Sashe 5
Rai Da Ruri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da yammah da suka dawo nihal ce ta fara shigowa babu ko sallama ta buɗe falo waya a kare a kunnen ta da alama waya take.
Bata yi aune ko saurare ba taji Ance "fita ki koma lokacin da kika koyo sallama sai ki shigo, fita nace!" ya firta mata da tsawa.
Da sauri ta katse wayar dan kashewa ma tayi gaba ɗaya jiki na rawa dan batayi zaton yana falon ba, Ammah na jin su da kallon su.
Komawa tayi bata da zaɓi har mimi ta shigo bakinta ɗauke da sallama suka amsa mata da sakin fuska ta nufe su ta musu sannu da gida kafin ta leƙa su baba A'ee a kitchen ta musu sannu, har lokacin nihal bata shigo ba.
Sai da ta gama tura baki da mita kafin ta shigo bakin ta ɗauke da sallama, zata wuce ɗaki Abdul ya sake ce mata "ke zo nan!"
Zuwa tayi tabi umarnin dole,hannu ya miƙa mata, ganin bata gane me yake nufi ba, ya firta mata "bani wayar ki keda kuke waya da har kike mantawa da sallama kamar ba ƴar musulmai ba haihuwar musulunci?"
Da sauri ta fara "laa yaya nayi fa kawai aciki nayi, kuma wallahi..." be bari ta ƙarasa ba ya miƙe yana sake miƙa mata hannu, da sauri ta ɗora mai wayar.
Ya karɓa yaga akwai security akai ƴa miƙa Mata buɗe min, da face lock ta buɗe ta miƙa mai, ya koma ya zauna ya fara duba kiran da ta gama, tasan tana da gaskia a wayar ta dan sun kurɓi ruwan da madarar Tarbiya Amman sai taji ƙirjinta na dukan tara-tara bama uku-uku ba dan ba abin mamaki bane ta taka ruwa ya Abdul yace ta tada ƙura, haka take kallon shi.
Yana dubawa da mintunan da ta ɗauka tana wayar yaga da ƙawar ta suke wayar yabi contacts ɗin ta tsaf babu wani abu da ya gani na rashin gaskia tun tana jiran shi har ta tafi ta barmai wayar, sosai ya lalube wayar har chart ɗin ta be kamata da laifin komai ba, kafin ya ajiye wayar a kusa da shi, suka fara hira da Ammah tana tambayar shi ko yaga tayi wani abu ne? Ya bata amsa da.
"a'a kawai dai daughter taki ce Ammah sai ana sa mata ido lamarin nihal in kin koma ummarah ki fara jefata a addu'a first kafin mu biyo baya" ya firta da gaskia yar shi har ranshi.
Dariya Ammah tayi kafin tace"toh Ai tare zamu har su Kaga kenan kaima, aka tayani itama sai tama kanta, dan ina tunanin Dadyn a nmai Alƙawarin kujera uku Sai yace ze cika biyu mu tafi tare, har yayan ku yaji yace shi ze biya har shi ma zamu haɗu acan, Kaga ko wanan maganar ita kaɗai ce bata sani ba dan da ta sani da ta ishe mu da surutu ƙawayen ta kuwa da sun fara mana suntirin tayata murna da zuwa tsegumi, mimi Ko Shiru kakeji Har masu aikin gidanan na sanar musu shiru nasan babu mai yayatawa itako na Barta a duhu"
"good Idea, Ai nihal ɗin ce dafa yanzu har maƙota sun shigo tunda ita kowa naka ne ga alfahari da arziki da nihal takeyi kamar ba ƴar gado ba kin taso a Abunan Amman kamar sabon shi ga, ni ai dan kince in Dena ce mata nafison mimi ne da na tattara ta nasa sata a kwandon shara, toh jini ɗaya ma baze barni ba da inada yadda zanyi da na maida ita kamar mimi to bani da wanan ikon, nima ai baki gayamin ba Ammah Sai Yanzu? "
Dariya Ammah ta mai" toh ba gashi ka sani ba, kuma ai nasan zaku yi maganar da dadyn ka Ko yayan ka ne shiyisa "
" haka ne to ya manta ko maganar ce bata zo ba kuma addu'a kam zata shashi kamar dan ita zamu tsabar addu'a, tafiyar fa zatayi ma'ana Ammah musamman da Naji da yayah"Abdul ya firta.
"sosai ma kuwa In sha Allah, ya karatun ka kuwa kun gama presentation ɗin?" Ammah ta tambaya.
"mun kusa dai Sai week ɗin nan in Sha Allah, ga project akwai fa aiki" Abdul y nuna alamar kamar ya gaji yana yamutsa fuska.
"toh ya za'ayi sai addu'a ai, Allah ze dafa Nadai gayama ga uncle D Nan duk wani taimako da kake buƙata shima ya gaya ma ga abokanen yayan ka kai ɗan gata ne ta ko ina baka da case nafi son ƙoƙarin Kane Ma dan Dama Kai mai ƙoƙarin ne da kana kwance za'ama komai toh nafison kaci gumin ka, ƙwazon ka ya baka komai sai Allah yasama abun Albarka Amman babu hanyar da bamu da shi"
"hakane Ammah shi yisa Nima bana kallon wanan nake abuna wani lokacin na samu mafita ta da kaina ba tare da su ɗin ba, Amman in wani abu ya gagara dole zan taɓo su musamman a final year ɗinan"
"hakane Allah ya taimaka, Ina Alfahari da ku ai, ko zaman mu a America kunyi gogaya da turawa baku zama marasa hazaƙa ba duk da kuna yara ne bare yanzu, Komai baze gagare ku ba Insha Allah"
Sun jima suna hira kafin suka tafi gabatar da sallah magrib, akaci abinci dare har lokacin wayar nihal na gurin Abdul kira kuwa ƙawayen ta sun kira kusan mutum biyar sai namiji guɗa ɗaya da yaga ansa Hafiz grp dsc Sai ya fassara abin a (group discussion) Kawai dan Har ɗagawa yayi sai yaji ya fara mata maganar group Assignment da aka basu yayi shiru kafin ya katse kiran.
A ranar be bata wayar ba gashi tana son amfani da kayan ta dole ta zuba ido sai mita da take tayi, mimi na ce mata "ai ba anan zakiyi ba kije ki same shine"
Taƙi kulata ta nemi mimi ta bata Aron wayar ta, mimin ta hanata Wai bata son gayyar ƙawayen nan nata masu katin samari su dameta awaya dan in suka fara waya basajin Kati dake basu suke saka katin ba har su dami mimi.
Washe gari da zasu school shine ta mai gaisuwar mutunci ya jaja Mata kunne da gargaɗi mai yaji ya bata wayar har da mai godiya dan ta zata baze bata a ranar ba sai taga ya bata.
Tasha tsokana kuwa wajen mimi Har tana ce mata "mai ladabin kura" nihal ta murguda Mata baki, zata mata rashin kunya ta murɗe bakin.
A shool Kowa department ɗin Shi da ban sbd course ɗin Kowa daban Kawai time ɗin lecture ɗin Su ne yake zuwa kusan ɗaya ko wani ya jira wani Amman da karatu ya fara zafi wata ran dole su tafi daban daban.
Nihal ta gama lecture ɗinta na 11:30am sun fito da bilkis da su dinner suna magana kan karatun su sai Faisal Abokin Abdul ɗin Su yazo wucewa ya gansu sai ko ya Tako har inda suke gefen wani hall"ƙanwata ya lecture? "
" yah Faisal Ina wuni Kwana biyu, Alhmd, mun fito sai 1 kuma zamu shiga"
Sai ƙawayen ta suka fara gaishe shi, duk yabi ya amsa, suna tsaye a haka sai wayar Faisal ta fara ringing alamun kira ya shigo ya ɗaga "Hello yaseen Abdallah ya Ne?"
Tun da nihal taji sunan da Faisal ya kira ta bada attention ɗinta a wayar da suke kamar da ita ake.
"OK, Ina kusa da hall ɗinan Inda ka sameni shekaranjiya"
Wani blushing nihal ta fara ganin kar a gano ta sai ta seta nutsuwar ta, har Faisal suka gama waya tana jin su, haka kawai yaseen Abdallah yake birgeta Kawai abun da yayi katanga a tsakanin su shi balaraben Libiya ne aiki ne ya kawo su Nigeria uncle ɗin Shi ya buɗe kamfanini yaseen ɗin yake kular mai da wasu inya gaji ya tafi yawo gashi ya gama karatun shi tun a Tripoli bare yace karatun Nigeria ne yake birge shi har masters Ne da shi yayi karatun shi kashi kashi yama girmi Faisal ɗin Kawai abota sukeyi Mai tsafta Saboda Faisal ɗin ƙwaro Ne kwanyar sa tana ja yana final ya ɗin shine Yanzu na masters to Abdul ya bashi alhakin kula da su mimi ne kafi ya gama shima ya dinga taya shi dan duk makarantar su ɗaya, karatun kowa ne daban.
Suna nan babu jimawa yaseen yazo ya parka Wata Benz ɗin motar da ta tafi da imanin su nihal gaba ɗaya dan kowa sai da yayi addu'ar (Allahuma arzukuni sayyara) Yana fitowa kallo ya koma kanshi maza da matan da suke wajen gashi yadda ya fito a wani haɗaɗen balarabe mai kwarjini da haiba ga kyau na
Asalin Larabawan Libiya,Amman in anso ganin munin shi za a fahimci yana da ɗan gatso a haƙoran shi.
Ganin ya nufi wajen su nihal sai kallo ya koma kan nihal a gulmar student Wajen nihal yazo, kowa da abin da yake tofawa, nihal kuwa class ɗinta ta tsaya tatarowa Har ta ɗauke ido daga kanshi dan kar raunin kallon shi ya shagaltar da ita.
Yana ƙarasowa yaba Faisal hannu suka gaisa da larabci dan Faisal ɗin ƙwaro Ne kusan yare uku ko huɗu yake ji kuma ƙwarare ne dan ƙwaramcewar shi ne yasa suke abota da Abdul dan shima yana jin duk yaruka ukun nan da shi da yayan shi na America, sunajin larabci, turanci da French ga Hausa yaren su na gado, saɓanin su nihal da suka ƙi dagewa a jin larabci da yi sosai har su goge da French gara mimi ma sukanyi French da Dady larabci Kuma da Ammah dan tasan addini sosai fiye da boko,duk da hakan ma suna iya magana da larabci sosai kawai basu goge bane musamman nihal.
Faisal suna gama gaisawa da yaseen ya fara cema yaseen shifa cafeteria zeje dan Ko break beyi ba, sai ko yaseen ya kalli su nihal ya fara musu magana da larabci alhalin yana ɗan jin Hausa Faisal Ne Kuma ya koya mai har waƙar Hausa yake bi ya ɗora a social media musamman TikTok.