Sashe 9
Sanadin Kenan Part 4 Complete Hausa Novel · about 11 min read
****
Watarana Amina na gyaran tsofaffin takardun ta na makarantar sakandire wani karamin littafi ya fado, ta dauka ta goge shi tana dubawa, a ciki ta ga lambar waya a kasa an rubuta Hafsa Datti. A take ta tuno kawarta ta makaranta Hafsa. Murmushi tayi tareda yin hamdala ta roki Allah ya sa ta samu Hafsa a wannan lambar wayar, bazata taba mancewa da Hafsa ba, ta dade tana fado mata a rai batasan ya zatayi ta riske ta ba, abinda ta sani kawai shine a Abuja take. Da gudu ta dauko wayarta ta shigar da lambobin.
Sai da ta gama abincin ranan His Excellency ta shirya komai a inda yake cin abincin tayi wanka ta kintsa a lokacin bai dawo daga office ba ta harde a hakimar kujerar falon ta ta soma kiran lambar.
Kira na daya, na biyu ta ji lambar ta shiga, ta fara ruri. Addua kawai take Allah ya hada ta da Hafsa Datti a wannan gabar na rayuwarta. Wata mutum daya cikin masoyan ta na hakika da bazata manta gudummuwar da suka bata a rayuwarta ba. Sannan tana bukatar aboki bayan yan uwa da dangi, aboki saanta wanda zata ke tattauna wasu alamuran dashi bayan Goggo.
Assalamu Alaykum.
Taji muryar wata kamilalliyar dattijuwa ta amsa.
Amin waalaikumus-salam . Ina yi ni?
lafiya lau yammata, daga ina? Ban dau muryar ba kuma bansan lambar ba.
Sunana Amina Masud, daga Bauchi nake magana, ni kawar Hafsa ce da mukayi makarantar sakandire tare. Don Allah ko zan iya samun magana da ita?
Allah sarki, Amina ke ce! Yau Allah ya hada Hafsa da Aminar ta. Kullum tana zancen ki, tana rokon Alla ya sada ku watarana kun rabu ba tareda karbar adireshin juna ba kullum cikin zancen take. Allah Rahim, ni mahaifiyarta ce, zan turo miki lambarta yanzu. Bata kasar nan tana aure a kasar Russia. Yanzu na gama magana da ita.
Amina tayi godiya sosai dadi fal ranta.
A take maman ta turo mata lambar Hafsa ta kasar Russia. Amina ta kira Hafsa Sunana Dr. Amina Masud Shira.
Tsalle Hafsa tayi ta dire akan mijinta. Amina! Dr. Amina? Ashe Allah ya cika buri?
Ya cika Hafsa. Im a proffessional physiotherapist, married to Maarouf Ji-Kas.
Maarouf Ji-kas wanne? Hafsa ta tambaya cikin mamaki. Murmushi Amina ta yi, ta daga ido tana kallon sa yana shigowa, idanunsu suka sarke dana juna bayan ya zare farin gilashin sa. Babbar rigarshi ya cire ya jefeta da shi ya wuce bedroomyana fadinnaji ana cewa Maarouf Ji-kas, ke da waye? murmushi tayi, tace wanda kika sani, I think shikadai ne me wannan sunan a Arewa. Yaya bayan saduwa? Mama ta gayamin kina Russia. Yaranki nawa? Don nasan bakya son karatu, Hafsa tayi ajiyar zuciya. Amina, tun farko na fahimci ke yar baiwa ce kuma mai saa a rayuwa, kina daga cikin mutanen dake cimma burirrikan rayuwarsu yadda sukayi fata. Na jinjina miki, na kuma sara miki ta yadda kika yi nasarar auren mutum irin Maarouf Habibu Ji-kas. Na sanshi a jaridu tun yana dan majalisa, na san sanda matarsa tayi accident ta rasu ta barshi da ya ba lafiya. Kada dai ince SANADIN KENAN?
Bakin Amina dai ya kasa rabo da murmushin SANADIN KENAN Hafsa, paralysed Amina. Kuma alhamdulillah ta samu lafiya. Baki bani amsar tambayoyi na ba.
Hafsa ta yi murmushi Eh, karatu kam bana son sa amma Baban Iman bai kyaleni ba saida nayi shi anan Russia na karanta (education) yanzun haka (lecturing) nake university din dana yi. Shi maaikacin embassy ne kwanannan zamuzo hutu zan iskoki a Bauchi insha Allah idan zamu samu ganin Her Excellency da sauki Ta karashe cikin dariya. Amina tace Hafsa ho! Kina nan yadda na sanki. Nace yarana nawa? Hafsa ta yi murmushi Iman, Imam da Amina, nayi miki takwara don kar in manta dake. Hawayen kauna suka cicciko idanun Amina.
Bansan kin dauke ni da muhimmanci har haka ba Hafsa da ban kai wannan lokacin ban binciko ki ba ko da da taimakon Yallabai ne. Nagode Hafsa, ki shafa min kansu, ina duban hanyar ku zuwa Bauchi, gaisuwa ta musamman ga Mahmoud.
A bedroom ta iske shi ya fito daga wanka kenan ruwa yana bin fresh fatar jikinsa. Kafin Maarouf ya juyo sai yaji Amina ta rungume shi ta baya. Sosai take cikin farin cikin da ya dade bai ganta ciki ba, sai ya taya ta farin cikin ta hanyar datafi kowacce sanya farin cikin. Sun farantawa juna yadda ya kamata da soyayya mai tsayawa a zuci. Suna kwance take bashi labarin samun Hafsa, ga mamakinta sai taga ya dakata yana yi mata kallo na rashin gamsuwa da labarin nata.
Amina bana son ki da kawa, bana so.
Gaban Amina ya fadi meyasa Maarouf?
“Abinda nakeso ki tambaye ni kenan. Muna zaman mu lafiya nida ke, banida matsala dake ta kowanne fanni haka kema, in ma akwai muna tattauna ta a junanmu mu magance ta ba tareda kowa ya ji ba, amma kinyi aminiya duk sirrin aurenmu zai zama a kunnenta. Kada ki dauka wayon ku daya ita budadden ido gareta tarbiyyar turai, ina tsoron ta canza maki tunani.
Amina ta kwantar da kai bisa kirjin mijinta jikinta yayi sanyi.
believe me Maarouf Hafsa ta gari ce, ba yau na santa ba. Amma ka fada min abinda zan kiyaye a kawancena da ita insha Allah zan kiyaye.
kinyi alkawari?
wallahi nayi, in ma kace in rabu da ita kwata-kwata zan yi hakan amma zan kasance cikin kewar ta.
Murmushi yayi wato dai bazaki iya rabuwa da ita din ba kenan shine zaki yimin wayo, irin wayon ku na likitoci da kikayo course wajen su Turaki.
murmushi tayi mai sauti ni kam na rasa me Baban nan nawa yake maka daka sako shi gaba, don baka san yadda yake son ka ba, ga yi maka campaign a fakaice, ga wanke laifin ka, ga-ga...... alherin Turaki mai yawa ne akan ka.
Dariya ta bashi sosai ya bubbugi bayanta kin ganki! To shikenan, albarkacin ki an daga kujerarsa daga yau daga matsayin commissioner zuwa na SSG. Kuma ke zakiyi masa wannan albishir din.Wata sumba da Amina tayi super ta mannawa Maarouf dinta,ta tabbatar masa tafi malamin nata godewa. Saboda kunyarta mai yawa ce,sau-tari sai ta kai zuciya nesa take iya kissing dinsa.
Bata bashi bashi damar yin commenting ba domin ta rufe bakinsa gabadaya da tausasan labbanta. Sai a washegari ne da yake cikin nutsuwar sa yayi mata conclusion na zancen Hafsa Datti. Yace ya amince suyi kawancen su amma, bai yarda ba bai amince ba,not in anyway, tayi zancen sa kowanne iri ne da Hafsa. Su cigaba da magance abinda ya shafe su a tsakaninsu yadda suka faro. Ko Goggo ta zama thirdparty. Amina ta amince da umarnin mijinta,ko dama can kullum cikin umarnin sa take. Zata iya sadaukar da komai akan Maarouf Jikas. Wani kwayan mutum guda daya da ruhinta ke so, zuciyarta ke kauna, gangar jikinta ke bege.
Allah kuma ya dauko yaya bata ba tareda tsimi ko dabararta ba. Yaya kuwa zaayi bazata zamto mai biyayya ga umarninsa ba? Da son duk abinda yake so tana so ko bata so,in cewa yayi ta gutsuro masa naman jikinta, shell do so willingly, without feeling any hurt,balle wannan kankanuwar biyayya? Wadda ko da bai fada ba ai tanada hankalin kanta. A abubuwa da dama sunna da raayi daya.Itama ba mai raayin hakan bace. Bazata taba iyatona sirrin sa ga kowa ba koda kuwa ga GOGGON data haife ta. Don haka da gudu ta amince da sharadin sa akan alaqarta da Hafsa Datti.
Da safe kafin ya fita suna karya kumallo, a bisa dining-table mara tsayisosaisuke zaune na zallar gilashi (raw glass) kowanne kujerarsa daban tana fuskantar ta dan uwansa, amma can a karkashin table din kafafunsu harde suke dana juna.Ya dauki wayarsa dake gefe ya kira Turaki. Amina na jin sanda Dr. Turaki yace breakfast nakeyi Yaa Maulaya yanzu zan fito, ai takwas din bata idasa cika ba ni bani na kira ka ba, ina sane sai 8:30 zamu fito. yar ka ke son magana da kai Ya mikawa Amina.
Murmushi tayi sosai ta karba Assalamu Alaykum my humble consultant amin waalaikumus-salam a daughter like no other, mun tashi lafiya? sai godiyar Allah! Yaa Maulaya ne yace inyi albishir da sabuwar kujera ta SSG. Zaayi taron kaddamar da kujerar rana ita yau. Allah ya taya ku riko bakidaya. Bata tsaya taji reaction dinsa ba ta mikawa Maarouf wayar. Tana ji Maarouf na cewa to menene abin kuka? You deserve it ne. What are friends for? Beside, kai ne SANADIN haduwa ta da alkahairin dana ke tare dashi a yanzu. Kai ka tsaya da hikimarka da zuciyarka daya saida na mallake ta, na samu kwanciyar hankali kuma kuka samu. Zan iya hakura da kujerar bakidaya na bar maka na zama mataimakin ka in ana yin hakan. Im rest assured zaka shugabanci alumma da gaskiya da amana. Don haka naga ba kujerar data kamace ka sai ta SSG. Daga ni har ita bamu cancanci godiyar ka ba.
Ya kashe wayar sa.
Da wannan amina da Hafsa suka cigaba da zumuncin su ba dare ba rana, zumunci mai tsafta da sanin ciwon kai. Amina na lallaba Hafsa ta koma makaranta ta yo Doctorate Degree ranar da suka dawo gida Nigeria zaiyi mata amfani. Hafsa na kara koyar da ita dabarun sace zuciyar miji ta hanyoyi masu kyau da maana. Ta bar ganin Maarouf baida raayin aure-aure komai dalili takeyi don haka ta tsaya ta kafa kanta yadda ya kamata yadda ko wata ta shigo saidai ta biyo bayanta.
Dr. Zainab Turaki ta kira Amina karo na farko da suka taba gaisawa tayi mata godiya akan kujerar Dr. Turaki. Ta bawa manyan yayanta maza biyu Aadil da Aabid wayar sunyi mata godiya. Amina taji dadi sosai, da wannan sabo ya fara shiga tsakaninsu suke gaisawa sosai don Zainab ta iya takunta bata zaqewa, respect ne da girmamawa tsakaninta da Amina kawai.
Anyi liyafar kaddamar da kujerar SSG, taro na farko na siyasa da Amina ta halarta, suka dumfaro dakin taron itada maigidan ta His Excellency Maarouf Habibu Ji-kas. Tana sanye da kyakkyawar doguwar riga ruwan makuba kirar Dammam ta zagaye fuskarta da mayafin abayar. Takalmin kafarta mai tsayi sosai, ta kama hannun Maarouf ta rike na rashin sabo. Kowa ya mike tsaye don nuna girmamawa yayin da suka shigo dakin taron na ( ) saida suka zauna sannan kowa ya zauna. Ga Gwamnan da maidakinsa Dr. Amina nanike dashi, ga mataimakinsa Prof. Bugaje da mai dakinsaZarah, sannan maigirma SSG da mai dakinsa Dr. Zainab da yaran su biyu. A haka aka fara gudanar da liyafar yadda aka tsara bayan mai gabatarwa ya gabatar da abinda ya tara su.
Anyi vedio anyi hotuna iri-iri, yan jarida sun samu babban (cover story) yau kowa ya ga matar Ji-kas da yake boyewaba Laila Ji-kas ba. Kowa kuma ya bude baki sai masha-Allah. A haka taron ya tashi.
Litinin na zagayowa Dr. Usman Turaki ya shiga sabon ofishinsa. Suka cigaba da gudanar da administration dinsu cikin ilmi da sanin makamar mulki. Talakawa na gamsuwa domin babu handama da cikin mulkinsu sai tsananin jin kai ga alummar su da bullo da hanyoyin kyautata musu. Kullum tunanin su shine, ta yaya zasu kyautata rayuwar alummar jihar su a fannonin rayuwa daban-daban? Ta yaya zasu ciyar da matasa gaba don sune shuwagabannin gobe. Ta yaya alummar karkara zasuji dadin rayuwarsu acan inda suke ba tareda gudowa maraya ba? Ta yaya zaa inganta lafiyar kananan yara daga ciwuwwukan zamani da suka addabe su? Ta yaya zaa samar da ingantattun mgunguna kyauta ga asibitocin gwamnati? Ta yaya malamin makaranta zaiji dadi ya san babu career mai daraja da kima irin tasa? Ta yaya? Ta yaya? Ta yaya Bauchi zata kere sauran jihohin arewacin Nigeria saanninta a fannonin ilmi, kiwon lafiya, infrastructure, aikin yi (employment) sanaoin dogara da kaida sauran alamuran cigaban rayuwa.
Sunan Jikas na kara yin fice a tsakanin gwamnonin Nigeria yan uwansa. He is ranked asthe best governor inthe North on initiating stabilisation and developmentdaga shugaban kasa na lokacin wanda suke karkashin jamiyya daya.
Anyi wannan taron karramawar a birnin tarayya Abuja inda shugaban kasa ya karrama shi, yayi kira ga gwamnonin arewa dana kudu yan jamiyyarsu (Northern People Congress) da aka fi sani da (NPC)kan suyi koyi dashi a hadu a ciyar da Nigeria gaba, jamiyyar su ta kara karbuwa a wurin alumma duk da cewa itace kan gaba.
Amina ta halarci wannan taron karramawar, karkashin rakiyar Hafsa da mai gidanta Mahmoud wadanda suka kawo mata ziyara daidai lokacin daga birnin Belarus din kasar Russia.Tana gefen damansa inda duk ya sanya kafa nan take mayar da tata. Ta shiga cikin jerin matan gwamnonin Nigeria dake karkashin (Northern People Congress). Dukkansu kuma tafi su zati da ilhama wanda tsarkin riko da addini ke haifarwa mai shi. Sannan kuma jikinta a lullube cikin abayat kirar Oman kai kace daga can tazo ba don kalar fatar jikinta ba.
Lokacin da Ilya ya murdo wa Goggo da Kaka abinda ke faruwa a Birnin Tarayya daidai wannan lokacin (live) a makekiyar plasma din falon Goggon, Goggo Hauwa ta gane Aminanta ce can kusa da matar shugaban kasa, ga Maarouf kamar ya maida ita ciki don kulawa, ya kasa boyewa duniya soyayyar da yake yi mata sabida tsohon cikin dake tareda ita, sai tasa kuka tana yi tana karawa tana yiwa Allah godiya.Kaka da Ilya na rarrashin ta. Ilya na fadin; dariya ai zakiyi Goggo ba kuka ba, kece SANADI. Shi kansa Ilyafarin-ciki kamar yayi yaya. A ganin Hajiya Hawwa, wani farin cikin yafi gaban ayi masa murmushi ko dariya, sai dai kukan. .....Alhamdulillah Alaa niimatihi. Shine abinda Goggo ke ambato har ba adadi.
*****