← Book details Ni Kishiyar Uwata Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 17

Sashe 10

Ni Kishiyar Uwata Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fuuuuu ta figi hannun baquwarta suka fice sukabar Janah tsaye da sanyin jiki Bata taba ganin rubabben gdaIrin nasu ba Bata tabajin lbrin qazamar rayuwa irinta gidansu ba komai kayi indai ka dorashi akan daidai ko ayi daidai to kazama me laifi, komawa tayi ta zauna ta rafsa tagumi cike da alhini da tunanin wannan qazamin gda nasu da haka ta miqe ta shiga ciki ta sake hada tagumi lkc zuwa lkc tana dauke hawaye.
Jitayi an maqaleta ta baya ta sauke numfashi tare da dagowa suka dubi juna Surry tace “kullum kina dorawa kanki damuwar da kikasan zata iya haifa Miki da matsala Janah yakamata Zuwa yanzun ace kin saba da wannan rayuwar taki da Kuma abinda rayuwar tazo Miki dashi Janah bafa komai kakeso Kuma yake samuwa da sauqi ba Ni yanzun ma wata damace na samu zanyi amfani da ita na tsula tsiyata"

Kama kunnenta tayi ta radanta Shiru Janah tayi tana kallonta tare da girgiza Kai tace “aa Surry kada kibishi bakida kowa acan yazo ya juyanki baya bayan ya gama cinye albarkar jikinki kizo kina cizon yatsa nidai Ina ganin idan da gaske yake sonki to ya fito kuyi aure inyaso duk indama yakeso sai ya tafi dake"
Harararta Surry tayi tace “bazaki gane ba zanjene kawai naga gari gari yaganni muyi qara'in rayuwa na dawo ke kinsanma wani abu ne har gda yace zai siyamin anan" zaro ido Janah tayi tace “nidai ban hango Miki ribar hakanba Amma idan ke kingano kije Allah ya tsare nikam bazan iya wannan kasadar Saida ranba"
Murmushi tayi tace “ai dama ke matsoraciya ce wai ya kuke ciki ne da baturanki?" Ajiyar zuciya tayi tace “nifa ya matsamin akan burinsa nason na gasqatashi harma ya fara cewa wai yanason gobe Mom dinsa zatazo zamuje mu gaisa tasamin albarka" Jinjina Kai Surry tayi tace “to ke ki yarda dashi Mana kuyi auren tunda dama burinki kenan" zubawa Surry ido tayi tace “to baki tunanin ba “addininmu daya dashiba" dariya abin yabawa Surry tace “to shine me yayi addininsa kiyi naki kawai shikenan yo ni innice ke inama zan wani damu da mgnr addini tunda ba kabarinmu daya ba"

*_Oum Hairan_*
[05/05 9:53 pm] Yar Mkrnt: *_NI KISHIYAR UWATA CE_*

*_Oum Hairan_*

Please sis novel dina na kudine 200 idan kina buqata ki biya ta Nan 0255526235 Fauziyya Tasi'u Umar GTB ko Kati MTN ta wannan number 09013718241 or VTU ta 09031307566, idan baki son group kinfiso ta PC zaki biya 500 ne idan baki siyaba kada ki karantamin littafi.

*_23-24_*

Zubewa yayi saman kujera a parlournsa yana mayar da numfashi ya dade kafin ya dauka wayarsa ya Kira matarsa Hajiya Bari'ah bugu uku ta daga Bai tsaya karbar gaisuwarta ba ya fara masifa yana fadin “uban waye yabawa Janah umarnin kula samari harma ta samu damar kawosu gdansa"
Tsaki Mom taja ta katse wayarta taci gaba da gudanar da harkokinta so shima a ranar bai waiwayi Janah ba itama Bata waiwayeshi ba burinta kawai gari ya waye ta fice daga gidan cikin saa kuwa har tagama shirinta ta fice Bai tashiba taji dadin hakan ta nufi makaranta, rabi karatu takeyi rabi tunani suna gama lecture wayarta ta hau ruri ta dauka tare da jan ajiyar zuciya ganin number Herrison ta Kara a kunnenta tambayar farko da yayi Mata tabata dariya shima yayi dariya tace.

“Sauri haka Babu ko gaisuwa" numfashi ya sauke yace “Mom ta dameni akan tanason mu daidaita dake ne kafin ta tafi so shiyasa nakeson ganinki" address na makarantarsu ta Bata bai kuwa Bata lkc ba sai gashi suka gaisa suka shiga hirarsu ta masoya kamar sun shekara haka sukeji Herrison akwai shiga rai ya iya rainon soyayya, dubansa tayi cikin yanayi na sanyin jiki tace “idan na amince da aurenka ya zamuyi da bambamcin addinin dake tsakaninmu?" Da sauri ya dago ya zubanta ido yace “wannan matsala ne kenan?" Dagansa Kai tayi tace “naji malamai suna fada addini na ya haramtawa mace musulma auren namiji Ahlil kitab Amma ya halattawa namiji musulmi auren mace ahlil kitab...."
Shiru yayi na dogon lkc kamar me nazari can ya dago yace “idan Kuma na yarda nabarki kiyi addininki nayi nawa fah Kuma ko baby's muka Haifa zasuyi addininki hakan zaisa nasameki?" Girgiza Kai tayi tace “aa addinina baibada damar hakan garemu ba" dafe kansa yayi yace “oh God Jannet inasonki bazan hqr dake ba kiyi tunani duk abinda kikeso zanyi Miki Kuma zan baki bazan taba hanaki addininki ba"

Murmushin yaqe tayi saboda Allah ya sani tanajin guy din a ranta Amma batasan ta inda zata bullowa lamarin ba jin tayi shiru ne yasashi bude motar ya koma inda take ya matsar da ita yatada motar suka fice daga school din suka nufi cikin Nassarawa G.R.A din gabanta yana faduwa Amma ta danne saboda ta fahimci shi ba abinda ke gabansa kenan ba,
Horn yayi aka bude Masa ya shiga yayi parking ya bude itama ya bude Mata suka jera duk da luguden da qirjinta yakeyi ta rinqa dakewa suka shiga har parlourn babbane sosai gwanin sha'awa nan Janah ta shagala da kallon parlourn ya hadu Fiye da hangenta da tunaninta taja fasali ta sauke daidai lkcn da yake qwalawa Mom dinsa kira ta fito daga dakinta ta fara tako step din tana amsa masa ajiyar zuciya Janah ta sauke Mom ta qaraso ta rungumeta tare da zaunar da ita tace “baka fadamin zuwanku ba" murmushi yayi yace “itama batasan zamuzo ba" Shiru ce ta ratsa ya tashi ya dauko Mata lemuka da sweet ya ajiye a area table din dake gurin ya tsiyaya yakai Mata bakinta ta janye da sauri sukayi dariya itama tana dariyar qasa qasa tana rufe ido.

Shiru Mom tayi can ta dago ta dubi Janah tace “Jannet kinason Herrison?" Tambayar tazo Mata a bazata tayi saurin zaro ido tare da kawar dakai ya dubi Mom yace “a culture dinsu idan kika tambayi mace tanason namiji tayi haka to tanasonsa Mom Jannet matata ce kawai ki fadawa Dad ya nemamin aurenta zan iya yarda da duk wani sharadi na addininsu matuqar zan sameta”Shiru ce ta qara ratsa gurin kafin Mom ta dago tace “jiya na kasa jurewa na Kira Dad dinki akan maganar aurenku Amma Bai saurareni ba qarshe yace karna qara kiransa so ko akwai wani Abu da kikeganin yasa yaqi sauraranmu?"Girgiza Kai tayi ta miqe tace “bansan komai ba illa kawai bayada raayin yimin aure yafi ra'ayin lalacewar rayuwata am kiyi hqr da abinda Dad dina yayi miki Mom zai wucce insha Allahu" da haka da dauki Jakarta ta fice daga gdan jikinta har rawa yakeyi saboda kaduwa da tashin hankali,
Da sauri Herrison ya biyota ya Kama hannunta batare da ta luraba ya hadata da jikinsa yace “sorry please ko munyiwa Dad dinki laifi ne Janet?" Dagowa tayi da idanunta da suka ciko da hawaye tace “babu abinda kukayi Masa ni qaddarata ce a haka iyayena basa neman maslaha ta Herrison kawai inaganin ka nemi wata ka aura wlh nasabata da tarbiyyata bata Kama da wacce zaa sadaukar da farin ciki dominta..."

Da sauri ya katseta ta hanyar rufenta baki da bakinsa numfashinsu ya dauke gabadaya na wani lkc kafin ya janye bakinsa a nata yace “ki daina kuka banaso meye damuwarki game da quality dinki da kikejin kamar ban cancanci sallama Miki komai ba?" Motarta ta shiga shima ya shiga taja suka fice suna tafe yana tambayarta takasa mgn sai hawaye kawai da take sharewa nacin tambayar tasane yasata dagansa hannu tace “kayi Shiru haka zan fada maka komai domin Kaine komai inaji a Raina zanyi uwar watsi da kowa nawa domin kubutar da kaina Herrison banason rayuwar da nakeyi taja dogon lkc nadama tazomin a lkcn da ban shiryawa zuwanta ba nasan qarshen alewa qasa so gara nayi tunanin nemawa kaina mafita kafin qurewar lkcn"
A qofar gidan ya danna horn getman din ya bude suka shiga yayi parking ya sake kallonta yace “yaushe zamuyi aure Jannet tun ranar dana fara ganinki naga damuwa a jikinki lkc baiyi bane da zan tambayeki dalilan damuwanki ki fadamin yaushe zamuyi aure mu samu nutsuwa?" Bude motar tayi zata fita domin kalamansa qara sanyaya Mata jiki sukeyi shima ya bude ya fito yayi saurin riqeta ta fada qirjinsa suka saki ajiyar zuciya tare daidai lkcn da mayafinta ya zame akanta doguwar sumarta ta bayyana ya dora hancinsa akai yana sunsuna Dad ya fito daga cikin gidan yana daura agogo kamar ance ya dago ya sauke gilashin idonsa akansu,
Wani Abu yaji ya taso daga qirjinsa ya caki zuciyarsa ya ɗige a gurin ya kasa ko motsawa daga wajen sai muzurai yakeyi itakam Janah taji baqon yanayi ta qara lafewa a jikin Harrison tana shaqar daddaɗan ƙamshin turarensa daya saukar mata da wata muguwar kasala, batare da sunyi auneba kawai taji ƙarar saukar mari hakan yasasu rabewa tare da rintse idonta da ƙarfi.

Jin wani tartsatsin marin ne yasata buɗe idonta ta saukesu kan Herrison da ya dafe kuncinsa bakinsa sai ɗigar da jini yakeyi tayi kansa da gudu taji an riƙe hannunta ta juyo da sauri ganin Dad yasata cin turjiya ta rushe da kuka tace “haba Dad don Allah kamar ba musulmi ba meye yayi maka da zaka fitar Masa da jin...." Itama sauke Mata kyawawan maruka yayi har biyu ya hankadeta tayi baya zata fadi Herrison yayi maza ya tareta bai damu da jinin da bakinsa ke fitarwa ba hasali ma ita yaketa zubawa sannu,
Sake fincikarta Dad yayi ya figeta ya watsata ciki ya koma gurin Herrison ya kora Masa warning me nauyi akan kula Masa yarsa, duk yanda yaso ya fahimtar da Dad yaqi fahimta qarshe ma sai ya hadashi da kuratan sojojin yace su fitar dashi daga gdan, cikin matsananciyar damuwa ya juya ya fita daga gdan a sanyaye zuciyarsa fal da tunanin halin da Janet zata kasance gurin wannan mahaifin nata"
Chapter 10 · 0% Book details