← Book details Shu'umar Masarauta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 27

Sashe 12

Shu'umar Masarauta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fulani Babba da sauri ta ƙarasa gaban Abubakar ta sa hannu cike da ƙunan rai ta ɗauke fuskarsa da mari, wannan ne karo na farko da ta taɓa sanya hannu a jikinsa da sunan duka. Zafin marin ya ratsa shi hakan ya sa ya ƙarasa cizge kitson kan Ruƙayya da ke bakinsa, sai kuma ya fashe da kuka yana gwara kansa da ƙasa. Cikin azaba ta sake ƙwalla ƙara take numfashinta ya ɗauke ta sume a wurin. Tamkar mayuwancin zakin da ya samu nama haka Abubakar ya tura sillin jelar kitson kan Ruƙayya da ya cizge cikin bakinsa ya fara tauna kafin wani lokaci ya haɗiye shi gabaɗaya. A firgice Fulani Babba ta shiga yayyafa wa Ruƙayya ruwa ta jima a kanta sannan ta sauke ajiyar zuciya a galabaice, ganin ta buɗe ido ya sa Fulani Babba ta ji farinciki har cikin ranta sai dai kuma wurin da ya ɗaye mata kitson tuni gefen kan ya kumbura suntum. Wani irin sara ta ji kan yana yi mata a daddafe ta iya miƙewa ganin haka ya sa Fulani ta ba wa Bayin da ke gefe umarnin su ɗauke ta zuwa cikin turakarta. Duk dauriya irin ta Ruƙayya sai da ta dinga zubda ƙwalla sakamakon yadda take jin kanta na sara mata kamar zai tsage gida biyu. Duk yadda Fulani babba ta so zaman Ruƙayya a ɗakin zuwa lokacin da zugin zai sarara mata fir ta ƙi yarda, don haka ta sake saka Bayi suka ɗauke ta tana gaba suna biye da ita a baya har cikin sashen Fulani Umaima.

Ganin a halin da aka shiga da Ruƙayya ya sa Fulani Umaima miƙewa zumbur! Bakinta har rawa yake ta furta. "Me ya faru da ita?"

"Laifi ne yayanta Sadik ya yi mata, wallahi tsatsayi ne Fulani don haka na zo da kaina ba saƙo ba..."

"Dakata Fulani! Hawainiyarki ta kiyayi ramata. Ba tun yau ba na lura da take-takenki dangane da kiranyen da kika yi wa Ruƙayya. Lokaci ɗaya kin sa an lashe kurwar yarinya ba ta ƙaunar zaman wurin mahaifiyarta, wannan fa ba shi ne karo na farko na ji labarin wancen shagirigirbau ɗin ya maƙure ta yana yi mata ƙamshin mutuwa ba. Amma an yi ta yanke ta gille, wannan shi ne karo na farko kuma na ƙarshe da zai sake taɓa kowanne bil'adama a sashenki." Fulani Umaima ta ƙarasa maganar tana kai kallonta wurin bayin da ke riƙe da Ruƙƙaya. "A samu Jakadiya ta gaggauta sanar da Mai martaba ina buƙatar ƙwararrun masu magani, don ban san dafin da haƙoransa suke ɗauke da shi ba." Da sauri suka shimfiɗar da ita suka fice, Fulani Babba ta ƙarasa gabanta ido cike da ƙwalla ta furta. "Wallahi ko a mafarki ban taɓa jin Ruƙayya ba 'yata ba ce, tamkar yadda na ɗauki su Khadija haka nake jin ta, ta ya ina sane zan bari Abubakar ya illatata." Sai da Fulani Umaima ta saki murmushin takaici ta furta, "Me ya sa bai kama Khadija ko Sakina ya illata ba, saboda kina baƙincikin kin haifi sauna, wawa, shashasha shi ne ni ma kike burin ƙarfi da yaji na rasa waɗannan biyun da Allah ya ba ni." Tsoron hukuncin da Fulani Umaima za ta yanke ya sake mamaye Fulani babba, ta tsugunna bisa gwiwoyinta don ta san kome Fulani ta gaya wa Takawa hawa yake ya zauna ɗaram. Ba tun yanzu ba ta jima da dawowa daga rakiyarta, don ta lura sai abin da Fulani Umaima take so Takawa yake zartarwa.

"Tabbas Abubakar bai kyauta ba amma ki dubi girman Allah ki yi haƙuri..."
"Idan ba ki yi gaggawar fita daga sashena ba wallahi sai na shayar da ke ruwan mamaki." Fulani Umaima na gama magana ta yi ciki cike da zafin rai. Fulani babba ta sunkuyar da kanta ƙasa tana zubar da ƙwalla, dama ya ya lafiyar kura ballantana ta yi zawo. Gari banza ma Takawa ba ƙaunar Abubakar yake ba ina ga an ce ya taɓa 'ya'yan gaban goshi. Cike da zullimi ta fara yunƙurin tashi, daga bayanta ta hangi Muhsin na zaune yana aika mata da saƙon harara cikin kallon tsana. A haka ta ƙarasa sashenta gwiwoyinta a sanyaye, ta windo ta leƙa Abubukar da ke zaune yawu na dalala. Sai a lokacin ta samu damar fashe wa da matsanancin kuka duk da tana da tabbacin bayin da ke zagaye da ita suna sauraronta.

"Ya Allah ba don ba ka so ko ƙaunata ka jarabce ni da wannan bawa Naka ba, Ya Ubangiji ina godiya bisa baiwa da wannan ni'imar da ka yi mini domin dubbunaina na buƙatar ko da makamancinsa ne. Ya Allah idan rayuwar wannan bawa naka mai tsayi ce Ubangiji ka yalwace shi da lafiyar ya zama kamar kowa, saɓanin halin da yake ciki. Idan kuma mai gajeren kwana ne Ubangiji ka gaggauta ɗaukar kwanakinsa ko na samu salama a rayuwata..." Kukan da ya ci ƙarfinta ne ya datse ragowar kalamanta.

"Allah ya sanyaya zuciyar uwar ɗakina Ubangiji ya ƙara wa Yarima lafiya." Baiwa Zainaba ta furta jiki a sanyaye kamar kazar da tono wuƙa.

"Zainaba na ɗauka ko kowa zai furta son ransa ke mai faɗa mini gaskiyar abin da ke cikin zuciyarki ne? A haka kike kiran Abubakar da Yarima kina ga ko a mafarki za a damƙa wa Abubakar karagar mulki ne." Tabbas kalaman Fulani Babba a turba suke domin kowa ya san halin da Abubakar yake ciki kuma ko a garin gaɓa-gaɓa babu wanda zai damƙa masa kujerar sarauta, ina ya san kansa ma balle ya san matsalolin talakawa? Sai da ta ƙara rissinawa ta furta. "Tuba nake ranki shi daɗe, In shaa Allahu Allah zai ba shi lafiya." Fulani babba ta amsa mata sannan ta wuce cikin sashenta.

Ganin har zuwa dare babu wani saƙo ya sa Fulani babba ta ɗan fara sakin zuciyarta, har ta zauna su Khadija na soko mata hira wani ta amsa musu wani kuma ta yi musu shiru. Suna cikin wannan yanayin Jakadiya ta iso da kiran da Maimartaba yake yi mata. Take ƙirjinta ya buga dum! Zuciyarta kamar za ta yi tsalle ta fito daga ƙirjinta, da ƙyar ta tattaro jarumtar haɗa kalmomin da ta iya furta wa Jakadiya. A gurguje ta watsa ruwa ta ɗan gyara jikinta, don saboda yadda lalurar fitsarin da yi mata kamun kazar kuku har ji take haka kawai kamar zarni na tashi a jikinta. Da kwalliyarta fes ta ƙarasa turakar Mai martaba ƙamshi na tashi, haka kawai wani lokacin yake jin kamar yana tauye haƙƙinta ko yana yi mata ba daidai ba, musamman yadda ya ga ta fige ta lalace kamar ba ita ba.

"Barka da hutawa Sarkina." Kalamanta ya ji na sauka a kunnuwansa, wani ɗaci ya ziyarci zuciyarsa kamar wanda ya haɗiyi maɗaci. "Barka!" Daga haka shiru ya biyo baya, ganin yanayin tarbar da Mai martaba ya yi mata ya sa jikinta ya yi sanyi. Cikin sanyin murya ta furta. "Allah ya taimake ka na ji saƙon kana son ganina."

"Wani hukunci muka yanke da muke ganin shi ne mafi alfanu babu cuta babu cutarwa." Mai martaba ya faɗa fuska a haɗe kamar dafaffan kwanannan kunun tsamiya. Ƙirjinta ya hau dakan lugude, gumi ya fara keto mata ta ko ina.

"Don haka ba ma buƙatar jayayya. Abubakar Sadiq zai koma ɗaya daga cikin ɗakunan gidan ajiya da gyaran hali, na sa a ware masa ɗaki guda wanda zai zauna a ciki, idan ya so duk wani abu da yake buƙata a aiwatar masa a can. Mun yanke wannan hukuncin ne domin sama wa lafiyayyun gidan nan mafita, idan yau ya nemi nasaka wannan jibi wancan watarana ina tunanin kaina zai dawo." Kafin dirar kalaman Takawa tuni hawaye ya gama wanke fuskarta. Cikin kuka ta zube a ƙasa hannuwanta biyu a saman cinyarsa ta furta. "Don Allah kada ka yi mini haka ranka shi daɗe, Allah ya sani Abubakar ba shi kaɗai na haifa ba akwai yayyansa Khadija da Zainab amma wallahi babu wanda na ke jin ƙaunarsa har a cikin jinina kamarsa. Wannan ƙasƙanci ne a ce jininka zai ƙare rayuwa a gidan ajiya da gyaran hali saboda ya kasance mai nakasa, in dai a kan Ruƙayya ne na yi maka alƙawari ko inuwarsa ba za ta ƙara gani ba ballanta shi. Don Allah ka..."

Cikin tsawa ya katse ta. "Ba mu san lokacin da raini ya gifta a tsakaninmu ba Fulani, da har ake neman yin jayayya da mu. Mu ba ƙananan mutane ba ne sanin kanki ne ba tun yau ba; ba ma taɓa magana biyu. Tashi ki ba mu wuri, wannan hukuncin ba zai tɓa canzawa ba." Fulani babba duk yadda ta so dakatar da hawayenta abin ya gagara, don haka ta fice daga turakar zuciyarta na tuƙuƙin ɓacin rai. Tana shiga ɗaki ta fashe da wani irin matsanancin kuka, ganin kukan na ta ba na ƙare ba ne ya sa su Khadija rungume ta suka fashe da matsanancin kuka! Yau ita ce rana ta farko da ta ji zama a cikin gidan ya gama fita daga ranta, ta kuma ji wani abu ya tokare mata maƙoshi game da Fulani Umaima sai dai kuma a ɓangare ɗaya shakka da tsoronta ya hana zuciyarta sanar da ita gaskiyar abin da ke ranta. Sun jima ita da yaran a haka sannan ta miƙe ta nufi ɗakin Abubakar, ta same shi a kwance kamar yadda ta barci. Sai da ta share ƙwallah sannan fito daga ɗakin.

Washegari tun safe Dogarawa suka cika umarnin Mai martaba, tun lokacin da aka fara jidar kayan Abubakar Fulani Babba take share hawaye don dai ba ta da yadda za ta yi.

"Idan kika matsa mana da magana wallahi ranki zai yi mummunan ɓacin da ba ki taɓa gani ba Fatima." A razane ta dubi Mai martaba, yanayinsa kaɗai ya tabbatar mata babu alamar wasa a tattare da shi. Dole ƙanwar na ƙi ta zubar da makamanta, ta rungumi ƙaddarar da ta afka musu babu sallama.
Chapter 12 · 0% Book details