Sashe 27
Shu'umar Masarauta Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Dare ne ya tsala sosai ban da kukan tsuntsaye da na ƙananan dabbobi babu abin da yake tashi, cikin sanɗa da ɓadda-bami take tafiya a hankali tana waige don kar wani ya ganta har ya fahimci abin da yake tafe da ita. Kamar yadda ta saba a duk daren da take neman biyan buƙatarta haka ta tunkari tsaunin Boka Mai zamani, kamar yadda ya ga zuwanta a cikin ƙoramar sihirinsa haka ya ji takunta zuwa kogon dutsensa. Tun daga bakin ƙofa Boka Mai zamani ya rungume ta a yunƙurinsa na son su fara aikata masha'arsu kamar yadda suka saba duk lokacin da ta ziyarce shi, a hankali ta zame shi daga jikinta tana faɗin, "Sha kundum ta ci gaba da rufa mana asiri dangane da ɓarnar da muke aikatawa Sarki Damina." Boka mai zamani ya bushe da mahaukaciyar dariya sannan ya furta, "Wane mutum In ji mutuwa shalelena? Asirinmu ba zai taɓa tonuwa ba don ba na jin wancan sakaran zai iya kusanto da Sha kundum cikin wannan Daular, hasalima rashinta tare da mu shi ne mafi alheri domin na tabbata idan tana yankin nan asirinmu ya gama tonuwa. Yanzu dai ya kamata a baiwa kura ajiyarta." Takawa ta fara yi a hankali tana zame ganyen da ke jikinta daga wanda ya rufe al'aurarta har zuwa na ƙirjinta sannan ta furta, "Ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai ya ke ba mudubina. Indai wannan ne ai ta kwana gidan sauƙi jariri a ɗakin mayya. Amma abin da yake tafe da ni bai wuce kan maganar wancan sakaran Yariman ba, shin maganar da na ji Sarki ya faɗa gaskiya ne zai iya warkewa? Saboda ina ɗagawa Sarki Damina ƙafa ne don na san a halin da yarima yake ba zai iya mulkar Daular nan ba." Boka mai zamani ya ƙarasa wurinta yana yawo da hannunsa a sassan jikinta sannan ya furta, "Tabbas a bincikena matuƙar Sha kundum ta bayyana a Daular nan zai iya warke wa amma da sharaɗin sai an bankaɗo sirrin da ba kowa ne ya sani ba kuma ba kowa ne zai gan shi ba. Mai wannan ikon yanzu haka ta bar duniya, Mai babbar Turaka ita ce ta san da wannan ɓoyayyan sirrin wanda ko da Sha kundum ba ta dawo daular nan ba matuƙar aka bankaɗo shi Yarima zai warke, yanzu haka gawar Mai babbar turaka na ɗakin yarima na kashe ta ne a lokacin da take ƙoƙarin sanarwa da Yarima sirrin ɓoyen da bankaɗe shi ba alheri ba ne a game da ke, ni kuma duk abin da zai muzanta shi zan iya kawar da shi. Sarki Damina yana kallonki a matsayin mahaifiyar Yarima alhalin Hasana ita ce Mahaifiyarsa kece Usainarta, Ko kin san har gobe Mahaifiyar Yarima tana raye a faɗin duniyar nan? Ko kin san Yarima ba shi kaɗai ne Ɗan da Sarki Damina ya mallaka ba? Ko kin san ƴaƴan Sarki Damina Uku ne a faɗin duniya? Idan bacci kike ki farka domin a duk lokacin da Damina ya gano kece kika nemi salwantar da rayuwar yarima da mahaifiyarsa na tabbata kashinki ya bushe. Ki yi duk abin da za ki yi ki nemo tagwayen jarirai ki kawo min domin na cika miki wani aiki da su idan ba haka ba komai zai iya faruwa, kuma ki tabbata jariran sun fito daga cikin jinin Maharba domin har gobe jininsu na tasiri akanmu tun da sune suka yi galaba a kan mu a lokacin da mummunan al'amari ya faru da Sarauniya Shakundum." Jakadiya da tun shigar Mai ɗakin Sarkin Damuna take laɓe a ƙofa ta riƙe bakin cikin mamaki, a hankali ta furta, "Tabbas Usaina ta cika tattaciyar marar imani amma na yi rantsuwa da Sarauniya Sha kundum da mulkinta sai kwaɓarta ta yi ruwa, a kullin fata da burina bai wuce Sarki Damina ya auri Jummai don na tabbata ko da tsiya da azziki sai Jummai ta haihu a gidansa. Jakadiya bata ƙarasa wannan tunanin ba ta hango harshen wutar itace kafin ta yi wani yunƙuri Bayin Sarki Damina suka haske ta da shi, a tsawace babban bawansa ya furta, "Jakadiya Lami me kike yi a wurin Boka mai zamani a talatainin tsohon daren nan duba da kin san haramun ne matuƙar ba a sanar da Sarki Damina wannan ziyarar ba?" Daga cikin kogon dutsen cikin Boka mai zamani da Usaina mai ɗakinsa ne ya kaɗa, nan take zufa ta fara keto musu cikin faɗuwar gaba ta furta, "Halaka ta zo mini matuƙar Sarki Damina ya san da ni a kogon dutsen nan." Kafin boka mai zamani ya yi magana daga cikin rijiyar da gunkin Sarauniya Sha kundum take suka ji wata irin tsawa wacce ta haddasa razanar Jakadiya ta faɗo cikin kogon dutse a hargitse. Ganin haka ya sa Sarki Damina da Fadawansa suka rufa mata baya, don ya kawo ziyarar cikin dare ne sakamakon mummunan mafarkin da ya yi akan Yarima da wata matashiyar buduwa mai ɗauke da kwari da baka a hannunwanta."
*Ummou Aslam Bint Adam*🌚
*Ummou Aslam Bint Adam*🌚