← Book details Shu'umar Masarauta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 27

Sashe 20

Shu'umar Masarauta Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Ka buɗe kunnenka da kyau ka saurari abin da Sha-kundum ta gaya min game da ku." Boka mai zamani ya faɗa fuska babu walawa. Shiru Sarki ya yi yana sauraron Boka. "Tabbas Sarauniyarmu Sha-kundum ta sake dawo wa kamar yadda ta faɗa a lokacin da numfashin zai ɗauke..." Baki na rawa Sarki ya katse boka da cewar, "A ina aka wanzar da ruhinta? A wane yanki ne mu sa a kawo mana ita? Idan ta kai bangon duniya na rantse da hatsabibanci Sarauniya da izzar mulkina sai na sa an ɗaukota a faɗin duniya." Boka ya bushe da wata irin mahaukaciyar dariya har yana birgima a ƙasa tamkar jakin da yake birgima a cikin sahara. Sarki sai da ya fusata ya doki ƙasa da tafin hannunsa sannan Boka mai zamani ya koma kan buzunsa  ya furta, "Haba Sarki Damina ai duk gaggawar ungozoma ta bari a haihu, haka duk mai niyyar yin sammako ya bari duhun dare ya gifta. Sarki Damina a kwai gaggarumar matsala, kamar yadda duk faɗin garin nan babu wanda ya taɓa gani ko jin sautin Sarauniya Sha-kundum sai ni, to tabbas a wannan karon ko ni ba ni da masaniyar a ɓangaren da wannan sabuwar sarauniyar take. Babban abin baƙincikin ma waɗanda suka sulwantar mana da ruhinta a cikinsu halitar Saruniya ta sake wanzuwa..." Tun bai ƙarasa magana ba jikin Sarki Balarabe ya fara rawa kamar wanda ake kaɗa wa gangi, a fusace ya miƙe tsaye yana huci tamkar kumurcin macijin da ke tsaka da fusata. A fusace ya furta, "Boka mai zamani ka na nufin Sarauniyarmu ta ɓullo daga cikin zuri'ar maharba da mafarauta ne?" Boka ya jinjina kai yana faɗin, "Ba harsashe ba ne Damina domin Sha-kundum ta tabbatar mini kuma kai shaida ne bata taɓa yin ƙarya, ta ba ni muhimmin saƙo gare ku na farautar Maharba a ko ina suke a faɗin duniya. Sai dai babban tashin hankalin ta yi alƙawarin ba za ta sake magana ba har sai na sada da ta da ainihin ruhinta. A sanyaye Sarki Damina ya furta, "Tirƙashi! Ana dara ga dare ya yi. Bayan wannan ina tafe akan buƙatar Yarima Nomau, babban boka lamarin ciwon yaron nan a kullin ƙara ta'azzara yake. A da muna haɗa shi da ƴan mata ɗaya zuwa biyu a rana amma yanzu har ta kai ga mata biyu ba sa iya gamsar da shi, kafi kowa sanin shi kaɗai na mallaka kuma har abada ba zan sake haihuwa ba. Idan na tuna ba ni da magaji lamarin na sake ɗugunzuma hankalina." Boka mai zamani ya hura ƙasar gabansa nan take wata ƴar ƙorama ta bayyana a wurin, sai da ya barbada wani garin magani sannan ya zura hannunsa ya warasu haɗe da runtse idanunsa tare da fara karanta waɗansu irin ɗalasuman tsafi, ƙirjin Sarki Damina ban da bugawa babu abin da yake yi saboda fargabar abin da Boka zai sanar da shi. Boka mai zamani ya jima a haka sannan ya buɗe idonsa yana kallon Sarki Damina haɗe da furta, "A kodayaushe maganar ɗaya ce! Kamar yadda na sanar maka Yarima Nomau ba zai taɓa warkewa ba matuƙar bai sadu da da inuwar wannan macen da nake gani a tattare da shi ba. Tabbas zai warke sai dai bazan taɓa ce maka ga wa'adin lokacin da zai ɗauka cikin wannan tuburewar ba. Na ga haske jingine da su daga inuwar yarinyar nan na ga akwai rabo a tsakani, sai dai ka fi kowa sanin yadda aka yi aka samu Yarima Nomau don haka idan har ya samu rabo da wannan yarinyar Ɗa ko Ƴar da za su haifa dole zai zama mallakin Babban dodo ne, idan ba haka ba duk daren daɗewa za su zama masifa a daular nan. Kuma wannan hasken ba komai yake bayyana mini ba illa kusantowar warakarsa, don na lura akwai yuwuwar samun waraka nan ba da jima wa ba." Ajiyar zuciya Sarki ya yi don tun da yake zuwa wannan kogon bai taɓa jin labarin da ya faranta ransa kamar na wanan ranar ba  Ya dubi Boka fuska ɗauke da murmushi ya furta, "Ya kai babban malamin madogararmu shin zan iya sanin wacece yarinyar nan kuma a wane yanki take?" Boka Mai zamani ya girgiza kai yana cewa, "Lamarin Yarima Nomau ya wuce duk yadda kake tsammani, daga ni har bokayen duniya babu wanda yake da wannan amsar don haka ina mai baka shawara kar ka wahalar da gangar jiki da ruhinka akan abin da babu takamaimar amsa. Wani hanzari ba gudu ba, daga bayan wannan inuwar na hango wata baƙar ƙura wacce ta lulluɓe sarararin samaniya sai dai ni kaina ban fahimci wacce irin ƙura ba ce koma dai wacce iri ce ina fatan za ta zame mana alkairi." Sarki Damina ya miƙe ya fara zagaye cikin kogon dutsen sai da ya zagaye boka mai zamani sannan ya ce, "Wannan ba zai zame mana matsala ba domin mun dogara da Sarauniya Sha-kundum da babban dodo na tabbata su za su kawo mana waraka a rayuwa. Yanzu wanne irin magani ta ba mu wanda za mu aiwatar mu da al'umnarmu?"

Boka mai zamani ya miƙe ya ƙarasa bakin rijiyar ya miƙa hannu ciki nan take ruwan cikinta ta kawo har sama sannan ya ɗebi ruwan da ƙoƙo ya miƙa wa Sarki Damina yana faɗin, "Wannan ruwan a je a zuba shi cikin kogon Ɗanbille duk wanda wannan annobar ta same shi ya ɗauka ya sha kai koda bata kama mutum ba zai iya wanka domin yin rigakafi. Wannan ce iya maganar da ta umarce ni na sanar da ku don haka za ka iya tafiya ya sarkin sarakunan duniya." Sanin ƙa'ida da dokar Sarauniya ya sa Sarki bai musa ba ya miƙe ba tare da ya furta koda kalma ɗaya ba, har ya je bakin ƙofa ya ji muryar Boka yana faɗin, "Ka da ka manta a kai wa Babban dodo Mai tsohon ciki biyu da idanun dattijai biyu." Gyaɗa kai kawai Sarki ya fice daga kogon dutsen.

Garin Dabur

   Daga cikin bukkar da nake kwance ina bacci na fara jin hayaniya sama-sama, ina yunƙuri tashin na ji muryar mahaifiyata ta karaɗe majiyar sautina da cewar, "Yau wacce baƙar rana muke gani da yammacin haka? Ya abar bauta kada ki yi fushi da wannan mummunan zunubin domin ba mu da sa hannu a ciki, ka hukunta masu wannan zunubin da gaggawa don sun cutar da ƴar tsintuwar da bata ji ba bata gani ba." Ihun da Kandala take jerawa ne ya sa ni fito wa saboda duk wanda ya ji kukan nata ya san ba na lafiya ba ne. Jikina ne ya ɗauki tsuma sakamakon ganin halin da take ciki kace-kace da jini, a gefe ɗaya mutane daga jinsin maza da mata sun yi carko-carko a kanta suna kallon halin da take ciki. A gabanta na tsugunna raina ya kai ƙololuwar ɓaci, na dube ta fuska babu walwala na furta "Waye ya yi miki haka Kadala?" Ilahirin jikinta rawa ya ke don haka na kama hannunta na haɗa su da nawa na sake furta, "Babu abin da zai faru da ke ki gaya min waye ya yi miki haka?" Cikin yanayin azaba ta furta, "Ban san sunansa ba amma na ji wasu suna ce masa Barde." Ban jira ragowar maganar ta ba saboda tun farkon ganin halin da take ciki shi ne mutum ba farko da ya fara faɗo min a rai, saboda sanin hali ya fi sanin kama. Barde riƙaƙƙen ɗan akuya ne baya iya kwana biyu ba tare da ya kusanci wala macen bil'adam ko dabba ba. 

Ina miƙe wa na riski muryar Goga ya fara fito yana busa ƙaho wanda yake alamtawa sauran ƴan uwa na nesa da na kusa akwai fita ta gaggawa. Kafin ya gama busar da yake tuni gidanmu ya cika damƙam da sauran ƴan uwa maharba da mafarauta kowanne yana tafe cikin shirin dawa, ɗaya bayan ɗaya na kalle su kowannen su yana jiran umarnin da zan bayar. Jin na yi shiru ya sa Goje  ya ɗaga gorarsa sama da hannun ɗaya, ɗayan hannun mai riƙe da kwari da baka ya sauke ya fara zabga mini kirari. "Burugu ce da kanta ba aike ba mace mai kamar maza ko cikin maza sai an tona. Cau cau cau cau ƙurungu mugun kifi sa'a a dawa sa'a a cikin gari wani aiki sai jan wuya makutsa daji, a lafiya uwar gidan kere amanar kura kyaci da gashi. Dawa dai, dawa gidan maza tsanani yana dajin Gurɓu ku bar faɗa musu wahalar sanar da su daɗin maza na cikin dawa mata na gida suna yin girki, wuya a dajin gwiɓau wuya a dajin fatalaki wuya ta ƙare a kan Barde yau ya taɓo ajalinsa." Ilahirin jikina ban da rawa babu abin da yake yi saboda tsumin da ya tayar min har nake jin da ace Barde na gabana babu abin da zai hana ban tsarge ruhinsa gida biyu ba, duk da kowa ya san Barde a cikin garinmu ba kanwar lasa ba ne.
Chapter 20 · 0% Book details