← Book details Sahra Hot Love Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 20

Sashe 18

Sahra Hot Love Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

A general falo suka tadda duk yan gidan banda samha da tun safe tafita school har yanzu bata dawoba, gaidasu duka sahra tayi tasamu guri gefen baby ta zaune tai tsim! tanajin hiran nasu..don ita batada nacewa. Kallonta majeed yayi ya kalli aliyu yace "nikan matar taka bata maganane !?." Harara ya zabga masa yace "kai ka maidata kurma?, ko kuma baku taba gaisawa bane!?." Tabe baki yayi yadaga kafada yace "naga ko yaushe shiru take ne!." Baby tadan bugi kafarta kasa kasa tace mata "sis kirinka magana don Allah,,, hakan dakike ba dadi." Kallonta tayi kamar zatayi magana sai kuma ta dauke kanta ..i'ta batasan mezata ceba. Turowa kofar falon tayi tashigo tana taku high hill din kafarta sai kara yake kwas2 gakuma chewing gum datake taunawa, murmushi small mom tasaki tace "wlcm back daughter." Kokadan bata jiba don hankalinta gaba daya yagama tafiya akan aliyu da yana ganin ta yawani hade rea kamar bai taba dariya..dukda de more especially ran nashi ba'a sake yakeba. So take ya d'ago ido ya kalleta amma hakan baiyiyu ba saima ido daya zubawa sahra da kanta ke a kasa, gaisuwan munafurci tashiga yi tafara gaidasu onebyone saida tazo kansa tawani kashe murya tace "barka da yamma ya aliyu." Kokadan baiso ya amsa ba ,,amma ganin rashin dacewar hakan yasa yace "brk!." Batare daya dago da ido ba bare yaga site din datake. Hakan dayayi yayi matukar bata mata rea ,, watode har yanzu bata ishesa ko kallo bama,,,lallai da sake. Wucewa tayi falonsu tana saka abubuwa dazata aikata. Sai karfe goma bayan sunyi dinner sunyi hira sosea har sahra tadan saki jiki da majeed yanda yake mata hira sosea na abin dariya suka tafi part dinsu. Yau aliyu baifita ko i'naba kasancewar weekend ne suna zaune falo bamai cewa kowa komai, dan satan kallonta yayi yaga idonta nakan TV yadan gyara muryansa kadan yace "ran Monday zaki fara fita school tareda baby..da yamma zakuje islamiya tare. nama shugaban makarantar magana hijab mai girma zaki sa,,,kisan irin rayuwar da zakayi acan don aure gareki!." Sosea maganar auren yadaki zuciyarta amma taji dadi sosea na komawanta school. "Ngde!." Tace tana kallon sa. Gyada kai yayi yace "anything 4 u dear.....bai karasaba yay saurin rufe bakinsa yadan saci kallonta yaga har lokacin tana kallonsa yace " am kishiga kitchen ki hada mana lunch yau!." Tashi tayi tadau hanyar kitchen saikuma ta juyo tace "me za'a dafa!?." "Anything u like!." Yafada yana mikewa kan 3sitter. juyawa tayi ya bita da kallo har saida tashige snn yatashi yazauna yafara tunanin "yakamata sukafa zaman aure! Irinna kowani mata da miji!." Zubawa store din dake cikin kitchen din ido tayi,, gakayan abinci kala2 tana tunanin wanda zata dafa , tafi minti shida a haka kafin tayi making mind dinta tayi coconut Rice da vegetables soup mai redmeat snn tayi banana shaka juice. Cikin awa daya da rabi ta hada kamai ta zubasu cikin designer food Flack's data gani cikin kitchen din tazuba su cucumber da cabbage data yanka cikin wani bowl taje tajera kan dinning. Koda tafito falo bayanan don tun shiganta kitchen yafita masallaci bai dawoba har yanzu. Wanka tayi tasaka wani atamfa da mami ta aiko mata tadanyi light makeup tayi sallan azahar snn tafito .. Kafeta yayi da lumsassun idonsa ya rinka kallonta yanajin wani abu yana tabar masa zuciya..sosea kayan yay mata kyau ya burgeshi kowani shape na jikinta ya fita .Ganin irin kallon da yake mata yasata zama kan kujera bashiri ta sauke kanta kasa murya a hankali tace "nagama!, yana dining!." Maganar datayine yadawo dashi yay saurin dauke kansa ya kalli dining area din. Sosea yadda tatsara gurin ya burge shi "she's nyc! I like her!." Yafada cikin ransa . tashi yayi yanufi gurin yace mata "bismilla, kitaho!." Tashi itama tayi tabi bayansa tazauna kan kujeran dake nesa dashi . ganin batada niyar aikata komai yasa yace "pls save us!." Dan kallonsa tayi taga i'ta yake kallo tatashi jiki a sanyaye tafara saving nasu. Spoon na farko saida yakusa sumar dashi ya lumshe idosa ya budesu yana kallonta santi na dibansa yace "testy!." Dan satan kallonsa tayi taga yakai spoon na biyu idonsa a lumshe yana kada kai,,murmushin da batayi tsammani ba tayi ta baida hankalinta kan abincin. Sosea yaci abinci yasha juice din saida yajishi yazo har wuya snn ya goge bakinsa yatashi , already i'ta dama tabar gurin. Zaman shiru sukayi a falon kowa da abinda yake sakawa aranshi , wayarshi yashiga Ring yaduba yaga samha ce,,,kallonta yayi yaga hankinta baya gurin ya kashe kiran ya ajiye wayar gefe. Kara kiranshi tayi akaro na biyar yadanyi tsaki yatashi yafita. ido hudu sukayi da i'ta tana daga gefe sai zarya takeyi tagagara tsayuwa guri daya. Hade fuska yayi sosea ya harde hanna yensa saman kirjinsa yana mata wani banzan kallo, kara sowa gurin tayi cikin sanyi murya tace "yaa aliyu don Allah ka saurareni ka karbi bukatata ka taimaka kota biyunne nayarda ka aureni wllh bantaba son wani da namiji kamar yanda nake sonka ba, dan Allah ka taimaka min." Takarashe maganar muryanta na rawa kamar zatayi kuka. Irritating look ya rinka binta dashi yana karasowa gabanta saida yagama mata kallon ta ya tsirtar da yawu ya nunata da yatsa yace "natsani duk wata macen da zata budi baki tace tana sona matukar bani nace ina sonta ba, kuma bakya daya daga cikin irin matan danake so...bakida tarbbiya, bakida kamun kai kokadan ..don haka baki cancanki kizama matata ba.." Sosea magan ganun suka doki zuciyarta ranta yayi matukar baci.. rufewa idonta yafara yi a hankali tayi baya zata fadi kasa yay saurin tarota.

SAHRA's WORLD inayinku😍
View wattpad @habiebahlurv

Beenaf/beelurv👄

💖SAHRA💖
Hot Love💋

26....
Chapter 18 · 0% Book details