← Book details Sanadin Kenan Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 13

Sashe 11

Sanadin Kenan Part 4 Complete Hausa Novel · about 6 min read

****
An daura auren Laila da Mahdi ranar wata asabar. Da sati ya zagayo ta yi walima ta tare a gidansa da ke cikin garin Dutse. Kudin da Maarouf ya ba ta da su ta yi amfani ta yi wa kanta komai ta kuma taimaka wa Mahdi ya kara gyara gidan ya fito fes! Ta sayi mota ta ja jari ta koma makarantar da Maarouf ke ta goranta mata. Komai na Maarouf ya zama bygone a gare ta, ba ta ko son tuno rayuwarsu ta baya, ta dumfari sabuwar rayuwarta da ikhlasi.

****
Hannunta kawai yake ja har zuwa falo na karshe, wanda daga shi za su tadda motocin da zasu shiga da masu mara musu baya. A nan ne ta daddage ta kwace hannunta ganin ba shi da damuwa don maaikatansa sun gansu a hakan. Wani irin kallo ya bi ta da shi wanda ita kadai ta san maanar sa.
Ya lura a cike take idanunta sun juye kamar ba ita ba. Wannan balai har ina? Yana zaman-zamansa ta daukeshi ta kaishi yanzu kuma zata yi masaprotestmara dalili, shi meye laifinsa?
Bayan fitowarsa daga wajen Laila yazo ya sametadon su tafi inda yace zasu tafi, budar bakinta sai cewa tayi ita ba inda zata, su tafi shi da Anty Lailah.
Da farko abin haushi ya bashi sai kuma ya koma bashi dariya. Ya fincikota yana fadin wallahi sai kin je, bana niyyar fita in fasa kan wani abu marasa tushe da madafa. Shine ya janyo ta tana turjewa amma karfin ba daya ba, a haka suka fito. Inda ta gode Allah basu hadu da kowanne maaikaci ba.
Suka fada mota yana dama tana hagu, mai tsaron lafiyarsa a gaba (securities) suka biyo su a baya. Sai da suka dauki hanyar barin gari ta ji ya ce da direban Shira za su je.
Suna tafe ba mai magana da dan uwansa, hadiyar zuciya kawai takeyi alhalin ba kuka tayi ba. Yayi banza da ita yana amfani da wayar hannunsa har suka isa.
A can bayan gari tsakiyar gonaki Amina ta ga an yi parking a daidai wani katon gate. Motocin suka tsaya, a nan duk suka firfito. Sanye ta ke cikin riga da zani na atamfa ta yi lullubi da wadataccen mayafi launin adon atamfar jikinta. Ta yi kyau kamar koyaushe. Don ita ba sai ta bata lokaci wajen yin kwalliya ba, kullum kyakkyawa ce ahalittar Ubangiji mara yawan kyalekyale. Kowanne kalar kaya ta sanya karbarta suke su amsheta su dace da zubin halittarta. Physiotherapist Amina Masud kenan.
Masu gadin gidan suka bude wawakeken gate din. Nan Amina ta yi arba da kasaitaccen gidan gona na kiwon tsuntsayen gida, amma tantabaru farare sun fi yawa. Bude baki ta yi tana kallonsa bakinta kamar zai tsage, ya wani kawar da fuska ya tamke ta, ta karasa inda yake ta manta ba su kadai bane ta kamo hannunsa, ta russuna saitin kunensa tace Maarouf Jikas! Im dying for you, my heart is itching da tamkewar fuskarka. Waiwayawa yayi da sauri don ba ahankali ta fada ba, babu wanda hankalinsa yake kansu cikin yan rakiyar nasu sun yi gefe sun samar da space sosai a tsakaninsu. Yayi ajiyar zuciya. Kai wannan yarinyar sai a barta. Ya kwace hannunsa ta kara rikowa ..... na tuba, na bi Allah na bi ka! Tayi conclusion da marairaice idanunta cikin nasa.
Bashi da katabus a duk lokacin da ta kira yi sunansa na ainihi, wanda ba kasafai take yi ba tun sanda ta fahimci fadar hakan na sanya shi a wani hali, tafi cewa (Your Excellency)a gaban kowa don ya zauna lafiya. Sai in sun kebe ne take kiranshi da duk yadda taga dama.
A take ya sassauto, hannunta dake cikin nashi ya bi da kallo yana murmushi infront of them Ameenah? Hawaye suka cicciko idanunta kayi hakuri in nayi laifi, bazan iya sakin hannun bane. Ta fada cikin emotion (shauki). Da gaske ya bata a very big giant surprise kamar yadda yace which she didnt expect. Tantabarunta ne fa sukayi wannan bunkasar. A mahaifar mahaifinta SHIRA.
Sai ya kara damke hannun nata sosai cikin tafin hannunshi, ya jata suka shiga zagaye gidan gonar lungu da sako. Sun kasa cewa juna uffan zuciyoyi kawai ke aiki, farin cikin Amina heighteneda lokacin da ta gane dukyawan tantabarun da ke ciki nata ne suka hayayyafa.
Sai da suka gama shirunsuka tsaya cikin dakin tantabarun suna fuskantar juna, ta mika hannu ta kamo aure daya ta dora akan tafukanta, suka tashi firrr!Suka koma tukwanensu alamun sun manta da ita, dada ne bazasu tashi ba. Zama zasuyi sai ta maida su da kanta. Ta dubeshi ya dubeta ya daga mata kafada alamun ita ta jawo sai sukayi dariya, anan ya gaya mata cewa duka wannan gidan gonar nata ne, mallakinta ne.
Ya hayo kwararru a kiwon tsuntsayen gida ne suna kiwata mata su. Tunda yanzu bata da lokacin hakan. Tantabarunta da ya amsa ne suka yi wannan albarkar bayan nan kuma ya kwaso nata na gida da iznin Goggo ya hade. Surprise din da ya ce zai mata kenan.
Tukuici ne ya ba ta for bringing happiness to his life, for her sacrifice to hisdaughters life(na kawo farin ciki a rayuwarsa da ta yi, da sadaukarwarta kan rayuwar diyarsa). To sai ta rasa me zata ce masa. Shi kuma me ya kawo cikin tata rayuwar?
Contentment, love,affection, devotion, family tie, and everything!Ita bata da abinda zata bayar tukwicin, banda mallaka masa kanta da komai nata wanda dama nasa ne. Kawai sai ji ya yi ta yi azama ta rungume shi tsam-tsam tana hawaye.
Ubangijin da Ya halicceta Shi Ya sanya mata kaunar tantabarun mahaifinta. Kwarai ta ke sonsu, ta maida su wani bangare na rayuwarta. Su ne kadai take kalla ta tuna ya bar mata wani abu na rayuwarsa.
Ta dade tana tunanin yadda za ta habaka kiwonta yau ga Maarouf ya cika mata burinta, ya hutar da ita, kuma a kasar mahaifinta (Shira).
Damka mata takardun gidan gonar ya yi, ya gabatar mata da maaikatanta, ya kuma gaya musu ita da su cewa, yanzu hakkin kula da gidan gonar da hakkin mallakarsa ya koma karkashin ikonta.

****
Shekaru uku kenan da auren Maarouf da Amina, tana goyon danta na biyu mai sunan Baban Maarouf wato Habib da suke kira ABBA. Wanda ya biyo bayan danta na fari Masud. (Hanif). Maarouf na gab da sauka daga kujerarsa don haka komai ya cakude musu, ba ya samun zama ko kadan, suna yawon kamfen gari-gari don neman samun kara hayewa gwamnatin Bauchi a karo na biyu.
Sosai suke kewar sa a gidan musamman Hanif da yayi mugun sabo da mahaifinsa. Hatta wanka in yana gida shi yake masa. Abba dan maman sa Hanif dan Abbansa.Kullum haka rayuwarsu take cike da soyayya tatacciya kamar Zuma. Sabuwa take komawa a ledar ta, kullum cikin mararin junansu suke.
To komai yayi farko zaiyi karshe. Yau shekarunsu hudu ba wata uku akan karagar mulki. Tenure tazo karshe sai fafutukar yadda zaayi a cigaba. Kai ya dau zafi komai ya cushe musu babu lokacin iyali ko kadan.
A irin wadannan lokutan Amina na yiwa mijinta uzuri, bata damunsa, bata nanike masa, bata binshi da korafin rashin zamansa a gida. Mayar da hankali take kan ibada da rainon yayanta tana kuma binsa da kyakkyawar addua.
****
Chapter 11 · 0% Book details