Sashe 3
Rai Da Ruri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana cikin tafiya ta ga wata mota tasha gabanta, sai tayi zaton parking motar zatayi sai ta kauce ma motar tayi kamar tazati gefe tayi tafiyar Ta sai, taji an kira sunan ta "Fateemah kin kusa makara fa kizo akaiki dan ki Isa da wuri"
dumm! Taji ƙirjin ta ya bayar sai ta fara tunanin in da yasanta har ma da sunan ta, bata fita daga tunanin ba, ya ƙara mata da wani tunanin "indai bakya son dukan makara kizo in ajiye Ki, in kuma kinfi son dukan toh Allah ya kiyaye Amman teacher zanzaro Yana Nan Har ya fara dukan yan makara kuma zakice na gaya miki"
Bata san lokacin da ta ɗago ba ta kalle mai maganar daga cikin motar da bama ta yadda da motar ba da mai motar gaba ɗaya sai gashi ya sake shayar da ita ruwan mamaki ya akayi yasan teacher zanzaro? Ta so zargin ko ya santa Amman zuciyar ta taƙi bata daman yadda da hakan, sai ta ma mamalakin motar kallon ƙarshe, fuskar shi rufe da nose marks da glass duk yadda taso gane ko waye ko ta san shi bata ita ba, sai kawai ta tsinci kanta da firta mai.
"malam nagode, Amman babu inda zan shiga yadda na saba tafiya haka zan tafi" bata jira me zece ba ta wuce shi tayi tafiyar ta.
Yaso bin ta sai kuma ya fasa ya ɗaga waya, yayi magana ta tsawo minti 30 kafin ya kashe wayar ya bar unguwar.
Fateemah na isa taga ana dukan makarar kuwa da gaske taji ranta ya ɓaci bata son abin da ze taɓa lafiyar ta yanzu jini ze taru ahanun ta ita tama manta yaushe rabon ataɓa lafiyar ta, cikin ayari ta shige jerin wanda suka jiran dukan yazo kansu, ana zuwa kan balaraba Sadiq ana zamɓaɗa Mata ɗaya tasa ihu ta kwasa da gudu zata gudu cikin harabar makaranta ya bita yasha gaban ta ya dawo da ita tana kuka sai da ya mata guda biyar masu zafi, hasana Usman kuwa da aka zo kanta gocewa ta dingayi Har yace sai ya mata goma, ana haka malam Malam Ali yazo ya nuna fateemah "sorry Sir Fateemah zo nan kiyi wani aiki pc ne yace na nemo yar class din ku mai hankali da nutsuwa ba irin masu ihun bulala ba" wanan maganar malam Ali ita tace ci fateemah ya kaita office tana ta ajiyar zuciyar ta tsira daga duka dan yau kamar da gayya yake dukan ma.
"yauwa Fateemah Sadeeq ga sabuwar ɗaliba tafi da ita ajin ku yau ta fara zuwa sai ki nuna mata abin da akayi da bata nan"
"OK sir" fateemah ta amsa.
"firdausi Usman abin dabaki gane ba ki tambaye ta baki da matsala sai ki dage"
"Tom malam" firdausi ta amsa mai, suka tafi har class tare da jagoranci fateemah suka sami mazauni suka zauna.
Bayan an fita break wasu daga cikin ɗalibai suka fara tsegumi Fatima da bata kula mutane sosai tayi ƙawa ashe girman kai ne yasa bata kula su sosai ita ba ƴar kowa ba, ita kuma firdausi tun da aka haɗa su take gani babu da wanda ta saba sai fateemah shi yisa taƙi matsawa daga kusa da ita, Fateema kuwa dama ba kowa take kulawa ba karatun da ya kaita shi kawai takeyi dan tana ss two ne yanzu daga sss one ta fara makarantar bata biye ma duk shirmen ƙawaye balaraba sadeeq Kawai take kulawa sai tsirarun ɗalibai masu nutsuwa Itama balaraban dan sunan baban su yazo ɗaya ne amma tafita rawarkai.
Har sai da aka tashi suka fito tare sanan suka rabu a hanya kowa yayi hanyar gidan su, fateemah ta samu suka rabu da firdausi.
Koda ta isa gida a ajiye dan tataki tayi kuma makarantar da tazara tsakanin ta da unguwar su, tana shiga cire kayan makaranta ta nufi bayi ta watsa ruwa Ummi nata mata sannu da dawowa.
Tana fitowa ta samu ummi ta rabza uban tagumi ta Lula dogon wani nazari da alama wani tunani take da yake son zame mata jiki, har fateemah ta fito ta tsaya na daƙiƙu bata san tana kallon ta ba sai da ta tsinkayo muryar ta.
"Ummi! Ummi!!" firgigit ta juyo takalle fateemah.
"ummi yaushe zaki rage ma kanki wanan tunanin ummi? Kefa kike ƙarfafar mu da Abdu tunda muka dangana muka yadda da ƙaddara mai kyau da mara kyau daga Allah take, sai ke kuma kika maye gurbin mu da tunani ko da yaushe in abin ya faɗo miki ko kika tuno, natabbata tunanin su..."bata ƙarasa ba, ummi ta datse ta.
" hmmmm BINTU iya juyama tunani baya inayi Amman sai yashaa gaba na in abun ya motso har yanzu gani nake kamar mafarki nake, kamar akwai ranar da zan farka daga mumunan mafarkin da na jima da imanin kamar babu ranar farkawa"
Fateemah ƙarasawa tayi kusa da ita ta dafata da kulawa da rarashi da tuna mata ƙarfin tawakkali da hukuncin ubangiji "Ummi duk munajin haka har masoyan mu da masoyan su, yadda na kasance ayanzu a gaban ki kaɗai ya isa mu godema gwanin hikima Mu Jinjina Mai mu cigaba da rungumar ƙaddara har iya rai da mutuwa"
"hakane kullin inna tuna hakan ko na kalle ki Ko na ga su Arfat Sai na sake gode ma Allah da wanan ni'imar, babu yadda zanyi ne na goge wanan ƙaddarar da Sanadin da tuni na goge Kodan samun nutsuwa ta da ku iyalaina a yanzu, Amman zan sake ƙoƙartawa, Kinji? Tashi kije ki sanya kaya, nagode da kulawa"
"hakane ummi, ke ɗin dole ta ce kuma gata ta duk abin da na miki ban bi yaki ba"fateemah na gama faɗa ta miƙe zuwa ɗakin ta da yake ko yaushe a gyare tsaf.
Bayan ta gama shafa mai babu jimawa aka kira sallah ta ɗauro alwala ta gabatar da sallah ta.
Bayan Abdu ya dawo ya kawo musu ýar tsarabar yalo da su Karas suka karɓa suna ta murna suna mai sannu da kasuwar da yake ɗan zuwa yake taya wani mai Shagon kayan masarufi jiran Shagon da tayashi awo,
"Ummi yau aka kawo sabuwar ɗaliba, duk sai naji na takura duk inda naje tana tare dani, dake pc da malam Ali ne suka haɗani da ita muka tafi class"
"ke dai kawai rashin son mutanen ki, Ina laifi an haɗa ki da ƙawa in halin ku yazo daidai ba shikenan ba sai ku taimaki junan ku, tunda kince duk ýan ajin ku da daman su sai ahankali" Ummi ta bata amsa Abdu nata lomar Tuwon Shi yana musu murmushi baya son Magana sai ya gama.
"kuma Ummi in Allah ya yadda bazan sake makara ba badan Taimakon rakata aji da zanyi bafa da na casu yau kamar dawa Ko casuwar shinkafa, tama fa taimake ni kawai zuwanta yau shi ya ƙwace ni a hanun teacher zanzaro"
"toh kingani ashe ma ta miki rana, sai ki riƙeta da kyau in kin yadda da ɗabi'u da halin ta, uwa Uma ilimi da mai da hankalin ta a karatu"
"toh gamu nan dai yau aka fara babu abin da zan fahimta tukunna, nadai Ara Mata wasu note books ɗina zata kwafi aiki, in tafiyar mu tazo ɗaya to Kodan na ƙarya ta ýan aji nayi ƙawance da ita in bata zo ɗaya ba sun jima basuyi tsegumin ba suje suyi tayi sunfi so kowa ya zama daƙiƙi kamar su"
"Kedai ki dage babu ruwan ki da kowa kiyi abun da ya kai ki" ummi ta sake jadada mata.
"in sha Allah, ummi na"
Lokacin Abdu ya kuskure baki ya zubar yana murmushi ya firta ma fateemah "Kinji dai Abin da ummi ki tace in wani abu suka miki akwai nagaba da ku babu ke babu ɗaukar doka a hanun ki, kuma maganar makara ki dinga shiryawa da wuri koni in narigaki ko ummin Ki tashi zan dinga ɗora miki ruwan wanka karaya kuma ko batare damu ba ki karya kiyi tafiyar ki"
"toh Abdu na Insha, Allah ya ja min da kwanan ku badan nafi kowa ba ya Allah" ta ɗaga hannu alamun roƙon ubangiji.
Ummi da Abdu suka mata murmushi suka amsa mata a zuciyar su suna jin wani abu agame da ƴar tasu tilo a yanzu, wanda Ada sun mallaki yara mata har uku lafiyayu har Suka girma suka Aurar da su har sun haihu a gidajen auren su dukan su biyun sai Autar su fateemah kawai yanzu.
Ranar Juma'a ma su fateemah da suka koma school duk saurin ta a makaranta ta sami firdausi, haka suka sake zama tare har aka tashi suka tafi gidajen su.
Ranar Asabar da sassafe fateemah ta shirya ma makarantar tahafeez ɗin su su a
Hanya suka haɗu da lubna Ahmad ƙawarta suka ƙarasa, suna zuwa suka bada hadda aka ƙara musu suka biya su hadisai kafin aka tafi break.
Ana shirin komawa break ne taji wani mugun abu ya mata dabaibayi mai kama da idanun kura a jeji da idan tasa maka arwa ko motsi bazaka iya ba ta ƙafar da kai a wajen kenan, itama kasa ɗogowa fateemah tayi ta fahimci wani mugun ido mai cike da tasiri ne ya mata ɗaurin huhun goro, Gashi ta kasa ɗagowa bare ta tabbatar, sai da lubna ta kamo hanun ta, ta samu kuzarin bin ta suka wuce ba tare da ta san me ya faru ba.
Har aka tashi suka tafi gida su huɗu da ƙannen Lubna, bilkisu da shema''u suna ta hira a hanya, dake unguwar su ɗaya sai ƙannen sukayi gaba ma suka barsu, lubna ta tsaya ma fateemah labarin wani saurayi da tayi Abban ta ya hanata, Ance yace ba yanzu ba fateemah nata bata shawarar bin umarnin iyaye dan ganin daidai a rayuwa.
08134624555
[29/03, 6:49 pm] Maman shaheed😍🥰: *RAI DA BURI*
PAGE 3
BY
MAMAN SHAHEED
Paid Book...
Ga Account ɗin da za'a biya 👇
3108794095
Fatima Abubakar
First Bank
Shedar biya 👇
08134624555
Ko Arewapen karatu mai fakasiti (capacity) 😍
Gidan su fateemah gidane madaidaici na masu ƙaramin ƙarfi, suna zaune lpy da Maƙotan su, makaratun da fateemah take zuwa duk ba wasu masu tsada bane Nadai ɗan talaka ne mai kwazo da son koyo.