← Book details Sahra Hot Love Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 20

Sashe 10

Sahra Hot Love Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Tashi yayi yaje kitchen yadauko plet da cokali da kofi yadauko lemo da ruwa yadawo dakin, zuba fried rice din yayi cikin plet yazuba yankekken vegetable dake cikin wani bowl ya ajiye can gefe tareda ruwa dakuma lemo. "Come nd it!...kuma karkibar ko d'aya cikin plet din!." Ba'alamar wasa yayi maganar. D'aga i'do tayi ta kallesa taga baya kallonta ta tako ta zauna gaban abinci..don rabon dataci abinci tun jiya da dare. Bismillah tayi tafaraci taji dadin abinci sosea don haka taci sosea abinta. L'ek'e2 samha tafara yi tanason fitowa amma gurin k'ota i'na sojojine , tunawa tayi da kofar baya takoma tafice ta k'ofar tayi part din aliyu . tabayan part din tabi tatsaya dai2 window bedroom dinsa tafara l'ek'e2 . sahra na cikin cin abinci taji abu nayawo jikinta ga cizonta dayake, dasauri daga hijab din taga cinnaka nan saman cinyar ta fasa wani uban ihu tayi kan aliyu batareda tasani ba. Riketa kakam yayi yana tambayarta amma kawai cewa take " kacirimin plss... Zafi wllh dan Allah kaciremin..." Kirjin samha ne yay bala'in dokawa jin ihun ta gakuga abinda take cewa, dafe kirjin tayi tafara ja baya tana cewa "nashiga uku ni samha..yaya zanyi da rayuwa ta ? Ina cikin duniya i'na raye aliyu yana kusantar wata mace! .." Hanu tadaura a kanta zata fasa ihu tatuno a i'nada take kuma da zarar tayi ihu securities zasuzo. Ahaka ta rarrfa takoma part dinsu tanaji kamar zuciyarta zata fashe ..kwan tawa tayi kan gadonta tana ayyana irin jarabar dazata jawo musu duka su biyun!. Ganin taki daina ihun sai hauka take masa yasa ya daka mata tsawa "ki natsu nace!." Cak ta tsaya sai hawayen dake zubowa daga i'donta . "meye ya sameki!?." Muryanta narawa tace "wani abu ya ...cijeni!.." Zaunarta yayi bakin gadon yace "i'na gurin, bud'e na gani!." Dago da jajayen idonta tayi ta kallesa taga fuskarshi a had'e bashiri tabud'e mishi gurin. Kurawa gurin ido yayi ko kiftawa babu yana bin cinyar da kallo "smoothy!." Yafada cikin ransa . cinnaka yagani kwance gurin ga yadda ta cijeta duk yayi ja abunka da fara. A hankali yakai haunshi gurin ya dag'e cinnakan yabude window ya wullarta. gaban mirror yaje yadauko wani karamin robber yadawo. "L "bude gurin!.." Yafada yana zama gefenta budewa tayi ya lakuto man cikin robar yafara shafa mata gurin a hankali yanajin wani irin laushi da haushi mara misaltuwa. Satan kallonta yayi yaga idonta rufe sai hawaye dake saukowa, kallonta yarinka yi har saida yaga alaman zata bude i'do snn ya maida dubansa inda hanun sa yake. Daukewa yayi da saurin ganin harya fara wuce cinya yatafi gaba da nn . yatashi ya ajiye man gefen gado yace"ki kwanta!. " tashi tayi tahaye can kuriyar gado ta kwanta ta takure guri daya.. Bargo ya dauko cikin wani kofa yakawo mata yakashe wutar dakin yakoma falo. Zama yayi kan kujeran yafara tunanin ta inda zai fara rayuwa da i'ta , dauko wani bargon yayi ya kwanta kan kujera da wnn shine karonsa na farko dazaiyi bcc kai. Daren ranar bai samu wani ishashshen bacci ba don daya fara yake farkawa kwata2 bayajin dadin baccin. karfe uku yatashi yayo alwala yazo yafara jera na filfilinsa harsaida yaji anyi assalatu snn yatashi yatafi masjid . tareda Abba suka dawo suna dan tab'a hira har abba yake dan kara tunatar masa gameda hakki aure , godiya yay mishi yashiga part din su mami Gaidasu bayan abba yawuce nasa part din. Dakin mami yafara zuwa ya gaidata snn yatashi yashiga bangaren small mom . samha tun karfe hudu tatashi tafito falo tanata zirga2 tana jiran zuwansa ..dama kullum da asuba yake zuwa gaidasu. Tana sanye cikin rigan bacci pink mai tsantsi yalafe jikinta tayi parking kanta batasa hulaba. Tanajin motsin bude kofa tazo tatsaya daf da kofar , turawa yayi kofan tabugeta tai baya zata fadi yay saurin tarota. Fadawa jikinshi tayi tareda dan sakin kara tana da noshi cewa "woyya Allah! ya aliyu ka bugeni a gurin nan.." Tafada tana nuna gefen cikinta. Kokarin taraba da jikinshi yake amma tarikeshi tana kukan karya sai rike gurin take . dafe goshinsa yayi yace "kinga samha! Kiyi shiru ya'isa!." K'inyin shiru tayi sai kara rike gefen cikin ta take tana kara sautin kukanta tace "ya aliyu barifa kaga gurin..am sure kajimin ciwo sosea." Without westing of time ta dage riganta tundaga kasa har kusan kirjinta! Snn takamo hanunshi zata daura gurin!. Fizge hanunshi yay da sauri ya wuce zuciyarshi na bugawa don bata taba mishi irin wnn barikin ba sai yau. Yana gadai small mom yafito ko inda samha ke tsaye bai ganiba yay wuce warsa yafita.Tun daga hanya yafara tunanin ta yadda zai tashi sahra tayi salla, yana zuwa kai tsaye yashige bedroom ga mamakinsa sai yaganta kan sallaya ga alqur'an gabanta tana karantawa cikin kira'anta mai dadin gaske. Jikinshi ne yayi sanyi yakoma falo ya zauna lokaci daya yaji ta burgeshi da wnn halin nata,,,amma bayan wnn ba wani abu kokadan wnda ya burgesa akanta shi baya sonta!. Komawa ciki yayi ya dauko wani qur'anin shima yafara karatunsa harsaida gari yayi haske snn yakwanta. Tana i'da karatunta ta maida Quran din muhallin sa ta nade abin sallan snn ta zauna bakin gado ta rafka uban tagumi tunanin abbanta ya fado mata. lakaci daya idonta suka ciko da kwalla tace . "I miss u abba.." Tafada hawayen na gangarowa. Kuka tarinka yi lokaci daya ciwon kai da zazzabi ya kamata , a haka tadan kwanta bacci barowa ya saceta. Karfe takwas da rabi karan doorbell yatashi aliyu, mika yayi tareda salati yaje yabude kofar . baby ce tsaye again hanunta da kwali dakuma karamin kit, murmushi yayi a ransa yace "baby trouble!." Gaidashi tayi tamika mishi kwalin tace "yayana gashi a matarka!, tai wanka tasa kufito muyi breakfast!." Karba yayi yana kada kai yace "to!,,ta gode!." Wucewa tayi ta tafi shikuma yarufe kofar yadawo falo ya i'jiye kayan kan kujera shiga bedroom. ganinta yayi takure can kuriyar gado ya tab'e baki a ransa yace "kamar wata mage!." Wanka yashiga cikin minti talatin yagama shirinsa cikin wata designer dark blue suit yayi bala'in kyau yasaka rolex watch dinsa da cover shoe yafita falo. Zama yayi gurin kayan yabude kwalin idonsa ya sauka akan pant da bra wasu blue set. Dagawa yayi yarinka kallonsu na yan wasu mintina snn ya ajiye ya daga doguwar riga blue i'tama mai robber...ajiye wa yayi ya daga site din jaka da takalmi daya gani shima yarinka kallonsu don sunyi batukar burgeshi . kit din yabude yaga kayan makeup da da lotions da performs kala2 Snn yarufe ya daukesu duka yashiga dasu bedroom. Shigansa yayi dai2 da farka wanta tatashi ta zaune kanta kasa tace "ina kwana!?." Batare da ya kalli inda take ba yace "lafiya!." Ajiye kayan yayi gaban mirror yace "u go nd fresh up...ga kaya nan!." Yay fice warsa. Tashi tayi tana cije lips dinta saboda yadda kanta ke ciwo tashige toilet don batason tamishi wani abun da zaisa ya daka mata tsawa. Brush tafara yi snn tai wanka ta dauki daya daga cikin towels din data gani a rataye ta daura tafito. Fitowanta daure da towel yayi dai2 da turo kofar dakin da akayi, kirjinta ne yabuga da karfi tai saurin d'urk'ushewa gurin.

View wattpad @habiebahlurv

Beenaf /beelurv👄

*💖SAHRA💖*
*Hot Love💋*

18....
Chapter 10 · 0% Book details