← Book details Sahra Hot Love Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 20

Sashe 4

Sahra Hot Love Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Har nine bai dawoba , hankalin sahra yayi kololuwa girn tashi sai zagaye falon take idon ta cike da hawaye tana adduan Allah yasa bawani abune yasami abban ta ba..don baya taba kaiwa 9 awaje. Dariyar mugunta kawai momy keyi a ranta ganin yanda tatashi hankalin "zakiyi kigama ne ae.." Tafada cikin ranta tana maida hankalin kam TV . zuwa karfe goma kuka kawai takeyi kamar ranta zai fita tazo gurin momy cikin shashshek'a tace " don Allah momy abba baice maki zaiwuce wani guri daga masjid ba..har yanzu baidawo ba kuma baya kaiwa haka a waje..am scare..ya Allah protect my father. " hada kai da gwiwa tayi taci gaba da kukanta, kokallon inda take momy batayi ba taci gabada kallonta. Bayan kusan kamar minti goma wayar momy tai ring tadauka tasa a handfree , daya dayan bangaren muryan wani kato ya bayyana yana cewa "munyi karkuwa da mijinki malam Yusuf Aliyu muna bukatar 500million nanda 24h kokuma kusami gawarshi a bolar unguwarku." Daga haka aka katse Koran . Fasa ihu sahra tayi tafada jikin momy tana rushewa da kuka, " nashiga uku zasu kashemin abba na.. I'na zamu samu wnn uban kudin , kitaimaka min dan Allah momy nikadai bazan i'yaba komai ba... kiyi wani abu akai pls." Dan bugu bayanta kadan tayi alaman rarrashi tana kukan munafirci tace "ni ba'abinda zan i'ya taimaka miki dashi , saidai shawara daya...i'n fadawa safwan kinsan duk yanda ubanki yake acikin darennan zai naimo shi." Shiru tayi tana tunanin maganar momy "to akwai yanda zanyi ne?, gara kawai afada mishi.." Tai deciding cikin ranta. Dagowa tayi da jajayen idonta tana kallon momy tace "na yarda..akirashi."Farin ciki ne yaziyarci zuciyar momy ta maida kan sahra saman cinyarta tana shafawa " yauwa kokefa daughter na, bari nakira shi..." Wayanta dake gefenta tadauka tai dailing no. Safwa. yana daga wayar momy tafasa i'hu cikin kidima take mishi bayanin abinda yafaru takara dacewa" gatanan tun dazu sai aikin kuka take ko abinci bata ciba ...zazzabi na neman rufeta." Murmushi yasaki yace "bata wayan." Gagara amsar wayar tayi sai shashshek'an kuka datake, lumshe ido yayi jin kukanta har cikin ransa . "taki karba.." Momy tafada yayinda tamaida wayar kunnanta. "Kisa wayar a hand free ." dasauri tasa tamaida wayar gefen sahra sosea, a hankali cikin muryarsa mai daukar hankali yace "kikwantar da hankalinki love..ganinan zuwa yanzunnan abbanki zai dawo." Daga haka yakashe wayar. Kara rushewa tayi da kuka still tana cinyan momy NA shafa mata bayanta. Bayan kamar minti30 ya i'so kai tsaye ya isa falon ya zauna daya daga cikin kujerun idonsa na kanta ko kiftawan kirki bayayi. "Sannu da zuwa.." Mganar momy tadawo dashi daga kallon dayake mata. Gyaran murya yayi yace "sahra!." Gagowa tayi ta kallesa batareda ta amsaba ,cigaba yayi da cewa "kinason abbanki yadawo?" Dasauri ta gyada mishi kai hawaye na saukowa a idonta . kallonta yatsayayi nakusan minti3 sannan yace " zanbiya duka kudin a sakeshi amma bisa sharadi daya idan yamaki..inkuma bai makiba zaki i'ya bari a kashe mahaifin ki awullar bola." Girgiza kai tafara da sauri tana hawaye tace "nayarda koma mene zanyi amma kada kabari sukashe abba na..narokeka." Kuka takeyi sosea harda majina "atop crying mana, yanzunnan zaa sakeshi tunda kince zaki amince." Balancing yay kan kujerar snn yace "sharadin shine a gabana kifadawa babanki zaki aureni asamana rana ayau dnn laraba ranar asabar adaura aure." Shiru kusan minti 2 batace komai ba .. I'donshi dana momy dakanta jira kawai suke suji abinda zatace . dago jajayen idonta tayi ta kallesa tace "na amince..zan fada mishi.." Tai maganar muryanta na cracking. Wani farin cikine yaxiyarci safwan jiyake kamar ya rungume ta yayi ta kissing dinta. Hakama momy datake summing kanta cikin katon gida mai beni t "Najidadi sosea dajin haka Allah yasanya alkhairi.." Momy tafada tana rungume sahra. Kuka sosea sahra tafashe dashi zuciyanta na mata zafi , tayi wnn abunne kawai don ceto rayuwar mahaifin ta ..amma safwan ba mijin aure bane. Tashi yayi yafita daga falon bayan yakarmi nõ din kidnappers din. minti kadan yadawo yaxauna yacewa momy "sukwantar da hankalinsu nanda minti talatin zaa dauko shi."

_Kubini a hankali akwai *very Hot Love* agaba._

Beenaf/beelurv👄
[26/08, 21:55] Habiba Novel Yobe: *💖SAHRA💖*
*Hot Love💋*

8.....

Bayan kamar minti ashirin wayan safwan yashiga kara, video call ne yashigo bashiri ya dauka ganin guards dinsa dasukaje dauko abban sahra ne, Ajiye wayan yayi yanda kowa zai kalla . da karfi tafizge jikinta daga rikon da momy tai mata tatafi gurin wayar da gudu tareda fashewa da kuka . daga daga cikin guard dinne yace "sir gashi munkarb'oshi can cikin wani jeji kuma munbasu kudin." "Yayi kyau safwan yace yana fallon abban sahra da kanshi yake akasa , juyowa yayi ya kalli sahra daketa faman kuka yayi gyaran murya yace" to alhmdllh tunda gashi ankarbo saiki fada mishi maganar damukayi." Afusace tadago da jajayen idonta tana watsa mishi harara tace "don rashin imani ko gida baizoba shine zan fada mishi." Daure fuska yayi ba alamar wasa yace "i'dan kinmanta abinda kikamin kwanaki ni banmanta ba, kokifada mishi kokuma amaidashi yanda aka karboshi abani kudina!." Kallon mamaki tarinka binsa dashi tana ganin rashin i'mani atare dashi waikuma ahaka zata aureshi. Ganin tana bata mishi lkc yace "inbazaki i'ya magana ba za'a maidashi, jiki a sanyaye tadago tace " abba!." Muryanta na rawa. Karo na farko a hankali yadago ya kalleta da i'donsa wanda sukayi ja saboda zafinda zuciyarshi keyi. Cikin kuka tafara magana tace "banida kowa sama dakai banaso inrasaka abba na, abba bamuda kudin dazamu taimaka maka dole saita hanyar safwan, hakanne yasa yanarda da aurensa domin yabada kudin da'ake bukata. Abba nayarda zan aureshi, kuma dis coming Saturday yace yakeso ayishi.." Shiru gurin yayi sai sheshekar kukanta dake fita, a hankali abban yabude baki zaiyyi magana saikuma yayi shiru dalilin wani tunani dayazo ransa. Dan sakin ajiyan zuciya safwan yayi ganin baice komai ba its means ya amince kenan, murmushi yasaki yayiwa guards din umarni dasu karaso dashi gida yakatse kiran. Momy kamar tadaka tsalle tayi rawa takeji , tadade tana jiran wnn rana sai yau Allah yakawo..jitakema kamar har anyi aure angama shi. Dan kallon site din da sahra take tayi taga har lokacin kuka take, zuwa gurin tayi ta dagota tana share mata tawaye tace "haba habibty meye na kuka kuma ayyanzu kingirma..kumama gacan abban naki ana kawoshi kikwantar da hankalinki. Fizge jikinta tayi tashige dakinta tareda banko kofa tafada gado tana kuka. Kallon safwan tayi tace " kaga saikabi yarinyarnan a hankali don wani irin taurin kai gareta." Daga kafada yayi yace "kiyi list duk wani abu dazaku bukata daga yanzu har lokacin auren saiki fadamin kudin zanturo maki. Ni zanwuce yanzu kafin sukaraso." Jikin momy har rawa yake jin maganar kudi tace"to shknn zanyi ..saida safe.." Baiko tanka mataba yafice driver yabude mashi mato yashiga suka tafi. Har bakin falo guards din suka rakoshi sukaimasa saida safe ganin yanzu yazama sirikin ogansu ya kamata suyi mishi biyayya. Kofar dakin sahra yatura yaganta kwance tafara bacci bayan kukan datayi mai i'sarta, wani tausayinta yaji ya lullubesa haka yarufa mata bargo yakashe mata wutan dakin yafita . misalin karfe biyun dare tafarka dawani matsanancin ciwon kai da zazzabi ko gani mai kyau bata i'yayi, a hankali tasauko daga gadon tana dafa bango tafice daga dakin. Kofar dakin abbanta tatsaya tanagani adan bude kadan, hangoshi tayi yana salla tadan sauke ajiyan zuciya takoma batare da tabari yaji motsinta ba. Da asuba ma dakyar tayi salla a daddafe takoma ta kwanta, karfe 6 momy tashiga kitchen tahada musu lafiyayyen breakfast cikin shauki don kwana tayi tana juyi tana murmushi har mafarki tayi suntafi dinner din auren sahra . karfe takwas momy tagama hadawa ta jerasu kan dining tawuce dakin abba don sanar dashi angama abin kari. Da sallamarta tashiga fuskanta dauke da fara'a tayi gurin dayake zaune kan kujera yana karatul Qur'an. Zama tayi gefenshi sai washe baki take kamar anbata kujerar makka, tsayawa da karatun yayi yajuyo yana kallonta. "Brk d sfya mijinna, inafatan katashi lpy?." Kallon mamaki abba yarinka binta dashi don rabon datai mashi irin haka tunkafin yarasa aikinsa ne , bayan lokacin dayarasa kuwa wani abun arziki baitaba shiga tsakanin suba. "Alhmdllh" yace mata yadauke kansa daga kallonta. Dan sanza fuska tayizuwa na tausayi tace "haba dear kamanta daduk abinda yafaru yawuce. Yanzu kataso muje break fast is ready. Am sorry minti biyu bari inkira sahra ." daga haka tafice daga dakin yabita da kallon shi har tsoroma take bashi wani zubin.

Masoya abin alfahari😍😍

_vote me on wattpad @habiebahlurv_

Beenaf/beelurv👄
[27/08, 01:29] Habiba Novel Yobe: *💖SAHRA💖*
*Hot Love💋*

9......
Chapter 4 · 0% Book details