← Book details Muguwar Suruka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 9

Sashe 8

Muguwar Suruka Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Suhaima kuwa tana jin abinda Safwan yace ta sume a gurin Momy ce ta tashi da sauri ta rik'e ta tana jijjiga ta, shiko Dady ko ajinkin sa don ya yarda da abinda Hajiya suka fad'a, ruwa Momy ta d'ebo ta yayyafa mata ta farfad'o.
Tashi yayi ya shiga d'aki ya kira Suhaima bai tambaye ta komai ba tana zuwa ta fara jin saukar duka ko ta ina yana fad'in ubanwa yayi miki ciki dama baki da mutunci wllh yau sai kin rai na kanki, dukan ta yake sosai Momy tun tana daurewa har ta gaji taje tana bashi hak'uri amma kunnan she ya toshe, sai da taje ta janye Suhaima sannan ya hak'ura ya zauna yana maida numfashi.
Yace wa Momy "Fatima wllh yarinyar nan idan bata fad'a min wanda yayi mata ciki ba sai naci uban ta.
Tace Alhaji Dan Allah ka kwantar da hankalin ka kayi hak'uri mubita a hankalin mu tambaye ta zata fad'a mana, yace toh muna sauraran ki kifad'a mana, tana kuka tace "Wllh cikin sa ne, yace "kenan k'arya zai miki kice ba cikin sa bane? toh bari kiji in fad'a miki ki tashi ki bar min gida dan cikin nan ba a gida na ba hankalin ta a tashi take bashi hak'uri Momy ma tana bashi hak'uri yace in tak'ara magana sai ran ta ya b'aci, tashi tayi don baza ta iya zama a gurin ba.
Shima Dady tashi yayi ya d'auki dorina yana dukan ta yana korar ta tashi tayi ta fitoh tana kuka sai ga Adnan ya shigo yana tambaya lpy ba wanda yayi masa magana sai Dady da yaga yana dukan Suhaima ta bar masa gidan sa fita tayi daga gidan tana kuka ta zauna a k'ofar gidan.
Adnan ne ya fito ya rik'e ta yasa ta a mota bai wuce ko ina ba sai k'ofar na'isa gidan kakar su wadda ta haifi Momyn su ya bata hak'uri tare da yi mata nasiha ya kwantar mata da hankali, tana kuka take fad'a masa abinda ya faru ran shi ya b'aci sosai yanzu Dady ya yarda da maganar wannan makirar matar ita ma Hajiya kakar su fad'a tayi sosai tace amma bashir bai yi tunane ba shike nan ki kwantar da hankalin ki kar kisa damuwa a ranki kinji tashi ki shiga kiya wanka ko kyaji k'warin jikin ki, shi kuma Adnan yayi mata sallama ya tafi.
Koda ya koma gida bai nuna wa Dady ya kaita wani guri ba sai dai Momy da ya sanar mata don hankalin ta ya kwanta a matsayin ta na uwa kuma mace mai rauni.
rh um
[9/2, 2:45 PM]
*MUGUWAR SURUKA*
EXCLUSIVE WRITERS FORUM*
_Writing by_ *:-pharteemarh*
_Story by_ *:-bebe'ath(yar gatan huda)*
dited by d eloquent
ditor_ *:-bebe'ath*
_*DEDICATED TO MAI IYALI TAWA*_
~page~
70to75
A gidan kakannin ta ta cigaba da zama hankalin ta a kwance tana zuwa makaranta ta maida hankali akan karatun ta sosai, Dadyn ta ko tunanin halin da take ciki bayayi bayaso ma ayi masa maganarta, Momy ce wani lokacin take kiran ta ab'oye idan baya nan ko in tana d'akin ta.
Akwana a tashi asarar mai rai yau ga Suhaimah ta kammala karatunta sunyi graduation, A lokacin cikin ta ya tsofa sosai, Bayan sati da yin graduation da daddare ta fara nak'uda cikin gaggawa Inna kakar ta takira Adnan a waya ya kaisu asibiti basu dad'e da zuwa ba cikin ikon Allah ta haifo 'yar ta mace kyakykyawa mai kama da babanta sak, gari na wayewa aka sallame su suka koma gida.
Safwan kuwa bashi da kwanciyar hankali kullum cikin tananin Suhaima yake yarame ko office yaje baya wani aiki sai tunani Saiham tai ta rashin kunya tana zuba fitsara don yanzu ma Hajiya tsoron ta takeji dan akwai sanda tayi laifi Hajiya take mata fad'a ta tashi tace kwalar ta zata dake ta shike nan Hajiya ta dai na zuwa gidan don tasan tabbas Saiham zata iya dukan ta.
Bayan suna yarinya taci Sunan Kakar Suhaima ta wajen uwa wadda take gurin ta wato Maryam ake kiranta da Ayman, taci gaba da kula da 'yar ta sosai har ta isa yaye bayan ta yaye tane taci gaba da karatu ta tafi low school tana karatun ta ba ruwan ta da tunanin komai har ta kammala aka rantsar da ita ta zama cikakkiyar barrister.
Hajiya Bilki tana gida Hankalin ta bai kwanta ba na d'anta bai kwanta ba, A haka Alhaji ya dawo yaji labari sosai Hankalin sa ya tashi ran sa ya b'aci yakira Safwan yayi mai fad'a sosai amma yasan ba laifinsa bane, Ita ko Hajiya a gurin yace taje ya sake ta saki biyu yadda ta hana 'yar mutane zama a gidan miji itama bazata zauna ba, Hankalin Hajiya ya tashi tayi ta d'ora hannu aka tana ihu tashiga uku ta fara bashi hak'uri amma ina baya jin ta yayi ficewar shi tare da yimata gargad'in kar ya dawo ya tarar da ita a gidan sa.
Gidan Momyn Saiham taje take sanar da ita abinda ya faru taji dad'i sosai a zuciyar ta amma a fili ta jajan ta mata.
Tana barin gidan ta rasa inda zataje gashi ita yanzu tsoran Saiham zake, haka tayi shahada ta koma gidan Safwan da zama Saiham bak'in ciki kamar ya kashe ta yanzu tana murna ta sake a gidan ta ita kad'ai wannan tsinanniyar mata zata takura mata, d'akin Suhaima ta gyara dama sun kwashe kayan Hajiya ta aika musu dashi.
Alhaji yana fita gidan su Suhaima ya wuce gurin Dady ya same shi ya bashi hak'uri akan abinda ya faru yace "Ina Suhaiman take yace "Nima bansan inda take ba yarinya zata zubar min da mutunci in barta ta zauna a gida na, Alhaji yace
"Me kake nufi bashir?
karka ce min kurar yarinyar nan kayi amma bakiyi min adalci ba baka yiwa mahaifiyar ta adalci ba kuma itama bakayi mata adalci ba yanzu baka tunanin halin da take ciki ko wani hannu ta fad'a, Allah sarki yarinyar nan Allah yasaka miki abinda akai miki yace "Toh sai anjima ni na tafi kuma insha Allah duk inda yarinyar nan take sai na sa annemo min ita bai ce mai komai
ba yawuce.
Hajiya tana zaune zaman gida babu dad'i komai ita keyi babu mai yimata wanki babu mai share mata d'aki sab'anin da da komai yimata akeyi duk ta rame tayi baki girki sai dai ta kwashi na k'asan tukunya wanda Saiham ta rage shima sai ranar da taga damar ragewa wataran ma bata rage mata, ga Safwan duk ya birkice duk abinda Saiham tace shi akeyi a gidan Hajiya ita takewa Saiham wanki ta share gida tayi wanke wanke babu mai kula ta a gidan wulak'anci kullum da irin salon da suke mata.
Hajiya na zaune a tsakar gida Saiham da Safwan suka fito daga d'aki hannun su rik'e da juna ta kalle su ko kallon inda take basuyi ba ta tashi ta sha gaban su tace "Yanzu kuna ganina amma babu wanda zai iya yimin magana kuna ganin halin da nake ciki amma baza ku kaini asibiti ba, wani bazan kallo Saiham ta watsa mata tare da hankad'e ta ta fad'i gefe tace ki mutum mana ina ruwan mu da zaki zo kina mana hauka a nan Safwan yaji wani iri amma babu yadda zaiyi ko bud'e baki yayi zaiyi magana sai yakama, Rik'o shi tayi tace "Dan Allah sweetheart mu tafi kar ta b'ata min rai suka shige mota suka wuce, ta saki baki tana kallon su wani hawayen bak'in ciki wani na koro wani.
[9/2, 2:46 PM]
*MUGUWAR SURUKA*
EXCLUSIVE WRITERS FORUM*
_Writing by_ *:-pharteemarh*
_Story by_ *:-bebe'ath(yar gatan huda)*
dited by d eloquent
ditor_ *:-bebe'ath*
~page~
75to80
Nadama sosai Hajiya bilki tayi taje tabawa Alhaji hak'uri ya kore ta tare da gargad'in kar tak'ara zuwa masa gida, da kanta taje ta same iyayen Suhaimah take sanar musu cewa duk abinda ya faru k'arya ne kuma ita ta saka Safwan yace ba cikin sa bane ko ta tsine masa duk ta fad'a musu muguntar da ta had'awa Suhaimah, tace "kuma abinda yasa idan na fad'a muku magana kuke yadda wani boka nasa yayi muku asiri amma ku taimaka ku yafen min dan Allah tana kuka tana fad'a.
Shi ko Dady abin mamaki ya bashi ya d'aure masa kai toh ita wannan mata wanne irin k'iyayya take wa 'yarsa haka da tayi mata wannan abu, Momy kuwa kuka take sosai tana Allah ya isa tsakaninmu da ke bilki bazamu yafi miki ba kin cutar da mu kin cutar mana da rayuwar yarinyar da bataji ba bata gani ba Dady ma kasa daurewa yayi sai da yayi hawaye yace bilki ki tashi ki bar min gida kafin insa a fitar min da ke kije ke da Allah dan cutar da kikai mana bazamu yafe miki ba, ta tashi ta fita tana da nasanin abinda ta aikata.
Suhaima suna zaune cikin kwanciyar hankali duk abinda take buk'ata Adnan yana musu basu da damuwar koma.
A k'ofar gidan su yaga Hajiya bilki a zaune kamar almajira yace "Hajiya lpy kike zaune anan tace "Adnan dan Allah ka taimaka katayani bawa su Alhaji hak'uri akan abinda ya faru sharrin shaid'ane takwashe kaf labarin ta bashi ya jinjina kai yace laila to tashi kije zan basu, ya shige gida ya barta a zaune a gurin.
Yana shiga gida yaga su Dady a zaune yayi tagumi Momy kuwa kuka kawai take guri ya samu ya zauna yace lpy na ganku haka, Dady ne ya d'ago idan sa wanda suka kad'a suka jajir yace "Adnan kaji wannan muguwar matar abinda tayi mana duk abinda take zuwa to fad'a mana akan Suhaima ashe k'arya take kawai k'iyayyace.
Yana hawaye yace "Me yarinyar nan tayi mata haka? wannan k'iyayyar tayi yawa
Shima Adnan hawaye yake amma na farin ciki da Allah ya bayyana gaskiya Suhaima tafi ta daga fushin iyayen ta yace "toh Dady yanzu sai muyi hak'uri tunda tanemi yafiyar mu ita kuma Suhaima sai muyi ta addu'a Allah ya bayyana mana ita aduk inda take.
Yace ameen amma in kaga na yafewa wannan muguwar matar toh sai naga Suhaima.
Tashi Adnan yayi yafita yace Allah ya bayyana ta bai wuce ko ina ba sai k'ofar nasarawa gidan kakar su da murna ya shiga Suhaima tana zaune tana gyarawa Ayman gashi suna hira da kaka sukaji sallamar Adnan yana zuwa suka gaisa ake sanar dasu abinda ya faru dukkansu sukayi murna, Adnan yace yanzu bazaki koma da wuri ba sai nan da wasu lokuta dama Dady ne mai matsala amma ita Momy nasan kukan farin ciki take, suka ce "haka ne kaka "tace kai amma gaskiya bilki ba k'aramar azzalumar mata bace kai ni ko a zamanin da ban tab'ajin *MUGUWAR SURUKA* irin bilki ba, tashi Adnan yayi yai musu sallama tare da basu kud'i suk'ara suyi amfani dashi ya tafi.
Dady abu kamar wasa ya ta da hankali neman Suhaima abu har yakaishi ga kwanciya a asibiti lamarin da ya d'agawa kowa hankali musamman Momy takira Adnan tace gaskiya yakawo Suhaima haka, kwanan shi biyu a asibiti bayacin komai yana kwance Momy tana zaune a gefen gadon Sukaji sallamar Suhaima kamar a a mafarki Momy batayi wani mamaki ba sai dai murnar ganin 'yarta da tayi, tayi kyau ta murje kamar wata balarabiya ga Ayman yarinya kyakykyawa, Shiko Dady basan lokacin da ya tashi ba yaje yarik'eta ya kura mata ido kamar wanda yaga sabuwar halitta yana hawaye yace Suhaima kice Allah nagode maka da ka bayyana min 'yarta cikin kwanciyar hankali.
A ranar suka koma gida Dady yayi ta bata hak'uri tace ita basuyi mata komai ba kuma ko sunyi ta yafe musu.
Rayuwa ta koma mai dad'i Ayman tana samun kulawa sosai gurin kakannin ta ga kud'i Allah ya bud'a musu suna shigowa suka k'era gida na gani nafad'a.
Chapter 8 · 0% Book details