← Book details Rai Da Ruri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 9

Sashe 9

Rai Da Ruri Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ana tsaka da haka biki ya taso a Jigawa bikin aure babar yarinyar malam Musa, har anko malam Abdu ya ma su Hindu suka tafi har shi Jigawan da tsarabar su ta kular abinci da wasu kofuna da plate duk na amarya, iyalan malam Musa kuwa sunji daɗin zuwan su, nan da nan aka basu ɗaki guda masauki, ƴan gari ma suna ta murnar ganin su sunyi kyau sun zama cikakun ƴan mata.

Akayi biki da duk wasu al'adu na bikin lafiya suka koma cike da tsaraba, har suna jin cewa ko yan Jigawa sun ishe su zama dangin su, ayanzu basu da wata damuwa.

Samari fa har Abdu ya fara gajiya da zuruntun su a ƙofar gidan shi dan Abun har mamaki yake bashi badan yasan shi da matar shi basu da irin shige-shigen nan ba da sai yace "ko maganin farin jini suka ba yaran nasu?" ganin abun ya fara yawa ya fara hana su fita.

Daga baya yayi shawara da ummi da mlm Musa da wani abokin shi anan kusa da shi da suka saba akan zece su fidda mji Kawai yayi musu aure dan tsayar da duk wani saurayi.

Suna gab da shiga aji uku na babbar sakandiri, yace "Acikin ku inaso kowacce ta zaɓi wanda taga zata iya rayuwar aure da shi sai yayi magana in ya shirya sure Sauran Kuma dukku salame su"

Suka ce "toh Abdu in Sha Allah" suka zaɓi wanda suke so kuwa basubi dukiya ba duba da har da masu motoci da attajirai a masoyan nasu suka zaɓi samari masu hankali da ilimin addini da na zamani akayi bincike akan su aka ga basu da aibu, aka umarci da su turo suka turo akasa biki suna candy da zarar sun gama makaranta sai aure sai abokin mlm Abdu da kanshi ya salami Sauran samarin ahankali suka Dena zuwa sai wanda zasu aura kawai.

Fateemah ma an fara girma an kusa gama primary anata murna.

Tun da akasa ranar bikin su Khadija mlm Abdu ya ɗan shiga damuwa ummi ce ma mai tausan shi akan Ai abin da Allah ya hore mai shi zeyi kuma Allah zai basu mafita ya dena damun kanshi har ya samu ya sami nutsuwa ba sosai ba.

Dama kudin auren su adanawa yayi, a kasuwa inda yake ma duk an sanshi ko bashi ya nema ana bashi dan baida wasa har limanci yana jansu a kasuwar dan yana da ilimin shi.

Lokaci nayi na biki ya samu da abin da aka bashi gudummawa na ƴan kasuwa da na mutan Jigawa masu kara ya samu ya ɗan karɓi bashi kaɗan yayi musu kayan ɗaki dashi da ummi da yaran sukaje kowacce ta zaɓi daidai ƙarfin shi, ya siya suka taho da su mota biyu aka zubasu a wani ɗaki da babu komai aka kulle.

Duk abu na talaka dai sun siya wasu kuma an basu gudummawa dan ummi ma ta fara zuwa Islamiya har tayi tsirarun ƙawayen Har sun Bata gudummawa.

Baƙin Jigawa suka zo ɗaki biyu aka ware musu a gidan maza aka basu ɗakin zaure suka sauka Gashi sun taho da kayan abinci babu abin da aka nema haka akayi bikin lafiya taro ya watse amare sunga ƙara da gata na al'ummar gari haɗuwar mutunci aka kaisu Gidajen su Sunata kuka ummi Har taya su tayi fateemah auta kuwa da taɓara wai itama a gidan su zata zauna duk da ta fara girma itama.

Bayan biki ahankali mlm Abdu ya fara biyan bashi d yaci har ya gama biya har wani kyau yayi sai ya fara gina fateemah duk abin da ya gani sai ya siyo ma fateemah indai kuɗin shi zai kai ko ya namu na masu ƙaramin ƙarfi dan ita kaɗai ta rage mai.

Khadija da Hindu suna zaune a gidan su lafiya da mazajen su wata iriyar soyayya suke nunama junan abin Har ya kusa ba mutum tsoro gashi sai Allah yasa dangin mijin duk suna son su dan yaran mlm Abdu suna da shiga rai kamar wanda ake koyama rayuwar zama da kowa lafiya shi yisa basu da matsala da kowa ko abokin faɗa basu da shi tun barin su Chadi basu sake sanin wani abu wai baƙin ciki ba sai farin ciki da samun ci gaba.

A shekarar su ta farko suka haihu Khadija ta sami ɗa namiji akasa sunan Abdu suke kiran shi musaddiq Hindu ma Namiji ta haifa Sunan uban mijin ake kiran shi Areef, akayi taron suna lafiya, daga baya kowacce ta koma koma gidan ta dan tsirar su sati biyu ne da haihuwar fateemah tasha renon yaran, masu jegon sun sami kulawa daga dangin miji da mazajen nasu ga abun arziki daidai ƙarfin su.

Tun da aka sami yaran nan kusan duk bayan sati biyu sai fateemah BINTU taje gidajen yayun Nata ɗan tayadu raino.

Fateemah har an shiga jss one an fara zama manyar yara tana ta karatun ta duk ranar da yayun ta suka zo gida sai ummi tayi da gaske take tafiya makaranta boko da Islamiya.

Yaran su nada shekara guda mijin hindu ya ɗauke su sukayi tafiya sakamakon kasuwa da ta tsaya mai sai abokin shi ya ja shi zuwa kudancin ƙasar nan, har sai da suka shekara biyu.

Duk sai Hindu da ƴan uwa da suka ji babu daɗi sai waya da sukeyi kawai, lokacin fateemah an shiga jss 3.

A shekarar su Hindu suka dawo gari akan yaci gaba da kasuwancin shi a gida kamar yadda iyayen shi suka nema.

Har sunje biki Jigawa gaba ɗaya gidan akwai wani da za a sake na nusaiba akan su ummi bazasu sami zuwa ba sai dai su Hindu da Khadija da fateemah sunce su zasu koma, basu koma ba ma aka daga bikin sai wata shekarar.

Rayuwar gidan mlm Abdu cike da jin daɗin yaran shi na zaune lafiya sai autar shi kawai, sai Hindu da ta sake samun ciki wata yara ta haifi yarta macce nimrah, lokacin kuma Khadija ta sami ciki mai laulayi har sai da fateemah taje ta ɗan zauna mata anan ƙanin mijin ta yaga fateemah ya fara nuna alamun so Khadija ta dakatar da shi ta nuna mai karatu zatayi kar ya fara ma ta dai mai bayani dake yana da fahimta ya haɗiye mugun yawun shi.

Yaron Hindu ya fara wayo, cikin Khadija kuma yana wata shida tafiya biki Jigawa yazo suka dinga zumuɗin zuwa bikin nan har anko Khadija ta musu da su Abdu sukace su zasu tsaya a bikin Maƙotan su na abokin malam Abdu, fateemah ma suna da karatun musaɓaka a Islamiya tafiyar tata a ƙila waƙala take su kuma yayun sunfi son su tafi da ita.

Mijin Khadija har ya hana ta tafiya bikin da yaga dai tana son zuwa sai ya barta, ranar suna zaune sai tace "Abban musaddiq da gaske fa in baka son naje zan iya haƙura, naga kamar bana hankalin ka be kwanta da tafiyar nan ba, sai na haƙura ai baka taɓa hanani ba kana da hujja in kace ba sai naje ba"

Ya mata wani kallon so da tatali ya rungumo ta yana shafa bayanta zuwa gadon bayan ta "toh in kin tafi wace dinga miki tausa a gadon bayan ki? Kinga cikin nan da ciwon baya yazo miki in bani ba wa kije da shi da ze dinga taushe miki bayan har ki samu ki ɗan ji daɗi acan"

Ƙara shige wa tayi jikin shi "kuma haka ne fa my Dee, hannun ka kawai Naji ajikina nutsuwa yake sani, umm nama fasa tafiya
Kasan kwanakin nan sai na dinga jin banaso nayi nesa da kai kamar wata zata ƙwace min kai, in mun samu kaɗai ci har ji nake kamar kar mu rabu, kuma fa abun kullin a ƴan kwanakin nan gaba yake ƙara yi fa my Dee "

wani hot kiss ya Bata Kafin Yace" wai kina jin yadda nake ji ashe, baki lura bana son nisa dake ba? "

" na lura mana, sai nayi zaton ko buƙata ce take hana ka nesa da ni"wani cakulkuli ya mata kafin yace "da baƙatar ma Amman begen Ki ne kan gaba da wata wutar son ki da kishin ki da yake sake ruruwa a ruhi na na kasa gane ko na meye"

"kace duk abu guda muke ji, to mu haɗiye junan mu kawai mu hutu"

"toh muyi hakan in ze yiwu"

Dariya suka sa gaba ɗaya, ranar wani irin faranta ma juna suka shagala da yi hatta girki ranar basu sami damar yi ba fita kuwa be samu yi ya fita ba,tafiyar ma sun kusa haƙura da ita, Amman a ranshi yana ganin in ya hanata be Mata adalci ba, sai ya amince taje kawai, sai da ta tabbatar har ranshi ya amince kafin ta yadda zatayi.

A washegarin ranar Ma ya ɗauke ta a babir ɗin Shi ya dinga zaga dangin shi da ita suna zuwa gidan gwagwo mahaifiyar shi ta karɓe musaddiq, suka sami damar yawon ziyarar su dan taga ga ciki ga yaro sau ta tausaya mata, har inda be taɓa kaita ba ya kaita basu suka goma gida basai sha ɗayan dare musaddiq ma a gidan su ya kwana
Chapter 9 · 0% Book details