← Book details Shu'umar Masarauta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 27

Sashe 2

Shu'umar Masarauta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jinjina kai ya yi ya furta. "Barkanki Fulanin Sarki Abdul'aziz." Shiru ne ya ratsa Fulani Umaima ta kawo ido ta sa wa Bamaguje, ya saki murmushi don ya san wace ce Umaima. Ga tsananin buƙata fal ƙirjinta ga kuma taƙama da izzar mulki, kallo ɗaya ya yi mata ya fahimci halin da take ciki. "Umaima kin yi ƙoƙari."

"Sanin haka ya sa na kawo ziyara a ranar da ka buƙata." Ta amsa masa a taƙaice.

"Kin aiwatar da komai yadda ya kamata, don haka kishiyarki ita da Sarki Abdul'aziz sai kallo sai hange daga nesa. Matuƙar ba asirin nan ne ya karye ba, ba na jin kishiyarki za ta sake ɗaukan ciki a doron ƙasar nan. Ke ba ma ciki ba ina mai tabbatar miki ita da sake yin wata mu'amala da Sarki Abdul'aziz sai dai a lahira idan ana yi. Ina ragowar kayan aikin?" Ya wurga mata tambaya. Jin haka ya sa Umaima ta saki malalacin murmushi ta ɗebo gashin Fulani babba da gashin Sarki Abdul-aziz, haɗe da ƙasar maƙabarta da ta gidan tururuwa ta miƙa masa ba tare da ta tanka masa ba. "Mun sakar mata lalurar fitsarin kwance, kuma mun saka mata lalurar mantuwa da warin jiki." Bamaguje ya faɗa yana jefa tarkacen da Fulani Umaima ta bashi a cikin wata tunkunya da ke cike da jini tana tafasa. Kusan duk abin da suke tattaunawa Maimuna tana jin su, haka kawai ta ji tausayin uwar ɗakinta ya ɗarsar mata. Musamman da ta tuna zallar cin amanar da take yi mata mai haɗe da zagon ƙasa.

"Ina maganar cikin jikinta ya kwana?" Fulani ta tambaya cike da izza.

Bamaguje ta ɗebi wani jini mai yauƙi ya watsa a jikin wani allon farin ƙarfe. Take waɗansu inuwoyi suka bayyana, yana fara nazartarsu sai gani ya yi ɗuff komai ya ɗauke. Cikin da damuna ya sake ɗiban jinin ya watsa har sai da ya yi haka sau uku sannan ya dubi Umaima cikin damuwa. "Kishiyarki a daren yau za ta haihu!" Dum! Fulani ta ji tsakiyar kanta ya sara kamar wacce aka buga wa guduma. Rai a ɓace ta dube shi. "Wanne irin mugun labari nake ji haka, zancen banza kenan ƙafa ta mutu ta bar takalmi. Cikin jikinta ya fi komai ɗaga mini hankali..." Da sauri ya katse ta.

"Tun fil azal kundunsa rubuce yake da zanen ƙaddararsa, cikin kishiyarki shu'umin ciki ne lulluɓe yake da almara tamkar yadda masarautarku ta kasance SHU'UMAR MASARAUTA. Kamar yadda na gaya miki a yau za ta haihu..." Duk dakiya da ƙarfin zuciya irin ta Fulani Umaima sai da hawaye ya suɓuto mata, Bamaguje ya tsaya yana kallonta haɗe da jinjina kai. "Yau shekarata biyar kenan a cikin masarautar nan ko ɓatan wata ban taɓa yi ba, tun Fulani babba na da goyon fari Takawa ya auro ni. Bamaguje kana son na ƙare rayuwata cikin ƙasƙanci da rashin mamora?" Girgiza kai ya yi, ya sauke ajiyar zuciya.

"Wa ya ce miki ba za ki haihu ba?" Fulani ta zuba masa idanu zuciyarta na bugawa. "Yanzu haka kina ɗauke da juna biyu na tsawon makwanni uku." Kamar a mafarki haka ta ji kalaman Bamaguje na ratsa majiyar sautinta. "Ki yi imani da ni Umaima matuƙar ina numfashi ba za ki tozarta ba." Sanyi ta ji har cikin ranta.

"Da kai na dogara Bamaguje na yi imani da kai tun da ba ka kunyata mahaifiyata ba na tabbata ba za ka tozarta ni ba." Ta yi maganar a raunane.

Wata ƙatuwar kunama ya ɗauko da hannunsa ya ce, "Ba ni hannunki." A firgice ta wurga masa kallon baka da hankali, ya saki murmushi don ya fahimce ta. "Umaima kenan kura kike ga tsoro ga ban tsoro." Umaima ta haɗe fuska kamar ba ita ba. "An ya kuwa? Kar fa ka manta ko kura ta rame ta fi ƙarfin gawurtattun karnuka, dalilin haka ya sa masallacin kura ba a ba wa kare limanci." Murmushi Bamaguje ya yi. "Kwantar da hankalinki kamar kin faɗa rijiya. Matso kusa ki ji." Bamaguje ya furta. Tun bai rufe baki ba Umaima ta matsa kusa da shi, raɗa ya yi mata a cikin kunne lokaci ɗaya ta bushe da wata iriyar dariya cike da farinciki. Ta koma mazauninta na farko tana sauraronsa. "Ki tabbatar da kin aiwatar da abin da na umarce ki, don kuwa kowa rai ya yi wa daɗi ba ya mai shi ba."

"Bamaguje kenan! Ai ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba." Umaima ta furta cike da nishaɗi. Kashe mata ido ɗaya ya yi yana ƙare mata kallo, ganin haka ya sa ta fahimci inda ya dosa. "Tukwina fa?"

"Ka sallame ni kenan?" Ita ma ta wurga masa tambaya. Gyaɗa mata kai ya yi Umaima ta miƙe babu ko kunya ta sauke rigar tsubbun jikinta, Maimuna ta sunne kai ƙasa zuciyarta na bugawa. A fakaice take ƙare wa tsohon kallo cike da ƙyanƙyami don ko ita da take baiwa gani take ba za ta iya haɗa jiki da shi ba. Bamaguje na shirin ɗora hannu a jikinta ta ɗan ja da baya haɗe da sakin murmushin mugunta. "Na sadaukar maka da kishiyata a wannan daren, shi ne tukwicin da zan iya yi maka." Ba ta jira cewarsa ba ta ɗora rigar a jikinta. Bamaguje ya gyaɗa mata sannan ya furta. "Za ku iya tafiya." Umaima ta yi masa jinjina da hannu sannan ta sake ɗiban ruwan da ta wanke fuska da shi ta nufi wurin da Maimuna ke zaune hannunta ɗauke da kunamar da Bamaguje ya damƙa mata.

Abin da suka aiwatar a farkon zuwansu yanzun ma haka ne ya faru, sai da suka koma daidai wurin da suka buɗe ido suka gan su tun farkon zuwansu sannan, Fulani Umaima ta ɗaga ƙahon ta runtse ido ta busa haɗe da kiran sunan Bamaguje. Ƙamshin ɗakin Fulani ne ya ankarar da Maimuna dawowarsu gida, cike da girmamawa ta zube ƙasa ta furta. "Allah huta gajiya uwar gijiyata."

"A kullin ina sake jaddada miki bakinki ƙanin ƙafarki Maimuna, duk ranar da kika bari kwaɓarki ta yi ruwa na ji sirrina ya fita za ki bambamce mini tsakanin tsaba da tsakuwa." Fulani ta yi maganar cikin sigar gargaɗi. "Maimuna ta duƙa kai ƙasa. "Wace ni uwar gijiyata? Kada Allah ya nuna mini ranar da zan aikata miki wannan zunubin ranki shi daɗe." Fulani ta taɓe baki, "Za ki iya tafiya." Da sauri Maimuna ta fice ko waige ba ta yi. Har za ta nufi sashen su na bayi sai uwar ɗakinta Fulani babba ta faɗo mata. Haka kawai ta ji sam ba ta kyauta ba. Zuciyarta ta ci gaba da azalzalarta da ta je ta ga halin da take ciki. Cikin sanɗa ta nufi sashen Fulani babba gabanta na faɗuwa. A haka ta ci gaba da tafiya har cikin ɗakin, ras! Ƙirjinta ya buga jikinta ya ɗauki karkarwa sakamkon ganin Fulanin a yashe babu sutura a jikinta. Wani tafkeken maciji ta gani a tsakanin ƙafafuwanta ya kafa kansa a saitin ƙasanta, ga wani irin gurnani da macijin ke yi. Idanun Fulani a rufe amma sai mutsu-mutsu take yi, da alama ma bacci take yi. Daga bayanta ta ji an dafa kafaɗarta, wani abu ne ya tsarga mata ta yi mutuwar tsaye cikin sanyin jiki ta waiwayo. Karaf idanunta suka sauka a kan Fulani Umaima da ta haɗe girar sama da ta ƙasa.

_Ummou Aslam Bint Adam_🌚
07062062624.
[10/4, 11:30 AM] Ameera Adam🌚: *SHU'UMAR MASARAUTA*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba. Ban yi shi don cin zarafin kowacce ƙabila da Masarautunsu ba.

SHAFI NA BIYU

Ras! Ta ji gabanta ya yi mummunan faɗuwa, lokaci ɗaya ta nemi yawun bakinta ta rasa. Cikin firgici ta buɗe baki za ta yi magana Fulani Umaima ta katse ta. "Me kike yi a nan kuma uban me kike leƙe?" Maimuna ta zube a ƙasa jiki na rawa ta furta. "Ki yi mini aikin gafara uwar gijiyata, na zo na ji ko Fulani nada buƙatar wani abu kafin na tafi." Da hannu Fulani Umaima ta nuna mata hanya, sum sum sum Maimuna ta fice jiki na karkarwa. Fulani Umaima ta leƙa Fulani babba da ke kwance, ta saki murmushi mai ɗauke da ma'anoni a hankali ta furta. "Mu zuba mu gani idan tusa na hura wuta, in dai ni ce yanzu kika fara gani." Daga haka ta fice daga ɗakin.

Fulani babba ta jima a haka sannan ta farka, a hankali take sauke ajiyar zuciyata. Duk da a mafarki ta ga Mai martaba yana kusantarta abin ya yi mata daɗi, ta ji farinciki matuƙa saboda idan ba mantawa ta yi ba rabon da wani abu ya shiga tsakaninta da Takawa tun cikin jikinta bai fi wata biyu ba. Danshin da ta ji a jikinta ne ya sa ta kai hannunta, da mamaki take kallon makwancin nata. Da ƙyar ta yunƙura ta tashi nan take fitsarin da ke naɗe da zaninta ya fara ɗiga, da farko ta yi tsammanin ko faya ce ta fashe mata tun da a halin da take ciki tana iya haihuwa a kowane lokaci, musamman da take jin ciwon mara sama-sama. Sai dai zarni-zarnin da ta ji ne ya sa ta shinshina hancinta. A hankali ta furta. "Fitsari? Ni kuma? Kai ina jin dai faya ce ta fashe." Gudun wasu-wasi ya sa da kanta ta ɗebo ruwa ta sa a katifar ta sauya kayan jikinta amma har lokacin gani take faya ce ta fashe mata. Banɗaki ta shiga ta yi wanka ta fito sannan ta ɗan ci abinci, a hankali ta ji mararta na ci gaba tsikararta daga baya bacci ya sake yin awon gaba da ita.
Chapter 2 · 0% Book details