← Book details Shu'umar Masarauta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 27

Sashe 17

Shu'umar Masarauta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba iya su Baffajo ba hatta sauran Bayin da ke wurin sai da suka rufa musu baya, sakamakon ganin wurin da Kamalu yake ƙoƙarin kai kansa. A tarihin masarautar babban kuskure zuwa rafin tsamiya da doshin magriba, hasali ma a ranar juma'a akwai abubuwa biyu da suka haramta ga mazauna cikin masarautar. Na farko, duk ranar juma'a haramun ne shan nonon shanu, awaki ko na raƙumi. Duk wanda ya yi gangancin karya wannan ƙa'idar kuma zai iya tsintar talatarsa a laraba, domin a labarin da yake yawo a cikin masarautar an ce shekara sama da ɗari an taɓa samun turka-turka tsakanin Sarkin da ke mulki da Bafulatanar Aljana kafin daga baya aka sasanta, amma wannan labarin kusan na kunne ya girmi kaka ne don babu wanda kai tsaye zai ce maka ga daga wurin wanda ainihin labarin ya fito. Shi kuma wannan rafin ana kiransa da rafin tsamiya sakamakon wata narkekiyar bishiyar tsamiya da ke girke a tsakiyar rafin, shi wannan rafin yana daga can gefen sashen bayi kuma rafi ne mai hatsarin gaske. Ba a taɓa ganin ya ci mutum ba, sai dai duk wanda ya yi gangancin shiga cikinsa ranar juma'a, zai fito lafiya ƙalau daga cikinsa amma a ranar za a neme shi sama ko ƙasa a rasa. Wasu daga cikin mutanen gidan masarautar sun ce faɗan Bafulatana ne ya shafi rafin yayin da wasu suka ce alƙwarin babban sarkin Aljanin ruwa ne yake cika dalilin wata yarjejeniya da ke tsakaninsa da Sarki Muhammad Safwan wato Kakan Sarki Abdul'aziz na uku. Sarki Muhammad Safwan ya yi mulki kafin hawan Sarki Abdul'aziz da shekara ɗari da biyar, har zuwa wannan lokacin babu tsayayyiyar wannan magana. Sai dai duk mazaunin cikin masarauta ya kwana da sanin masarautarsu ta sha bambam da sauran masarautun da ke wannan nahiyar musamman a kan al'amura masu rikitarwa da ban mamaki.

Da sauri Baffajo ya sha gaban Kamalu cike da damuwa ya furta, "Kamalu hai ina za ka je ne, can ba ka ganin kududdufi ne?" Tsohon da ke riƙe da hannun Kamalu ya sakar masa murmushi haɗe da faɗin. "Tabbas sun kasance iyaye masu baka kulawa amma ka sani dakatarwarsu tamkar komawar cigabanka baya ne." Jin Kamalu ya yi shiru ya sa Inna wuro ta furta, "Kamalu ko wani abu yana damunka ne?" Girgiza kansa ya yi ya furta, "Inna wani ne ya ce na je cikin ƙoramar can." Ras! Gaban Inna wuro ya faɗi, tana shirin yin magana daga bayansu suka ji an furta.

"Tun wuri ku kama ɗanku idan ba haka ba wallahi matuƙar ya shiga cikin wancan rafin a yau sai dai nan gaba ki haifi wani." Uwar Bayi ta yi maganar cikin halin ko-in-kula. Take jikinsu ya ɗauki karkarwa, Kamalu na kai dubansa wurin tsohon ya ga ya tsuke fuska rai a ɓace ya furta. "Kai ba kamar kowa ba ne, jininka yana da bambamci da nasu don haka ba koma ne za ka riƙa bankaɗa musu sirrinka ba." Yana gama faɗar haka ya ɓace masa. A lokacin tuni Baffajo sun riƙe hannuwansa bibbiyu sun koma da shi cike da tsoro. Komawarsa babu jimawa Jawahir ta farfaɗo tana yin wata irin shaƙuwa mai ƙarfi, duk wanda yake wurin sai da jikinsa ya yi sanyi ganin halin da ƙanƙanuwar yarinya take ciki. A hankali take sauke numfashi, Mai gado ta sa ruwa da ɗankwalin kanta ta goge mata jinin fuskarta. Buɗe baki ta fara yi alamar tana buƙatar abinci, a nan ne kuma hankalin mai yankan kaba ya koma ga rina domin Mai gado ta manta sam da batun nonon da za ta bai wa Jawahir. Cikin damuwa ta kalli wata Dattijuwa.

"Baba don Allah ku taimaka mini ko da nonon akuya ne yarinyar nan shi nake bata." Kusan lokaci É—aya suka kalli juna a firgice, Uwar soro ta ce. "Baiwar Allah sai dai kam ki bata wani abin ba nono ba domin yau juma'a kuma duk ranar juma'a ba a shan nono a gidan duk wanda ya sha ya dinga aman nono har a zare ransa." Mai gado na jin haka ta rushe da kuka, don É—an kwanakin da ta yi da Jawahir ta shiga ranta sosai.

"To ke me ya sa bakya ba ta nono?" Mai soron baƙi ta sake wurga mata tambaya." Mai gado har za ta fallasa alaƙar da ke tsakaninsu da Jawahir sai kuma ta tuna da kalaman mahaifiyarta a lokacin da ta haife ta. "Tun lokacin da na haife ta babu ruwan nono a jikina, kafin zuwanmu nan har magani mun nema amma a banza kare ya sha tsamiya." Waɗannan kalaman na Mai gado suka ƙara dasa tausayin Jawahir a zuciyoyin mutanen da ke wurin, "Bakin da Allah ya tsaga na tabbata ba zai hana shi abinci ba, akwai baiwa Zinaru da ke shayarwa mai zai hana a roƙi alfarmar yau ɗaya ta shayar da ita?" Uwar tuwo ta furta. Zuciyar Mai gado ta yi ƙal ta ƙarasa wurin Baiwa Zinaru da ke goyon ɗanta mai kimanin shekara guda. Take Zinaru ta amsa ba ta musa ba, sai dai tana ɗaukar Jawahir ɗanta da ke gefenta ya ƙanƙame mahaifiyarsa yana tsanyare wa da matsanancin kuka haɗe da cusa kansa cikin jikin mahaifiyarsa. A lokacin babu wanda ya kawo komai a ransa don a tunaninsu ma kishine irin na yara yake yi don ya ga an ɗauki wata yarinyar, kai tsaye Zinaru ta rungume Jawahir ta fara shayar da ita, wani irin zuuu! Zinaru ta ji tamkar wacce aka kafa wa shocking har tsakiyar kanta. Ga wata irin zuƙa da take ji Jawahir na yi kamar za ta fige maman jikinta, suna nan tsaitsaye ruwan nono ya fara dawo wa Jawahir ta hanci da kunnuwanta. Wannan yanayin da ta shiga ya sake faɗar da gaban mutanen wurin, cikin masifa Jakadiya ta fara magana. "Wannan wacce irin masifa aka kawo mana saboda Allah, yarinyar tun da aka kawo ku sai faɗar mana da gaba kike yi." Mai gado jiki a sabule ta karɓi Jawahir ta fita zuwa bakin wata bishiya ta zauna cikin sarewa ta fara zubar da ƙwallah. Jawahir ta jima a haka sannan nonon da ke fita daga jikinta ya dakata da zuba, ba ta yi ƙasa a gwiwa ba ta sake goge mata haɗe da saka ta a baya ta goya ta. A ranar kusan kwanan zaune mai gado ta yi cike da rashin sabo da zaman baƙunta, uwa-uba rashin kyakkayawan makwancin saɓanin wanda suka saɓa kwana a ciki.

Cikin Dare.

Wata doguwar hanyar ya bi samɓal yana tafiya wacce babu komai sai dogayan bishiyu, tsawo da girmansu ya haddasa wa wurin duhu mai ban tsoro. Daga bayansa ya ji kamar ana bibiyarsa don haka ya yi saurin waigawa cikin tsoro da tashin hankali, wata baƙar mage mai ratsin fari ya gani tana tafe tana shinshina sawunsa. Tun bai yi wayo ba yake ƙaunar kyanwa don haka ya tsugunna da niyyar kai hannu kanta, da sauri ya ji an fisge shi gefe waɗansu surutai na tashi sama-sama a cikin kunnuwansa. Waigawa ya yi bai sake ganinta ba, ya ci gaba da tafiya. A jikin wata murgujejiyar bishiyar kuka ya hangi wata rantsatstsiyar karaga, "Je ka ƙarasa kan karagarka." Ya ji an furta masa. Wani irin sanyi ya ji yana ratsa shi, jiki a sanyaye ya fara takawa da niyyar hawa kan shimfiɗar da ke ɗauke da karagar, ga mamakinsa sai ji ya yi wannan baƙar magen ta hankaɗa shi gefe ɗaya. Ta ɗora wani mulmulallan abu mai kama da ƙawai a kan karagar, sannan ta fara zagaye karagar cikin ƙasaita. A can ƙasa ya faɗi kansa ya bugu da wani farin dutse take jini ya fara ɗiga, dafa wurin ya yi cikin azaba sai gani ya yi magen ta ƙaraso tana lasar jinin da ke zuba daga goshinsa. Ta fara ɗaga kanta tana da alamar tana son kai wa kansa farmaki wurin da ragowar jinin yake ɗiga. Ganin ta dumfaro shi ya sa ya ci gaba da ja baya zuciyarsa na dakan luguje, ganin haka ya sa magen ta fara wata irin dariya fiƙoƙinta na zubowa ƙasa ɗaya bayan ɗaya. Duk wurin da fiƙar ta faɗa sai ƙasar wurin ta rufta har ta yi tsalle za ta damƙi saman goshinsa. Firgigit Kamalu ya tashi cikin matsanancin tsoro, firgici da tashin hankali. A lokacin dare ya tsala sosai, ban da munsharin mutanen ɗakin da kukan tsuntsaye babu abin da yake tashi. Jin abu na gangaro masa a goshi ya sa ya kai hannunsa ga mamakinsa ya ji ya taɓa abu, da sauri ya yunƙura zuwa wurin aci-balbal ɗin da ke kunne a gefen ɗakin ya haske. Rass! Gabansa ya faɗi, jikinsa ya ɗauki karkarwa kamar mazari.

"Jini!" Ya furta a kiÉ—ime.

Yana shirin komawa ya tashi Baffajo ya sanar da shi abin da faru ya ji an dafa kafaÉ—arsa.

"Wannan gidan ba irin kowanne gida ba ne, sai ka ɗaura ɗamarar juriya da jajircewa. Gadon gidanku ba a sansu da sarewa ba, ka zama jarumi mara tsoro a haka ne za ka ƙwaci kanka. Ka gode wa Allah da ba ta yi nasarar yagar naman jikinka ba, kuma kada ka ɗauka za ta haƙuri. Wannan daɗɗaɗiyar mummunar manufa ca tunkafin haihuwarka, zan yi takaici ƙwarai matuƙar ta yi nasara a kanka kamar yadda ta ci galaba a kan mahaifiyar..." Sam Kamalu baya fahimtar kalaman da farin dattijon ke gaya masa, cike da damuwa ya katse shi. "Don Allah wane ne kai? Ya aka yi ka san mafarkin da na yi?" Murmushi Dattijon ya yi, "Yaro man kaza! Da sannu za ka fahimci turbar da nake son ɗora ka, izza da ƙasaitar jinin Sarki Muhammad Safwan ba za ta tashi a banza ba. Ba ni zan bayyana wa duniya waye kai ba, izza da tasirin jinin sarautar da ke jikinka ne zai bayyana wane ne kai. Ni Aminin Kakankakanka ne, ina bibiyar al'amarinka saboda waɗansu muhimman abubuwa da tasirinsu. Ta so mu je ka wanke ciwonka a wancan rafin, idan gari ya waye kada ka sanar da kowa mummunan mafarkinka hatta Baffajo da Inna wuro, domin wannan gidan sarautar cike yake da idanu mabanbanta."
Chapter 17 · 0% Book details