← Book details Rai Da Ruri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 9

Sashe 2

Rai Da Ruri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙwafa ya mata ta wuce bedroom ɗin su da sauri ta ajiye jakar ta ta faɗa bathroom.

Mimi kuwa tsayawa tayi tambayar Abdul ina Ammah, yace tana sama tasan Dady baya nan ta haura sai da ta mata barka da gida kafin ta sauko, ta wuce ɗakin su.

"kede mai hali baya fasa halin shi kullin magana ɗaya, laifi uku cikin ɗaya ko Ince a mintunan da basu wuce shabiyar ba"

Nihal a fusace da tsiwa tace "me nayi kuma sai ki lisafo min su Naji"

"mara kunya gurje miki baki zanyi ni, kin dawo kin samu yaya a falo baki iya mai sannu ba sanan bakiga Amma ba ko ajikin ki, nan mun dawo ɗaki kamar ba mace ba jaka a gado Takalmi a capet, hijab a bedside Kamar ba mace ba ki canja hali gidan wani zaki"

"duk ni kaɗai, wlh badan nasan uwa da uba ɗaya bane suka haife mu da nace kin tsaneni"

"yanzun ma kin faɗa ai, halin ki ne abun tsana, ki gyara"

"anƙi ɗin"

"ke kika sani" mimi ta ɗage kafaɗa, kafin ta kwashe komai da Nihal ta zubar ta adana a inda ya dace ta adana nata ma, ta shige bathroom.

Abdul na kamalawa, Ammah na sakowa Daga Sama.

"yauwa Abdul kazo ka karɓo min saƙon a Shagon ƙaraye na samu na ware wanda zanyi amfani da shi dan kar nazo gobe na manta jibi kana makaranta"

"toh Ammah uwa ta gari yanzu kuwa" ya taso yana goge baki da tissue.

"Amma wai Nihal kullin magana ɗaya meyeke damun ta ne?"

"me tayi maka kuma dan Allah bana so kana sa damuwar Nihal ko wani abu bare har ya dame ka ka mata addu'a ai da sauƙi ma yanzu, me tayi?"

"hmm shikenan dama kawai naga sun dawo mimi sai da ta ganki hankalin ta ya kwanta tasan kina lafiya, Itako ko oho, nima fa kamar bata ganni ba sai da na kira sunan ta kafin ta min magana, Wai ni? mimi?" ya nuna kanshi d mamaki.

"kayi haƙuri koni haƙuri nake da ita bawai dan banda yadda zanyi da ita ba sai dan kawai na rabu da ita da halin ta, haka Allah ya yota ya tsindumo ta cikin mu dole mu karɓe ta a yadda take duk da haka muna yima tufkar hanci Ai Kaga da wani gidan ta samu da yanzu wata maganar ake ba wanan ba, tsangwama, kyara, zagi, duka, rashin ja ajiki baya gyara yaro, ku tayani da mata addu'a ku dena biye mata tunda mun fahimci bata da Aljanun komai sai banbancin Ɗabi'a kuma kai fa nata ne tafi ji da kai akan yayan ku"

"ai munafuka ce haka dai take cewa tafi rainani ai, Abayan ido na ta nuna ni wanta ne a gaban Idona dani da banza duk ɗaya a wajenta"

"assha! Bana son irin furucin nan dan Allah, a dena kar na ƙaraji"

"toh Amman in sha Allah" ya faɗa da girmamawa ta miƙa mai makullin motar ta da Atm, ya karɓa, ta mai a dawo lafiya ya fice.

Maman shaheed ce😍💃🏼
[29/03, 8:04 am] Maman shaheed😍🥰: *RAI DA BURI*

PAGE 2

BY
Maman shaheed

Free pages basu d yawa, guda 5 ne..

Ga Account ɗin d za'a biya👇
3108794095
Fatima Abubakar
First Bank

Shedar biya...
👇
08134624555

Fitar Abdul keda wuya, nihal ta fito falon ta samu Ammee, sai a lokacin taje gareta.

"Amme sannu da hutawa"

"yauwa, an dawo?" kawai Ammee ta bata amsa dan in da sabo ta saba da halin nihal dan ma tana tsaye akanta.

"eh Ammee, yaya Abdul fa?"

"baki da number shi ne na baki?" Ammee ta bata amsa.

Sai taga kamar baƙar magana, Ammee ta gaya mata,gashi babu wasa a fuskar ta.

"a'a Ammee, naga bangan shi bane kawai"

"uumm, sai ki tafi neman shi" Ammee ta sake bata amsa ba tare d ta ko kalle ta ba.

Ganin dai Ammee kamar a fusace take da ita sai ta lalaɓa tabar wajen, musamman da taga fitowar, mimi tasan in suka haɗu Sai ta gane tayi ba daidai ba.

Kitchen ta nufa dan neman abin ƙwalama da zata ɗan sa abakin ta, tama su baba A'ee sannu, da Laraba, dan aikin girki suketayi na gidan gaba ɗaya.

Abdul be jima ba ya dawo da wata babbar Leda guda ɗaya, da saƙon Ammee, ya ƙarasa har gabanta ya bata, tana ta mai sannu sa da dawowa, sai da Ammee ta duba komai taga dadai ne saƙon Nata kafin ta ware na kitchen tasa aka Haura mata da sauran saman Dady.

Bayan magrib kowa na falo suna zaune gaba ɗayan su, sukaji motar Dady da alamu ya dawo ne, Nihal ce ta zabura zata tashi taje dan yimai oyoyo, wani mugun kallo da Abdul ya mata shi ya tsaida ita dan inda sabo ta saba da Dadyn ta musamman da yake nuna mata itace auta shiyisa take duk wasu abubuwa dama babban wansu ne dodon ta da ya dawo gidan komai nata yake setuwa.

Abdul ne yaje ya taro Dadyn ya riƙo mai jakar shi har suna ɗan taɓa hira a hanyar, sai da suka shigo, nihal ta tafi da sauri.

"sannu da zuwa Dady, an dawo lafiya"

"yauwa, lafiya lau ya naga kina behaving Kamar mara gaskia?"

Da sauri kowa y kalleta, tayi mitsi-mitsi da idanduna kafin ta bashi amsa "Dady babu komai kawai na gaji ne da muka dawo daga Islamiya"

"OK, sannun ku toh, Allah yayi albarka"

"Ameen" ta amsa.

"Dady sannu da zuwa, an dawo lafiya?" mimi ta firta.

"mimi lafiya ya gida ya karatu?"

"Alhamdulillahi Dady" mimi ta bashi amsa.

"my love an dawo? Ya hanyar?" Ammee ta jefo Mai nata tambayar d ta bari kowa y gama nasa.

"My Dear lafiya lau, ya kuka wuni, Koma lafiya dai ko?" Dady y tambaya.

"lafiya lau, sannu da hanya, muje ka yi wanka kafin sallah sai kasa wani abu acikin ka ko?"

"OK Dear, Yauwa Abdul jeka mota a sit ɗin baya akwai Leda guda biyu ka kwaso su ka hauro min da su"

"OK Dady" Abdul ya amsa ya tafi.

Bayan Dady d Ammee sun haura, sai nihal ta fara raraba ido tasan tsaraban su ne Dady ya kawo maybe Har ta matsu taga meye.

"meye haka kikeyi kamar wata me jiran wani abu ko wacce ta bada ajiya? Ke dai naga ranar da shekarun girma da na hankali d nutsuwa zasu zo miki ke kam" mimi ta zunguri kan nihal.

"toh ke wai ina ruwanki dani ne? Ke kike ganin banda nutsuwa naga ai nutsuwar yaseen Abdallah ya gani yake kirana ƙanwar shi"

"ina rabaki da wanan jan kunnen ki tsaya matsayin ki, ki kama kanki, in kinƙiji kuma toh"

"to Wai sis me nakeyi da baya dadai, kawai dai kinfi so Kowa ya zama kamar ke, baki da wani say, sai kara d kawaici da rashin son nuna kedin kinsan kanki nikam Bazan iya rayuwar ki ba, in abu yamin yamin kawai in bemun ba kawai bemin ba shine gaskia zance" nihal ta faɗa tana mai miƙewa dan taro yah Abdul da ya shigo da Leda, wani mugun kallo ya mata ta tura baki ta fasa karɓan Ledan ta ja da baya.

Mimi ta bushe Mata da dariya, ta na mai miƙewa ta nufi kitchen, yah Abdul yayi saman Dady.

"kyaji da shi, Ai ba dukana yayi ba ko zagina"

"oho dai" mimi ta sake firta mata tana gab d shiga kitchen ɗin kafin ta shige.

Yah Abdul da kanshi bayan Ammee da Dady sun nuna mai yadda zeyi yaba kowa tsaraban shi, ya sakko ya ba su nihal da miki har masu aikin gidan kowa godiya yayi yana sa Albarka, nihal ko gani tayi kamar nata yayi kaɗan tasan d tana wajen nata sai yafi haka yawa, Amman Abdul na falon da tayi yunƙurin haurawa sama tasan me ze buyo baya dole ta karɓa da haƙuri, daga baya da taga su mimi da yah Abdul suna hira har ta ɗan sa musu baki, yana ba mimi labarin ze fara koyarwa a darul hadith, ganin Nihal tasa baki ya kama kunnen ta yana mata gargaɗi inyaji maganar Sai ta sani, shine ta toshe bakin ta har Ammee ta sauko bata sake sa musu baki ba a hirar su.

"yauwa Dota mimi jeki haɗa ma Dadyn ku komai na buƙata da zeyi amfani da shi a kitchen ɗin sama na girka, mai abin d zeci iya bakin shi, bari uwar rigima ta biyo ki da lemun shi"

"Ammee... Uwar rigima kuma? Yaushe rabon da ki kirani da wanan sunan da Dady ya hana?" mimi ta faɗa tana taɓara.

"na kira sunan asamin gas ko ki kai ƙarata gun Dadyn, ba sunan ki bane? Tashi ki haɗo ki kaimai sama ni kafin Inzo in sameki a wajen saura in kin kai ki tsare shi da surutu ya gaji kar ki barshi ya huta"

Sum sum Nihal ta miƙe, mimi kuwa ta jima da haurawa saman.

"yauwa Son ya zakayi ne da karatun ka da wanan rigimar da kake neman ƙarama kanka?" Ammee ta tambayi Abdul.

"kai Ammee duk zan iya karatun da nakusa gamawa koma na gama za'ace, final exam Kawai Fa ya rage min kimin addu'a kawaiAmmee dan Allah"

"toh Banace a'a ba Amman karka sa rai, sai Dadyn ka ya nutsu zan mai maganar duk da kasan ba lalai ya yadda ba, in be yadda ba sai kayi haƙuri"

"toh Ammee, Amman ze yadda da yaddaki Ma in sha Allah"

***
"BINTU kizo kiyi maza karki makara" Ummi ta firta ma Fateemah.

"toh Ummi Safa Kawai zansa, yanzu zan fito"

Babu jimawa matashiyar budurwar ta fito "toh Ummi sai na dawo, Ina Abdu na?"

"yana wanka ki tafi nace kina mai sallama, yi sauri"

"toh ummi saina dawo ace mai na tafi"

"toh Allah ya tsare da nawa da nashi Allah ya bada ilimi mai Amfani"

"Ameen Ummi" BINTU ta amsa mata.

"yauwa sai ki lalaɓa kuɗin ze osheki ai ko?"

"eh ummi In sha Allah
,sai na dawo na tafi" ta fice ba tare da ta ji me Ummi ta firta ba.

Hankalin ta a ɗan tashe ganin ta kusa makara take tafiya, da takunta na sauri-sauri gudu-gudu babu abin da take buƙata illa ta ganta cikin school ɗinsu.
Chapter 2 · 0% Book details