← Book details Sanadin Kenan Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 13

Sashe 13

Sanadin Kenan Part 4 Complete Hausa Novel · about 6 min read

GASKIYA DOKIN KARFE!
Shekaru uku kenan da kafuwar sabuwar gwamnatin (NRC) a jihar Bauchin Yakubu, tun kafin a kawo wannan lokacin talakawan jihar suk soma dandana kudarsu a hannun sabon gwamna Abdallah Ganjuwa. Hatta ruwan sha da na amfani ya gagare su, wutar lantarki sai a yi wata ba a kyallaro musu ita ba, jinkirin albashin maaikata da sauransu. Wannan kadan ne in aka yi laakari da yadda rashin tsaro ya bi ya addabi jihar, sata, sane, kwace da fashi da makami, hanyar Bauchi ba ta biyuwa saboda yan fashi da suka mamaye ta kuma gwamnatin ta kasa yin komai akai, haka kebantattun unguwanni basa shiguwa, babu wani kokari dagagwamnatin jihar ta kasa yin komai sai sata da itama ta sanya a gaba.
A yadda talakawa suke tunzure da sabuwar gwamnatinsu da da-na-sani wajen zabenta la-shakka da lokacin mulkin soja ne, sai sun yi mata juyin mulki.
Allah-Allah suke ta gama cin-zalinta ta kara gaba su dawo da gwamnatinsu mai adalci. Ko da wannan (rumours) ya shiga kunnen Maarouf tsaki ya yi, ya ce, ina! Siyasa ya gama ta, ba ya fatanta, ba ya sake kwadayinta.
Matasan Bauchi wadanda suka san sun amafana ne karkashin (Maarouf Foundation) har suka tsaya a kan diga-digansu sun ci alwashin sake tsayar da tsohon gwamnansu duk da ya bayyana raayinsa na ba ya shaawa, ba ya bukata. Ilya ne ja-gabansu suka yi tattaki suka tadda Baba da Alhaji Mansur da kokon bararsu na su shawo musu kan Engineer Maarouf ya yarda da kyakkyawan kudirinsu su sake tsayar da shi takara a karo na biyu.
Baba da Alhaji Mansur suka sanya shi a gaba a wani yammaci, su billo ta nan ya billo ta can wajen nuna ba ya raayi, siyasa sai ta neman aljannah ce ta rage masa.
Su kuma suna fadin jihadi zai yi in ya koma ya ceto alummarsa daga hannun wannan azzalumin shugaba.
Haka yana ki yana komai matasan Bauchi suka yi gangami suka sai masa (form) na tsayawa takarar gwamna a karo na biyu. Ilya ne shugaban kamfen a birni da kauyuka, ya tsaya wa kamfen din da jikinsa, lafiyarsa da aljihunsa, ba su samu kwanciyar hankali ba sai da suka maida shi kan kujerarsa ta gwamnan Bauchi a karo na biyu.
Amina ta hakura da aikin asibitinta a karo na biyu ita ma, Maarouf ya bude mata asibitin kula da masu lalurar shanyewar barin jiki nata na kanta, ta ci gaba da kula da Goggonta da yan uwanta.
A dalilinta sai da dukkan danginta suka baro kauyen Shira suka dawo maraya, ta sama musu abin yi. Wadanda ba sa son zaman marayar sun samu abin yi mai karfi a kauyen, Hassan dan Baffa Bilya na cikin wadanda ba sa son zaman marayar shi da iyalinsa, shi ta nada wa alhakin kula da gidan gonarta na tantabaru da tsuntsayen gida da ke Shira.
A wani hutu da Maarouf ya dauka na karshen shekara Amina ta jajibeshi suka yi Sierra Leone tare. Ya ga tarba ta mutumci da karramawa daga dangin Amina. Yaran duka har Amina karama sun ji dadin hutun su a Sierra Leone sabida basu taba fita daga cikin Africa ba saboda patriotism din mahaifinsu. Gara Amina little taje Saudiyyah sau uku. Maarouf da Amina suna adduar Allah ya basu tsawon rai su cika barinsu akan Aadil (babban dan Dr. Turaki) da little Amina, wanda ke ajin farko a jamia yana karantar medicine.
Rayuwar Maarouf da Amina ta ci gaba da yin albarka cikin niimomin Ubangiji masu yawa, sun tara iyali masu albarka.
Suka ci gaba da cin gwamnatinsu cikin kwanciyar hankali da burin neman kujerar da ta fi wannan a can gaba idan mai duka ya yarje masu da lafiya da nisan kwana.
****
Masha Allah laquwwata illa billah.

Nan na kawo karshen littafin
SANADIN KENAN 1, 2, 3&4, sai mun hadu a littafina na gaba mai suna:-
AUREN KWANGILA.
Taku har kullum.
Sumayyah Abdulkadir Takori.

DANDANO DAGA
AUREN KWANGILA!
N
isawa AbdulAziz yayi, ya sauke numfashi mai nauyi, Ishma, wata musiba ce ta tunkaro ni nake so ka taimaka min. Nikuma nayi maka alkawarin yi maka duk abinda kake so a duniya, zan kuma dinga raba albashina biyu ina turo maka rabi har ka gama karatun ka ka tsaya da kafafunka.
Maganganun sounds funnya kwakwalwar Ismael Dakata. Daga ji ba abin alkhairi Yayan zai nema ba tunda har sai ya biya laada.
Ni kuwa me zan yi maka da har sai ka biya ni Yaya Azeez? Gaya min ko me kake so in yi maka kawai in har na alkahairi ne zanyi. Zan iya fansar da raina don in cece ka. Amma wace irin musiba ce wannan da iyayenmu bazasu iya yi maka maganin ta ba sai ni?
Su suke son jefa ni cikinta ai Ismael subhanallah! Please Yaya kada ka sake fadin haka, nayi amanna bazasu taba jefa ka a musiba ba sai alkhairi ga rayuwarka. Yanzu dai me kake so inyi? A shirye nake da in taimaka in har zai tafiyar da damuwar ka. Wallahi ba sai ka bani komai ba zanyi, nima ka sanya ni cikin damuwa matuka
Abdulaziz ya canza rikon wayarsa daga kunnen dama zuwa hagu, ya juya ya tabbatar babu kowa a cikin dakin kuma babu motsin kowa daga waje.
So nake ka bugo waya wa Mammah, ka ce mata ka dade kana son Hafsat, don Allah a baka aurenta, ka kasa maida hankali kan karatun ka saboda soyayyar ta, ka ce sonta kake tun tana yarinya, ka nuna mata irin wani abu zai iya samun ka dinnan idan baka samu aurenta very soon ba, sauran kalaman ka tsara abinka ai kai ba yaro bane tunda na baka topic din, ka gane?
Mamaki ya gama kashe Ismael a tsaye, sai da ya lalubi kujera ya zauna Yaya wace Hafsat din? Ta gidanku mana? kana nufin Suhaana? nifa Ishma sunannakinnata ba duka na rike ba, kuna kiranta da sunaye barkatai, I dont know! Ta wajen Mammah dai .
Don Allah Yaya muyi magana ta fahimta, Hafsat-Suhaana Addar Mammah?
A ginshire Abdulaziz ya rausaya da kai Eh, ita, don naji Baba Azumi ma ta ce mata Addar.
Dariya ta kama Ismael amma ya gimtse, yanzu ya gano bakin zaren duk da bai gayamasa ba. Mamakin Yayan nasa ya kama shi matuka, amma tunda bai fito fili ya gaya masa dalilin bukatar tashi gareshi ba, bari ya bishi a hakan.
Yaya akan me to? Akan me zanyi hakan? Akan me zan yaudari Mammah inyi wasa da hankalinta akan abin da ba haka yake a zuciyata ba? Yaya Hafsat mai martaba ce a wajen Mammah damu bakidaya da muka rayu tare muka san wacece ita, wace irin martaba Allah ya yi mata.
Kasancewar ta ba jinin mu ba, baya nufin bama kaunarta ko don kaunar da mahaifiyarmu ke mata. Yarinya ce ta gari, amana a hannun mahaifiyarmu, ta yaya kake tunanin zan iya playinggame akanta? To akan me ma?
AbdulAziz ya hadiyi miyau, jin makoshinsa ya bushe kyamas, ga dukkan alamu bazai samu nasara a plan 1 ba, amma dai bari ya cigaba da turzawa tunda Ismael dai a kasan sa yake.
Akan duk kaunar da kuke mata bata kai wadda ke tsakanina daku ba......!!!

AUREN KWANGILA!

Yana zuwa bada jimawa ba, goron sabuwar shekara Insha Allah. Tare da SUMAYYAH ABDULKADIR.
Nuwamba, 2018
Chapter 13 · 0% Book details