← Book details Ni Kishiyar Uwata Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 17

Sashe 17

Ni Kishiyar Uwata Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Shiru kotu tayi tsayin lkc kafin daga bisani alqali ya magantu ta hanyar bada umarnin abawa shaida na gaba dama ya fito ya fadi abinda zai fada, nan take shaidun Momy suka rinqa fitowa daki daki suna bayani inda shikuma lauyan Dad ya kafe kaida fata a qarshe dai saida likitoci suka shiga cikin lamarin domin shari'ar tazo qarshe amma ankasa gane me gsky tsakanin mom da Dad dole tasa aka shiga bincike na qwaqqwafin records na abubuwan da suka faru shekarun baya a asibitin da aka saci jaririyar anan aka gano cikakken sunan matar ministern dashi kansa aka fara bibiyarsu tashin farko da Alh Mahmoud Abbas ya bawa Bashir damar zuwa su gana a lkcn da yabada umarnin a kawowa baqinsa ruwa wata matashiyar budurwa ta shigo dauke da tire din kayan motsa bakin ba bashir ba hatta Mahaifinsa da suke tare da lauyan gwamnati saida sukayi kamar su dige don tsananin mamakin kamar da take tsakanin budurwar da sukaji an ambata da Maryam lauyan ya kasa jurewa ya magantu da cewa “Dr Bashir wannan ai matarka ce ko?" Girgiza kai yayi yace “Janah batakai wannan haske ba kuma tafi wannan jiki kadan sannan da ciki a jikinta"

Jinjina kai sukayi nan suka zayyanewa Alh Mahmoud Abbas abinda ke tafe dasu yayi jim yana tunani kafin daga bisani ya dago yace “ina yarinyar take?" Dagowa Bashir yayi yace “tana nan cikin garin abuja suma suspect din suna hannu dukkansu idan babu damuwa zamu iya zuwa ayi duk abinda ya dace tabbas Murjanah yar'uwar Maryam ce"

Miqewa sukayi dukkansu suka dunguma suka nufi gdan Bashir dake nan qasan inda suka samu Alh Mahmoud Abbas harda Hajiya Hafsa da maryam da Khamal da Jamal qannensu itadai Murjanah tana dakinta a kwance abin duniya yayi mata zafi tajiyo hayaniya a parlour ta miqe ta dauki hijjab dinta tasa zuwa yanzu cikinta yayi nauyi sosai daqyar take daga qafarta ta fita parlourn ja tayi tayi turus lkcn da sukayi ido biyu da Maryam gabanta ya bada wani ras suka zubawa juna ido suna kallon kallo bata hango bambamcin dake tsakaninta Maryam din ba saida taji Hajiya Hafsa tace Alhmdllh tagwai na sun dawo" sai suka nufeta da gudu suka rungumeta Hajiya Hafsa ta fashe da kuka tana cewa wlh Alh basai anyi wani gwajin jini ba wannan yatace ta cikina lkcn dana haifesu tabbas biyu na haifa amma aka sace daya akace bana cikin hayyacinane shiyasa naji kamar biyu"

Shi kansa Alh Jikinsa yayi sanyi share hawaye kawai yakeyi ya matsa ya kamo hannun Murjanah yace "taho yata" sai kuwa ta fada jikinsa ta rushe da kuka tana cewa “tabbas qaunar jini a ruhi take ahli basa buya zuri'ah inta hadu da zuri'ah jini ke amsar saqo an cutar dani an rabani da gatana an gurbatamin rayuwa saboda son zuciya Allah ya Isana bazan taba yafewa duk me hannu cikin lalacewar rayuwata ba....."
Rufe mata baki Alh Mahmoud Abbas yayi yace “yi shirunki yata nima bazan yafe ba" daqyar Bashir ya rarrasheta yajata suka fita babban asibitin qasa na National hospital Abuja suka nufa inda akayiwa ma'aikatan inda Dad yake tsare waya suka fito dasu nan akayi musu duk wani abu na gwaje² tsakanin Dad da Abba kawai kallon kallo akeyi yama rasa irin matakin dazai dauka tun baimaji asalin abinda ya faru tsakaninsa da yarsa ba.

Kwana uku aka basu na result suka koma gda nan fah Maryam ta tubure ita gurin yar uwarta zata zauna itama ta kafe saidai su tafi tare shi kansa Abba yanason ya gana da yar tasa amma yakana irintasa tasa yace suyi zamansu idan sun huta sazo ita da Maryam din Mahaifin Bashir ne yace baza'ayi hakaba su tafi itama taji dumin iyayenta Bashir baiso ba saidai bazai iya cewa komai ba da kunya hakanan ta kama hannun yar'uwarta suka shiga hada kaya yana kallonsu saida suka gama Maryam tace “amma Yaya Bashir saita haihu zata dawo ko?" Harararta yayi tayi dariya taja trolly din ta fita Janah ta miqe ta matsa gabansa ta ruqo hannunsa saita fashe da kuka ta rungumeshi shima ya rungumeta tace “bazan taba mantawa da halaccinka gareni ba Yaya Bashir kasoni tun lkcn da ban cancanci asoni ba ka qaunace ni ka nunamin qauna inasonka mijina Allah yabarmu tare yabani ikon faranta maka" matseta yayi yana sunsunar wuyanta yace “tun kina cikin tsumman goyo nake sonki Janah da sonki zan mutu nidai burina kada ki canzamin saboda ganinki tsakanin danginki kinji, ki kulamin da kanki zan tafi kano yau nima akwai wani aiki da zanyi na sati daya a Aminu kano idan na gama lkcn kinsha nonon da bakisha ba kinqoshi sai mu dawo ko?"

Lakace masa hanci tayi ya zaro kudi ya bata me yawa yace “ki kulamin da babyna" da haka suka fita suka koma parlour sukayi sallama suka tafi suma suka dauki hanyar kano,
Tunda taje gdan iyayen nata take samun gata qauna sosai Hussainanta da yan uwanta suke nuna mata ga iyayenta komai Janah, abin har kuka yake sanyata, kwananta biyar a gdan da yamma suna taya Hajiya aiki a kitchen ta tsugunna zata dauko flat bayanta ya riqe tayi qasa da sauri tana kiran sunan Allah dukkansu sukayo kanta da sauri suna riqeta ta sake dafe mararta tana riqe da hannun Hajiya tace “wayyoh Hajiya kiramin Yaya Bashir mutuwa zan...."

Rufe mata baki tayi tace “aa ba mutuwa zakiyi ba ina tunanin haihuwa ce" nan sukayi ciki da ita Abba suka kira suka fada masa abinda ke faruwa nandanan ya juyo gda lkcn abun yaci tura yana zuwa yace su tafi asibiti suna zuwa dake ansan matar waye a asibitin babu bata lkc sukayi mata duk abinda ya dace aikuwa kamar sun janyo ciwon nandanan sai haihuwar tazo da gaske ta haifi yarta mace kyakkyawa me kama da Bashir qatuwa da ita nurse din na zuwa ta fada musu Abba ya kira Mahaifin Bashir ya sanar dashi haihuwar kafin wane wannan haihuwar ta cika dangi

Ai Bashar kasa jiran satin yayi ya dauko mota ya nufo abuja gani yake idan ya jira jirgi ma bazaije da wuri ba bakwai na dare sai gashi a asibitin lkcn janah na baccin hutu saboda tasha dinki babyn tanada girma saida aka qarata,
Yana shiga Maryam da Hajjah kakarsu Janah ta wajen uwa suka haushi da tsiya shidai dake ba mai surutu bane dariya kawai yakeyi ya matsa ya duba Janah ya gyara mata allurar ruwan dake jikinta ya dauki jaririyar a gadonta ya zuba mata ido hawayen farin ciki suka zubo masa yace “Alhmdllh ya Allah"
Washegari Mamee da zugarta suka dira a Abuja sunzo ganin baby Bashar yaso yima yarsa Huduba da Hafsa sunan mahaifiyar Janah amma janah tace aa Fatima zaasa mata sunan Mamee murmushi yayi yace “shikenan na hqr nanda one year zan qara baki wani babyn kinga saimu samu Hajiya" duka takai masa ya goce daidai lkcn da wayarsa tayi ring sunan Abbansa yagani ya kara a kunnensa suka gaisa yace “Yanzu aka kirani daga Prison din da Gen Habeeb yake wai ya zuciyarsa ta buga ya mutu bayan tabbatar masa da akayi yanada HIV dagashi har matarsa yanzu haka mun dauki gawarsa mun tafi Mambila acan zaayi masa sutura" Allah ya jiqansa kawai yace ya aje wayarsa yaci gaba da wasa da babynsa.
Kwana bakwai akayi suna na bijinta abinka da jikar fari ta kowanne bangare a sunan ne Nasir Abokin Bashar yaga Maryam ya nace akan yana sonta to dama matarsa ta mutu cikin ikon Allah suka daidaita kansu wata biyu akasha biki amarya ta tare a gidanta itama anan Abuja rayuwa tanata albarka abubuwa duk sun shude sai tarihi inda Momy ciwo yaketa cinta a tsaye taqi yarda cewa tanada HIV sai yawonta takeyi janah nason taimaka mata amma iyayenta da mijinta sun hanata ga rashin miji ga rashin aikinyi tun lkcn shari'ar nan aka koreta a aiki ga ciwo duk wani abu da take dashi ta siyar a gurin yawonta taqi ta daina fita qasashe harkar lesbian dinta wata tafiya dai da tayi bata dawo ba.

Tunma ana nemanta har an hqr a cikin shekara ta biyu da haihuwar Janah ta qara sullubo danta namiji wanda yaci sunan mahaifinta Mahmoud wata daya tsakani Maryam ma ta haifi diyarta mace akasha suna rayuwa taci gaba da tafiya cikin jin dadi wadata da kwanciyar hankali zuri'ah nata qaruwa soyayya na bunqasa komai yana tafiya daidai cikin hukuncin Allah.

_Tammat Bi hamdullah_

_A qarshe dai ina qara baku hqr na tsayawata cik da rubutun wannan littafi sakamakon laluri daya addabi rayuwata watannin baya lkcn da naji sauqi kuma nayi loosing phone dina da fatan duk wanda na batawa zaiyi hqr, me qafa hudu ma yakan fadi balle me biyu am sorry please my luvly Fan's sai mun hade bayan sallah insha Allah a sabbin littafaina guda biyu *ZARRAH* da *DAN MAFIYA(to the world)* tabbas wannan rayuwa tana cike da sammatsi da qalubale shin bakwaso jin meye asalin dalilin da yasa ya zama *DAN MAFIYA* ba? Akwai rikici da rudani cikin wannan cakwalkwallan labari mai sanya zuciya cikin zullumi tabbas an dade baayi tamkarsa ba koma nace baayin ba._

_Takun dai Oum Hairan_

*_Oum Hairan_*
Chapter 17 · 0% Book details