← Book details Sahra Hot Love Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 20

Sashe 15

Sahra Hot Love Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Rakub'e ya ganta bakin gado ta tallabi fuskanta da duka hannayen ta,,, murmushin da baiyi zatoba yaji ya kubce masa yawuce wardrobe dinsa yadauko wani farin yadi mai kyan gaske da farin hula da takalmi. A gefents ya ajiye kayan yace "zoki tayani dressing!." Wara ido tayi ta kallesa ganin har lokacin towel ne jikinshi yasa ta dauke kanta tatashi tafita daga dakin duka. Akaro na biyu yakara yin murmushi yafara shirinsa. Sosea kayan yay mishi kyau ya dauran hulan saman kansa yasa takalmi yafito falo hanunshi rike da vail maidan girma,, Akan cinyanta ya ajiye mata yace "taso muje!."yay gaba.. bamusu tabi bayansa sukayi parking lot . Dakatar da securities da suke shirin hada masa motoci yayi yace baya bukatar tafiya da kowa shikadai zai fita, nuna mata dayan site din yayi tazaga tashiga shima yashiga yama motar wuta suka fice daga gidan . Babban kanti sukaje yasai mata hijab kusan kala ashirin dinkakku sabbin design masu stones, haka ya dinga yawo da i'ta har sai kusan magrib suka dawo haka kuma ba wanda yay ma wani magana cikin su . dadare a main house sukaje yin dinner kowa ya hadu suka fara cin abinci. samha ko inda suke bata kalla ba i'ta kadai tabarwa kanta shirin datake yi akansu. Murmushi abba yayi daya tuno drama dasukayi da hajja dazu yace " Aliyu, kasan dazu hajja tazo?." Murmushi shima yayi yace "eh abba, tashiga gurina." "Alryt..kakula dai sosea.. don kasan halinta. Har suka gama cin abincin ba wanda yakara magana naja ta tattare dishes din kowa yay nasa guri . mami kama hanun sahra tayi suka shiga falonta basu tsaya nan ba suka wuce bedroom ta zaunar ta bakin gado ta dauko wani abu a fridge cikin kofi yayi sanyi tamika mata" daughter ki shanye wnn!." Amsa tayi cikin ladabi tai bismilla tafara sha . ...sosea abun yay mata dadi gazaki don haka nan da nan ta shanye sa ta ijiye kofin. Kallonta mami ta rinka yi tunda taji labarinta da abbey yafada abba takejin tausayinta sosea sonta na shiganta . shiru ba maicewa komai mami takatse shirun ta hanyar cewa "SAHRA sunanki yake ko?." Gyada kai tayi tace "eh..." Murmushi mami tayi tace "suna mai dadi. Inaso ki kwantar da hankalinki ki daukeni kamar uwa ...kirinka cemin mami kamar yanda sauran suke fada kinji ko?." "To mami." Kad'a kai mami tayi tace "gud gal." Tashi tayi tabud'e wani karamin bag ta dauko wani roba tamika mata...hanu biyu ta amsa robar kafin mami tace "zaki rinka diban spoon daya kina hawada da madara kinasha ,,,kullum zaki rinka yin hakan. Bude fridge tayi ta dauko wani dogon gora da wani abu ciki shima ta mika mata tace " kirinka shan wnn koda yaushe idan yakare ki fadamin karkiji kunya..kuma kirinka shan fruit sosea karkiyi wasa dashi kinji yata?" Gyada kai tayi tace "to mami...nagode." Turo kofar baby tayi tashigo tazauna hafara musu hira hakama mami don ita macece wayayya wanda ba ruwanta , hira suka rinka janta dashi harta dan saki jiki dasu sai karfe goma aliyu yazo suka tafi. Shiya farayin wanka yadauki bargonsa yatafi falo , kashe wutan yayi ya kwanta bayan kamar minti shida yayi juyi ya rungume pillow yana danyi murmushi. haka kawai yakesom ganinta!. Rike kanshi yayi ya girgiza aranshi yace "OMG! What's comes over me haka..Allah kasa bawani abu nakeji kan yarinyar nan ba, Yaa rab choose d best for me. Lumshe idonsa yayi bai dade ba bacci yay awun gaba dashi. Washe gari Monday karfe bakwai da rabi yay shirin office yazo yatsaya bakin gadon yana kallonta, son fada mata zai fita yake amma baisan ta inda zai tasheta ba,,,buge idonta tayi a hankali tasauke kan fuskarsa ... dan baya kadan yayi yadan sosa kai yace " zan fita office!. " batace komai ba sai kanta data sauke kasa . saida yakara repeating snn tace "a dawo lpy!." Har yaje bakin kofa ya juyo yace "kishiga kitchen kitada breakfast wa kanki, nd inzakije main house ki tabbata hijab kikasa kuma karki tsaya general falo falon mami zaki shiga ..karki bari samha ta rabeki ko kadan!." Yafice tabishi da kallo. ajiyan zuciya ta sauke ta koma baccinta. Coffee kawai yasha gurin mami yay mata sallama yafita, baby yagani tafito daga dakin ta yace "rabin rai karkije kiranta na hada mata breakfast dinta inta tashi daga bcc zataci." Dariya tayi tace "na love yayana...banga laifinka ba .wllh yaya nayi mamaki wai kaine kake zuba love da mace har su hada mata break?." Dogon hancinta yaja yana murmushi yace "zaki cikani da surutu bye natafi." Yafita ita kuma tashiga bedroom din mami tana murmushi. Sai kusan sha daya ta farka tai wanka tashirya cikin doguwar riga batayi wani kwalliya ba tafito tashiga kitchen. Tsayawa tayi tana tunanin abinda zata dafa daga karshe tai deciding ta soya farin doya sai tayi egg source tahada dashi. Cikin mintuna dabasufi arbain ba tahada da shayi mai kauri tafito falo,,,tararwa tayi da angyara ko i'na hakama bedroom data leka ko'ina gyare kamar baa taba amfani da gurin ba,, ,dawowa tayi tazauna a ranta tana cewa "duk inda kudi da hutawa suke tofa akwai a wnn gidan!." Da azahar bayan tayi salla zaman shirun ya i'sheta ta dauki hijab din ta tafi main house. A falo taci karo da samha tafito cikin english wears da dogon takalmi kafarta hanunta rike da bag zata fita , matsiyacin kallo ta rinka binta dashi tana yamutse fuska tazo ta bangaje sahra dake rakube gefe tana jira saita wuce snn i'tama ta wuce gudun karta mata ba dai2 ba... Kallon tara saura kwata tai mata tace "kidai zauna cikin shirinki don rana a tsaka zansa kibar gidannan!." Taja tsaki tai gaba. Jiki a sanyaye tawuce zuciyarta fal tsoro batasan me wnn baiwar Allah take nufi da i'ta ba..saidai taita adduan Allah yashiga tsakaninta da i'ta. Da sallama tashiga falon mami taganta zaune da waya a hanunta tana dannawa, zama tayi kasa ta gaida mami cikin faraa ta amsa tace "kinata zama shiru ke kadai ko? Gashi baby tatafi school." Murmushi tayi batace komai ba. "Kin gaisa da gida kuwa tunda kikazo?." Girgiza kai tayi da sauri tace "a'a." Hawaye na cika mata i'do , ganin haka yasa mami dagota ta zaunar ta gefenta tana dan buga bayanta alamar rareashi tace"karkiyi kuka mana habibty! , idan yadawo zansa yakira maki gidan saiku gaisa..karki damu." Rarrashinta mami ta dinka yi tana mata hira har tadan wartsake . Sai karfe hudu da rabi ya dawo, part dinsu yawuce yaga batanan yay murmushi yashiga wanka .. riga Polo yasa da bakin wando bayan ya fito yadauki wayarsa yafice main house. Suna zaune i'ta da mami suna kallo ya samesu yazauna gefen mami ya daura kansa kan shoulder dinta bayan ya gaidata. "Sannu da dawowa!." Yaji ta fada, "yawwa!." Yace yana satan kallonta ta gefe. Langwabar dakai yayi jikin mami yace "mami yunwa." Yafada kamar wani karamin yaro. Shafa kansa tayi tana murmushi tace "son kadaina wani abunfa ka girma, agaban matarka kake min shagwab'a?." Kunya ne takamashi yadan sosa kai yace "mami yunwa fa nakeji." Kallon sahra tayi datake dan murmushi saboda drama din dasuke tace "habibty pls kiyi saving mijinki gacan abincinsa dinning nizan dan shiga ciki. " to mami." Tace snn tatashi tanufi dining din. Mami tace "bari inshiga ciki inhuta tun d'azu i'na zaune ." takarasa maganar tana tashi. "to mami , a huta lafiya." Yafada shima yana tashi yanufi dining area. Kujera yaja ya zauna yarinka kallonta yanda take zuba abincin a hankali cikin natsuwa , gabanshi ta ajiye masa bayan tagama zubawa tajuya zata tafi yariko hanunta tai saurin juyowa tana kallonsa.

🙆🏿‍♀nikam na bani,,,naita rusa uban typing sainayi post kucemin yayi kadan akaro yakukeso nayi🙆🏿‍♀🏃🏻‍♀.

Dan Allah masu cewa daga farko kudinga zuwa wattpad akwai can.
View wattpad @habiebahlurv

Beenaf/beelurv👄

💖SAHRA💖
Hot love💋

23....
Chapter 15 · 0% Book details