← Book details Rai Da Ruri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 9

Sashe 8

Rai Da Ruri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suka haɗu da Faisal na Islamiya dan Ranar Asabar d Lahadi baya shiga Islamiyar Amman yau ya shigo saboda abokin shi Abdul yaka yadda abin yake tafiyar mai,har suka shiga aji aji dan ya gabatar ma da ɗalibai sabon malamin su wanda ze ɗauke su Qur'ani da tajweedi, ko da aka zo ajin su fateemah har aka shigo da shi aka gama gabatar da shi bata ɗago ba bare ta ganshi tana ta gyara hadda ta da malami ze shigo ya karɓa dan har Wani runtse ido take irin kar wani abu ya ɗauke mata hankali tana ta motsa baki, Abdul ko yana ta satar kallon ta,har suka fita bata dago ba dan b jimawa sukayi ba.

Bayan an yi break an dawo, Abdul ya shigar musu sai anan fateemah ta ganshi ganin farko shima ji tayi kamar ana kallon ta shine ta ɗago idanun ta masu kama da madara dan tabbatarwa, tayi tozali da shi, daga shi har ita kowa ɗauke idon shi yayi daga kallon ɗan uwanshi, yaci gaba da musu bayani kafin ya musu ƙarin Qur'ani, kowa ba ƙaramin jin zaƙin muryar Shi yayi ba aajin wasu ko ma shi suke bi da kallo ba karatun ba sun shagala sosai karatun mai daɗin sauraro kamar ba daga bakin shi yake fitowa ba.

Ganin wasu kamar ba karatun suke ba ya fara tashin wasu daga ɗaliban suna biyawa wanda ya kula basu bada hankali da nutsuwar su ba, duk ciki babu wanda ya iya biya mai sai da ya tashi fateemah taji duk kamar an ɗaureta dole ta aro nutsuwa ta biya mai da ƙira'arta mai daɗi da Abdul ya sake yabawa, kafin yace ta zauna aka mata kabbara ya mata jinjina, kafin yace sauran ma su zauna ya sake maimaita musu.

Har aka tashi fateemah taji bata son su sake haɗuwa da sabon malami, shi ko yanzu ji yake dama iya ajin su yace ze ɗauka dan so yake ya karance ta sosai ya bata ruwa daga ruwan Ilimin da yake da shi dan ya fahimci mai ƙwazo ce.
[06/04, 9:17 am] Maman shaheed😍🥰: *RAI DA BURI*

PAGE 5

BY
MAMAN SHAHEED

Paid Book...

Last free page... 😔

Ga Account ɗin da za'a biya 👇
3108794095
Fatima Abubakar
First Bank

Shedar biya 👇
08134624555

Ko aje Arewapen...

_Gidan mlm Sadiq Abdu_

Asalin Kakanin Shi ƴan Chadi ne, iyayen sa sun rayu da Kakanin shi ba sosai ba daga baya suka koma wani ƙauye nesa da garin sakamakon wani abu da ya taɓa faruwa a dangin su, har aka samu rabuwar kai kowa yake kusan zaman kanshi.

Malam Sadiq Abdu da wasu suke kira shi da mlm Abdu kawai har sunan ya bishi musamman da ya sami canjin gari.

Daga baya mlm Abdu ya rayu daga shi sai iyayen shi dama su biyu suka haifa shi da ƙanwar shi da ba san inda ta fi ba tun wani mamaya da aka taɓa kawo ma garin babu tabbas tana raye ko bata raye Har iyayen shi suka haƙura suka rungumi ƙaddara.

Shima dama dun acan garin ya fara fuskantar ɓacin rai da kunci da camfe camfe saka makon Yara mata da Allah ya bashi babu namiji ko guda ɗaya
Shi ko da mai ɗakin shi ummi habiba sunji sun gani har Kakanin su suna son yara matan ahaka bayan su huɗu a duniya babu mai ba yaran kulawa sai tsangwama da kyara da canfi a haka suka taso har suka fara tasawa.

Zaman be musu rashin dadi basai da aka sake samun mace matsayin auta, Kakanin sun rungumi yaran sosai su suke tausan ummi da Abdu Har suka sami nutsuwa.

Ana tsaka da haka wata rana maman Abdu ta rasu sakamakon gajeriya rashin lafiya sun shiga cikin ruɗani sosai lokacin gashi su Khadija da Hindu sun fara tasawa girma ya fara zuwar musu sai ƙanwar su ƙarama.

Ganin irin faɗi tashin da Abdu yake baban shi ya tattara duk wani abu da yake da shi yaba Abdu akan yabar ƙasar yaje ya gina kanshi da iyalin shi, Abdu ya dinga kuka da ummi suka nuna bazasu iya tafiya su barshi ba, shi kuma gani yake in Abdu yaci gaba da zaman wajen baze taɓa samun ƴa'nci ba da yaran shi wata kila ma suƙi auruwa duk da kuwa kyan da Allah ya musu musamman ƙaramar da aka haifa ga Tarbiya iya Tarbiya da nutsuwa da suke da shi Amman banu mai mu'amala da su sai yasu yasu kawai.

Ƙarshe dai sai da baban Abdu wato Abdullahi mai ainahin sunan Abdun ya Sai da gona da gidan da ya malaka ya sake danƙaaa Sadiq kuɗin sanan ya karɓa yana kuka, a karo na ƙarshe ya nemi da Sadiq ɗin ya tattara iyalin shi da su bar gari suyi nesa da garin ko barin ƙasar ma.

Sadiq tun baya so har suka karɓa da ya tuna abubuwa da dama ga son ganin ya inganta rayuwa da Ilimin yaran shi gatan shi da Allah ya bashi.

Amman be bar garin ba sai da mahaifin shi Abdu suka doguwar tafiya ta hanyar abokin shi suka sauka a Jigawa suka fara ganin garin da yanayin komai na garin har ya ɗan taɓa noma a garin ya fara sabawa da mutane, an mai tallan gona da gida duk be siya ba tukunna sai baban shi ya fara tashin lafiya hankalin shi yayi matuƙar tashi, sai da suka kai shi asibiti aka dinga jinya, Amman dake Allah yayi ƙasar shi a Jigawa take anan Allah ya karɓi ran shi, Sadiq da ummi sunyi kuka har su Naja Khadija gani suke kamar gatan su ne ya ƙare yanzu basu da Masoya sai tsirarun yan Jigawa da aminin mahaifin shi da yake jan su yake tausayin su dan yasan komai akan su.

A shekarar Sadiq ya cire amfanin gona sosai har ya siyar ya sami Alkhairi.

Ana haka Allah yasa Sadiq ya fara shiga garin Kano tun yana shiga da kasuwanci har wasu abubuwa suka fara ribatar shi yaji nan ne ya dace yazo ya gina rayuwar shi da Ilimin yaran shi mai tushe bawai dan Jigawar babu Ko bata dace ba kawai dai shi dai yaji kanon ta birge shi ne fiye da har ƙasar haihuwar shi da ya baro.

Koda ya nemi shawarar aminin shi be Mai baƙin ciki ba ya bashi goyon baya har dashi aka wuce mai gaba suka shiga kanon har aka sami madaidaicin gida suka shiya Sai aka sami wani shago shima da haya suka nema sai aka nuna musu sai dai su siya dan siyar da shi za ayi suka siya kuwa.

Aka ɗan gyara gidan ranar da aka gama gyaran gidan su Sadiq Abdul da Malan Musa a gidan suka kwana suka sake shiga kasuwa suka ɗan sisiyo abun buƙata na gidan suka sai katifu guda biyu suka saka a ɗakuna biyu da sauran kayan amfanin gida daidai ƙarfin su, dan basu Da komai sai abun da suka samu a Jigawa dan Jigawa sun musu karamci bazasu taɓa mantawa da su ba inda aka fara nuna musu so, tatali, kulawa da ja ajiki musamman mlm Musa da iyalan shi biyu da dangin shi dole ce kawai tasa zasu bar garin.

Da iyalan malam Musa aka taho rako su har da wasu tsirarun yan garin dan an saba, har Kano suka rako su ana ta koke koke masu kuka, wasu daga iyalan malam kala kamar amaryar shi mmn nusaiba da su Rafi'at duk sai da suka kwana a kanon an zama kamar ƴan uwa sai washe gari suka tafi da niyar duk ai basu rabu ba, asu dinga ziyartan junan su.

Malam Sadiq Abdu da Taimakon malam Musa suka zuba kawayan hatsi a Shagon da ya shiya, ya fara gwada sana'ar awo.

Ahankali ya ƙara wasu abubuwa a gidan, ganin ana samun wuta sai ya samu ya sai musu kayan kallo da wasu kujeru na hannu mai L shape suka saka a baban falon gidan, su Nana Khadija da Hindu ya samu ya fara ciku cukun mayar da su makaranta, nan da nan kuwa aka karɓe su suka fara daga sss one dan duk tare suke tafiya.

Ya sami Islamiya ma ya sasu mai kyau sai yaji hankalin shi ya kwanta ya fara mu'amala da ƴan unguwar suma sun riƙe shi da amana.

Ana haka su Nana Khadija da babu mai zuwa wajen su sai ranar tayi mafarkin Wai anzo Ana kamar gasar aure maza kala kala a ƙofar gidan su har sai sun zaɓa ita da Hindu sai suka ji kamar wani ƙulli ne ya kunce wanda da ya musu dabaibayi, tana farkawa ta gane mafarki ne tayi addu'a ta fara sanar ma ƴar uwar ta, aiko itama ta sanar ma ummi, ummi abin ya bata mamaki har Abdu Amman suka barma Allah komai ummi tayi sadaka da kyakyawan niya akan koma meye Allah ya nisanta su daga sharrin dukkan abin halitta.

A ranar ba a kwana ba sai da saurayi ya biyo nana Khadija har gida abun ka da bata saba ba ko kare be taɓa shinshinata ba sai abun ya mata wani iri taƙi kula shi ma kamar ma tsoro yake bata dan yadda yake mata kamar yaga wata sarauniya kamar ya sace ta yake ji, da ƙyar ta mai ƙaryar an mata miji suka rabu badan ya haƙura ba.

Bayan sunyi jarabawa ss two suna da ƙawayen su daidai gwargwado, ganin yadda ƙawayen suke da samarin su sai yasa suka fara gogewa akan tsayuwa da saurayi mai mutunci da kula su, shima sai da ummi tayi da gaske da Taimakon nasiha da shawarar ta Hindu d yaya Khadija suka fara tsayuwa da samari.

Lokacin ƙanwar su fateemah tana primary, gashi suna son ta kamar su haɗiye ta itama ta saba dasu sosai ita tasa ma Sadiq sunan Abdu ma har ya bishi itace ta juya sunan tun tana yarinya akan shi har yayun suke dariya suke faɗa har ya zauna a bakin su.
Chapter 8 · 0% Book details