannan takobin izuwa cikin kirjin larbisa, ta mike tsaye daga kanta ta waigo tayi arba da wanda yayi mata tsawar, ba wani bane face mahaifinta mafarauci imshal.
.
Mafarauci Imshal ya kasance dogon mutum mai kirar sadaukai sai dai girma ya kamashi sosai domin shekarunsa zasu kai kusan arba in gaba daya gashin kansa sajensa da gemunsa duk farin gashine, yana rike da wata doguwar sanda a hannunsa ya rataya kwari da baka a bayansa rigarsa, wandonsa da takalminsa dake kafarsa duk anyi sune da fatar damisa.
.
Koda jaruma shumaira ta hango mahaifinta Imshal sai ta rugo izuwa gareshi ta dukar daki tana mai nuna girmamawa a gareshi, A wannan lokaci ne sarauniya larbisa ta mike tsaye tana mai dafe gefen kirjinta inda
shumaira ta soka mata takobi don har dan jini ya fito kawai sai sarauniya larbisa ta sunkuya cikin biyayya ta gaisheda tsoho Imshal. Imshal ya karbi gaisuwar yana mai kare mata kallo sama da kasa sannan ya karewa dakarunta kallo ya dubi shumaira yace akan wani dalili kike yaki da wannan mace mai daraja? Shin bakya ganin alamar cewa mai mulki ce.
.
Koda jin wannan tambaya sai shumaira ta dago kai ta dubi imshal ta ce yakai abbana kayi sani cewa haka kawai wannan sarauniya tare da dakarunta suka shigo cikin dajin nan suka dasawa dabbobinmu wawa, bisa wannan daliline na tarwatsa dakarun nata kuma na umarcesu da su fice daga cikin dajin nan tun kafin fishinmu ya tabbata a kansu amma saboda naci sai wannan sarauniya ta biyoni har cikin garken dabbobi, ni ina ganin cewa kawai ka kyaleni na gama da ita yanzu domin da ita da yaran nata su gane cewa ruwa ba sa an kwando bane kuma bakin rijiya ba wajan wasan yaro bane.
.
koda jin wannan batu sai tsoho imshal ya bushe da dariya sannan ya hade fuska ya dubi shumaira yace ai ruwa baya tsami banza, shin a farkon bayaninta gareki bata gaya miki cewar tana da wata bukata ba a wajanki?
.
Cikin alamun sanyin jiki shumaira tace ta gaya mini cewar tana da wata bukata a wajena amma saina gaya mata cewar bata da abinda zata iya biyana da shi don haka babu abinda zan iya yi mata koda jin wannan batu sai imshal ya gyada kai yace yarinya kinyi hanzarin yanke hukunci shin bakya tunanin cewa bukatar da tazo mana da ita wata kila a sanadinta ne muma zamu fita bakin cikin da ya addabemu tsawon shekaru bakwai.. Shin kin manta ne cewar na gaya miki zamu iya nasarar samun abinda muke nema a cikin wannan shekara idan kin hadu da wadansu bakin jarumai guda uku?
.
Koda jin wannan batu sai jikin shumaira yayi sanyi ta sunkui da kanta kas ta kasa cewa komai daga can kuma sai ta dago kai da sauri ta dubi tsoho imshal tace amma ai wannan sarauniya ba ta da kama ko siffa irin ta mutane ukun dakayi mini bayani imshal yace hakane amma dai ki tsaya muji abinda ya kawota wajanmu babu mamaki a sanadin hakan a samu dacewa cikin nutsuwa tsoho Imshal ya dubi sarauniya Larbisa yace yake wannan sarauniya ma abociya kyawu da karjini wace bukata ce dake tasa har kikayi tattaki kikazo har wannan daji namu?
.
Kafin larbisa ta budi baki tace wani abu sai tsoho Imshal ya kara tarar numfashinta yace amma kafin kice komai ya kamata ku fara yiwa raunikan jikinku magani yana gama fadin hakan sai ya bude wata jaka dake rataye a bayansa ya dauko wani farin magani me maiko da kauri kamar daskararren nonon shanu ya mikawa yarsa shumaira yace ungo ki shafa a rauninki kuma ki shafawa bakuwar tamu cikin alamun damuwa shumaira ta karbi maganin ta fara shafawa kanta sannan taje ta zauna a gaban larbisa ta kama shafa mata fuskarta a daure babu annuri, su kuwa su sadauki Humaisu sai hankalinsu ya kwanta sukayi murna da ganin yadda tsoho Imshal ya karbesu hannu biyu, bayan shumaira ta gama sawa larbisa magani a rauninta sai tsoho Imshal ya dubi larbisa yace yake wannan sarauniya kiyi sani cewa ni yanzu na karbeku keda jama arki a matsayin bakina saboda haka yanzu zan kaiku zuwa gidana domin ku huta in yaso bayan kun nutsu saimu zauna mu tattauna mu dake idan har zamu iya taimakon juna zamu iya yarda da buqatarki, idan kuma ke
kadaice zaki amfana damu to sai dai muyi miki fatan samun nasara ki kara gaba, koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube sarauniya larbisa, ta dubi Tsoho Imshal cikin murmushi tace nayi farin ciki da wannan tayi da ka bani ya kai Abul Shumaira kuma zuciyata ta bani cewa nima zan iya baku taimako bisa taku bukatar.
.
Tsoho Imshal yayi murmushi yace sai an gwada Sannan ake sanin na kwarai yana gama fadin hakan sai ya kama hannun shumaira suka nufi bayan wani katon dutse yana mai yafito su larbisaa, Da hannu cikin hanzari larbisa taje ta kama dokinta ta hau tabi su.
.
Tsoho Huzallatul marwas ne ya fara bin bayanta sannan sadauki Humaisu da sauran Dakaru. Ana zagayawa bayan wannan katon dutse sai kowa ya cika da mamaki bisa ganin wani dankareren gida wanda aka ginashi da duwatsun wuta Gidan katone kuma anyi masa fasali na gidan sarauta dauke da bangare bangare, banbancinsu da gidan sarauta kawai shine babu bayi, dakaru da kuyangi mutum daya kacal suka gani a cikin wannan gida kuma ba wani bane face larisa mahaifiyar Jaruma shumaira
lokacin da larisa ta hango mijinta imshal da yarta shumaira tare da bakin mutane sai tsoro ya baibayeta domin wannan shine karon farko a iya zamansu a cikin wannan daji da ta ga sun zo mata da mutane har gida don haka bata yarda ta bude kofar gidan ba sun shigo har sai da suka matso kusa taga cewar babu wata alamar damuwa akan fuskar mijinta da 'yarta Ita kanta larisa shekarunta sun kai hamsin da biyu koda uku amma saboda tsananin kyawun jikin da Allah ya bata mutum ba zai taba zaton ta kai hakan ba.
.
Da isowarsu tsoho Imshal ga larisa sai ya gabatar da sarauniya Larbisa a gareta sannan ya gaya mata cewa ita da jama arta bakine masu mahimmanci, cikin farin ciki larisa ta karbi sarauniya larbisa tana maiyi mata barka da zuwa, nan take aka kaisu sadauki Humaisu izuwa wani bangare daban na gidan ita kuma larbisa sai tabi jaruma shumaira izuwa dakinta.
.
Cikin hanzari shumaira ta dafa ruwan dumi ta kaiwa larbisa kewaye ta shiga wanka kafin larbisa ta fito daga wankan tuni shumaira ta shirya musu abinci. Larbisa na fitowa daga wankan sai itama shumaira ta shiga wankan sai da ta fito daga wankan sannan suka zauna tare bisa wasu kujeru dake karkashin wani tebur suka fara cin abincin, tsawon yan dakiku da fara cin abincin dayansu baice uffab ba.
.
Abinda ya daurewa shumaira kai shine ganin yadda larbisa ta saki jiki take ta cin abincin Alhalin ba abinci ne mai dadi ba irin nasu na sarakai Abincine irin wanda kowane talaka zai iya ci musamman mazauna daji cikin matukar mamaki shumaira ta dubi sarauniya larbisa tace yake wannan sarauniya menene dalilin da yasa kika saki jiki kike ta cin irin wannan abinci namu na talakawa alhalin nasan a guzurinki akwai irin naki abincin da kika taho dashi?
.
Koda jin wannan tambaya sai sarauniya tayi murmushi tace ai dokar bakunta itace yin koyi da irin mutanen da ka riska, ni kaina nayi mamakin yadda akayi naji ina matukar jin dadin wannan abinci naku amma fa babu abinda ya bani mamaki a yanzu sama dake, koda jin haka sai shumaira ta dago kai da sauri ta dubi larbisa cikin mamaki tace ke kuma me nayi wanda ya baki mamaki? Larbisa ta ajiye cokalin da take cin abinci gami da yin ajiyar numfashi sannan tace gani nayi da farko baki karbeni da wata daraja ba har ma yakata kikayi kikauda batun matsayina na sarauta yanzu kuma sai gashi kina yin biyayya da hidima a gareni.
.
Yayin da shumaira taji wannan batu sai tayi murmushi tace ai nima nayi amfani da maganar manya da suke cewa idan babba ya rike girmansa dole ne karami yayi masa biyayya. Lokacin da kika shigo cikin wannan daji namu ke da jama arki baki hanasu kokarin yi mana sata ba dalilin da ya sa na ki karbar bakuncinki kenan tun da farko amma yanzu dana gane cewar wata kila kina da mahimmanci ga rayuwata shi yasa nake yi miki ladabi da biyayya larbisa ta bushe da dariya sannan tace ai kowane mutum yana da rana komai kaskancinsa shin zaki iya gaya mini babban burinku na duniya keda mahaifinki wanda har kuke tunanin zan iya taimaka muku a kansa?
.
Sa adda shumaira taji wannan tambaya sai tayi murmushi tace me kikeci
na baka na zuba ehm wato ( what are you eating na baka is falling down )
zakiji amsar wannan tambaya taki idan mukayi zama na musamman mu dake kuma a sannan ne muma zamuji taku bukatar a wajanmu, kodajin
wannan batu sai sarauniya larbisa tayi murmushi tace tabbas zancenki dutse ne, haka dai shumaira da larbisa suka ci gaba da hira har suka gama cin abincin kuma dare ya raba sannan suka kwanta sukayi barci, .
.
Kamar yadda aka karrama sarauniya larbisa hakama aka karrama sadauki humaisu da dukkan dakarunsa suka ci suka sha sukayi hani'an kuma suka kwanta a masauki mai kyau, Al amarin da yayi matukar daure musu kai kenan suka cika da tsananin mamakin yadda wadannan mafarauta suka tara arziki mai yawa haka.

+++±+++++++
Chapter 1 · 0% Book details