← Book details Rai Da Ruri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 9

Sashe 4

Rai Da Ruri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau ya kama Lahadi da wuri fateemah ta shirya dan tafiya tahafeez, kafin ta fita ma ƙawarta lubna ta biyo mata suka tafi bayan tayi shara da wanke-wanke dan bata so ta barma ummi aiki.

Bayan sun bada hadda aka musu ƙari, har lokacin break yayi sukaje sukayi suka dawo lokacin ana ta shirye-shiryen sauka da ƴan sauka fateemah na ciki da ƙawayenta.

Bayan ta dawo gida taci abinci ta koma dake wuni suke acan.

Ummi taso ta dinga kaimata Abincin ta hanata dan bata so mahaifiyarta ta wahala akanta na ɗawainiyar Kai mata abinci.

Tana gab da komawa ne bayan tazo cin abincin ciwon mara ya turniƙe ta wanda tama manta shaf da lamarin shi ashe tana gab da baƙon watanta ne, komawa makarantar da bata yi ba kenan dan in ya tashi mata baya mata da sauƙi dan ma ba duk wata takeyi ba wani lokacin har kusan wata uku takeyi kafin tayi wani lokacin kuma wata biyu in yazo dai ta kan sha wahala har suma take kafin ta farfaɗo ko ta kusa fita a hayyacin ta, yauma har suman tayi Sai abin Yama ummi daɗi da ya sameta a gida, ta sake ƙudirar aniyar sake mayar da ita asibiti dan ganin likita karo na uku..

Sai da ta sami bacci na wasu awwani kafin ta samu sassauci sai a lokacin ta tuna da makaranta ma, bayan ta yi wanka ta gyara ta rasa yadda zatayi dan akwai karatun da bata so ya wuce ta tasan ummi bazata barta ta koma ba dole ta haƙura.

Har lokacin tashi yayi, lubna tazo gidan su da sauran litattafan ta da ta bari a makaranta.

"ya naganki haka? Ko abun ne?" lubna ta tambayi fateemah.

"hmm bakijini shiru ba, shine y kusa halakani" ta bata amsa.

"wani irin halakawa kuma in da sabo ai kin saba duk da ba'a ba a sabo da wuya, duk da ke ɗin jaruma ce ji nake da nice da yanzu sai gawata"

"Hmmm haka dai kika ce da kece ma wataƙil ki fini dauriya"

"ina fa nafi ki, Kedai Allah ya rabaki da ciwon nan lafiya duk da wasu sunce wai sai Aure, to uwar me zesa Sai a auren ze dena ya Dena yanzu mana, nima fa ɗan guntun ciwon da nake fadeela tace min ina Aure zan neme shi na rasa, na tambaye ta dalili munafukar taƙi faɗa"

"ke hawar wani tambaya kike ni banma taɓa ji ba sai a bakin ki kuma in jikina duka kunne ne ban yadda ba"

Lubna ta miƙa ma fateemah sauran litattafan ta "yauwa ustaz Aliyu ya mana karin Arba'una da gulubul maram duk in kin sami lafiya na biya miki iya inda na fahimta in da ban fahimta ba ya biya miki ko kya tsinta a muraja'a ɗan nasan baki da matsala"

"toh shikenan nagode"

"yauwa barin tafi kafin mama ta fara turo min su shema'u "

"yauwa to nagode sosai"

Lubna tama fateemah sallama ta wuce gida.

******

"wanan shine tashi na uku da zan miki daga shi babu ƙari sai dai Ko yaa Abdul yazo ya tashe ki Ko Ammah"

Nihal Najin Mimi ta ambaci sunan Abdul ta buɗe ido da ƙyar ta fara turo baki "Alhudahuda sarkin karatu, kina shiga hakki na wallahi shiyisa jami'a tafi daɗi karatun ƴanci ka shiga lokacin da Kaga dama, ai dan haka na dage sai da aka Mana jumping na 2yrs ɗinan da yanzu bamu shiga jami'ar ba ma da yanzu banyi kyan ganin nan ba ma inajin"

"ke dai kika sani kiyi saɓo ko firta abin da ze iya fitar dake daga musulunci naga hankalin ki na nisa dake wani lokacin, ba dani zakiyi ba sai dai kiyi da bangon ɗakin nan" mimi na gama faɗa ta fara shirin barin ɗakin.

"wai kafirtani kike son yi ne? Mena faɗa da, aki kafirta ni? Ba gaskia na faɗa ba kinfi kowa takura min a gidanan" nihal ta Mike ta shige bathroom.

Mimi kuwa ta fice ta barta da mitar ta.

"Good morning yah Abdul" mimi ta firta ma Abdul d suka haɗu a baban falon su.

"morning sis meemee, kin tashi lpy?" ya mayar mata da kulawa.ya tambaye ta

"lafiya lau"

"ina yarinyar nan bata tashi ba ko?" Abdul ya tambaya yana kanne ido.

"eh toh yanzu dai ta miƙe zata shirya" mimi ta bashi amsa.

"Hmmm, in bata fito ba nan da 20mints ki wuce makarantar ki kuma sai na hukunta ta a gidanan"

"Ok yaya" kawai mimi tace.

Suka zauna a dining zasu fara break Kenan, sai ga Ammah da Dady sun sauko.

Da sauri mimi ta fara gaishe da Dady da girmamawa da shaƙuwa irin ta ƴa da uban ta, kafin ta juya ta gaishe da Ammah ta amsa da walwala atare da ita har tana shafa kan mimi tana sa mata albarka kafin suka, zauna dan Dady yau a falon ƙasa yake son yin break da iyalan shi.

Dady har ya buɗe baki ze tambayi nihal, kawai ya hango ta tana tahowa, Abdul ne yayi wata muguwar ƙwafar da sai da kowa ya kalle shi, Ammah ta mai wani kallon kafin ta firta "akwai wani Abu ne son?"

"a'a" kawai ya bata amsa ya fara haɗa tea.

Shiru tayi badan ta yadda ba, har nihal tazo Ammah ta fara gaisarwa ta rungume ta Kafin ta koma kan Dady ta mai side hug "morning Dady"

"morning daughter, Sai Yanzu aka tashi?" Dady y tambaye ta.

"eh Dady baccin ma bai ishe ni ba" sai muryar Abdul taji yana firta mata.

"ko zaki koma? Akwai wanda ya miki dolen tashin ne?"

Shiru tayi sai sum sum da tayi ta fara neman wajen zama ba tare da ta amsa mai ba, shi ko ya tsare ta da idonduna.

Tana son gaishe shi mata kasa sai da ƙyar ta iya firta "yaa Abdul Ina kwana?" tana turo baki tana kallon Ammah da ta haɗe rai.

"da ban kwana ba zaki ganni" da sauri ta fara haɗa tea, Dady yana ta kallon su yana murmushi, Ammah na haɗa mai abin da ze karya da shi.

"son yi mata ahankali ko dan health ɗinka kaji? Ka dena sa damuwa kowa a ranka"

Shiru Abdul yayi sai amsawa da yayi da kai kawai dan haushi nihal ɗin ta bashi.

A haka har suka gama Dady ya fita tare da rakiyar Ammah da Abdul sai su mimi da suka wuce bayan Dady ya tafi, gidan ya rage daga masu Aiki sai Ammah d Abdul ɗinta.

"Ammah Na kunyi maganar da Dady?"

Ammah taba Abdul Amsa da "son yace abar maganar sai ya dawo sai muyi, yace kuma dole yayan ka ya sani shima muji amincewarshi Ko rashin Amincewar"

"Ammah!"

"Abdool!" itama ta kira shi kafin ta ɗora da "ka bari zamuyi maganar anjima kaji?"

"toh Ammanh" ya amsa da bin umarnin ta.

Kafin suka shiga wata hirar.

Abdul nata chart a wayar shi da yayan sa "haba yaya munyi missing ɗin ka fa sosai"

Broh H
"me ka rasa da bana kusa da kai?"

Abdul.
"kai yaya ganin ka ne kawai, irin innayi tsokanababu mai tare min" sai yasa tura mai sticker dariya.

Broh H.
"kayi tsokanar ka mai lasisi kai da kake da Fahaad har wani ni kake nema?"

Sai da Abdul yayi dariya sosai kafin ya bashi amsa "hakane fa kuma fa yaya"

Broh H
"ya nihal fa tana ta halin koh da sauƙi nade ce ka Dena biye mata duk abin da tayi ka sanar min komai ƙanƙantar sa, mimi bani da case da ita, karatu dai sunayi sosai yadda ya kamata ko?"

Abdul.
"eh kasan ba'a rasa ta da cases Mu Ai itace ciwon kanmu a gidanan, mimi ko normal baiwar Allah"

Broh H
"me da me tayi ko ta sake gigin kawo wani mai tsautsayin ne gida?"

Abdul.
"a'a kawai dai ka share yaya ba wani big case bane sai nasu makara ko yau mimi ta rigaya shirin Islamiya, ga raina mutane in taso wulaƙancin"

Broh H.
"OK banni da ita zanyi magana da ita in sun dawo, inaso ka karɓi wayar ta kamin investigation akai in and out dan kanta Yana rawa a university Nan bawai dan Ina zargin ta ko tunanin zata aikata wani abu ba sai dan karta tara banzayen contacts a wayar ta Ko chart da kowa, Har da ce min wai na sai musu mota fa last week, yarinyar Nan Ko guda ɗaya ce ita da mimi, Nace to ta bari sai ta zama Ammah wacce ta kawo ni duniya ba dan naga kamar umarni taso bani, shine bata sake maganar ba har yau.

Dariya kawai Abdul yayi da, kafin ya amsa mai da "Hmmm ai kanta yana hayaƙi yarinyar fa kaine maganin ta Nifa ma fa saboda su Dady da Ammah nake rabuwa da ita da na motsa saboda issue ɗin ka, ni wani lokacin bani jin daɗi ma sai naga kamar mai wata muguwar lalura ake kallo na, Alhalin lafiya na qalau ta kowanne fanni yanzu dai kam"

BrohH
"kai dai ka dena biye mata, kuma ba kallon mara lafiya ake ma ba, ai koni kama fini lafiya ƙanina tunawa suke da baya da abin yaƙi ɓace musu Amman lafiyayen mutum ne kai Ai ƙanina"

"yauwa yayah Kaine Kawai kake kallo na a haka shiyisa raina fansa ne a kanka, luv u so much my nakusa da ran, Bayan Dady fa sai kai wallahi Allah" sosai kalaman yaman Yama broh nashi daɗi kuma dama dan yayi farin ciki ya firta mai, dan suna ji da junan su jini ɗaya ba wasa ba yana kyautata ma ƴan uwanshi gaba ɗayan su,baya Shayin musu komai duk abin da suke so ze musu ko nawa ne ze iya kashe musu duk shi yake ɗaukan nauyin su Dady kawai ƙara musu yake.

Bayan sun gama chart ɗin sukayi sallama saboda brother nashi ze shiga office,a ƙasar da yake.

Murmushi ya dingayi bayan yaba Ammah labarin yadda sukayi da Yayan nashi tana ta musu addu'a da ɗorewar zumuncin su da yadda suke kula da junan su har iya rai da mutuwa, kafin ta koma kan mimi da nihal.
Chapter 4 · 0% Book details