← Book details Ni Kishiyar Uwata Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 17

Sashe 16

Ni Kishiyar Uwata Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lkc ya rinqa tafiya sosai Janah ta samu kwanciyar hankali da farko Mom taso dagansu hankali Amma da Bashir yayi Mata kyakkyawan kashedi saita shiga hankalinta ta dainayi musu zarya a gida qarshe ma dauke matarsa yayi suka wucce Lagos kasancewar aikinsa yabar dashi Abuja ya koma Lagos watansu biyu a Lagos Janah ta fara rashin lfy sosai zazzabi amai da ciwon ciki dole sukaje asibiti suna zuwa aka sanar dasu ciki ke gareta wayyoh murna gurin Bashir kamar ya goyata haka suka dawo gida cikin tattali da kulawa ya Kira iyayensa ya fada musu suma sukayi musu murna da fatan alkhairi bayan ya gama wayar ya dawo kusa da ita ya zauna tare da sanya hannu ya dago kanta hawaye takeyi sosai mamaki da tsoro suka cikashi ya dagota jikinsa sosai yace.
“Meye Kuma dalilin kukan?" Cikin sanyin jiki tace “inaso ace Nima inada Wanda zan Kira na fada masa abin farin ciki ya sameni Amma banidasu mahaifiyar da zan iya sanarwa damuwata tayi fushi dani akan abinda nasan banida laifin komai akansa
[05/05 9:53 pm] Yar Mkrnt: *_NKU_*

*_39-40_*

Shafa sumarta yayi yana murmushi yace “shine kikemin asarar hawayenki my life ok naji kinaso ki fada musu kinsamu ciki to me kikeso suyi miki?" Shiru tayi saikuma abin yabata kunya ta rufe idonta tana dariya shima dariyar yayi yace “jibi zamuje Kano akwai wani Abu daya taso na gaggawa akan case dinki da Dad naso mu qyale mgnr ta tafi a haka tunda abin yariga ya wucce so shi yakasa ganewa yanata yimin barazana da rayuwata dole na daukaka qara a cikin hakanne Mom take sanarwa sudin basune mahaifanki ba wai....? A tsorace ta dago ya sake fadada murmushinsa yace.
Wannan mgnr da Mom ta fada ita ta qara hargitsa komai alqalin yace dole sai kinje anyi gwajin qwayoyin halitta idan suka tabbatar da kedin ba yarsu bace to daganan Kuma zaa matsasu su Fadi yanda akayi suka sameki"

Dafe kanta tayi cikin sanyin jiki tace “ya Allah" kwantar da kansa yayi a jikinta yace “kada ki wani damu kanki Babu abinda zai faru sai alkhairi" da wadannan kalaman ya mantar da ita komai Saida yaga ta samu nutsuwar zuciya sannan ya shirya ya fice daga gdan ya nufi office dinsa.
Kamar yanda ya tsara din hakance ta faru kwanaki biyu suka dauki hanyar Kano a gdansu Mamee suka sauka an gyara musu part din nasu tsaf Mamee ta tareta da fara'arta tana tambayarta ya jikanta

Amsawa tayi cike da kunya ta dan zauna ta huta a parlourn sannan ta nufi part dinsu ta kwanta domin hutawa Saida ya shigo sannan sukayi wanka sukayi azahar ta fita ta tarar da Mamee a kitchen ta Kama Mata aikin sunayi suna hirarsu Nan mamee take Bata lbrn irin badaqalar da aketa tukawa da dad shi yace ita yarsace Mom tace ba yarsu bace ita yanzu haka kotu tabada adadin kwanakin da zaa qara zama inda aka buqaci Mom ta gabatar da shedarta.
Jikin Janah ya qara sanyi tace “a gdan marayu suka daukoni ko Mamee? Ni dama rayuwata tayi Kama data mara gata Allah dama...." Rufe Mata baki Mamee tayi tace “koma dai mene Murjanah qaddararki ce Kuma kinsan Babu mutumin da yake qetarewa qaddararsa yanzu Rana da lkc kawai zai bayyana Mana koma" mirgina Kai tayi cikin sanyin jiki a haka suka gama aikin Janah ta shige dakinta ta rungume pillow tana hawayen tausayin kanta Koda yake wani bangare na zuciyarta tanajin dadi da addu'ar Allah ya tabbatar Dad ba mahaifinta bane.

*********

Ranar litinin 3/3/ kotun ta qara zama ranar dole Janah Saida ta halacci zaman kotun inda duk take a darare tana zaune ne kusa da mijinta da surukarta inda gabadayanta batada kuzari musamman lkcn da taga an shigo da Dad ya kalleta yayi qwafa ta sunkuyar da kanta daidai lkcn Mom itama ta shigo ita da lauyanta tare da wasu mutane guda uku dukkanninsu zama sukayi kowa da abinda yake tunani kotun ta dauki Shiru na Dan wani dogon lkc kafin a fara gabatar da shari'ar wata Mata da miji sannan akazo kan tasu tashin farko Murjanah aka fara Kira gabanta ya bada wani ras har saida Bashir ya tallafota tare dayi Mata murmushin qarfafa gwiwa ya miqar da ita ta fito Saida ya rakata har gurin da aka nuna Mata sannan ya juya ya koma ya zauna itadai gabanta cigaba yake da faduwa ta jiyo muryar me gabatarwa Yana cewa “baiwar Allah munason jin cikakken sunanki da alaqarki da wadannan mutane guda biyu Gen Habib da Hajiya Bara'ah"
Cikin rawar murya tace “Murjanah Habib Macchido" kallonta kowa yayi kafin me gabatarwar yace “nasabarki dasu fah?" Shiru tayi na dan lkc kafin ta dago idanunta da suka ciko da qwallah ta saukesu akan Bashir Jinjina Mata Kai yayi hakan yasa Mata qwarin gwiwa tace “iyayena ne" sake dubanta yayi yace “iyaye koko mahaifa?" Sake bashi amsa tayi da cewa “mahaifa" duba takardar yayi yace “waye Bashir Mu'az a gurinki Kuma meye alaqarki dashi?" Dubanshi tayi ya kanne Mata ido tace “mijina ne rayuwata tane shidin" take gurin ya dauki ihu Saida Mai shari'a yayi tsawa sannan aka nutsu akaci gaba da karanto Mata qunshin tambayoyi tana amsawa ciki harda tambayar meye asalin abinda ya kawo baraka tsakaninta da iyayenta har ta yanke shawarar barinsu ta koma hannun aminin mahaifinta inda har takai ga sunyi Mata aure batare da sahalewar iyayenta ba?"

Kamar yanda Bashir ya karanta Mata haka ta rinqa bada amsa abinda ya kada zuciyar lauyan Dad ya tashi domin dakatar da lauyan da yake kare bangaren Bashir din inda alqalin ya hana faruwar hakan daga bisani ne bayan abubuwa sun lafa lauyan yace “Hajiya Bara'ah takasance mahaifiya a gareki inda Gen Habib Macchido ya kasance mahaifi so yanzu kuma wata ta bullo mahaifiyarki tayi da'awar basune mahaifanki ba meye kika sani game da hakan?" Girgiza kai tayi tare da share hawaye tace “bansan komai game da hakan ba Kuma bazan iya cewa komai ba sune suke da baki magana Nima su nake sauraro" gdy lauyan yayi ya koma ya zauna me shari'a yabawa lauyan Dad damar yimata tambayoyi Amma yace bashida abin cewa. Nan aka sallameta ta koma mazauninta inda aka Kira sunan wata Mata ta fito da alamun matar taga gararin rayuwa ta hau saman gurin tsayawar alqalin da kansa yace ta gabatar da kanta da abinda ya kawota.
Cikin kuka ta fara da cewa “Sunana Dr Abidat Solomon Asalina Ni mutuniyar Ibadan ce aiki ya kawoni Abuja Inda nake aiki da wani babban asibiti me zaman kansa ranar wata Litinin Dana manta date din wasu Mata da miji sukazo asibitinmu lkcn nice akan aiki da fari nayi tunanin petiant ne Saida muka zauna suke zayyanemin qudurinsu ba wani Abu mijin ya fadamin ba sai cemin da yayi suna buqatar jariri namiji sabuwar haihuwa daga naira million daya zuwa million goma zai iya bayarwa domin cikar burinsa.

_*NKU*_

_Last page_

_And ina me matuqar baku hqr na dakatar da rubutunnan da nayi batare da neman uzuri a gurinku ba wannan ya fsrune sakamakon wasu qwararan dalilai ina fatan zaku fahimceni kuyimin uzuri banyi don wulaqanci gareku ba._

_41-42_

Numfashi Abidat Solomon ta sauke kana taci gaba da cewa “Da farko naqi aminta da qudurinsu duk da kasancewar ba sabon abu bane a gurina amma ganin cewa da gaske sukeyi matar da qaton cikinta na tsumma tana roqona na taimakesu na basu baby kada asirinsu ya tonu, so sai tabani tausayi na yanka musu kudi masu tsoka suka bani advance suka tafi akan cewa muna samun baby zan kirasu.
Haka kuwa akayi kwanaki uku da faruwar lamarin matar wani Minister tazo haihuwa cikin ikon Allah ta haifi yara biyu duka mata saidai bata cikin hayyaci, taimako daya na samu abokin aikina ya fita dauko jini nayi sauri na sace yarinya daya nakai bayi na bude abin flushing nasata a ciki, mukaci gaba da kula da petient dinmu har tasamu dama muka kaita dakin hutu ita da babynta sannan muka fadawa danginta sukayita zuwa ganin mejego da yarinyarta, koda aka kira minister akace masa matarsa Aysha ta haihu baby girl sai yace ai sunje Egypt ance musu yara biyu ne mata,
Qwarai zufa ta rinqa ketomin domin itama mejegon yara biyu tace tana gani idan sunje scanning
Cikina ya duri ruwa sosai na shiga rudu ganin asiri na yana shirin tonuwa domin da gasken gaske wadannan mutane sun kafe akan yaransu biyu ne koda naga abin ya dan lafa saina sulale dama lkcn tashina ya kusa naje nasa jaririyar a cikin jakkar kayana nayi sallama da kowa na fuce.

Ina zuwa gda nayi mata wanka nasa mata kaya na dauki waya na kirayi Gen Habib Macchido na fada masa an samu baby amma baa samu namiji ba mace aka samu, da farko Hajiya Bara'ah taso taqi yarda ta amshi macen amma da sukazo sukaga yarinyar fine girl sai suka cikamin kudina harda qari suka karbi yarinyar nan sukace sunason muje dasu gdansu azuwan nice na karbi haihuwar cikin dare akayita.
Haka akayi muka tafi na kwana a gidansu nidai bacci na kwana inayi amma asubar fari sai naji gdan ya fara cika da mutane nan mukayi sallama na tafi nabar Hajiya bara'ah nata narkewa ita a dole me jego sai liqawa babyn nono takeyi taqi amsa hakan yasa suka sake nemana na rubuta musu magani da madara, nidai daga wannan lkc ban qarabi takansu ba sune dai suke bibiyata sunamin Ihsani haka rayuwa taci gaba da tafiya bamusan ya akayi ba nidai naga an sallameni daga aiki a asibitin da nake wannan dalilin yasani komawa Ibadan naci gaba da rayuwata acan cikin qunci abubuwa sun qara lalacewa nakasa samun aiki sai wahalar neman abinda zaa kula da kai kasancewata marainiya babu uba balle uwa kwatsam kwana uku da suka wucce naga dirar motoci a qofar shagona sukayo wuff dani wannan shine abinda na sani game da wadannan bayin Allah"
Chapter 16 · 0% Book details