Sashe 26
Shu'umar Masarauta Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Fuskar abar bauta ce ta fasalta irin farincikin da ta yi da mu, don haka ta É—aga hannunta sama ta wara Æ´an yatsunta nan take wani mulmulallan haske ya dira a kai. Ta dube mu ta sake kallon haske sannan ta furta, "Albarkacin tsafi da sihiri, albarka da tabbata a gare ku ya ku wannan zuri'a ta mafarauta masu albarka. Shin akwai mai son a bincika gobensa don sanin abin da zai faru da shi? Akwai mai ciwo mu warkar da shi? Ko akwai mai son mu ninka nasara da tsaririn tsafinsa don ya gagari kowanne rauhani a dajin farauta?" Tun bata rufe baki ba mahaifina ya É—aga hannu sama, kasancewar mahaifina sarkin Maharbin yankinmu ya sa mutanen garinmu suke matuÆ™ar ba shi girma domin mutum ne mai adalci da son talakawansa. Ganin mahaifina ya yi magana ya sa alummar da ke wurin suka fara kai masa gaisuwa cikin girmamawa, "Sarki ya zo mutuwa ta zo, mutuwa mai kai Æ´an maza Æ™asa ko da son rai ko babu. Abar bauta ta riga da ta buÉ—a maka kwarankwatsa dubu sai ka gama lafiya amanar Æ™auran garin Dume, amana ta kai mana amana ta kai maka mun baka amana ka ba mu gaskiya ko sun Æ™i ko sun so sai mun bar wuya a dajin Gagarar maza. Sa'a dai maza sa'a dai uban dawa wuya mai sa Æ™arar kwana ga Æ™ananun maharba uban dawa sai ya kai labari ko da daÉ—i ko babu." Sunkuyar da kai Mahaifina ya yi alamar gaisuwar tana kai masa sannan ya É—ago ya amsa musu da cewar, "Dawa dai mazaje! Ba kyau ba daÉ—i, idan wuya ta yi wuya yaro ke guduwa ya bar babansa. Kwarankwatsa dubu ranar Talata mai zuwa sai na kai hallitun dawa dubu biyar da É—oriya É—an butar uwa, Abar bauta ta buÉ—e mana dai." A hankali muka riÆ™a takawa har kan tudun tsira sannan mahaifina ya tura ni daga gabansa kaÉ—an ya fara yi mata magana."Abar bauta ta yafe min kada ta yi fushi da ni a yau ma na sake dawowa da 'yata Kyauta domin ta shiga lamuranta. Æoyayyun al'amura na sake bayyana a tattare da ita, don haka na sake dawowa da ita don na ji ko akwai wani taimako da Abar bauta za ta yi domin Kyauta ta rinÆ™a rayuwa kamar kowa." Daga can duhu-duhun wurin da mutane ke tsaitsaye na hango wani matashin saurayi yana Æ™ara kutso kai sakamakon jin bayanin da Mahaifina ya yi, muna haÉ—a ido ya sakar mini murmushin da ban san dalilinsa ba, sai dai abin da ya É—aure min kai ba kasafai na cika tozali da matashin ba sai a ranaku makamantan waÉ—annan da muke kai wa Abar bauta kukanmu.Hasali ko kaÉ—an ba ya daga cikin zuri'armu domin gabaÉ—aya mun san kanmu waÉ—anda suke rayuwa a yankin. Ina cikin wannan tunanin na riski muryarta tana faÉ—in, "Akwai É“oyayyun lammura game da Kyauta don haka nake gagara bincika abin da yake damunta, a duk lokacin da na bincika gobenta ba na samun biyan buÆ™atata. A duk faÉ—in yankin nan babu wanda zan bincika rayuwarsa ta gaba na samu tangarda sai Kyauta, ina mai yi maka albishir da cewa ita É—in ta musamman ce don haka waÉ—ansu abubuwa suke baÆ™untar rayuwarta. Babban abin da za mu saka a gaba shi ne, mu mayar da hankali wurin zagaye garin nan domin idan muka zagaye gari na yi ammana da tsafi da sihiri babu abin da za same mu." Wurin ne ya yi tsit muna sauraron ci gaban bayanin da abar bauta take. Sai da ta sake hawa can Æ™ololuwar samman tsauninta sannan ta ci gaba da cewa, "Albarkacin ranar talata da nasarorin da ke cikinta muna miÆ™a wuya ga alÆ™aluman tsafi akan zan sanar da talakawa su nemi waÉ—annan kayan tsarin su aiwatar da shi domin neman warakar su. Da farko za ku saro kan wani Æ™asurgumin kumurcin maciji da ke Dajin Bawaya, sai ku kawo min na jiÆ™a shi da ruwan sihiri haÉ—e da tumfafiya, idan ya kwana É—aya a jiÆ™e sai a dake kan macijin ku samo mana ruwan kogin haladu a wanke idon matasan makafi a haÉ—a da Æ™asar kabarin Jarumi Baushe uban YaÉ—iya, idan kuka yi haka ku kawo min na haÉ—a sauran mahaÉ—in da kaina. Zan baku shi ku je ku zagaye garin nan da shi kuma duk abin da za ku gani kada baki ya furta ko zuciya ta tsorata, duka waÉ—annan abubuwan za a same su ne a cikin Æ™asa da kwana biyu." Duk da zuciyoyinmu sun fara karaya bai hana mun amsawa abar bauta ba, tana gama jawabin ta dafa raunin da ke jikina haÉ—e da É—aura min wata baÆ™ar fata wacce da alama ta baÆ™ar wahainiya ce. Nan take raunin jikina ya warke wani Æ™arfi ya ratsa ni tamkar wani abu bai taÉ“a faruwa da ni ba, daga haka ta sallame mu sannan kowa ya watse gidansa. Â
Sannu a hankali na rinƙa waige-waige don ganin na lalaubo matashin da nake ɗora zargi a kansa, amma sai haƙana ya gagara cim ma ruwa. Na neme shi sama da ƙasa na rasa! Dama na san za a rina wai an saci zanin mahaukaciya. A duk lokacin da na yi tozali da shi haka ce take faruwa don haka nake tunanin yana tattare da mummunar manufa game da yankinmu. Saboda na tabbata banza ba ta kai zomo kasuwa, kuma tamkar wanda yake wa rufa ido ban taɓa ji wani ya yi magana ko ƙorafi akansa ba. Kasancewar ba a ranar na saba ganin hallitun da ƴan uwana ba sa iya ganinsu ba ya sa na ja bakina na yi shiru, amma haka kawai jikina ya ba ni ziyararsa a gare mu ba alheri ba ce.
Matashin saurayin na barin wurin kai tsaye ya bi ta wata ɓarauniyar hanya da ke ƙarƙashin ƙasa, cike da fargaba ya rinƙa falfala gudu don yana tsoron tonuwar asirinsa musamman da ya tuna irin kallon zargin da Kyauta take yi masa. Sai da ya yi gudu mai nisa sannan ya isa wurin wasu rundunar dakarun mayaƙa, haki yake yi kamar ransa zai fita sannan ya sanar da su duk abin da ya ji game da yankin su Kyauta sannan ya ɗora da cewa, "Matsala dai ɗaya ce kamar yadda na gaya muku a baya, duk lokacin da na shiga yankin nan ba na iya ganin kowacce halita da idona face manyan dabbobi da ƙanana. Da taimkon Shugaba Usaina ta ba ni wani laƙani shi ne nake iya ganin yarinya ɗaya da idanuna kuma nake iya jin sautin abin bautarsu, ita ma a yadda na lura tana ganina sai dai ina tsoron kar asirinmu ya tonu." Shugaban Dakarun ne ya bushe da dariyar ƙeta sannan ya furta, "Ka gama aikinka don haka za ka iya tafiya ga Daularmu mai albarka, na tabbata idan muka kai wa Sarki wannan zuri'a ta Maharba sai ya yi mana ƙarin girma ya ɗaukaka darajarmu.
Runtse idonsa matashin ya yi tare da faɗin, "Shugaba Usaina! Shugaba Usaina." Nan take wani haske ya mamaye wurin babu jimawa ya ɓace ɓat. Gurfane yake a gabanta yana sauraron abin da za ta faɗa, sanin faɗin rai da izzarta ya sa ya ƙagara har ya ɗago don a tunaninsa ko ta bar wurin bai sani ba. Suna haɗa ido ya sauke kansa ƙa sa cikin girmamawa ya furta, "Sha kundum ta dafawa aikinki." Miƙewa ta yi ta fara taku ɗaiɗai ta rinƙa zagaye shi sannan ta furta, "Na saurari bayaninka don haka ina mai umartarka da ka iya bakinka idan ba haka ba sai na fisge rai daga gangar jikinka. Tabbas Boka mai zamani ya yi gaskiya Sha kundum ta sake bayyana a wannan yankin da kake min leƙen asiri sai dai babbar matsalar da har yau ya gagara bayyanar da suffar yarinyar. In dai ina numfashi Sarki Damina ba zai taɓa samun cikar burinsa na jininsa ya gaji karagar mulkinsa ba, na yi rantsuwa da abar bauta sai dai zuri'arsa ta ƙare a wahale yana ji yana gani zan gina Daular nan da jinin da ba na shi ba." Ta kai ƙarshen maganarta a tsawace kamar wacce aka ɓata wa rai, a razane matashin ya gyaɗa kai yana shirin sake magana ta katse shi da cewar, "Fitar da sirrina tamkar ka sanya takobi ka datse rayuwar da kake ciki ne, ka kiyaye idan ba haka ba wankin hula zai iya kai ka dare." Godiya ya yi mata sannan ya tashi zai fita ta sake katse shi da cewar, "Ka tabbatar da ka bawa yarima mugunyar ruwan sihiri a daren nan kafin wayewar gari." Amsa mata ya yi cikin ladabi sannan ya fice daga ɓangarenta.