← Book details Sanadin Kenan Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 13

Sashe 12

Sanadin Kenan Part 4 Complete Hausa Novel · about 6 min read

A daya gefen tsohon kwamishinansa na kananan hukumomi da mai ba shi shawara kan ci gaban karkara da ya sauke sun dade da fito da sabuwar jamiyyar adawa (opposition party) da suka sanya wa suna NRC (Northern Region Congress) sun fito da karfinsu suna yakar (NPC) ta karkashin kasa da ta duk sauran hanyoyin da zasu iya.
Tsohon kwamishinan Abdallah Ganjuwa da tsohon mai bada shawarar Yushau Saminu sun tsaya neman kujerar gwamna da ta mataimakinsa.
Lokacin da Maarouf ya samu wannan labarin daga bakin Turaki da sauran kwamishinoninsa a dakinsu na zartarwa bai yi mamaki ba, in kanna siyasa ba abinda bazaka gani ba, sun ci gaba da kulla wadda za ta fishshe su ne kawai ba su sanya su a lissafinsu ba balle har su dame su.
Amma abin mamaki abin da kuma yaa kada yan hanjinsu shi ne yadda alummar jihar da dama suka soma karkata zuwa (NRC). Lokacin da aka yi (primary election) Maarouf ne ya ci, a can su kuma Abdallah ne ya ci. Allah kadai ya san irin kulle-kullen da suke yi wa (NPC) har da bin bokaye da yin kazafi iri-iri gare su. A cewarsu, mabiya jamiyyar (NPC) masu ruwa da tsaki dukkansu sumumu-kasau ne, wai macijin sari-ka-noke, kasancewarsu tsofaffin jiga-jigan jamiyyar suka rinka fidda sharri kala-kala da suka shirya musamman da rahotanni na karya da alkawurra iri-iri masu ban mamaki ga alummar jihar.
Da yawa an karkata gare su tunda Maarouf din ai dan Adam ne kamar kowa dole a wani fannin yana da kasawa. Duk da kokarin su Ilya na shiga birni da kauye suna karyata zargin da ake yi wa jamiyyarsu da kare gwamnatinsu an ce wanda ya riga ka kwana dole ya riga ka tashi, Abdallah da Yushau ba rana daya suka fito ba, kwanton bauna suka yi wa (NPC) suka rarake kasansu kamaryadda suka ci alwashi. Sannan bokayensu sun dade suna shiri a kan wannan lokacin kan Maarouf da magoya bayansa.
Lokacin da zabe ya matso ya zama ko lokacin gidansa ba ya da shi, ya shiga damuwa. Yadda ya shiga damuwa haka iyalinsa, hatta Abba da ake goyo ya san rayuwar gidansu ta sauya. Amina sai ta kwashe sati guda cur bata sanya Maarouf a idanunta ba. Hakan baya damun ta addua kawai take ba dare ba rana, idan mulkin nan alkhairi ne a gareshi Allah ya maimaita masa, in babu alkahairi tana rokon ubangiji ya fitar dashi daga ransa ya huta suma su huta.
Ranar zabe duk suna (polling unit) na mazabarsu shi da iyalinsa, Amina rike da hannun Hanifa Abba yana kwance a kafafunta, anyi-anyi a karbe shi ya ki sai kuka yake yi, ta zauna don ta shayar dashi ya ki yarda ya kama nonon sun rasa abinda ke damunsa, Dr. Turaki ne yayi nasarar karbar sa ya fita daga wajen dashi, Amina ta rasa abin da zatayi ta rasa me ke mata dadi kawai sai ta tsugunna ta soma kuka.
A cikin tawagar harda Goggo, Kaka Maryama, Inna zulai, Dr. Zainab Turaki da nata iyalin, Ilya da iyalinsa, yaransa biyu shima, Hajiya Saude wadda aka fi sani da Hajiyan Ji-kas, Alhaji Mansur da daukacin iyalinsa, Uwa uba mahaifin da ya haifeshi Mallam Habibu, Dr. Umar Bolori da family din gidansu duka, da duk wani makusancinsa suna tattare a rumfa guda anan suka jefa kuriunsu.
Aka taru akan Amina ana lallashin ta wadda baa san kukan me take ba, ita kanta bata san kukan me take yi ba ko me ya sanya ta kukan, ta san danta lafiyarshi kalau yanada damuwa ne irin ta kananan yara ga iyayensu har suka dawo gida, amma da tayi tsam da zuciyarta sai ta fahimci Maarouf take tausayawa, tausayi mai dumbin yawa domin jikinta ya gama bata zaben nan basu da nasara.
Suka dawo gida suka zauna gaban radio.
Aka tafka zabe aka gamaa karo na biyu, Maarouf Habibu Ji-qas ya fadi. Wato ya sha kaye daga abokin karawarsa Abdallah Ganjuwa. A lokacin da zuciyarsa ta afu ga son ci gaba da kujerarsa!!!
Bai san yana son mulkin har haka ba, sai lokacin da kafafen yada labarai suka bayyana an kayar da shi. Kayarwa daga abokin takarar da bai taba zato ba.
Ya shiga damuwa ba yar kadan ba, Amina dake gefe ta kashe radion, ta shiga karfafa masa gwiwa tana tunatar da shi muhimmancin yarda da kaddara mai dadi ce ko mara dadi, tana ankarar da shi tarin niimomin Ubangiji a gareshi, kada ya butulce, ta cigaba da tuna masa; sanda ya bashi mulkin nan fa ba kokarin sa bane ko na magoya bayansa, ya gode maSa, ya karbi sauyin da hannu bibbiyu.
Ya bude ido yana kallon ta,wani irin kallo mai tsayi da zurfi, a zuciyarsa yana fadin ko da ke kadai na tsira zan iya rayuwa a duk inda na tsinci kaina. Sabo ne turken wawa!!!
A fili ya rinka maimaita kalmar Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Har sau uku. Wata irin nutsuwa ta zo masa. Ya runtse idonsa ya bude su a kanta, ya mika mata tafukan hannayensa biyu ta kama ta mikar dashi tsaye. Toilet ya nufa ya dauro alwala ya tada sallah. Amina ta mara masa baya ta hanyar janyo hijabinta ta bishi sallahr.
Sosai suka samu nutsuwa, da gaske ne samun mata ta gari shine cikar rabin addini. He thank ALLAH for this blessing, yana rokonsa ya tashe su tare har a gidan aljannah.
Ya kwantarda kai a kafadunta, ta rike shi sosai a jikinta. Tuni ya manta da komai.
****

SAUYIN RAYUWA
Suna ji suna gani ranar wata asabar suka tattara suka fito daga gidan gwamnati, Amina kullum cikin kwantar wa da maigidanta Maarouf hankali ta ke har ya ware ya saba da sabuwar rayuwarsa. Suka share gidansa na Fati Muazu, sabuwar rayuwa ta fara.
Ameena little ta gamaprimary a shekarar. Mahaifinta ya kai ta makarantar sakandire ta kwana ta Nigerian Turkish dake Kanoaka sanya ta a J.S.S 1. A shekarar ne kuma Amina ta kara haihuwar yarta mace mai kama da ita a komai. Ta roki Maarouf alfarmar ya sanya mata sunan kakarta da ta rasu a wannan shekarar, mahaifiyar Goggo, wato Maryama, suna kiranta Maryam.
Amina ta koma bakin aikinta a asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa (ATBU Teaching Hospital), da taimakon Dr. Turaki. Maarouf ya koma (contract) din gine-ginensa, saidai samun kwangilar gine-ginen ya ja baya ba kamar da ba, tunda gwamnatin dake bada kwangilar ba tasu bace.
Sauyin rayuwar da suka samu za su iya cewa mai yawa ne. Abin da za a ce shi ne ba sojoji babu bodyguards da masu take baya, babu (security), babu maids rututu da sauransu, bayan wannan babu ta inda rayuwarsu ta canza ba su nemi komai sun rasa ba sai mulki da abin da ke zagaye da shi.
Bayan barinsu gidan gwamnati Ilya ya zama babban yaron Maarouf shi ke kula da harkokin gidansa kuma ya yanka albashi yana ba shi duk wata duk da bai kai wanda yake karba lokacin da ana gwamnati ba, cike da godiya da kyakkyawar zuciya yake zaune da uban gidansa.
A tsayin shekaru uku na zaman su gidan Maarouf na Fati Muazu Links, Amina ta sake haihuwa, wannan karon ma diya mace ta haifa. Maarouf ya yi mata kuhtbah da sunan mahaifiyarsa, wato Saudatu.
Shekarunsu biyar kenan da aure yayansu hudu, maza biyu mata biyu da babbar Yayarsu Ameena, wadda ke zana jarrabawar kammala karamar sakandire a wannan shekarar daga Nigerian Turkish.
****
Chapter 12 · 0% Book details