← Book details Sanadin Kenan Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 13

Sashe 6

Sanadin Kenan Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*****
Laila ta isa gidansu yamma lis almajiri dauke da katuwar akwatunta, mahaifinta ta fara arba dashi a kofar gida ya shimfida tabarma yana kishingide yana sauraron radio, tun daga nesa ya hango ta tana tafe amma ya sawa ransa ba ita bace mai kama da ita ce, ina Laila ina tafiyar kasa da dirkeken akwati haka kamar mai barin gari?
Bai tabbatar itace ba saida ta tsugunna a gabanshi tana gaishe shi tana share hawaye da gefen gyalenta. Muryarta ba ta fita sosai saboda kukan da ta ci. Dagaci ya ce, Laila ce?
Ta ce cikin dusasshiyar murya, Ni ce Baba.
Ya ce, Lafiya kwaram-kwaram da yammacin nan kamar korarriya?
Da farko Laila ta so ta boye wa mahaifinta gaskiyar cewa, Maarouf ya sake ta, sai kuma ta yi tunanin gara ta gaya masa ko ba komai Maarouf na ganin girmansa idan ya nemi alfarmar ya maida ta dakinta zai yi masa. Don haka ta bude baki ta ce, na dade a garin nan, ina gidan mahaifiyarsa, mun samu sabani ne. Jiya kuma ya sake ni. Amma saki daya ne. Don Allah Baba ka je ka ba shi hakuri.
Dagaci ya gyada kai cikin matsanancin takaici, Ya yi kyau. Na tabbata halin naki na tsiya da ki ke shukawa a gidan da giggiwarki ce ta ishe shi. Ga gidan nan tunda zamansa ki ke shaawa kafada daya da uwarki sai ki shiga ki yi ta zama ki ji in zaman gidan dadi ne.
Amma ni ko sawuna ba zai taka inda Maarouf yake ba balle in wani ba shi hakuri alhalin ban san me ki ka shuka masa ba. Haka siddan yaron nan yaron kirki ba zai sallamo ki ba, da ma ina jin wai-wai a kan wulakancin da ki ke wa yan uwanki saboda Allah ya rufa miki asiri. Duniya ta fi bagaruwa iya jima Laila, ga gidan nan ki zauna haka kawai ba za ki zo ki daga min hankali ba ina zaman-zamana lafiya.
Ya nuna mata hanyar cikin gida, ya ce, Wuce ciki.
Sabon kuka Laila ta sakar wa Babanta, fadi ta ke,
Wallahi ba abin da na yi masa Baba, sabon aure ya yi shi ya sa ya sake ni.
Maigari ya ce, Yanzu na ji magana. Ya yi sabon aure kin yi masa tashin hankali ko? Saboda gidanku ba mata uku ris ki ka tashi ki ka gani ba. To madallah wuce ciki na ce ki gama idda ki auri wanda ba shi da mata. Kada in kifta ido in bude in sake ganinki a wajen nan duka za ki sha wallahi.
Tana kuka ta ja akwatinta mai tayoyi ta shige cikin gidansu kamar ta dora hannu a ka ta zabga ihu.
Matan gidan uku duka suna tsakar gida har mahaifiyarta, kowacce da sabgar da ta ke yi. Mahaifiyarta ce mai girki, don haka talgen tuwo ta ke yi, mai bi mata Larai tana tankaden garin kuka.
Sai amarya Laminde ita kuma tirken awaki ta ke sharewa. Ga kannenta nan matasa da kanana kowa abin da yake yi daban. Jin karar akwatunta duksuka juyo suka dubi hanyar shigowarta.
Babar Laila Inna Saade ta washe baki amma ganin yanayin Lailan sai gabanta ya fadi ta bar abin da ta ke yi ta shige daki, ta fi so ko ma mene ne ta ji shi a daki ita kadai ba gaban wadannan masu son ganin hanjin nata ba.
Kai tsaye kuwa Laila dakin mahaifiyar tata ta wuce. Ta jefar da akwatin gefe ta samu waje ta hada kai da gwiwa ta ci gaba da kuka. Inna Saa ta ce,
Ke lafiya? Mutuwa aka yi?
Laila ba ta amsa ba sai hadiyar zuciya.
Tambayar duniyar nan Innar ta yi Laila ta ki gaya mata komai har ta fusata ta fita ta kyale ta. Kishiyoyin kuwa abin nema ya samu tattaunawa suka shiga yi tsakanin Larai da Laminde.
Wannan akwatin dai ko saki ko yaji. In ji Larai.
Laminde ta ce, Ko kuma an nado mata dankaren duka ba, an koro ta. Ahayye!
Ita dai Inna Saa ba ta tanka musu ba ta wuce murhunta ta ci gaba da tukin tuwonta zuciyarta a jagule.
A daren ranar Laila ba ta runtsa ba sabida cizon sauro, ga Innarta ta hada ta shimfida da kananan yayanta sun jike ta sharkaf da fitsari. Bargon da ta kwanta a kai kuwa jinsa ta ke kamar karzuwa saboda kaushinsa a fatar jikinta.
Wancan zuwan da ta yi da Maarouf ya dage sai ta kwana biyu karbar matar gwamna Inna Saade ta yi mata, gadon audiga ta bar mata ta kwana ita ta kwana a kasa da yake an san bakuntar arziki ta zo. Sai yanzu ta shiga nadamar rashin gyarawa Innarta daki a lokacin da ita ta ke cikin kololuwar daular rayuwa.
Washegari da safe kuwa koko da dumamen tuwo Innar ta dangwara mata a gabanta ko uffan ba ta ce mata ba, cike da haushin ta ki gaya mata abin da ya kawo ta ta barta da kishiyoyi suna yada mata habaici. Shi ma Dagaci bai yi wa kowa zancen Laila ba ya ja bakinsa ya yi shiru, harkokinsa kawai yake yi.
Sai da Laila ta kwana uku a gidansu ganin ba wanda ya zo biko, sannan Maigari ya gaya wa uwarta sakinta aka yi. Hadiyar zuciya ne kawai Inna Saade ba ta yi ba, amma ta fashe da kuka mai karfi wanda ya janyo hankalin abokan zamanta suka zo kofar dakinta suna tambayar ko lafiya?
Ko kula su Inna Saa ba ta yi ba, amma maigidansu ya gaya musu Laila aure ya mutu don shi a wurinsa duk an zama daya. A fili suka jajanta suka wuce dakunansu farin ciki fal zuciyarsu suna labarta wa yayansu har wadanda ke gidan miji sun aika musu.
Yan uwan Laila, Asiya da Sadiya in ban da Allah ya kara ba abin da suke yi, ba za su taba manta wulakancin da ta yi musu da za a yi (swearing in ceremony) na mijinta ba, suka ce za su zo ta ce ba ta gayyatar gayyar naayya.
Wani cikin gidansu bai taba taka muhallin da ta ke ba, hatta uwar da ta haife ta, to juyayin me za su taya ta don yau ta ga juyin rayuwa? Da ma an ce ka taka duniya a sannu domin ba matabbaciya ba ce.
Kwanan Laila biyar a gidansu ko kofar dakinsu ba ta iya fitowa saboda habaicin su Laminde da dariyar ketar kannenta da yayyenta maza. Kuka ta yi shi har ta gode Allah, nadama kuwa ba irin wadda ba ta yi ba.
Ranar da ta cika kwana bakwai Inna Saade ta soma tila mata wanke-wanke da wankin kayan fitsarin kannenta da girkin gida in ya zagayo kanta, ta ce ba zai yiwu kina kwance a daki ina dafo abinci ina kawo miki alhalin kin fi ni karfi ba.
Ai shi zaman gida cudarni in cude ka ne ba irin gidan miji ba, shi ya sa ki ka ga ko mu da muke kauye lallaba aurenmu muke balle mai auren gwamna ta ce sai abin da ta ke so za ta yi?
Haka Laila ta ci gaba da rayuwa a gidansu cikin wani hali na tagayyara da fita hayyaci. Gaba daya ta zuge ta fita hayyacinta, fatar jikinta ta canza kala hatta gashin kanta ya san uwar dakinsa ta samu gigitaccen sauyin rayuwa na farat daya.
Ba irin kiran da ba ta yi wa Maarouf a waya, ba ya dauka sai ta koma yi masa sako (text) ko karantawa ba ya yi yake gogewa. Ga lokaci na tafiya tsoronta Allah tsoronta lokacin cikar iddarta.
Babban abin da ya kada ta hatta Hajiya Saude ba ta kara waiwayarta ba, kuma tana da labarin ya zo Ji-Kas har sau biyu a bakin kaninta mai bi mata. Haka Laila ta rungumi kaddara ta maida alamarinta ga Allah.
Kullum ta yi sallah sai ta roki Allah ya juyo mata da hankalin Maarouf, in hakan ba za ta yiwu ba tana rokon sa ya fiddo mata wani mijin cikin gaggawa mafi alkhairi a gare ta, ta yi aure ta huta da masifar gidan ubanta.
Chapter 6 · 0% Book details